x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - YAN ZAMAN MAKKAH BOOK 1

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 37750 words

Category: Romance Story +18

Views 124

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
nan na zaure har yanzu akwai mutane a cikin gidan nan wasu ma kwana za su yi.
tashi yayi jikin sa duk a sanyaye ya buɗe dakin su hafizu shiga su kayi mommy ta ƙara mai maita mata tambayar dakyar yumna ta iya cewa sakina ta saka yayi saki biyu na fito ina amai tace cikine dani
salati mommy ta saki shikkenan magana ta ƙare innalillahi wainna ilaihir raji'un haka suka shiga maimaitawa mommy tace '' Allah ya isa tsakanin mu da ita yarinyar da take al'ada wanne ciki insha'Allahu akan ya'yanta zata ga ciki alfarmar annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama sai dai ta gani akan nata badai akan kiba, ni daman tun da ta iya rufe ido ta ci mana mutunci nasan bata da imani bata da tsoron Allah yanzu maganar da muke yi da malam kenan a cikin daran nan a ranar da aka daura muku aure ta saka a yi miki wannan sakin hulakancin gaskiya matar nan bata da imani ko yan baki ba su soma watsewa ba insha'Allahu yumna sai kin zama wata makaranta kawai zaki koma da zarar takardun ki sun fito ta mai dake ƙaramar bazzawara.,
malam kasa cewa komai yayi ko da ya tashi binciken Mamman da man ance mahaifiyar sa tafi karfin mahaifinsa ashe kuwa haka abin yake da ya sani ƙeya da be haɗa wannan auren ba dama ya bar yarsa tun farko da ta nuna bata so bakomai haka Allah ya tsara daman auren su na wani lokaci ne , duk da ba'a shedar ɗan yau amma yasan halin kowa daga cikin ya'yansa ita dai yumna barta da daukan magana amma wallahi baya zarginta balle gashi nan ance ma al'ada take yi wannan mata ta cuce su bakomai Allah yana nan ma dakata.
dakyar ya iya cewa yumna kiyi hakuri kiyi hakuri kiyi hakuri Allah yana tare da me gaskiya wata ran zatai nadamar abin da ta faɗa miki kafin su hafizu su zo ku tashi ku koma cikin gida..
da sauri mommy tace '' a'a duk da dare yayi kawai mu koma gidana ai haka kamar tozarta kai ne..,
haka ne wallahi Allah ya rufamana asiri amin mommy tace ta tashi ta shiga yusra ta kwaso muku kayan su suka fito daman tun ɗazu kaka ta tafi buɗe Boot tayi ta zuba kayan sannan ta rufe.
yusra ta shiga gidan gaba saboda ita zatai tukin daman ta matsu su tafi so take yi ta ganta a gidansu amma mommy tace ba yau ba sai gobe sub koma gidan yumna zuwa jibi su tafi.
tamkar an warke ta daga Makanta taga mommy ta kamo hannun yumna ta buɗe baki za tayi magana mommy ta hade rai ta buɗe gidan baya ta shiga ganin haka itama ta tsuke bakin ta kwantar da kan'ta tayi a cinyar mommy tana kuka zazzaɓin jikin'ta ya ƙara tsanani ba irin abin da yumna bata saka aranta ba wayar ta da take makale da ita a cikin zaninta ta ciro tace '' mommy ajiye min..,
cikin tausayawa mommy ta karɓar ta ajiye mata ba karamin tauyasin yumna take ji ba , dan ma yarinyar tana da karfin zuciya da wata ce faɗuwa za tayi idan ta ji wannan zance.
sai karfe goma suka isa me gadi ya buɗe musu gate lokacin juraij ya dawo daga aiki shima turus yayi ganin yumna ta fito abinka da babban gida ga wadatar hasken wutar lantarki tamkar rana jikin sa a sanyaye ya ƙara so yace '' mommy sannun ku da zuwa..?,
Yauwa juraij yanzu ka dawo..
Eh wallahi yanzu na dawo nama biya ta gidan su ahlam jikin nata da sauki ba kamar jiya ba.
