x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 13 - YAN ZAMAN MAKKAH BOOK 1

  • 36001 words
  • 37750 words
  • Out of 37750 words

Category: Romance Story +18

Views 126

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
tsuliyar dodo dan ubanki ina ruwan ki da rayuwa ta kaga shegiya yar bakin ciki tafiya ce ba fashi sai na yi ta , muna sauka zan ce musu su kaini ka'aba na roki Ubangiji na haɗa da munafukai da yan hana ruwa gudu duk Ubangiji ya hana daku yayi magananin ku shegiya me mutuwar zuciya ni an faɗa miki irin kice to buɗe kunnuwanki da kyau ki jini billahilazi wuwarramanu ko mamman be sake ni ba , sai na saka ya sake ni dan wallahi in har be sake ni ba sai na yanka mai ticket din tashin mutunci kala kala sai ya gwammace kiɗa da karatu dan uwar babanki
dan haka bara na fito mutu miki a mutum ni wannan sakin gaba takai ni kuma itama innar su hindatu zata ci jakar uban'ta wallahi na dawo sai na siya gidan su na saka an rushe shi,
Cikin yanayin zafin rai da fusata bakin malam har rawa yake bakin ciki ya tokare mai zuciya tari ya fara yana cewa yumna ko bayan raina karki sake ki dawo cikin gidan nan na yafewa duniya ke in har na isa da ke ki dawo ki zauna idan kuwa kika saka kafa kika tafi to wallahi ban yarda ba ki kara tako kafar ki cikin gida na da suwan kin dawo karya kike ki ɓata min suna, karya kike ki zubar min da mutunci na..
Inna hadiza tace '' da kyau abin da tun farko ya kamata kayi kenan ka tsaya kai mata sako sako..,
runtsai ido yumna tayi ashe rashin arziki shamsiyya ta shiyar mata hmm dai-dai take da su tace '' malam tun farko fa kai kace na tafi kuma yanzu kace ba in da zani..,
Yumna in har na isa da ke to ki dawo ki zauna cikin yan uwanki..
to kawai tace ta kashe wayar ta mai dai ta inda take tana cewa wallahi ba wannan Maganar ko a kotu maganar farko ake dauka dan haka nayi nan munafukai ne suka zuga ka shegu masu tafiya da lahira da ƙoƙon dambu sai naci kan uwar su a hannu a hankali zasu gane wace ce ni.
ɗaukan kayanta tayi ta ɗora akai ta ci gaba da tafiya tana zancen zuciya har ta isa lokacin tana shiga ana ƙoƙarin jera mutane a mota da sauri ta ƙarasa ta turmusa ta shiga zama tayi tana sauke ajiyar zuciya yumna nura da sauri ta ɗago cikin mamaki tace '' lah Layla ashe kin zo..?,
dariya tayi tace '' eh wallahi amma ki sauka kafin wancan ya gano ki ko baki ga saka mutane yake ba yana kiran serial number su...,
ke kyale sa wallahi naga guri ba in da zan sauka kina tunanin wannan uban yawon namu motar nan ba tai mana kaɗan ba ai wallahi kawai barsu salon ace sai gobe tun da har yau nayi sallama da kowa to bazan koma ko ina ba..,
Ke dan uwarki fito na saka kine taji muryar wanda yake jera mutane ya fadi haka da sauri ta juyo tace '' me uwata tayi maka, ka zage ta haka kurum ina ma laifin kace min na fito sai ka zage ni..,
a fusace yace '' zaki fito ko sai na fusgo ki tun kafin ki tafi kin fara mai da mana da magana ina da mun kai ki ai sai dai ki ce zaki dauki hannu ki dake mu..,
a fusace ta fito tana murguda mai baki sakar baki yayi yace '' oga kallo yarinyar nan anya kuwa ba hakura za mu yi ba kaga tun yanzu neman fasa min baki take..,
wanda a ka kira da oga yace '' muga visa ki..,
da sauri ta kunce kayan ta, ta ciro ta miƙa mai , amsa yayi ya gama dubawa yace '' wannan ba a nan motar za a saka ta ba a can take...,
da sauri ta dauki kayan ta tabi wanda ya yi mata alama da ta bishi kara chanje kayanta su kayai sannan suka nuna mata gurin zaman ta ba dadewa motar su ta tashi a hankali ta fara tafiya har kuma ta hau titi ta soma gudu tamkar zata tashi sama ware ido sosai yumna tayi tana kallon garuruwa har suka zo filin tashin jirage nan ma ƙara duba su a kayi tare da yi musu rubutu a cikin visa su sosai yumna take baza ido domin ta ga layla amma na iya ba labarin'ta wata zuciyar tace to ko ba jirgi ɗaya za su hau ba ne.
bata da me bata wannan amsar a haka aka yi gama checking din su sannan aka basu set number su shiga yumna tayi tana kalle kalle zama tayi cikin farin ciki ina ma tana da babbar waya ta dauki kan'ta photo kallon matar kusa da ita tayi zata haife ta tace '' ina kwana..,
matar da taci uban jambaki ga belching dena taunar chingum din'ta tayi ta fara kallon ta sama da ƙasa sannan tace '' lafiya qalau ke daga ina kike..?,
murmushi tayi tace '' yumna nura Agadez ni yar garin Agadez ce ..,
kai ta gyaɗa tace '' oh kema kenan neman arziki kika fito da kananun shekarun ki..,
gyara zama tayi tace '' aunty wa zai zauna yaga zama ai nima fitowa nayi a dama dani..,
