san na kwanta wallahi nayi bacci saidai ina tsoran fadan maman mu yanzu idan ta fara faɗa wallahi har bayan isha barin ta ga ba abin da na siyar mata..,
Allah ya kyauta yanzu dai gobe zaki goma
zaro ido tayi tace '' ina ba inda zani wallahi yanzu ma murde min da yayi zafi suke ba..,
kinga yadda sukai fa ta fadi haka tana daga mata rigar ta dariya fa'iza ta fara yi har da riƙe ciki tace '' kai jama'a shi yanzu mado me zai yi da wannan lemon tsamin wallahi dole yayi miki zafi...,
harararta tayi tace '' ai kinsan da haka kika kai ni..,
sannan kuma son zuciya shike dawainiya dake waya ce miki haka siddan namiji zai dauki kudi ya baki lallai kinyiwa kanki karya.
muguwa wallahi bazan ƙara daukar shawarar ki ba.
cewar nana
Fa'iza tace '' yauwa kamar tafiyar nan ce makka haka kurum idan dai ba fita za kiyi ki nema ba , ba za su baki kudi ba.
ba ance ana bara ba a bakin harami saboda suna tausayawa miskinai
wata harara ta zabga mata tace '' ai kinsan haramin soron ubanki ne dole ki zauna kiyi bara a nan bara na kirawo na'ima kuji me take domin la lura idan ba haka nai muku ba sai kun kai kanku mahalaka ita fa bama a garin makka take ba tana Labanon a gidan wasu arna take aiki..cemin tayi mijin matar yayi itama matar ta lallaɓo tayi.
gyara zama tayi dan jin wayar na'ima tana ringing cikin Sa'a aka ɗaga hello na'ima ya kike..?,
Lafiya qalau fa'iza yau kin tuna dani..
cewar na'ima.
kullum kina raina kawata ki warware wannan kullin da kikai yumna da nana suna ƙoƙarin tawowa zasu nemi agent din ki suma yayi musu visa su tafi makka ki fada musu ayyukan da ake yi kinsan dai ke ba'a makka kike ba ko haka kwanaki da jimawa kika ce min..
wani takaici ne ya turake ta , tace '' a gidan uban wa nace miki ba'a Makka nake ba to ina aiki ne da gidan Sarkin makka abdulaziz..
buga cinya nana tayi tace '' fa'iza be kamata idan ke ba zaki ba ki hana wani ya tafi, duk kinbi kin addabi kanki akan munce za mu je Alhamdulilah Magana a bakin me ita tafi dad'i gashi nan tace a gidan sarki ma take aiki duk wani dan bakin ciki sai dai ya mutu..a ko ina ba'a rasa na Allah.
EPISODE 4
Tashi fa'iza tayi tace '' na nuna muku gaskiya kun ki bi ko to wallahi kuje ga Duniya nan zata koya muku hankali..,
dariya nana tayi tace '' ta dai koya miki hankali mu dai tafiya ce ba fashi sai munyi..,
Dariya fa'iza tayi tace '' to Allah ya kaiku lafiya.,
amin ya Allah nana ta faɗa tana fita daga cikin gidan
kai tsaye gidan su yumna ta nufa a hanya suka ci karo da ita riƙe da kaza da sauri nana tace '' yar malam kaza kika siya ne..?,
haɗa rai yumna tayi domin sarai ta san halin nana kuma bata son munafurci da tsaigumi dan yanzu sai taci uban'ta tace '' eh kaza na siya ban isa bane..?,
dafa ta nana tayi tace '' Allah ya wuci zuciyar ki ni bada wata manufa na faɗa ba..,
wani kallo tayi mata tace '' to sai an jima domin sauri nake ina da a bin yi..,
sosa kai Nana tayi tace '' yumna ya maganar tafiyar mu makka.?,
chak yumna tayi ta juyi tace '' tana nan ba fashi ki nemo kudin tafiya ARLIT domin acan agent din na'ima yake da zafi zafi ake bugar karfe gwara muyi da gaske dan naga yan hassada sun soma tu somu a gaba yawa wanda nace zan tafi yawan karuwanci kowa aibata garin nan yake kai Allah isaka ranar lahira muna ɗaya daga cikin yan kallo, domin wallahi Ubangiji bazai bar masu yiwa garin manzo sharri ba.,