Mommy tace '' to Allah ya kara sauki nama kirata ɗazu naji ya jikin ta wayar ta a kashe..,
insha'Allahu zan faɗa mata kallon yumna yayi zai wuce mommy tace '' juraij ina son ganin ka..,
gaban sane ya faɗi amma sai ya dake yace '' to mommy..,
buɗe motar sa yayi ya ajiye kayan da ya dauko ya bi bayan su.
lokacin mommy ta shiga daki yusra ta hau sama domin bacci take ji yumna ce a zaune a parlour be bi takanta ba ya nufi bedroom din mommy sallama yayi tana zaune ta rafka uban tagumi sai ya ya kara magana sannan taji shi.
da sauri ta ɗago tace '' juriaj ashe ka shigo,
zama yayi a ƙasa ya tankwashe ƙafafuwan'sa yace '' mommy me yake damin ki naga kin yi tagumi Allah ya saka lafiya wallahi na shiga tashin hankali sosai dana ganki a cikin wannan hali..,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' juraij wallahi ina cikin matsala kai kaɗai ne zaka iya fiddani a cikin wannan matsalar taufiq baya nan yana karatu da shi zanwa magana..,
kallon ta yake cikin mamaki domin be san ina zancen ta ya dosa ba temako kuma yau mommy ce take neman temakon sa to duk yadda aka yi ba ƙaramin abu bane wannan dan haka yace '' mommy Dan Allah ki faɗa min me ke damu ba ki..?,
ajiyar zuciya ta sauke ta share kwallar da take ƙoƙarin gangarowa a kurmin idon'ta tace '' yau an daurawa yumna aure a yau uwar mijinta, ta saka aka sake ta daman tun daga tarbar da tayi mana wallahi nasan ba mutuniyar kirki bace..,
gumi ne ya shiga yanko mai ya shiga uku yasan yanzu haka shi momy zata ce , ya auri yumna ba zai iya adalci ba , ba zai iya haɗa ahlam da ko wacce mace ba , ba zai iya ba ji yayi ya shiga cikin wani irin hali wanda ya kasa fassara shi to wacce siga.
tissue ta yago ta share hawayen ta tace '' kai nake da yaƙinin zaka iya riki min amana ko bayan raina ba zaka taɓa iya tozarta yumna ba , taufiq yana da wata dabi'a da wani hali ba ko wanne abu ya ke so ba , idan na tursasashi ba lallai yace min ba zai iya ba amma abin zai dinga ci mai rai ƙarshe ya haifar mai da wata lalurar kai nake da ya ƙinin za ka iya yi min wannan aikin kai zaka iya riƙe min wannan amanar duk da ba lallai ka amsa ba amma ka riƙe min ita ina so ka aure yumna tun da be ɗora mata idda ba
habawa ji yayi tamkar an dauko ringimeman dotsai an ɗora mai akan zuciyar'sa ina bazai iya ba duk ba ba zai iya yiwa mahaifiyar sa musu ba amma ba zai iya yin adalci ba ƙasa magana yayi tun da ya sunkuyar da kan'sa ƙasa be dago ba har ta gama zancen ta bakin sa na rawa yace '' mommy auren ta zanyi...?,
kai ta gyaɗa mai ,
baya son zubar hawayen mahaifansa baya son abin da zai saka tayi kuka yana da kuma maganin damuwar ta , ya saka yi mata bakin sa na rawa yace '' mommy ki gafarce ni bazan iya auren ta ba , saboda Muhsin yana son ta ba zan iya zama da abin da aminina yake so ba ina da yaƙinin Muhsin zai iya riƙe wannan amanar wallahi tun da ya ganta yake min maganar ta sai da na gaji na faɗa mai an mata miji duk da haka be hakura yanzu haka yau da nake ce mai yau ake ɗora mata aure wallahi yana kwance akan gadon asibiti idan aureta ban mai adalci ba hakika na cika bakin amini wata kila ma hakan ya kawo karshen alakarmu saboda so mugun abu ne zai iya haɗa mu duk irin amintar da take tsakanin mu dan Allah mommy karki ce ban bi umarnin ki ba amma me zai hana taci gaba da karatun ta yadda zata iya dogara da kan'ta zata tallafi rayuwar maraicinta har Allah yayi abin da ya tsara..,
ya faɗa yana riko hannunta tare da goge mata hannunta.
