x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - YAN ZAMAN MAKKAH BOOK 1

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 37750 words

Category: Romance Story +18

Views 122

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
kamar tana cikin wani hali
cikin dare zata kirata kenan bata da yancin ɗaga waya a lokacin da taga dama kuma tayi niya.
Sai wanda aka dibar mata da sauri tace '' zato zunubi ko da ya kasance gaskiya ban dai san me ke faruwa ba wannan tambayoyin nawa bani da me bani amsar su..,
Tana cikin wannan tunani ahlam ta shigo wani kallo ta wurga mata yace '' ke Wallahi kibi a sannu kafin na rugurguza miki kasusuwan ki dan rainin hankali daga ganin baki sai ki dinga wata kwarkwasa kina canza salon tafiya ke gaki me neman miji ko...?,
Dariya yumna tayi irin ta rainin wayon nan tace '' nai miki kama da wacce za'a kasa a fefe ana tallanta nan da kike gani na yau sauran sati takwas biki nan..,
turus ahlam tayi wani dad'i ne ya rufe mata gwara ai mata aure ta huta ganin yumna a cikin gidan ta zai saka ciwon zuciya ya kamata gashi bata da kunya dai-dai take da ita duk Maganar da ta faɗa mata , tana da amsar bata hakan ba karamin bakan ta mata rai yake ba juyawa tayi ta fita tana jan tsaki.
bacci n yayi awan gaba da yumna me cike da mafarkai kala kala ,
tana cikin wannan bacci taji an maka mata pillowcase da sauri ta tashi tana zare idanuwa ido hudu tayi da juraij da sauri ta ja baya tana dauke kan'ta a hankali ta furta wallahi Allah ya isa ai wannan ba tarbiyar musulunci bace ka dinga yawo da kai sai gajeran wando.
zaro idanuwanta sa yayi ya nuna kansa yace '' me kike faɗa ni kike faɗawa wannan maganar..,
sosai tashin ta da yayi ya ɓata mata rai domin mafarki tayi gaba a gaban ka'aba tana sauke farali dan haka ta shi tsaye tayi ta kau da fuska tace '' da wanda ya tsargu..dashi nake.,
Kifa mata mari zai yi ta zube a ƙasa tare da sakar wata ƙara da sauri ya toshe kunnuwan'sa saboda jinsa yana barazanar daukewa na wucin gadi.
da sauri ahlam ta shigo tana cewa honey me ya faru lafiya daga ina karar nan take ganin yumna a kwance da sauri ta kama hannun juraij tace '' kaga tun kafin abin da yarinyar nan take fadi ya tabbata akan mu, ka mai da ita inda ka dauko ta Please ba danni ba wallahi ganin ta acikin gidana bani da kwanciyar hankali ko kaɗan kai min wannan alfarmar kai daga jin karar nan kasan ba mutum ne yayi ta ba jibi yadda ta sheme a ƙasa tamkar wata gawa ni na hakura da rama abin da tayi min wallahi sweet bakai tunani ba ka kawo ta gurin mu...,
fita sukai suka rufo mata dakin da sauri ta tashi tana dariya tace '' waya ce da ni ba niba nima nace dashi ba shi ba wallahi kun dinga haduwa da abubuwa kala kala tunda ku baku san kawaici ba na dinga gasa muku aya a hannu shegu masu kan jimina..,
wayar tace tayi ringing da sauri ta ɗauka tsaki taja a duniya bata taɓa ganin mayan mutum ba sama da Mamman tana ji wai wai ana maye maye to tana kyautata zaton yana ɗaga daga cikin mayun wannan wacce irin bakar jaraba ce ɗagawa tayi tace '' haba Mamman ina bacci na ba zaka barni ba na sarara na samu hutu da jin dad'i gaskiya abin da kake yi baya dacewa..,
ɗanne ɓacin ransa yayi yace '' kiyi hakuri bansan bacci kike ba na zata kin gama wayar ne kuma yau ina so muyi waya mu dade..,
to kashe zan koma bacci haka kurum kai ba damar kabar mutum ya huta wallahi Mamman idan kana min bita da kullin nan baza mu taɓa zama lafiya ba dan katin da ka turo min ne shi ne sai na biya shi ta hanyar baka lokacina saboda tsabar cutarwa
be tsaya jin karshen faɗan ta ba ya kashe wayar sa zuciyar'sa na tafasa yace '' wallahi ilu yarinyar nan daba dan son da nake mata ba da tuni na rabu da ita kwata kwata bata da kirki...
