x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 12 - YAN ZAMAN MAKKAH BOOK 1

  • 33001 words
  • 36000 words
  • Out of 37750 words

Category: Romance Story +18

Views 128

02 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
abin yumna ya fara bata tsoro ganin haka yumna tashi tayi, ta tafi dakin ta turo kofar tayi ta murza key, zama tayi a kan gado ta zuba ta gumi tabbas idan ba tai musu wuta wuta ba to wallahi ba za su yarda da wannan tafiyar tata ba ɗaukan waya tayi, ta nemi number Na'ima har ta katsai ba'a dauka ba dogon tsaki taja ta ajiye wayar a fili tace '' ke daman tsiyar ki, kenan ai ta kiranki a banza..,
kwanciya tayi tana , ta wassafe wassafe a zuciyar ta , limshe idanuwan'ta, tayi tasan yanzu ba za su taɓa fuskanta ta ba , sai lokacin da nasara ta zo mata yanzu kowa kallon bai bai zai mata idan kuma nasara tazo sai a dinga dama nice, sun manta a baya abin da suka ce tabbas me hakuri yana tare da nasara zata shanye komai zata dauki komai tasan wannan duk abin taki ake zuba mata.
bacci ne ya dauke ta kiran sallar magariba ne ya tashe ta, tashi tayi ta dauro alwala ta , tayar da sallama bayan ta idar ta ƙara jaraba number Na'ima still bata dauka ba message ta rubuta mata tace '' Assalamu alaiki Na'ima ban yi fushi ba , na kira ki amma ba kiyi picking call din ba na bugo ne na sanar dake nima ina nan tawowa, ki turo min sunan unguwar da kike zan kawo miki ziyara sannan ina godiya da yi min hanyar tafiya makka da kika yi Allah ya bar zuminci..,
turawa tayi ta ajiye wayar ji tayi ana knocking din kofar dakin ta banza tayi domin hausawa sunce da zafi zafi ake bugar ƙarfe..,
ko da yusrah ta gama bugunta bata buɗe ba sai ta juya ta tafi gurin mommy tace '' mommy taki budewa..,
tana faɗar haka ta zauna ajiye chokalin hannunta tayi tace '' to bara naje naga ko lafiya..,
Juhud da take operating system din'ta ta ɗago tace '' mommy sai kace wata yarinyar karama ki kyale ta idan ta gaji zata fito ne ita fa bari ba shegiya bace da uban'ta amma zaki damu kanki..,
shiru mommy tayi ta bar gurin ƙara zuwa kofar dakin yumna tayi, ta fara bugawa still tai mata shiri hakura tayi ta barta.
bayan sallar isha ta kwanta tana addu'ar Allah ya fahimtar da yumna gaskiya.
Wasa wasa ƙaramar magana tana ƙoƙarin zama babba yumna har washegari bata fito ba Alhaji ma yayi mata magana taƙi buɗa kofar gashi aranar taufiq zai koma Ingila acan yake karatun sa tafiya su kayi rakiyar sa zuciyoyin su duk ba dad'i.
a bangaren yumna kuwa itama ba ƙaramin buguwa tayi ba kwana ɗaya da rabi da tayi ba abinci.
bayan tafiyar su fitowa tayi a wahale ta dade a kwance a parlour yawa wata matacciya haka suka shigo suka ganta da sauri mommy ta ɗagata numfashin'ta sai kaiwa yake yana komowa cikin sauri tace '' juraij zo ka duba min yarinyar nan sakin jikin ta tayi hakan da tayi ba ƙaramin daga hankalin su yayi ba , ban da juhud da juraij ko a jikin su mommy taɓa kirjinta tayi numfashin ta sai kaiwa yake
yana komowa zama Alhaji yayi yace '' to ku kuyar da mana ku bita da addu'a, Allah ya tsare ya kare ba wayon mu ba ba dabarar mu ba Ubangiji shi yake tsarawa yake kuma ikon sa..,
jikin mommy yayi sanyi tace '' Alhaji mu bar wannan maganar za muyi ta , juraij wai ba magana nake maka ba ..? ka mai dani yar iska yawa da dutsai nake magana..,
Mommy yarinyar nan ku barta duniya ce ɗaga hankalin da taga kuna yi shi ya saka take wani abin tana nan ma anyi mata wannan sharrin balle ta tsallaka wata ƙasar.
