miki komai za kiyi shekara ɗaya kina biyan mu kafin ki fara cin gashin kanki kina.
kannata ne ya kulle tace '' saboda me aka fi son bazaurawa...,
Masha Allah kina da kyan kai da kikai min wannan tambayar dalilina da yasa muka fi son daukan zaurawa saboda su, suna da yancin kan'su sannan duk abin da aka saka su za su yi, duk wani aiki na gida za su iya yin sa..
shiru tayi tana sauraron sa sannan tace '' a gaskiya ni bani da aure amma sai bayan nayi aure na fito sannan zan yi wannan tafiyar saboda a gidan mu balallai a barni ba ,
okay ba matsala ko yaushe kika shirya zaki iya zuwa sannan akwai ka'idojin mu bama daukan mace mu kaita batare da anyi general check up ba sannan albashin ki na watanni goma sha biyu wato shekara ɗaya zamu riƙe shi saboda mun yi miki dawainiyar kaiki da kuɗaɗen mu , sannan wannan company na zata dena iko da ke ba sai bayan shekara ɗaya dole kibi dokokin mu idan mace taga ba zata iya zama ba tana bukatar canjin waje ko dawowa to fa sai ya biya mu tas abin da muka kashe har da ribar dubu dari bakwai....
da sauri ta ɗago jin abin da yace na ƙarshe murmushi yayi yace '' naga kin kalle ni maganar tayi miki nauyi ne akai..?,
yumna tace '' kusan haka ne ,
cure hannuwansa yayi guri ɗaya ya sarke su yace '' wannan company yana kashe makudan kuɗaɗen gurin tafiyar yan aikatau dole zai mai da kudin sa har da riba..,
ajiyar zuciya ta sauke tace '' hakane amma kawata batai min wannan jawabin ba ...,
wace ya sunan ta a wacce shekara ta tafi..?
ya jero mata wa'yannan tambayoyin
yumna tace '' sunan ta Na'ima hamidu Poussin yar Agadez ce shekarar ta ɗaya bana jin ma ta cika ɗaya amma kuma ta turo da kudade a gyara musu gida ya akai ta samu kudi bayan kune da kudin ta bata gama biyan ku ba..,
Murmushi yayi yace '' oh na gane ta sosai ana samin alkairi a cikin tafiyar idan har mutum yayi amfani da damar sa sai ya tara abin duniya bayan ya gama ko kuma yaga ya gaji da zaman sai ya dena ya dawo gida ya ci gaba da harkokin sa da facaka da kudin sa son ran sa akwai matan da suka zama hajjiyoyi ko bayan sun dawo to ƙaramin mutum ma be isa ya kalle su ba suna da yancin kan'su sun san me ne yancin su, su suke zama matan mayan shuwagabanni da manyan yan kasuwa kinga kamar ke yadda kike da wannan kyan ina me tabbatar miki idan kika je zaki samu alkairai masu tarin yawa mayan kuɗaɗe sai dai kiyi kyautar su badai a baki ba...,
kallon agogon wayar ta tayi tace '' hakane Nagode sosai lokaci yana ja gashi saka min number ka idan na tashi zan kiraka..,
karba yayi ya saka mata , sannan yace '' tsaya a dan kawo miki abin jiƙa maƙoshi muna ta koro bayani na barki ba wani dan abu..,
murmushi tayi tace '' a'a wallahi Nagode sosai Allah ya saka da alheri..,
amin ya Allah yace tai mai sallama ta fito tafiya ta fara tana ta tunane tunane kala kala har ta kusan zuwa gida ta rasa gano bakin zaren to ita da take so tayi shekara ɗaya ta dawo mene amfanin zuwa aikin nan shekara ɗaya fa za tayi tana kwaɗago amma cikar burinta da mafarkin rayuwar ta fa shikkenan sai tayi shekara biyu lokacin ta tara abin da take iya ganin zai fiddasu daga cikin talaucin da suke ciki ,
har ta ƙarasa bata dena wannan tunanin ba tana shiga aka tada sallar magariba juraij ne ya fito yana sassarfa da alama masallaci zai je matsa mai tayi tana kai da kan'ta shima da yake yana da uzurin gaban sa be kulata ba ita tun da ya kusan targaɗa'ta ta dena shiga sabgar sa ba ruwanta dashi tunda mugu ne.
