x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - LIFE PARTNER

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 73416 words

Category: Love Stories

Views 346

17 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
zaune gaban Umma tana mata bayanin inda taga Yusuf, Umma ta numfasa ta ce "To ke a ganinki wajenwa yaje?" Anty Khadijah ta ta6e baki ta ce "Ina xan sani Umma, ai badan CMD ya kirani ba wallahi saina shiga dakin, kuma abin haushi dana gama aiki naje room din na samu ba kowa ciki" Umma na jijjiga kafarta dake kan kujera ta ce "Bari dai yazo, nasan maganinsa kuma" tana rife baki sai gashi ya shigo da sallama, duk cikinsu babu wanda ya amsa, Anty Khadija ta wani hade rai ta juya kai gefe, a hankali ya karaso cikin parlorn ya zauna kan sofa ya ce "Sannu da gida Umma" sai a sannan ta kalleshi ta ce "Ai da wucewarka kayi Yusuf, how many times kake diban kafafuwanka kabar gidan nan ba tare da kaje ka gaisheni ba, sai yanzu zaka wani zubamin jaar fuskarka kacemin sannu da gida, gadin gidan nakeyi?" Tinda ta fara magana kansa na kasa, sai da yaji ta dasa aya ya dan dago kansa ya ce "I'm sorry, almost sometimes banasan naje kina bacci ne na tasheki shiyasa, amma insha Allah bazan kara ba i apologize" Umma taci gaba da taunar chewing gum dinta ta ce "Inaso kuma ka fara hada lefe, saika turomin kudi ta account dina" Cikin sauri ya dago kansa yana kallanta ya ce "Lefe kuma Umma, ni ban tsayar da matar aure ba har yanzu" Umma ta dalla masa harara ta ce "Jiddan uban waye yace yana santa?" Yusuf ya gyara hulan kansa ya ce "It's before Umma, but ni yanzu bani da ra'ayin aurenta, sabida she isn't my type" Anty Khadija ta juyo tana kallansa ta ce "Kama samu zata aureka kenan? Kai har kanada hurumin za6ar matar aure, kaida kake fama da ciwon zuciya mutuwa ko yau ko gobe" nunata Yusuf yayi da yatsa ya ce "Enough Khadijah, don't let me show u d bad side of me, i Yusuf don't fight, but idan kika kara shiga rayuwata i swear to almighty Allah u will regret" daga haka ya kalli Umma ya ce "Saida safe Umma" Umma data hangame baki tana kallansa ta ce "Lalalala karka sake ka kirani da Umma dama, ai zaifi maka ka kirani da Fatima sunan da ubana ya rada min, Khadijan daka fada Aisha ka kira baka saya ba, shekara biyu ta baka a duniya idan baka sani ba yau ka rubuta ka ajiye, wawa kawai" ba tare daya juyo ba ya shige dakinsa ya rufo kofar, Anty Khadija da ranta ya gama 6aci ta mike zata nufi kofarsa Umma ta rikota ta ce "Sa ido kiga ikon Allah Dije, maza kwantar da hankalinki" cije baki Anty Khadija tayi ta koma ta zauna tana huci tana huhhuro hanci.