hmmm ni zan faɗa maka wacece ita nida take neman naɗa min duka a cikin gidana har da cewa na fice na basu guri ina fuffuka zan naɗe tabarmar kunya da hauka kai wannan yarinyar kamar jikar aljanu nifa da zan faɗa maka kaji yasin karabu da ita domin wannan ko a cikin gidan ka , baka isa ka faɗa mata taji ba saboda ko a waje ma kuna marmarin juna baka fada mata taji ba balle kun gogu da juna sai abin da yayi gaba wallahi ina jiye maka abinda zai je ya dawo..,
Cewar ilu
Shiru Mamman yayi domin yasan sarai gaskiya ilu ya faɗa amma me ya zaiyi da sonta besan wanne hali zai shiga ba idan har be aure ta ba .
Dariya mado yayi yace '' ba zai taɓa daukan shawarar kaba shi yasaka ni ban wahalar da yawun bakina ba shi kansa ta malam da yake uban'ta ba jin maganar sa take ba idan tai maka laifi gun wa zaka kai ƙarar ta..?,
shiru yayi yana kallon kasar gonar sa dafa kafadar'sa madu yayi yace '' naga baka da amsar bani amma amsar ita ce babu wanda za ka kai wa karar yumna kowa yana son ya auri mata , tagari ya samawa ya'yansa uwa ta gari ita kan'ta yumna tarbiyyar da akai mata bata dauka ba kana ganin zatai wa ya'yan ku tarbiya a bokina ka yi tunani karka daukar wa kanka ƙara da ki yashi.. domin wallahi yumna ba zatai maka biyayya ba idan kai baka bita ita baza ta bika ba.,
Ƙasa cewa komai yayi duniya tai mai zafi tabbas maganar su haka take amma baya jin zai iya rabuwa da yumna,
CIKIN GIDAN MALAM
yaya lafiya naga kin kasa tsaye kin kasa zaune..?,
Cewar baba lami
zama inna Hadiza tayi tace '' komai yana shirin lalace mana mutukar wannan yarinyar ta auri yaron nan mun ƙade..,
cikin rashin fahimta baba lami tace '' saboda me kika faɗi haka mene namu kuma aciki shi yaron nan ba wani a bin kuzo a gani ne da shi ba..,
tabbas bashi da wani abin kuzo a gani amma ke kina ganin inhar ta aure shi ba zata bar kowa da kwanciyar hankali ba kinsan dai halin ta ba sai na faɗa miki ba ina tunanin zan yi duk yadda zanyi naga abin nan ya fasu..
Lah yaya karki fara ba ruwanki idone naki da kan'sa zai yanka mata takarda ke kinsa halin ta idan bata zame maka dole ba wa zai zauna da ita ga dukan ya'yan mutane dan ma dai mahaifiyar dai-dai take da ita wallahi ɗiyar Moussa wasa ce wallahi tana yi mata yi mata za tayi auren nan ba wani karko zai yi ba ke dai kawai ki zuba ido zuru ma ta ishi mara ɗa kunya.
inna Hadiza tace '' wallahi kuwa shi ya saka naso malam ya rabu da ita kawai a cikin yan uwanta ya bashi wata tun da ita ga abin da ta fadi wallahi na kawo kai naji wannan maganar kisa kinsan yadda zuciyar ta take a bushe zata aikata balle tana da wa'yannan mutanan..