dariya ta sheke da ita tace '' ai kuwa kin yi kyan kai wallahi yanzu rayuwar nan idan baka tashi ka nema ba , to kana cikin takaici da bakin ciki dan wallahi wannan numfashin da muke shaƙa da ace a hannun dan adam yake to yasin wani hanaka shekar sa zai yi dan haka tashi mu nema ya zame mana dole ni kinga aurena na ballo na tawo haka kurum zan zauna ne ina cin garau garau mijina ga bakin talauci haka na tsallake ya'yana na ce na tafi nemo arziki..,
hmmmm aini dake kamar dan juma ne da dan jummai sai dai banbancin wasu abubuwan
da sauri ta kalle ta , ta miƙa mata hannu suka tafa tace '' Masha Allah kenan zamu ce ta tarar tawo mu tafi ya akai aka haihu a ragaya..?,
limshe idon'ta tayi tace '' labarin yana da tsayi amma zan baki shi tas..,
dariya ta sheƙe da ita lokacin kuma aka soma sanarwa jirgi zai tashi kowa ya saka belt tare da kashe waya ko saka waya a play mode da sauri suka fara sakawa a hankali jirgin su ya fara tashi yana ƙoƙarin keta hazo dad'i ne ya kamata yumna tace '' aunty na yarda da komai nufin Allah ne yau gamu a cikin jirgi wanda sai wane da wane suke shigar sa..,
dariya tayi tace '' tabbas Allah ya nufa sai fatan dacewa da samun rahamar Allah...
haka ne wallahi ta faɗa tana kwantar da kanta a jikin kujera tare da kallon saman cikin jirgin.
wata mace ce ta soma zagawa ganin kaya a gaban yumna tace '' ki ɗauke shi ki saka a loka..,
to tace ta tashi ta bude abin saman kan'ta daman taga mutane na sakawa amma tace ita gwara kayanta a kusa da ita yafi mata sauki haka kurum taje su zurare ta ƙasa ya za tayi da za ta saka idan taje can..
gama sakawa tayi ta komai ta zauna sosai suka dinga keta hazo har suka sauka gama saita kan'sa jirgin yayi suka fara fitowa zare ido yumna ta fara yi tana kallon wannan matar tace '' aunty ya ban ga ka'aba ba , kamar wa'yannan mutanen ba larabawa ba kin gan su ba jallabiya sun ci ƙananan kaya..,
nima abin da na gani kenan amma ai larabawa suna saka kananun kaya suna cikin wannan maganar wani mutum ya ƙaraso yace '' kune wa'yanda kuka tawo daga niger ko..,
kallon mamaki su kai mai ganin yayi hausa raɗau dukkan su kusan su ashirin suka ce eh mune.
okay ku biyo ni.....
bin bayan sa su kayi, har suka isa wani guri wani mutumin ne sukai magana da matar nan da suka zauna guri ɗaya da yumna sannan ya tafi be kula ba ya ban gaje yumna da sauri yace '' yi hakuri..,
yumna tace '' bakomai wallahi,
sosai tayi mamakin jin yayi hausa kenan daman yan kasar makka akwai masu jin harshen hausa kenan
tana cikin wannan tunani ta dauko mata kayanta ya miko mata amsa tayi ya juya ya fara tafiya.
fara binciken su a kayi zuwa gurin yumna su kayi suna bincike kayan ta suka dauko wodar ibilis da wasu kayan maye..
nan danan gurin ya dauka jami'an tsaro suka hallara a gurin kuka ta fashe da shi ganin an rutsa ta da bindiga,
ankwa wata yar sanda ta saka mata kuka ta fara yi domin bata san me tayi ba kallon aunty tayi da sauri matar ta matsa da ga gurin cikin Muryar kuka tace '' wallahi ba abin da nayi me nayi...,
bindiga wani ya saka mata a maƙoshi
wasu motoci ne suka shigo airport din a guje suka za gaye wa'yanda suka rutsa yumna buɗe motar wani yayi suka tura ta ciki kanta bugar glass din motar yayi hawaye na bin kuncinta sosai ta shiga cikin wani irin tashin hankali gashi ba damar yin magana duk sun rutsata da bindiga a kuje suka fita tamkar zasu tashi sama tare da yin jiniya kuka sosai yumna take yi ta shiga uku bata da kowa sai Allah Ubangiji ya zama gatan ta..
ba irin dana sanin da ba tayi ba tuni yunwar da , ta fara ji ta neme ta , ta rasa ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba lokacin da suka iso police tasion irin tsaron da ta gani ba ƙaramin guri aka kawo ta ba baza ta iya karanta komai ba domin rubutun da aka yi a bakin kofar gurin kamar larabci kamar ba larabci ba kan'ta ne ya ƙara juyewa ta shiga wani irin hali tusa ƙeyar ta su kayi da bindiga har suka shiga ciki a wani guri me raga aka ajiye ta zate ido ta fara ganin jami'an tsaro sai bincike suke yi a cikin wata computer wasu kuma na daga abin da ita tasan bata saka shi ba a cikin kayan ta ba suna rubutu a ciki da kuma wata takarda wasu ne suka ƙara fita.
duk sanyin gurin wani irin gume ne yake keto mata tun daga tsakiyar kan'ta.
a hankali ta furta ya Ubangiji ka fitar dani daga cikin wannan azzaluman mutanen..
hawaye na bin fuskar'ta zuciyar'ta tamkar zata faso kirjinta ta fito...

END OF BOOK 1

DOMIN SAMUN UPDATING BOOK,2
KU YI PAYMENT 500
8141785374 Amina alhasan Muhammad opay
Ku turo da shedar ku ta wannan number
08141785374
Yan niger kuma zaku turo ta my nita 1000fcfah
Idan ya zama complete document ya koma 1k ku hanzarta biya domin karanta ci gaba.





End Ads