farantin ta ta sauke ƙasa tace '' amin ya Allah nima fa abin ya soma ban mamaki har kura ita ce zata cewa kare maye yanzu fa'iza tana nan mene bata yi, naga kwana ki bayan tafiyar ki da kika zo kika tarar damu muna kallon wannan video har kika ce ba kyau to wallahi ce min tayi mu gwada ba kunya ta dinga taɓa min abubuwana har sha tayi.,
zaro ido yumna tayi tace '' ke nana bana son sharri mayya ta zama kome..? me ta taɓa miki..,
kauda kai nana tayi tace '' kema yumna kamar ba wayis ba so kike a dinga fadar abu gatsal ba sakayawa..,
kai yumna ta jinjina daman ta gane kawai so take ta ƙara tantance wa domin tasan wanne kalar ɗiban albarka za tayiwa fa'iza ajiyar zuciya ta sauke tace '' to na fahimta kuma yanzu dai bani da wani lokaci da a yau naso ma na tafi amma abu ne samu ba dan haka zan bari sai gobe, gwara muje ɗiban yan aiki da za ayi a saka mu a sahun gaba kar duk a cike guri me dan malasa.,
daukan farantin ta tayi ta dora aka tace '' wallahi kuwa gwara muma mu samu guri me dan danshi kai Allah ya kai mu ranar da yau zan wayi gari a garin manzo sai naje naga ka'aba wallahi..,
dariya yumna tayi ta limshe ido tace '' amin ya Allah wallahi har na gano ni a makka..,
lah lah lah ba malam ya hanaki wannan maganar tafiyar ba wallahi sai na faɗa mai cewar shamsiyya da sauri yumna ta juyo tace '' kutumar ubancan lallai yau zan ɓalla ƙasusuwan ki wallahi sai na ladabtar dake ko wani kika ga yana Magana ba ki baza ki ƙara saka mai baki ba a cikin zancen sa dan uwar babar ki .,
kafin kace me tuni shamsiyya ta ci kafar kare ta arta a guje da gudu yumna ta bi bayan ta , still bata ajiye kazar nan ba shaf ta manta da ita ma kawai ƙoƙarin kama shamsiyya take wani uban birki ta ja a kofar gidan su ganin wata iriyar mota har daukan ido take tasan dai malam bashi da wasu yan uwa masu kudi
dan haka momy ce ta zo ganin ta farin ciki ne ya kamata ganin faduwa tazo dai-dai da zama da sauri ta shiga cikin gidan nasu ta ajiye kazar inna Hadiza a soro.
kaza ta azabtu kasa motsi tayi sai ta rakube guri ɗaya gaban yumna ne ya fadi ta dungure ta da kafar ta batai wani motsi ba tasan shamsiyya sarai ta ga kazar inna a hannun ta amma ai ba zata rasa abin da zata fadi ba dan haka ta shiga cikin gidan Inna Hadiza da sauri tace '' yumna ance ke kika daukar min kaza ta..,
zaro idanuwanta tayi tace '' gata can ganin ta nayi yara suna ƙoƙarin kama ta shine na ci ubansu na dauko ta na ajiye miki ita a zaure..,
bata tanka ta ba , ta nufi hanyar zaure ita kuma yumna shiga cikin gidan tayi tana zare ido can ta hango momy a guje ta ƙarasa gurin ta tare da rungume ta cikin farin ciki tace '' mommy dani zaki tafi ko..?,
murmushi tayi tare da gyara mata zama a kan cinyar ta baba lami tace '' yumna baki iya gaisuwa ba ne katuwar ki da ke zaki hau mata kan cinya..?,
Murmushi momy yusra tayi tace '' ah barta bakomai kuruciya ke damun ta.,
taɓe baki baba lami tayi ta ci gaba da aikin iza wutar ta indai yumna ce ba'a ci mata alwashi shege ba bakon mutum ɗaya bane dan haka zata koya mata darasi ne kala kala.