cewar Juraij ran mommy ne ya ɓaci da jin wannan maganar juraij dan haka tayi shiru bata ce mai komai ba.
runguma ta , tayi, tana yi mata addu'a
ko Allah zai saka zata dawo dai-dai.
ranar yadda mommy yaga rana haka ta ga dare washegari malam ya zo tun da mommy take mai bayani yayi ƙasa da kan'sa Alhaji na gurin shi daman Juraij yana gurin aiki .
Mommy ta ƙara da cewa kawai mu barta sai a tayata da addu'a dan yau ne ka haife shi baka haifi halinsa ba zan yi magana ma da hajiyar mu itama nasan ba zata ki ba , kuma da alama duniyar ce tai mata zafi take ƙoƙarin barin gurin da aka santa duk ranta hankalin'ta ya dawo jikin'ta zata dawo gida zata waiwayo mu, idan muka matsa abin da zai faru yafi na yanzu dan zata iya illata kan'ta idan haka ta faru wa za'a zaga mu ne a ciki..,
Alhaji ma yace '' nasan da ciwo dukkan mu ba haka muka so ba amma tun da , tace ita ga abin da ta za barwa kanta shikkenan ga hanya nan Allah ya bata sa'a iya gata muna yi mata ko da ace ba zata zauna a can agadez ba to ga nan, nan ta zauna ta ci gaba da karatunta har Allah ya fito mata da miji tayi auren ta amma ya kanne idanuwan'ta ta toshe kunnuwan'ta, bata tunanin wannan ɓacin rai da ta saka mu zai iya zame mata matsala a rayuwar ta sufa iyaye ba abin wasa bane , ba lallai bane wata ran ta budi ido ta gan mu, a lokacin kuma sai tai ta cizon yatsa tana dama nayi kaza , dan haka kawai kayi hakuri wannan ita ce jarabawar ka , dan kana malami ba wai ana nufin cewa ba za'a jarabe ka ba a gwada imanin ka wannan abin nasan ka sani ƙara tuna maka nake malam...,
ajiyar zuciya ya sauke ya ɗago idanuwan'sa yace '' taje na barta..,
hamdala su kayi duk da sun san bawai dan yana so ba kawai ba yadda ya iya ne
hamdala yumna tayi a ranta duniya zata koma mata sabuwa bayan sallar la'asar sallama yayi musu ya tafi tare da cewa kawai baya bukatar ta ƙara zuwa Agadez ya yafe daga nan tayi tafiyar ta ,
ko a jikin'ta haka tace '' to malam Allah ya kiyaye hanya..,
be ce mata komai ba ya fice daga dakin ranar haka ta wuni cikin jin dad'i farin ciki ba'a magana duniya tayi mata dadi sai shirye shirye take ba ruwanta da haɗa ran da su juhud suke yi mata juraij kuwa yafi kowa yi mata kallon banza abin da tayi ba ƙaramin ɓata mai rai tayi ba murmushi take yi ta wuce ta bashi guri
Washe garin
da za su tashi tana tsaye a harabar gidan tana shawagi da yake garin yayi limshi alamar ko wanne lokaci ruwa zai iya tsugewa a guje motar sa ta shigo ko dai-dai ta parking din'sa be yi ba ya fito cikin sauri kusan dariya ce ta kusan kubbucewa yumna ganin yana sauri kamar zai tashi sama bin bayan sa tayi da kallo ta taɓe baki tace '' a haka zaka ƙare mijin tace duk ka wani firgice ɗan kadangaren da na saka mata a tsakar daki shi ne take zunduma wannan ihun wallahi kaɗan kuka gani tun da ni zaku tsana akan nace zan je na nemo arziki kamar kowa..,
be dade ba ya fito yana kwalawa masu wanki da guga kira cikin badda kama ta karaso kamar bata san me ya faru ba tace '' yaya lafiya naga hankalin ka a tashe..? ni fa wallahi ban iya zaman gaba, ba..,
tamkar ya ɗora mata ashar sai kuma su yaga rashin dacewar haka tunda wanda ya kula ka , ai daraja da dashi sannan kuma tabbas ba kyau zaman gaba yace '' wallahi kadangare ahlam ta gani a kusa da ita , ta kirani ni, tace kamar ta ga wulgawar mutum to sai dai kallo take bata gama tantance mene bane sai taga kadangare yana yawo...,
zaro manyan idanuwan'ta tayi ta ɗora hannu aka tace '' innanallahi wainna ilaihir raji'un amma dai ba abin da yayi mata..?,
banza yayi mata ganin masu yi musu wanki da guga sun ƙaraso yace "dan Allah mati Ka iya fitar da kadangaren..?,"
kallon kallo suka shiga tsakanin mati da Haruna dakyar mati ya iya cewa wallahi oga ko son ganin shi, bana son yi ai wannan muguwar halitta ce..