Baba lami tace '' Allah ya kyauta amma wannan lamari abin a dage da addu'a ne..,
tab duk wanda ya iya allon sa ya wanke ya sha ni da yiwa yarinyar nan addu'a a'a har bada saidai idan na sako al'ummar musulmi baki ɗaya ta shiga cikin su.
cewar inna hadiza
Nazeefa ce ta shigo tana cewa a she Mamman besan da tafiyar yumna ba ɗazu na hadu dashi yake tambayar tana ina nace tayi tafiya zuwa arlit ya buga mata waya taƙi ɗauka.
hmmm kinga ko shi yasaka nace ba ruwanki shima yasan me ya aura ai yumna kara da kiyashi ce daukan mara sani amma shi ya dauka shi da yayi rayuwa a gurin malam ga yarana nan kala kala, ya rasa wa zai aura sai ita Allah ya basu zaman lafiya amma wannan zama hmmm
Dariya inna Hadiza tayi tace '' gane min hanya lami wai makaho yaso gulma yace gane min hanya..,
zama nazeefa tayi tace '' wallahi dan baki ga yadda ya ban tausayi ba halin yumna sai ita..,
Shamsiyya da take cikin daki tace '' cewa fa tayi ya turo a karbi kudin sa amma be turo ba wallahi da wuya yumna ta samu me sonta tsakani da Allah sama da shi tayiwa kanta kiyamul laili tabi maganar malam ko dan samin rahamar Ubangiji..,
tab ke kika san wannan idanuwanta sun makance babban burin ta , ta jita ta tafi makka
Cewar baba lami.
Dariya shamsiyya tayi tace '' hmmm Allah ya kyauta..,
amin suka ce
wannan kenan
Har akai kiran sallar isha tana zuba ido taga kiran na'ima amma ba kiranta ba labarin ta lamarin nan ba karamin takaici yayi wa yumna ba , ta dade a zaune a ƙasa ta zuba ta gumi har juraij ya shigo bata sani ba ji tayi an dunguri ƙafar'ta da sauri ta ɗago suka haɗa ido ɗauke kai tayi bata ce mai komai ba zama yayi yana kallon ta yace '' anya kuwa ba wani mugun abin kike saƙawa ba...,
ba tare da ya kalli inda yake ba tace '' kasan sau da dama mutane gani suke abin da suke aikatawa shi kowa ke ai katawa dan haka bazan iya yin ja yayya da kai ba tun da abin da ke cikin zuciya ne ya fito fili...,
ja kujera yayi ya zauna yace '' magana kike..,
kai ta girgiza bata ce komai ba murmushi yayi yace '' ashe ke mara kunyar karya ce da ki mai maita da na tumurmusa ki a gurin nan ba aljanu zaki tayar ba ko abin da yafi aljanu ne sai nayi maganin ki..,
jingina tayi da jikin gano bata ce komai ba ta kifa kan'ta a kan gwuiwar'ta..
tamkar an wullo ahlam haka ta shigo tana sauke ajiyar zuciya a jere a jere cikin sarkewar murya tace '' sweet daga shiga toilet sai na neme ka na rasa ashe kana nan..?,
ɗagowa yayi dariya abin ya so bashi kishin ahlam yana bashi mamaki babban temakon da Ubangiji yayi mata shi ne shima bashi da ra'ayin auren mata biyu ita kadai ta ishe shi rayuwar'sa.