Mommy kasa magana tayi wannan ita ake kira da tsaka me wuya taso ace yumna ta auri Juraij daman tun farko shi taiwa sha'awar'ta sai kuma ya kawo mata ahlam ba yadda ta iya ta amince da auren ta tabbas ba za ta ita tauye mai hakkin sa ba duk abin da ya faɗi gaskiya ne zata bar zancen auren nan Allah ya zaɓa mata abin da ya fi alkairi dakyar tace '' bakomai wallahi Juraij Allah yayi maka albarka ya shige mana gaba daman nima cewa nayi ko a dakin mijinta ta ci gaba da karatu amma wannan abin har abada bazai bace mata a rai dan Allah ku jata a jiki ku hanata zaman kaɗaici duk abin da za tayi karku kyareta sai abu yayi mata yawa ku bita a hankali komai yana da lokaci komai zai wuce tamkar ba ayi shi ba...,
insha'Allahu ya fada yana tashi ba karamin sanyi yayi ba lokacin da ya samu nutsuwa da amincewa da tayi da maganar sa..

Copy is not allowed
Domin jin audio din Yan zaman Makkah Ku danna wannan link din sannan kuyi subscribe Dan Allah.
https://youtu.be/cDE5bjYY2HY
___________________
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6817816be532b4a92550458c
Episode 13
sai da safe yayi mata ya fita har zuwa lokacin yumna tana kwance akan kujera ta , takure guri ɗaya.
wuce ta yayi ya fita tana ganin fitar sa ta miƙe ba karamin bacci take ji ba dai-dai lokacin mommy ta fito kama hannunta tayi ta kaita har dakin ta , wanda da aka sauketa a cikinsa kwanciya tayi akan gado tare da yin addu'a mommy ta ja mata kofa rufe idanuwan'ta tayi zuciyar ta na mata wani irin suya , bawai bakin ciki take da Mamman ya sake ta ba a'a daman abin da take nema kenan kuma sai ta samu, babban bakin Cikin da sharrin da mahaifiyar sa tayi mata , ba zato taji hawaye na bin kuncinta sharewa tayi ta gyara kwanciyar ta ranar yadda taga rana haka taga dare zazzaɓi ne ya ƙara rufe ta ko iya daga idanuwanta bata yi ga ciwo da kan'ta keyi tamkar zai fashe gida biyu.
ji tayi anyi knocking kofar ta , ba damar tayi magana tayi shiru ko da aka turo kofar ko iya ɗaga kai bata yi
ashe mommy ce ,,
zama tayi a kusa da ita Alhaji yace '' yumna ya jikin naki..?,
dakyar ta iya cewa Alhamdulilah da sauki..
sosai ya tausayawa yarinyar saukar sa kenan a ƙasar mommy take bashi labari shine ya shigo domin ya duba ta ,,
kwalla mommy ta share tace'' Alhaji anya kuwa ba za'a kaita asibiti na , jikin nata yayi tsanani..?,
Alhaji yace '' tun da ga taufiq nan ya dawo, ya duba ta da ace juraij be tafi wajen aiki ba da shi ya kamata ya duba ta tun da daman ɓangaren mata ya karanta.
ajiyar zuciya ta sauke tace '' to bara na kirawo shi Allah ya saka be kwanta wannan shegen baccin nasa ba , yawa na mutuwa..,
zauna ki kula da ita,zan kirawo shi
to tace ta shafa kan yumna da yayi zafi raɗau tamkar garwashin wuta.