innanallahi wainna ilaihir raji'un amma dai mati wallahi kun bada maza kuna maza kuna tsoran kadangare..
ta faɗa tana kallon juraij domin ta yi haka ne da biyu
aikuwa ya gane sarai ita daman ba'a zaman mutunci da ita sai anyi na tsiya juyowa yayi yace '' dan ubanki shige muje ki ɗauke shi..,
Zaro manyan idanuwan'ta tayi ta nuna kirjinta tace '' na shiga uku ni, ku, kuna maza baku ɗauke ba sai ni gaskiya ba zan iya ba..,
Haɗe rai yayi yace '' shige mu tafi ko na kwarfe ki..,
ƙara kallon juraij tayi a karo na biyu tace '' sai kace wata ruwa zaka ce zaka kwarfe ni..,
kallon su mati yayi yace '' ku koma bakin aikin ku..,
To suka ce masa suka juya suka tafi yumna tana cikin tunani , bata ankara ba taji ana janta tamkar kayan wanki.
Ihu ta shiga zab gawa amma ko a jikin sa sai da ya dangana ta da parlour sa fisge hannun ta tayi tace '' wallahi abin da kake baya dacewa kai , ka kasa sai kace ni nayi..,
Mari zai zabga mata ƙadan gare yayo kan'su da gudu suka , fita har da ahlam yumna tsayawa tayi tana dariya har da riƙe ciki ganin kamar ba namiji ba ya biyo su a guje nuna shi take tana zabga uwar dariya har da riƙe ciki,
biyota yayi ta shiga parlour mommy da gudu.
Bayan mommy ta shiga ta ɓoye tana danne dariyar ta mommy tace '' juraij lafiya me ya faru..,
leko da kan'ta tayi tace '' mommy gudun kadangare yake..,
sai ta ƙara fashewa da dariya har da buga cinya tana cewa namiji da gudun kadangare hhhhh wallahi mommy wannan abu ya ban dariya tare muka dinga gudu dashi yana ƙoƙarin rikoni wai kar mu tafi mu barsa.
a fusace Juraij ya zagaya bayan mommy zai fisgota ta dawo gabanta tana cewa wayyo Allah kinga akan na fadi gaskiya shi ne zai dake ni..
Haba juraij sai kace wani yaro ka dinga beye mata
Mommy ta faɗa tana danne dariyar ta , duk jarumtar juraij baya son ganin kadangare barin irin babban nan wanda har canza kala yake sabo da girma.
juyawa yayi bece komai ba .