bata tarar da kowa ba acikin parlour dakin da aka sauke ta nan ta shiga ta dauro alwala ta tada salla bayan ta idar ta, tashi ta fito bedroom din mommy ta shiga sallama tayi tana zaune tana jan carbi durkusawa tayi tace '' mommy na dawo...,
Murmushi tayi ta ajiye carbin hannunta tace '' to ya suke da fatan suna Lafiya qalau..?,
murmushi yumna ta mai da mata tace '' alhamdulilah suna lafiya tama ce a gaishe ki da ba dan tafiya zan yi ba ta , tazo kun gaisa..,
Allah sarki ba damuwa wata ran ta zuwa idan kin zo garin.
tashi tayi tace '' nima haka nace mata ..,
fita tayi ta zauna akan kujera tana game da wayar ta a yanzu da ta kawo karshen wannan matsalar tata sai take jin bata da wata sauran damuwa malam da sauri zuciyar ta , ta buga tasan ba lallai ya amince da tafiyar ta ba , amma zata yi duk yadda za tayi ya amince idan kuwa yaƙi to za tai mai layar zana sai dai ya shafa yaga babu ita haka kurum su kenan ba wani me jin dad'i kowa wanda zai aura faƙiri ne haka ma wai gwara ita da zata auri mamman saurayin shamsiyya keke ne dashi yana yawo yana siyar da su karas da ɗa'ta..
dan haka wallahi ba zata kashe kan'ta ba haka kurum sai kace an yiwa malam kauri da kan kifi ya kasa fahimtar idan burin ta da mafarkin ta ya tafi..
ke da sauri ta ɗago ganin juraij sai ta kau dakan ta tace '' na'am..,
tashi kije ki share min daki na dana ahlam..,
da sauri ta kalle sa tace '' tafa ce idan ta ƙara gani na a cikin gidan ta sai ta yanka ni..,
ni nace miki, ki tashi kije kiyi aikin da na saka ki.
tashi tayi bata ce komai ba ta fita tana shiga pary din ta , samun ta , tayi tayi ɗare dare tana kallo Oni jikar mutum goma kowa da irin tashi salon kaddarar ita kuma wannan tata ta kallo ce kuma lalurar kallon a waya take yin ta ..,
ta faɗi haka tana shiga cikin dakin ahlam juyowa tayi tace '' baki iya sallama bane ko ce miki akai nan chochi ce..?,
ɗaga kan'ta sama tayi tana karewa dakin kallo tace '' ikon Allah sai nake ganin kamar na shigo chochi jin wasu maganganu na tashi tamkar na arnan da suka dade ba su san waye Allah ba , bisa dukkan alamu ma sallar da aka yi ta magariba ba lallai sun yi ta ba..,
Da sauri ahlam ta tashi tace
"Are you even in your right mind? Do you know what you're saying to me..?,,
murguɗa mata baki tayi tace '' aikin san bana jin turanci da kiyi min da yaran da zan gane na baki amsa dai-dai da abin da kika faɗa min..,
fasa marin ta tayi taja kwafa ta dauki wayar ta , tabar gurin tsaki taja ta fara gyare gyaren gidan ranta duk a ɓaci ta rasa ahlam wacce irin mace ce wannan ƙazanta haka kullum sai dai ta bulluwa jikinta turare taci kwalliya tamkar zata je gasar sarauniyar kyau amma daki ba kyan gani. gama gyara parlour tayi ta tafi bedroom nan ma kaya ne sunfi set ashirin a ajiye a gefen gado ga Landry basket amma ba amfani kwashewa tayi ta gyara ko ina tare da sala Room freshener sai karfe takwas sannan ta gama komai ta fito ko arzikin kallo bata samu ba daga gurin ahlam balle a kai ga godiya a gaje ta koma tana shiga tayi sallah bayan ta idar ta fito kan dining table ta nufa ta zuba abinci ta fara ciki bayan ta gama tayi wanka ta kwanta.