tashi yayi yace '' mu tafi ko..?,
kallon rashin fahimta take mai tace '' me kake yi anan..,
dariya abin ya bawa yumna dan haka tayi dariyar ta son ranta sannan tace '' yanzu aunty ahlam dan ya zo guna muna sirri tsakanin wa da kanwar'sa shi ne sai kinji abin da yan uwa suke cewa to sirri ne idan abin ya matso kya ji..,
dafe kan'ta tayi da ya sara mata lokaci guda anya kuwa baza ta cirewa yarinyar nan hakura ba , ya za'a yi ta dinga gasa mata magana son ranta juyawa tayi bata ce komai ba ranta a ɓace tana zuwa parlour ta dauki wayar ta ta shiga bedroom din ta zama tayi tamkar wata yar bori rasa ina zata saka kan'ta tayi anya kuwa bata daɓawa kan'ta huƙa ba anya kuwa bata cuci kanta ba wata mace tana ta yarda ta shigo rayuwar su tamkar wata kububuwa haka , ta tashi ta fita kitchen ta nufa huƙa ta zaro ta shiga dakin da ita tace '' maza kwaso kayan ki,ki bar min gida..,
Ahlam kanki ɗaya kuwa wai me isaka zargin ki yayi yawa ki sani fa baza mu taɓa zaman lafiya ba idan har kina zargi..
wani murmushi tayi me ciwo tace '' a gaban ka ta gaggasamin magana amma da yake kai ma munafuki ne kai shiri ka tsuke bakin ka to wallahi ina me sanar dake da babbar murya mijina yafi karfin ki..nafi karfin da na zauna dake a matsayin kishiya ta sai dai yar aiki amma ke baki isa ba nayi rayuwa aure tare da ke ba dan haka maza kwaso kayan ki, ki koma inda kika fito haba buri yayi kama da mutum yarinyar nan har tana da karfin gwuiwar kallon idona ta gasa min magana son ranta kai kasan a inda ka dauko ni dan haka baka isa ka wulakanta tani ba wallahi kayi kaɗan...,

dakyar ya samu ya cire hukar hannun ta yumna ta dake ta kasa koda motsi tasan ko giyar wake ahlam tasha ba zata iya daukar huƙa ba ta caka mata dan haka ta dake fita da ita yayi ta zauna tana sauke ajiyar zuciya tace '' mahaukaciyar banza kina wannan haukan wata zata aure shi baki sani ba.
kiran sallar isha akai ta tashi ta dauro alwala tayi sallah bayan ta idar bacci ya kwashe ta a gurin misalin karfe biyun dare kira ya shigo wayar yumna a gigice ta tashi bata , taɓa riskar irin wannan yanayi ba cikin lokacin nan a kira ta ɗan haka sai kiran ya zame mata baƙon abu gare ta.
wastsakewa tayi da sauri sakamakon ganin kiran na'ima ta ɗaga tace '' wallahi na'ima naji tsoro kira da wannan talatainin daren tun bayan sallar magariba nake saka ran ganin kiran ki..,
ke wallahi bana samin damar zama ne yakike ya kowa da kowa..?,
cewar na'ima
yumna da bacci ya kauracewa idanuwanta tace '' wallahi suna lafiya qalau daman ni da nana ne za mu tawo garin da kike muma mu yi aiki shi ne zaki bani number din agent din ki..,
dam jim tayi sannan tace '' wallahi a dai yanzu bani da number sa ban kuma san a ina zan samu number sa ba kwanaki na buga mai taƙi shiga da tana ringing ba'a ɗagawa sai kawai naji haushi na goge number..,
inyeee kin sami duniya dole ki goge number sa yumna ta faɗi tana alyini domin bata san ina za ta sami agent din da zai kai ta makka aikatau ba.
amma yumna zan turo miki address din wajen in har kika je zaki same shi insha'Allahu.
okay turo min ba damuwa sai na bincika.
na'ima tace '' amma yumna ba ance an saka ranar auren ku ba to shi mamman din ne zai barki, ki tawo nan..,
hmmm ke dai Allah ya kyauta amma ba jimawa insha'Allahu zan zo nema na nemi arziki dole nima na zama ana sawa dani a sahun manya manyan mata masu faɗa aji ko shekara ɗaya nayi na dawo.
wata ƙara taji da wasu surutai cikin daga murya ta fara cewa na'ima hello hello na'ima me ya faru kit kiran ya katsai sosai ta shiga tashin hankali dan daga jin ihun nan ba na dad'i bane ƙara kira tayi sai dai har ta gama ringing ba'a dauka ba , sai dai bata hakura ba ta ƙara kira sai dai wannan karon a kashe wayar take.