ajiyar zuciya ta sauke ta zauna akan carpet tana sauke numfashi tuno ahlam tayi da ƙaton ciki tana cewa baby karka gudu ka barni dariya ta ƙara shekewa da ita tace '' su baby manya..,
kallon ta mommy tayi tace '' lafiya me ya faru kike magana ke kaɗai..?,
ba komai mommy
dauke kai tayi tace '' dazu naje gurin mutumin nan da kika bani number sa , nayi bincike na tabbatar da gaskiya..,
da sauri ta ɗago cikin mamaki tace '' mommy yaushe kika fita har wajen kenan kinje..?,
Eh naje yumna kuma yayi min bayani
gaban tane ya faɗi karfa ya faɗa mata gaskiyar duk abin da ya faru da yadda tsarin su yake tace '' mommy me yace miki wanne bayani yayi miki..,
gyara zama mommy tayi tace '' yayi min bayani wanda ya gamshe ni saboda yace duk lokacin da mutum ya so dawowa yana iya dawowa sannan a guri me tsabta suke kai mutum wanda addinin sa ko imanin sa ba zai taɓu ba sai dai in mutum ne ya kaucewa dokar da suka shinfida mai amma su aiki suke yi da addini abin yayi min dad'i wallahi har ayoyi da hadisai yake karanto min mutumin masani ne kuma babban mutum wanda yasan kan'sa duk ya nuna min shedar kasar nan tasan da zaman su akwai sa hannun hukuma da dama ya nuna min..,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' to Allah dai ya dafa mana..,
amin ya Allah mommy tace ,
Bayan sallar isha ta shiga daki ta kwanta bacci me cike da jin dad'i har hango kan'ta take a makka.
Washegari
da asubar fari ta shirya kayanta ma tas ta haɗa su ta daure su a zanin atamfa wayar ta kuwa soke ta tayi ta saka a kugu
mommy ce ta shigo turus tayi ganin ikon Allah lamarin na yumna tamkar wacce aka jefe anya kuwa wannan abin da take yi lafiya qalau take
mutum yana cikin gatan sa yace sai yabar cikin gatan sa ya koma wata uwa duniya ta sani sarai ba yadda suka iya da ita shi ya saka suka barta kuma malam ma fushi yake da ita amma ko a jikin ta duk da be buɗa baki ya furta ba fuskarsa ta nuna abin da yake zuciyar sa ajiyar zuciya ta sauke tace '' yumna badai da safe zaku tashi ba..?,
cikin farin ciki tace '' a'a ba da safe za mu tashi ba nice dai kawai na shirya domin kinsan jirgi baya jira sai dai a jira shi..,
hmmm Allah ya kyauta ta fadi haka zuciyar ta na mata wani irin suya Hajiyar su ma faɗa tayi tace a kyale ta duniya tafi bagaruwa iya jima tas zata koya mata hankali idan dai son abin duniya mutum zai yi to ba shakka zai girbi abin da ya shuka kuma zai halaka tana cikin wannan tunanin ne yumna tace '' mommy wallahi saboda murna bazan iya cin abinci ba Allah ya sani ba ƙaramin farin ciki nake ciki ba ‘‘ O,, Mamman yana nan yana figar talaucin sa ba damuwa idan na dawo zan bashi dan na jari...,
da sauri mommy ta kalle ta sai kuma tayi shiru domin bata da bakin magana juyawa tayi ta fita zama tayi a parlour zuciyar ta ba dad'i da ace juraij ya aure ta ba yadda za tayi dole ta zauna,
ga maganar abokin sa da yayi mata ma lamarin babu shi domin ya koma gida hutu be kuma ƙara yi mata magana ba , Allah dai ya tsare rayuwar ta
mommy mommy mommy
da sauri ta ɗago tace '' juhud har kin shirya yau da wuri haka..?,
zama juhud tayi tace '' mommy tunanin me kike yi haka..?,
ba komai juhud
hmmm wallahi nasan ba zai wuce na yarinyar nan ba haka kurum kun dauki son duniya kun ɗora mata kun kasa hanta abin da tayi niya tun da tace sai tayi sai ku zuba mata ido gata ga hanya nan karta tsaya a makka ta , tafi bangon duniya wannan matsalar ita , ta shafa ni wallahi ko san ganinta ba nayi haka kurum ta jefe ki a cikin tunani kina ga ranar da malam ya bar gidan nan idon sa yayi jajir ko wannan hakkin da ta kwasa wallahi Allah ba zai barta ba

da sauri ta ɗaga mata hannu tace '' juhud ya ishe ki, tafi bana son kara jin komai daga, gare ki..,
tashi tayi jikin ta a sanyaye tace '' mommy Allah ya baki hakuri amma wallahi yarinyar nan..,
Cikin ƙara ji ta tari numfashin ta, tace '' nace miki bana son jin komai daga, gare ki, ki tafi inda zaki Allah ya kiyaye hanya..,
juyawa tayi tana cewa amin..