tun asuba tayi wanka ta shirya wani irin zumuɗi take tun da ta kashe wannan wutar gwara taje can itama ta ayi wacce za ayi,
karayawa tayi direba ya kwashi kayayyakin ta ya saka aboot sanan ta shiga Alhaji ya bata kuɗi godiya tayi mai suka dauke hanyar Agadez lokacin da suka isa karfe goma da rabi fitowa tayi malam da yake zaune yana biyawa almajirai karatu ta ɗago ya kalli Hajiya mommy yace '' sannun ku da zuwa..,
durkusawa tayi tace '' yauwa malam mun same ku lafiya..?,
Malam yace '' lafiya qalau alhamdulilah ya kuma ya yaran namu da me gidan naki..?,
murmushi tayi tace '' alhamdulilah suna lafiya qalau..,
masha Allahu Allah ya kara shiryar mana da su kan tafarki madaidaici ina juraij yake yau ban dashi kuka zo
Mommy tace '' amin ya Allah baya nan yana gurin aiki..,
to Allah ya temaka Allah ya bada abin da ake nema..
tashi tayi tana amin ya Allah.
Malam barka da safiya.
Barka dai yumna kin dawo lafiya.
lafiya qalau alhamdulilah.
shiga cikin gidan mommy su kayi su baba lami suka tarar suna zaune suna hira gaisawa suka yi sannan suka kawo musu abin kari kunun tsamiya ne da ƙotsai, mommy tace '' alhamdulilah wallahi na koshi..,
Inna hadiza tace '' a'a kodai irin namu ne ba zaki ciba abin da kunyi tafiyar mota duk abincin ya zazzage..,
a haba yau na sana zuwa gidan nan wallahi na koshi
Cewar mommy.
to ba damuwa yumna ba magana kin ja gefe kinyi shiru,
da sauri yumna ta kalle su tace '' nafa gaisheku...,
Baba lami tace '' haka ne wallahi..,
Kaya aka shiga shigo dashi su baba lami wannan ta kalli wannan wannan ta kalli wannan ganin kamar za'a buɗe shagon sai da kayan kitchen da na daki..,
shugowa malam yayi, yayi mata godiya haka ma su baba lami inna Hadiza tace '' to yumna ki dubu irin kokarin da wannan baiwar Allah tayi ki daure ko me zai faru kiyi koyi da halin manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama kiyi hakuri shi zaman aure ibadane yi nayi bari na bari shikkenan ko dan martabar mahaifinki da gidan da kika taso karki kalli na waje su baki sha'awa kowa fata yake ya sami irin ni'imar da kika samu kalli kaya kamar yar gidan wani attajirin me kudi dan girman Allah kiyi hankali ki nutsu..,
ƙasa tayi da kan'ta ta ta share kwallar karya tace '' insha'Allahu zan yi iya bakin kokarina da yardar Allah ba za kuji wata matsala daga gurina ba..,
Dad'i ya kama malam ganin yadda suka haɗu sukai mata faɗa kuma taji ta amsa albarka ya saka mata ya koma zaure domin ci gaba da karantu
Karfe biyu mommy ta tafi tare da bata kudi sosai tayi murna.
karfe takwas na dare mamman ya aiko kiran ta ,
sai da ta gama ɓata lokaci sannan ta fita tana wura hanci tsayawa tayi a kofar gida ta jingina da kofar gidan su tace '' barka da dare..?,
Barka dai masoyiya kinga kuwa yadda kika koma tamkar wata balarabiya ke daman matar manyan ce irina...