tashi yayi yace '' mommy zan fita waje naga nan ba network zan kira ahlam ne naji ya jikin nata.,
ɗago kai mommy tayi tace '' hmmm har yau ka kasa fahimtar wace ahlam Allah dai ya fahimtar da kai so ya rufe maka ido.
ƙasa cewa komai yayi ya zura wayar sa a aljihu yace '' mommy sai kin fito.
kallon mamaki take mai tace
''juraij baka ga yar uwarka ba ne ko magana bakai mata ba ,
zaro kuɗi yayi a aljihunsa yace'' ungo ki bata ,
ƙin amsa tayi tace '' maganar kudi nayi maka ce wa nayi baku gaisa ba yanzu ko bayan raina ba zaka iya ci gaba da rike amanar da aka bar min ba yumna marainiya ce bata taso ta san daɗin uwa ba taso na riƙe ta amma mahaifinta yaƙi.,
zama yayi a zahiri yarinyar ta bashi tausayi amma da ya tuno zuwan sa da yayi lokacin da mommy ta aiko shi ya zo ga gane mata ya take ita lokacin bata kasar nan yazo ya tarar taci kwalar wani namiji suna bawa hammata iska ta rufe idon ta yasan cewa bata da mutunci,tun daga nan ya gane yarinyar bata da wata isasshiyar tarbiya cikin deep voice din sa yace '' ya karatu ..?,
sosa kai tayi ta ɗauke fuskar'ta, haka kurum taji ta tsani wannan mutumin bata son rainin hankali ita kuma ta lura halin sa ne kamar ma wani gani gani yake mata waishi gashi me kudi to ai itama ta dauki hanyar yin kudin sai ma ran da yazo ya ta rushe musu gidan su tace '' Alhamdulilah an ma bamu hutu.,
oh Allah ya temaka ya faɗa yana ficewa daga dakin zamewa yumna tayi tace '' mommy zan biki..zaki tafi dani.,
kama kumatun ta tayi tace '' yumna me zai yana idan dai malam ya yarda sai na tafi dake.,
kalar tausayi ta mai da fuskar'ta tace '' mommy.,
na'am yumna ta fadi haka cikin kulawa da nuna soyayya
yar kwalla yumna ta ta share tace '' mommy bana son auren nan malam yace dole sai an yi ni wallahi bana son sa nafi so nayi karatu ina so naci gaba da karatuna.,
ba karamar damuwa mommy ta shiga ba tabbas ilimi me zurfi yana da kyau amma me ya malam zai tauye burin yarsa bayan yasan amfanin karatu duk wani mataki da ta taka ilimi ne ya ja mata ajiyar zuciya ta sauke lokacin da ta gama tunanin tace '' yumna bani da ikon dakatar da mahaifinki amma zan faɗa mai idan ya yarda shikkenan, amma ba auren bane illa inhar mijinki zai barki Alhamdulilah sai ki ci gaba ba wani abu bane mata nawa ne suke karatu suna gidan maza je su idan har ka saka kanka za kayi Allah zai dafa maka.,
kwalla ta kara sharewa ta kifa kanta a kan gwuiwar'ta tace '' shikkenan ni yanzu bani da gatan da za'a iya tsaya min na zama duk abin da nake son zama bana son sa wallahi idan na aure shi zan kashe shi ne na kashe kaina..,
zaro ido mommy tayi da sauri ta tashi ta fita leƙawa waje tayi cikin Sa'a ta tarar da malam tare da juraij suna hira sallama tayi cikin sakin fuska malam yace '' a'a badai har zaku tafi ba , ba zaku bari a gama sanwar rana ba..?,
zama tayi tace '' malam ba yanzu za mu tafi ba , yanzu ma tasowar da nayi wata babbar magana ce ta taso dani..,
cikin mamami malam yace '' Allah ya saka lafiya,
murmushi tayi tace '' lafiya ba lafiya ba malam akan maganar auren yumna ne.,
ganin yayi shiru yana sauraren ta, ta ci gaba da cewa tace min wallahi idan har aka aura mata shi saita kashe shi ta kashe kan'ta malam kai malami ne kasan illar yiwa yara auren dole zamanin da da yanzu ba ɗaya ba , yanzu idan muka matsa lamarin ya ɓaci azo ana dana sani..da tace min karatu take son yi da nace mata mace tana da aure tana karatu ba wani abu bane sai ta saka kuka tace ba zata iya zama dashi ba zata kashe kanta ta kashe shi ne.