cikin tausayawa tace '' yumna sannu me yake damun ki..?,
kasa magana tayi sai bakin ta da yake rawa alamun tana so tayi magana ba halin yi hawaye mommy ta share mata , tace '' kiyi hakuri akwai Allah, komai yayi zafi maganin sa Allah..,
kai kurum ta gyada da kyar, ta riƙo hannun mommy Assalamu alaikum..
da sauri mommy ta juyo jin muryar taufiq tace '' wa'alaikas'salam..,
ƙarasa shiguwa yayi yana cire medical glasses din'sa yace '' wannan ce mara lafiyar..?,
mommy ta kalle sa tace '' eh..,
dan jim yayi sannan yace '' mommy ban tawo da komai ba ko , kayan sawata ban tawo da su ba , tun da na san ina dasu anan sai dan abinda zan yi amfani dashi, dashi na tawo , ko za aku kaita asibiti naga jikin nata yayi tsanani..,
tashi mommy tayi tace '' dauko mota ka kai mu..,
to yace ya fita Alhaji ya ci karo dashi yayi mai bayani yace to ba damuwa ya dauko ya kai su bayan ya gama dai-dai ta parking din'sa, ya dawo daukan ta yayi domin ba zata iya tafiya ba har cikin mota ya saka ta mommy ta shiga suka fati kai tsaye asibitin da yaza mo mallakin juraij wato J.M international hospital suka isa cikin gaggawa suka amshe ta saboda yanayin jikin nata kai tsaye emergency room suka shiga da ita.
mommy jin gina tayi da bango taufiq yace '' mommy me ya haddasa mata wannan ciwon ne..? ,
zama tayi akan waiting chair tace'' taufiq labarin yana da yawa mudai samo kan'ta sai nai maka bayani..,
jan bakin sa yayi ya tsuke ya zauna kusa da ita.
Wannan kenan
AGADEZ
karfe goma malam ya shirya domin zuwa gidan su Mamman yaji ba'asin abin da ya faru har kawo i yanzu ba wanda yasan me yake faruwa da yaji nazeefa tana cewa zata gidan yumna hanata yayi yace shi baya son irin wannan daga yin auren har zata fara sintiri ko gidan shamsiyya be yarda ta je ba.
yana gama fadar haka ya fice kai tsaye gidan su Mamman ya nufa bayan ya isa ya aika yaro ace yana sallama da mahaifin Muhammadu..,
shiga yaron yayi ya fara rangaɗa wata uwar sallama yace '' wai inji malam NURA me sittin yana sallama da baban Muhammadu..,
Innar su hindatu da take gaban wuta tana dumamen tuwo tace '' je ka , kace mai baya nan..,
da sauri sarkin fawa ya fito yana cewa haba tabawa me ya saka kike haka ne tun da dai kin raba auren nan hankalin ki , ya kwanta ai sai ki ci wake ki sha ruwa kaf garin nan ana darajja malamin nan amma shi ne kika ce a faɗa mai haka..?,
tamkar da dutsai yake magana bata dago Kai ta kalle sa ba girgiza kai yayi ya fita yana saɓa babbar riga a kafaɗa.
samun malam yayi yana tsaye a kofar gidan nasa gaisawa sukai sannan yace '' bisimallah shigo zaure...,
Malam yace '' a'a barshi nan ma ya isa..,
Allah annabi yayi mai sannan ya shiga ba yadda ya iya daduma ya shinfida mai suka ƙara gaisawa sannan malam yace
'' naji wani abu to domin na tabbatar shi ne na zo naji gaskiyar magana me ya faru yumna tace min Muhammadu ya sake ta..?,
kunya ce ta rufe Sarkin fawa kan'sa yana ƙasa yace '' to, haka Allah ya nufa daman auren ba me dadewa bane, mahaifiyar sa , ce tace ya saketa wai saboda ta shigo mai gida da ciki Allah shi ne masani wallahi dole tai mai ya sake ta , ba yadda ya iya , wallahi nauyin ka ne ya hani zuwa na same ka mu tattauna amma insha'Allahu zan wa tubkar hanci da yardar Allah zata dawo dakinta saki biyu yayi mata , abin da nake zargi daman bata son ta shi ya saka tayi mata wannan sharrin..,
kai kurum malam ya jinjina yace '' Allah ya saka hakane yafi alkairi bakomai Allah zai fitarwa da kowa hakkin sa alhamdulilah tun da kun gane ba haka bane ba damuwa ,ko za ku iya bani takardar ta..,
dan Allah kayi hakuri nasan ba akyauta muku ba wallahi ba yadda zanyi cewar sarkin fawa.