_Two week ltr_
Rafi'ah ce kwance a gefen Abba tana fada mishi abubuwan da zatai na saukarta, Abba ya dan kalleta yana shafa kanta ya ce "Bafa aure bane Mamana" ta dan turo baki cikin shagwa6a ta ce "But Abba ya kamata amin duk abinda nace gaskiya, nice fa first born dinka" yana murmushi ya ce "Kuma Mamana hakama, to kimin list din duk abinda kikeso" ta washe baki ta ce "Insha Allah, i will do so when i have time" Abba ya ce "Good, are u not celebrating world heart day today?" Ta mike zaune tana kallan Abbannata ta ce "I am Abba" ya ce "What have u done for the day?" Ta saki murmushi tana kallansa ta ce "Nayi addu'a Allah ya bani lafiya, dama duk wanda yake suffering da wannan ciwan, and i thank God for giving me such a loving parents like you, i love u Abbana" daga haka ta rungumeshi, Abba ya shafa bayanta gentle ya ce "Allah ya miki albarka ya kuma baki lafiya, but i think u have to go and celebrate there" ta zame jikinta a nashi ta ce "Zanje Abba, ina jiran Ummi ta dawo a office, because i can't leave you alone" Abba yaja hancinta yana dariya ya ce "Thank u mother, zo ki gayamin me ake a taron naku idan kunje" ta gyara zamanta ta ce "Firstly we introduce ourselves but not all, after then ana bada shawarwari akan yadda mutum zai kula da kansa sabida kar yana samun attack sosai, da kuma what medicine to take idan ka samu attack, after then u rushed for emergency, but the main abinda ake ta fada is heart rest, anaso a kullum mutum ya dinga nutsuwa ya daina sawa kansa damuwa da yawa" Abba ya bata side hug ya ce "Excellent, i hope kina bin duk abinda aka fada?" Ta daga masa kai ta ce "Sosai ma Abba, i really enjoyed this day in life that's 29 of September" Abba ya bata light kiss a forehead dinta ya ce "Proud to have u daughter, gobe insha Allah zan kaiku gidan Umma tinda yanzu kinji sauki sosai" Rafi'ah ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Do u mean gidansu Anty Amina?" Ya ce "Of course, Ita kadai ce uwar data ragemana a yanzu" Rafi'ah ta kwantar da kanta akan shoulder dinsa ta ce "Allah ya jikan Baban Kaduna" Abba ya ce "Ameen" ta dago kuma tana kallan Abba ta ce "Wai Abba da Babanka da Umman Anty Amina waye babba?" Ya ce "Babana ne babba, sai Baba Mu'azu sai kuma Umma" Rafi'ah ta ce "Ohk, i was thinking itace Babba fa" Abba ya girgiza kai ya ce "No, just because she a female".
Karfe 3 da rabi Ummi ta shigo gidan, a tare suka amsa sallamarta, Rafi'ah ta mike tayi hugging dinta tana mata sannu da zuwa, Abba ya kalleta ya ce "U are welcome, but u look so tired Ummu Rafi'ah" Ummi ta danyi murmushi ta ce "Na gaji kam, yau nayi lectures biyu two~two hours, after then mukai meeting sai to 3 muka fito" Abba ya mata sannu sannan ya mike yana kallan Rafi'ah ya ce "Call Abdul for me, it's time for prayer" Rafi'ah ta nufi dakinsa tana fadin "Tin da muka dawo a school yau Abdul yake bacci, wallahi Ummi babanki ya zama kasa" Ummi ta dalla mata harara ta ce "Be careful with me" dariya sosai take ta shige dakin Abdul ta hau kan gadon ta dinga mintsilinsa a baya tana ya tashi, da kyar ya mike ya shiga toilet sannan ta fito tana dariya ta ce "Ummi yau 29 of September, zanje taron heart day" Ummi ta ce "But not alone, Mustapha ya kaiki ya jiraki, sannan karki yarda magrib yayi maki a titi" ta ce "To insha Allah, in kawo maki abinci?" Ummi ta girgiza kai ta ce "I want to bath first" Rafi'ah ta nufi upstairs zuwa dakinta ta shiga wanka, ba dadewa ta fito shafa body lotion sannan tasa peach din doguwar riga, kanta ta fara combing tana ta aush tana 6ata rai kamar an sata dole, bayan ta gama ta saka scarf sannan ta yafa veil din rigar tayi simple make up, woooow!!! fans just say masha Allah here, the beauty can't be describe in one sentence, saina gama page dinma ban gama gaya muku irin kyau din datai ba loooool, turare masu kamshin gaske ta fesa sannan ta dauki flat shoe ta saka ta dauka small side bag ta jefa phone dinta da tissue a ciki sannan ta fita. Tana saukowa downstairs ta samu Ummi zaune nan inda ta barta, ta danyi murmushi ganin kallan da mahaifiyarta ke mata ta ce "Nasan nayi kyau ko Ummi?" Ummi ta maida hankalinta ga TV ta ce "Karki kai magrib Rafi'ah, fatan kuma kinyi sallan la'asar?" Ta ce "Insha Allah Ummi bazan kai magrib ba" Ummi ta ce "Sallan fa?" Ta ce "I'm on