gyara zama yayi jikin sa yayi sanyi be san me yumna take son zama shi kuma irin tashi ƙaddarar kenan yace
''hajiya Rahama duk na fahimci abin da kike so na fahimta amma kinsan ba saboda haka tace ba zata auri yaron nan ba saboda ta tafi Makka aikatau ne , me take so duniya tace min na hana almajirina auren ya'ta lamarin yumna sai addu'a amma tun da haka ta zaɓa shikkenan magana ta ƙare zan bashi wata daga cikin ya'ya na ita kuma tai abin da taga dama tun da abin har yakai da za tayi kisan kai ina neman tsari bama iya zuri'a ta ba gaba ki ɗaya zuri'ar al'ummar musulmi.,
innalillahi wainna ilaihir raji'un aikatau
Cikin takaici yace '' wallahi aikatau irin su yumna fa aurar dasu shi ne masalaha idan yaro kaga yana da alamun rashin ji yi addu'a Allah ya fito mai da miji yayi aure shine babban hutun mutum sai kuma ka bishi da addu'a shi yasa kika ga nace bazan janye ba amma tunda tayi wannan maganar shikkenan na hakura amma ta sani ba inda zata ,
shiru mommy tayi sannan tace '' wallahi na rasa abin da zan ce tabbas zancen ka gaskiya ne irin haka auren shi ne mafita .,
cikin takaicin halin yumna malam yace
''yauwa yanzu wacce shawara kika yanke a fasa ko kuma ayi ina tsoron randa yumna zata zamar dani karamin mutum da wanne ido zan kalli mahaifan yaron nan nace yar ciki na kasa tankwara ta tabi abin da nake so, bayan da tana son shi bani na haɗa su ba tambayar ta nayi shin kina son sa tayi shiru tana jin kunya me to kinga kenan tana son sa banyi kasa a gwuiwa ba na saka yar uwarta nazeefa ta tambaye ta tace eh tana so to yanzu kuma ɗan ita ce uwar mu sai tace ta fasa wallahi wannan maganar kisa da kikai ba ƙaramin daga min hankali tayi ba amma bakomai zan faɗawa Allah, Ubangiji ya shige mana gaba‚‚
mommy tace '' to shikkenan malam duk hukuncin da ka zartar yayi dai-dai tabbas ba ita ta haifi kan'ta ba dan haka dole tabi abin da aka ga ba illa bane ba Allah ya daidaita lamarin.
malam yace'' amin ya Allah..,
duk wannan maganar da suke juraij yana zaune yana danna waya ko tari me ba kamar ma ba ya gurin,
tashi mommy tayi tace '' malam ka huta lafiya zan shiga daga ciki..,
to Hajiya Rahama
cewar malam
bayan tafiyar malam ya tashi yace '' juraij bara na saka a kawo mana ruwan alwala lokacin sallah yayi.,
ajiye wayar sa yayi ya duba agogo yace ''eh wallahi lokaci yayi.,
wani almajiri malam ya kirawo ya shiga cikin gida ya kawo musu ruwan alwala ba jimawa sai ga almajirin malam ya dawo da ruwa amsa sukai suka fara alwala bayan sun idar malam ya shiga Masallaci domin tada Sallah gaba ki ɗaya masallacin ya cika da al'ummar musulmi domin gabatar da sallar la'asar.