murmushi malam yayi har yanzu kamilar fuskar sa bata nuna damuwa ba ko ɓacin rai yace '' ba damuwa Allah ya yafe mana baki ɗaya..,
godiya yayi mai ya ci gaba da cewa bara naje na saka shi ya rubuta takarda.
to malam yace mai yana jiran sa be jima ba ya fito amsa yayi, yayi mai sallama ya ta fito yana tafiya tana zancen zuciya abin duniya duk ya ishe shi, maganar mutanen gari ma ta ishe shi, ace aure daga kwana ɗaya anyi saki to bakomai yasan Ubangiji jaraba shi yayi ya gwada imanin sa , Allah ya bashi ikon cinye wannan jarabawar har ya isa gida be dena tunani ba.
koda ya isa a waje ya zauna yana karatu almajirai suka zauna yana karbar haddar kowa tare da ƙara musu wani sosai yaji zuciyar sa tayi sanyi tabbas Alkur'ani waraka ne , maganin damuwane al'ummar annabi mu dage da ibadar Allah.
ko dan muga haske a cikin rayuwar mu.
#####
Sai karfe 1:40 aka fito da ita an saka mata oxygen sannan an ɗaura mata drip a hannunta kai tsaye daki suka shiga da ita mommy za tabi bayan su taga Juraij ya fito ashe dashi aka shiga ba ƙaramin mamaki tayi ba da ganin sa da tayi saboda ɗazu bata ga an shiga da shiba tace '' juraij daman kana ciki..?,
cire glove yayi matsawa yayi kusa da wani automatical dustbin tuni ga buɗe ya jefa su yace '' kirani su kayi akwai wata kofa a baya tanan na shigo..,
nifa ince ya jikin nata..?
juraij yace '' da sauki damuwa ce tayi mata yawa amma insha'Allahu zuwa anjima zata warware..,
to Allah ya yarda mommy ta faɗa tana shiga world din da aka kai yumna tura kofa tayi taufiq ne zaune yana danna waya zama tayi a kujerar da take facing din sa tace '' bata farka ba ko..?,
ɗagowa yayi ya kalli yumna da take kwance yace '' a'a ko motsi ba tayi ba , amma wani likita yace min sai nan da karfe biyar zata farka sun mata allura ne..,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' Allah ya kai mu darai da lafiya..,
amin ya Allah ya faɗa yana tashi zura wayar sa a aljihunsa yayi yace '' mommy ni zan tafi zan turo miki yaran nan sa taya ki zama wallahi wani irin bacci nake ji duk na gaji..,
Wallahi kuwa akwai gajiya yau ka sauka kuma kuma baka huta ba , Allah dai yayi albarka sai dai in yusrah juhud yanzu haka nasan ta , tafi gurin aiki, itama yusrah ko ta tafi makaranta Allah masani.
Cikin kaunar mahaifiyar tasa yace '' amin ya Allah to zan dai duba na gani duk abin da ake ciki za kiga nayi miki waya ya jikin ahlam..?,
mommy tace '' da sauki hice ko ka kirawo ta..?,
shafa sumar kan'sa yayi yace '' eh na kirawo ta maman su ce ta ɗauka tace tana bacci amma zata faɗa mata..,
To Allah ya ƙara sauki ciki ne me laulayi ga haɗo da rashin lafiya kullum ba lafiya wallahi tun ina ganin yarinyar nan lanjarewa take har kuma naga ashe ba lanjarewa take ba cutar ce Allah dai ya raba lafiya haka wani cikin yake sai ranar da aka sauke shi ake samun sauki
End Ads