period" daga haka ta nufi kofa ta ce "Saina dawo" Ummi ta ce "Allah ya tsare" da Ameen ta amsa sannan ta fita ta kullo kofar, a parking lot ta samu Mustapha yana ta goge mota, yana kallanta ya washe baki ya bude mata back seat ya ce "Kaga turawan asali, Gaskiya Hajiya karama saurayinki yaji dadi, koda wannan kyan aka barshi yaci nasara, bare aje ga hankali, nutsuwa, kyauta, mutunci ga kuma kin fito gidan manya" Rafi'ah couldn't hold her laugh, ta dinga dariya kafin ta ce "Nikam naji dadina da wannan zancen" Mustapha ya ce "Allah kuwa gaskiya nake fada miki hajiya karama, sai wani walkiya kike kina haske ido" Ita dai dariya kawai take yaja motar suka fita a gidan.
15 minutes ya kaisu inda zasuje, bayan yayi parking Rafi'ah ta fito tana kallansa ta ce "Ka jirani anan, ba dadewa zanyi ba" ya duka cikin girmamawa ya ce "An gama kyakkyawa" daga haka ta juya tana dariya ta shiga cikin hall din, everywhere is silent sai muryar mutumin dake kan stage yana magana da loud speaker, Rafi'ah ta samu seat ta zauna ta maida hankalinta gun mai maganar, shawarwari sosai ya bayar ga masu fama da ciwan zuciya, kusan minti 10 yana bayani sannan yayi musu fatan alkhairi ya bayar da loud speaker, mutumin daya kar6i loud speaker ya danyi karin bayani sannan ya kira Doctor Yusuf akan shima ya fito ya bada tasa gudummawar a matsayinsa na likita kuma mai fama da wannan cuta, cikin light steps Yusuf ya karasa kan stage din ya kar6i loud speaker, shadda ce fara ajikinsa tsaha aiki sai hula baka da half shoes dinsa baki, daga hannunsa kuma kana iya hango wristwatch dinsa black colour sai zoben azurfa dake kyalli a yatsarsa ta tsakiya, cikin sweet voice dinsa yayi wa kowa sallama sannan ya fara bayani da english kamar haka "If you are opting to celebrate this day, it is important to try and be more attentive to your own heart health. There are a number of different ways that you can do this. This includes following a healthy diet, quitting alcohol, stopping smoking, and getting involved in physical exercises..." The hall is so quite harya gama bayaninsa in his good and meaningful English, bayan ya gama ya mikawa na gefensa loud speaker sannan ya sakko akan stage din, daga haka the audience break into rapturous applause. Saurin mayar da kanta gefe tayi ganin ya nufo inda take, bayan ya karaso yaja kujera ya zauna yana kallanta ya ce "Hy" ba tare data juyo ba ta ce "Why not salamu alaikum?" Yusuf ya shafa beard dinsa yana kallanta ya ce "I'm sorry, Assalamu alaikum" ta danyi murmushi ta ce "Wa'alaikumus salaam" ya ce "How are u?" Ta ce "I'm fine and u?" Ya ce "Alhamdulilah also" tayi shiru tana kallan mutum dake bayani akan stage, Yusuf ya ja chair dinsa kusan nata ya ce "Is that all for d greeting?" ta ce "What again? Naga ai mun gaisa" ya girgiza kai ya ce "Actually no, wannan karan shine na hudu da muka hadu, i think we have to introduce ourselves to each other" Rafi'ah ta danyi murmushi ta ce "Ok, but u start" ya ce "Noo, u start" ta dan turo baki sannan ta ce "Ai kasan sunana" ya ce "Amma kuma na manta" ta dan harareshi ta ce "Ohk Sunana Yusuf Muhammad, I'm the first born of the family, kanina guda daya sunansa Abduljalal, my father works with CBN in Abuja, mother is a lecturer, i'm in SS2 now, ina hadda 5 a islamiyya, Abbana dan Kaduna, shi kadai iyayensa suka haifa, Ummi na kuma 'yar nan Kano ce, su biyu a familyn su ita da yayarta Anty Halima, she is living here in kano also, amma bata ta6a haihuwa ba, Matan Abbana guda biyu ne, so i think this should be my brief history" Yusuf ya saki murmushi yana kallanta ya ce "Nice to meet u Yusuf, hope u are ready to hear mine?" Ta daga masa kai tana murmushi, ya ce "As u know sunana Fatima Muhammad, but they do called me Rafi'ah, ni kadai iyayena suka haifa, sun rasu ta dalilin accident when i was 18 then, lokacin dana gama secondary school dina, both Father and mother are from kano, i did my first degree in Dubai where i studied Medicine, and then goes for PHD where i specialize in Pediatrics, i'm now staying with my father's sister and her daughter, Ammina ma su biyu ne agidansu, akwai sister dinta dake unguwar rimi" Rafi'ah ta sauke ajiyar zuciya jin iyayensa duk sun rasu, a hankali ta ce "Allah ya musu rahama" ya ce "Amee, Can u pls help me with your digit?"...