da sauri ta ɗago jin furu cinsa na ƙarshe tace '' Mamman kai sauri ka faɗi abin da ya kawo ka saboda bacci nake gobe zamu fara zana jarabawa..,
murmushi yayi yace'' wallahi na ƙagu ku gama jarabawar nan na ganki a cikin gidana kin zama mallaki na yumna ranar ba ƙaramin dadi zan ji ba wallahi yau ga yumna ta zama mallaki na muna tare da juna kai Allah ya nuna min ranar nan yasin ranar sai nayi sadakar nama asan cewa yau dan gidan sarkin fawa zai auri yumna zubin larabawa matar manya...,
kallon sa tayi yaci hular kauraye dan tsan hannun sa da guro da yake rigar jikin sa yar shara ce...
dauke kai tayi ita bata san wacce irin kaddara ce ta kai ta ga soyayya da mamman ba gaba ƙi ɗaya alamun rashin wadata ta game ko ina na jikin sa rigar duk ta kode dan hala wutsiyar ragumi tayi nesa da ƙasa dole ta nuna mai banbancin tsakanin ita dashi ta rabe mai tsakanin a ya da tsakuwa...
Copy is not allowed
Domin jin audio din Yan zaman Makkah Ku danna wannan link din sannan kuyi subscribe Dan Allah.
https://youtu.be/cDE5bjYY2HY
___________________
https://www.arewabooks.com/chapter?id=6817816be532b4a92550458c
Episode 11
Masoyiya ya kikai shiru kin barni ina ta zuba yawa ya'yan kaɗan ya..
dafa kan'ta tayi tace mamman ciwon kai nake ina buƙatar hutu kazo ka ci kani da zance kaga sai an jima.
sakar baki yayi yana kallon ta har ta shiga cikin gidan su shafa kan'sa yayi yace '' bakomai aski idan ya zo gaban goshi yafi zafi..,
kai tsaye gidan su ya nufa tun daga soro yake jin tashin muryar mahaifiyar sa da sauri ya ƙarasa tare da yin sallama mahaifinsa ne ya amsa amma ita ko kallon inda yake ba tai ba ta ci gaba da cewa Wallahi idan har kina son zaman lafiya karku kawo min wannan mara kunyar yarinyar cikin gidan nan kaf garin nan waye ban san ta ba a fagen rashin kunya yau kusan sati uku kenan ta ganni a hanya ko nunawa ba tai ba , ta sanni balle ta gaisheni dan haka kuka sake ta shigi cikin gidan nan sai ta dandani ƙudar ta sai na gasa mata aya a hannu me ake yi da mara tarbiyya ya kwalla fa rai sai ya aure ta , duk yabi ya rame ya kan jame ni wallahi da ace yar uwar ta ce nazeefa bazan ce bana so ba daman ko lokacin da kakai kuɗi badan raina ya so ba , bana son ta bana son wannan auren ba da yahuna za ka yi shi ba..
Yan zu asabe abin da ki kayi in kyau ta kenan me yarinyar nan tayi miki duk kin bi kin tsane ta ita ba aikata wani abin take ba na ba dai-dai ba amma lokaci ɗaya kin tsane ta haba asabe abin da ki ke aikatawa be dai-dai ba yanzu an kusan biki shine kike tada mana da hankali da me yaron nan zai ji da kunji kunjin biki ko da abin da kike yi..
cewar baffa mahaifin Mamman
Mamman wuce wa yayi bece komai ba zama yayi a daki ya zabga tagumi inna tayi yumna tayi dame zai ji,
Kwance yayi ya rasa in inda zai saka kan'sa saboda tashin hankali yana son yumna baya son abin da zai raba shi da ita ,
yana so su gina ingantacciyar rayuwa me tsafta wacce zata ginu har zuwa tsufansu share zufa yayi lokaci ɗaya zazzaɓi ya rufe shi gyara kwanciyar sa yayi ya kudindine a bargon sa da ya gaji da cin duniya duk ya farfarke.
daga haka bacci ya dauke shi
Washegari yumna suka fara jarabawa tun da suka fara bata ƙara saka Mamman a idonta ba duk kiran da zai mata bata ɗaukar wayar ace warta zai takura mata rayuwa har suka gama. washe garin da suka gama aka kawo kayan lefen su ranar inna Hadiza har rawa tayi domin saurayin shamsiyya yayi bajinta ya zuma mata kaya, Mamman kuwa ba wani abin arziki
ashe abin azuciya yake bawai karfi bane haka. Baba lami tace suna zaune suna cin abinci yumna ko bi takanasu ba tai ba to ita me ne haɗin ta da wannan kaya ko a zuciyar ta bata ji rashin dad'i ba, saboda sai kana son mutum kake kishin sa.