dafa kan'ta mommy tayi ta lula duniyar tunani har lokaci yaja bata sani ba a guje yumna ta fito tana cewa mommy mommy mommy.
da sauri ta ɗago tace '' yumna me ya faru..?,
cikin murna tace '' yanzun nan aka bugo min waya, wai na zo za'a gama haɗawa mu ayi duk wani bincike da ake yi sannan sai mu tafi kin san fa muna da yawa..,
mommy tace '' to bara salisu ya kai ki..,
a'a barni abin da gurin ba nisa ni daman na gama haɗa kaya yauwa idan kin yi waya da gida kice kina gaishe su jirgin mu ya tashi insha'Allahu duk wani kunci na rayuwar su zai zama tarihi idan na samu dama komai yayi dai-dai zan kira ku mu gaisa amma dan Allah kar wanda ya kirani ya taku ramin ina aikina kin san fa basa son Kiran waya wallahi idan na kirawo Na'ima dakyar take dagawa dan haka kar wanda ya kirani haka kurum su koreni su dawo dani niger ban tari abin arziki ba..,
salati mommy ta saki, amma ko a jikin yumna sai ma ƙara washe baki take dan ita bata ga abin aibun da tayi ba gaskiya ta fadi haka kurum ayi mata kutungwila ayi mata kafar kwaɗo su dawo da ita Niger babu shiri.
shiga daki tayi ta fito da kayanta a ɗaure a zani ta ɗora su a kanta cikin washe baki tace '' to mommy saduwar alkairi duk ki faɗa musu fa karki manta da ace ina Agadez da ko wanne gida sai nabi nayi musu sallama..,
Mommy ta dago da kyar saboda sarawar da kan'ta yake mata tace '' Allah ya kiyaye hanya ya bada sa'a..,
cikin farin ciki tace '' amin ya Allah..,
ta faɗa tana tafiya cikin farin ciki yau har wa'yanda bata yiwa magana a cikin gidan ta dinga bin su tana yi musu sallama so sai ma'aikatan gidan suke mamaki tsayawa tayi akan mati tace '' to mati Allah ya kirani..,
da sauri ya ɗago ya dena gugar da yusrah ta bashi yace '' ikon Allah mutuwa kenan za kiyi..,
wani kallo tayi mai na anya kuwa kana da hankali sannan tace '' a'a lahira zan tafi ku shikkenan ba yiwa ɗan adam kyakkyawan zato sai ku zargi mutuwa dan nace Allah ya kira ni to ba wannan kiran nake nufi ba yau makka zan tafi duk wani bukata da kake da ita sai ka rubuta min a takarda domin muna sauka cewa zanyi akai ni harami na dafa ka'aba na roki Ubangiji..,
dariya ya fara yi har da riƙe ciki sanan yace '' uhmm uhmmm yumna a ɗinga haɗawa da insha'Allahu..,
banza tai mai ta fara tafiya wayar ta ce taji tana ringing da sauri ta ciro ta , ta ajiye kayan ta a harabar kofar gidan nasu ɗagawa tayi tare da karawa a kunne tana cewa hello shamsiyya bana son bakar jaraba tun ba saba har kun fara kirana..,
shamsiyya tace '' ke da hallacan wannan tafiyar da za kiyi bata gaba na wallahi tun da kin zaɓi bin yawon duniya da ki zauna gidan miji zaman bautar aure...,
kuttumar ubancan kayya sa lallai yau kin taɓo
End Ads