jingina tayi da bango tana tunanin me ya faru haka har na'ima ta saki ƙara kuma taki daga wayar ta ,
karon farko a rayuwar ta da , ta mike ta dauro alwala ta gabatar da lafi'la tare da rokon Ubangiji Allah ya shiga lamarin ta ya cika mata burin ta bayan ta idar ta zauna har akai kiran sallar asuba yadda taga rana haka ta ga dare ana kira ta tashi ta yi sallah ta dade nan ma tana rokar Ubangiji ya cika mata burin ta na tafiya makka Allah karya taɓar da ita.
ya Ubangiji Allah ya saka tayi tafiyar nan a sa'a ta faɗa hannu me kyau hannun da zata sami abin duniya bayan ta idar ta zauna a lokacin kuma ta ƙara kiran number na'ima sai dai har yanzu a kashe take to me yake faruwa ta fara zargin anya kuwa lafiya,
tana cikin wannan tunanin ne akai knocking din kofar dakin ta tashi tayi ta buɗe fuskar nan ba walwala tace '' ina kwana..,
shima fuskar sa a ɗaure take tamau ba ɗigon annuri a fuskar sa yace '' lafiya kije ki ɗora mana petit déjeuner (breakfast) da wuri nake fita office so bana son ɓata lokaci..,
shiru tayi tamkar me tunani tana sane tayi haka , tayi hakan ne domin ta bata mai rai ilai kuwa sai da ya magantu yace '' ke ba magana nake miki ba..,
da sauri ta ɗago tana taɓa kunnen ta tace '' oh ban ji ba me kace..,
wani kallo da yayi mata dole ta hadiya sauran zancen ta batare da ta shirya hakan ba miskilin murmushi yayi ya juya ya rufo mata kofar ta ahlam ta zaune akan kujera tana cika tana batsaiwa zama yayi yace '' ni zan shirya na fita na siya restaurant domin bazan iya cin kirkin yarinyar nan ba , tun da ke zaki iya sai kici ko ba komai ta sauke nauyin da ni ya kamata ace na sauke tun da ke bakya iya shiga kitchen..,
dauke kai tayi tace '' nifa har yanzu ina kan bakana sai ta bar min gida gwara na girka da kai na ko da abin da ke ciki na zai zube..,
da sauri yace '' a'uzubillahi da bakin ki kike fadar haka haba ahlam me yake damin ke ne..,
Cutar da ka zaɓa min ita take damuna ban da rainin hankali yarinya ta dinga faɗa min magana amma ko sau ɗaya baka saɓa mata halitta ba sai dai idan akwai wata a ƙasa.
girgiza kai yayi ahlam tayi nisa bata jin kira yarinyar da an kusan bikin ta amma ta dinga fadar haka yace '' baki san an kusan bikin ta ba me zan yi da ita sanin kan kine da ina da sha'awar ƙara aure da tuni nayi amma ki bi ki dinga daga hankalin ki me kika nema wanda bana yi miki shi komai ina miki domin farin cikin ki amma bakya gani..kullum zancen ki kishiya,
Wannan littafin na kudi ne ki biya ni ki karanta halalin ki,
500 kacal idan ya zama document ya koma 1k

Amina alhasan Muhammad opay
8141785374
Ku turo da shedar biya ta wannan number 08141785374
Yan niger kuma 1000fcfah
ku turo ta my nita
Amina Muhammad alhasan 08141785374
sai ku turo min da shedar biya ta wannan number 08141785374
Free ya kusan karewa.
https://youtu.be/_IOc2pOwgKk
Copy is not allowed
Episode 9
Juraij idan fa kana so ni da kai mu zauna lafiya a cikin gidan nan to wallahi ka fitar da yarinyar nan daga gidan nan abincin ma na hakura zan shiga kitchen da kai na , na dafa ana dole ne ni wallahi duk wani zance da zaka faɗamin wai an saka mata rana an kusan bikin ta
End Ads