wannan kenan.
cikin gida kuwa tun da mommy ta dawo take wa yumna faɗa kamar gaske duk abin da take fadi tana binta da to ganin lokacin sallah yayi yumna da take haɗa salla tayi tace '' mommy an kira sallah..,
mommy tace '' Allah yayi miki albarka yar gidan mommy.,
amin tace tana tashi ta fita bayan ta zuba musu ruwa a buta ta leko dakin tace '' mommy na zuba miki ruwa..,
nan ma albarka ta saka mata ta taso tayi alwala baba Hadiza sakar baki tayi yau wacce rana yumna na sallah akan lokaci lallai aljanun yumna shu'umai ne.
ta kuwa ɓangaren zuciyar yumna bawai ta amshi auren bane a'a akwai wata a ƙasa dole za ta hakura amma ko sati uku bata iya tunanin za tayi a gidan Mamman ba tare da ya bata takardar ta ba idan ta zama bazzawara tana da ikon yin komai ba me hanata bata hangowa kanta wata illar abin da zata aika ba ita kawai cikar burin ta take nema burinta ya cika a saka ta a matsayin na manyan mata masu amsa sunan su mata .
dole ta cika burinta ta ko wacce hanya jin an dafa ta da sauri ta ɗago daga duniyar tunanin da ta lula tace '' mommy..,
hannun mommy ta miƙo mata ba gardama ta miko mata ta riƙe ta suka shiga daki bayan sun idar da salla mommy tace '' yumna tunanin me kike ɗazu ki sakawa zuciyar ki hakuri komai sai kiga ya zama tarihi ki zama tamkar mahaifiyar ki ba ruwanta magana ma bata dame ta ba Allah ya kai rahama kabarin halima wallahi matace ta gari.,
kwalla yumna ta goge tace '' amin ya Allah insha'Allahu zanbi abin da kika ce.,
yauwa yar albarka ta faɗa tana buɗe jakar ta kudi ta dauko masu yawa ta bata noke ka faɗa tayi tace '' biki zanyi hutu fa muke yi..,
to jeki ki faɗawa malam sannan kuma ki bashi hakuri.
da sauri ta tashi ta fita akan igiya ta dauki mayafin'ta ta fita waye har yanzu yana kan tabarmar sa sallama tayi tamkar wata mumina malam da ya riga ya karan ce ta tsaf ya dauke kansa zama tayi tai shiru ta matsai kwallar karya tace '' malam dan Allah kai hakuri ka yafe min na dena wallahi zan zauna dashi yau ba mamman ba ko wani kace na aura zan aura mommy tai min wa'azi naji na ɗauka duniyar nan nawa take idan yau mune gobe ba mu bane dole sai muna sakawa zuciyar mu hakuri muna koyi da halin annabawa zan rungumi kaddarata.
dan shiru malam yayi yana auna kalaman ta anya kuwa ba da wata a ƙasa ba yafi kowa sanin halin yumna ita din kaska ce sannan da musa ce bata ladabi a banza yace '' yumna anya kuwa..,
hawaye ta matso dakyar ta share fuskarta tace '' wallahi malam da gaske nake karka kasa shakku akan komai Ubangiji ke shiryar da bawa a lokacin da ya gadama a kuma lokacin da ya so dan girman Allah ka yafe min shima zan bawa mamman hakuri komai ya wuce mu dawo kamar da.,
shiru yayi yana ƙara nazarin maganar ta anya kuwa ba wasan kwaikwayo za tai mai ba yumna fa yumna fa karfa ya sakan kance ta zame mai yar kunama yace '' to Allah ya yafe mana baki ɗaya ..,
amin ya Allah malam dan Allah ina so nabi mommy daman ai na ce maka idan akai hutu zan je kaga tun bikin da tayi ban ƙara zuwa ba