Shamsiyya ce ta kallo yumna ta gefen ido ita fa wannan kwantan ɓaunar da tayi bata gane mai ba anya kuwa ba akwai wata a ƙasa ba duk son duniya irin na yumna ta nuna ko a jikin ta ko dai wani abin arzikin Mamman yake tsara mata shi ya saka mata sauke mai buhun tujara akan sa ba.
Assalamu alaikum
baba lami tace '' wa'alaikis'salam...,
yaron da aka turo yace '' wai yumna tazo inji Mamman..,
kallon ta baba lami tayi taji me za tace, ita kuwa yumna bama ta nuna ba taga yaron balle a saka ran za tayi magana wannan yarinya ba dai kafiya da taurin kai ba yawa kafurar farko haka baba lami ta ce a zuciyar'ta afili kuwa sai tace '' yumna ke fa ake kira..?,
ajiye wayar ta tayi akan cinyar ta , tace '' baba ai ke zaki bashi amsa bani ba , yanzu ina magana ina saka kafana ina fita hmm labari zai sha bamban zaki kwashe min albarka ne kuce bani da kunya...,
inna Hadiza tace '' ta Allah ya kyauta kai jeka kace tana zuwa..,
tashi yumna tayi ta saka hijabinta ba wanda ta yiwa magana ta fara tafiya da sauri baba lami tace '' yumna ba zaki dauki daduma ba kullum baki da tunanin karrama bako ki saka mai abin da zai zauna sai ki bar shi a tsaye sai kace wani soja..,
Jingina tayi da bango jikin ta duk yayi sanyi zuwa sati me zuwa tasan i yanzu tana gidan Mamman dan haka jikin'ta yayi wani irin sanyi amma zuciyar nan a tsaye take tana nan akan kudurinta tace '' nazeefa jeki, ki dauko min..,
tashi nazeefa tayi cikin sauri karta dake ta , ta miko mata amsa tayi ta fita yana zaune akan wani dutsai shifiɗa dadumar tayi ta zauna tace '' gani...,
da sauri ya ɗago ajiyar zuciya ya sauke yace '' wallahi ban ma san kin iso ba , ina ta tunani na zata ba zaki fito ba wai masoyiya me ya canza min ke lokaci guda na kasa gane kan ki bakya daukar waya ta ko zanyi kira ɗari ba zaki dauka ba dan girman Allah yumna ki tausayawa zuciya'ta dame zanji ke kiyi innar mu tayi wallahi ina cikin matsala..,
kura mai ido tayi ta kasa kiftawa azuciya ta tace kai taga me sauƙi ce ƙasa yayi da kan'sa ya ci gaba da cewa ki tausaya min, ko yaya ta gurin ki na samu rangwami.
ajiyar zuciya ta sauke ta dauke kan'ta daga kallon sa da take tace '' Mamman auren mu ina tunanin ba me dorewa bane tun yanzu ka fara korafi jarabawa nake ina son hutu amma kai baka fahimtar haka ko wanne bawa akwai irin tashi ƙaddarar ka dinfa saukaka kanka Ubangiji shi ne masanin gaibu..
da sauri ya ɗago yace '' to shikkenan wallahi yumna ko me kika yi daidai ne agurina bakya taba yin laifi zan jure komai nasan wata ran sai labari..,
anya kuwa Mamman ba jinsin mayu bane kai akwai lauje cikin naɗi irin wannan naci haka turkashi ta raya wannan a cikin zuciyar ta , afili kuwa sai tace '' dare yana yi..,
da sauri sauri yace '' to dame dame kika tsara ina so