_More comments is needed pls, let me see how much u appreciate the book SHARIK HAYATI_

*Join my Facebook grp @Real~Teemarh fans*

*Follow me on wattpad @Real~Teemarh192*

*SHARIK HAYATI*

_08103810398_
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_17~18_

A hankali Rafi'ah ta dago kanta ta kalleshi, tayi saurin dauke idanta ganin kallanta yake, Yusuf ya gyara hulan kansa yana kallanta ya ce "Ko bazaki bani ba?" Still kanta na kasa bata ce komai, ya ce "Fatima" ba tare data kalleshi ba ta ce "Na'am" ya ce "Won't you give me?" Juyowa tayi ta dauka phone dinsa dake kan table ta rubuta masa digit dinta sannan ta ajiye wayar, ya dauka yana murmushi yayi dialing phone din, ba jimawa wayarta dake cikin jaka ta fara kara, Yusuf yayi hanging call din yana kallanta ya ce "Thank u much" ta ce "U are welcome" mikewa tayi ta dauka side bag dinta zata wuce yayi saurin riko hannunta, tsayawa tayi cak ta kasa juyowa, ya sake mata hannunta ya ce "Won't u say bye" a hankali ta ce "Sai anjima" ya ce "Ki zauna kici abinci gashi suna kawowa" Rafi'ah ta girgiza kai ta ce "I'm ok" ya mike yana kallanta ya ce "Let me drop you" ta ce "Tare nake da driver" Yusuf ya ce "Ohk safe, Allah ya kaiku lpy" a hankali ta ce "Ameen" daga haka ta kama hanyar fita a hall din, tsayawa tayi jin sunanta daya sake kira, ya karaso inda take tsaye ya ce "Naga mood dinki ya canza, hope ban maki komai ba" ta girgiza kai a hankali ta ce "Not at all, i just want to rest" daga haka tayi gaba ta barshi tsaye a wajen. Tana isa parking space Mustapha ya bude mata back seat ta shiga ta zauna shima ya shiga mazauninsa ya ja motar suka wuce, tinda suka fara tafiya Rafi'ah ta limshe idanuwanta ta jingina da kujerar motar kamar dai me bacci, a zahirin gaskiya kuma labarin Yusuf kawai take tunawa, duk sai taji tausayinsa deep down her, tin yana kamarta kenan ya rasa iyayensa duka biyu kuma at the same time, hawaye masu zafi taji sun sakko mata, tasa gyalen jikinta tayi saurin gogewa, daga haka ta maida fuskarta jikin window tana kallan mutane. Suna isa gida ta fito a hankali ta shiga ciki, ba kowa a parlor sai karar Fan dana TV, ta wuce upstairs tana kiran sunan Ummi, a bakin kofa suka kusan cin karo, Ummi dake kallanta ta ce "Lafiya kamar an jefo ki?" Veil dinta ta cire ta ce "Lafiya kalau, Ina Abbana?" Ummi ta ce "Ya fita dazu, ya taron?" Silently ta ce "It was fine" daga haka ta wuce dakinta ta rufo kofa.
Da daddare Rafi'ah na kan dinning tana cin indomie data dafa, Abba ya kalli Ummi dake yayyanka Mango ya ce "Why is Abdul don't want to stay with us always? I have been monitoring him since, sai yayi ta zama a daki what's the essence?" Ummi ta ajiye knife din hannunta ta ce "Kasanshi da san kallan ball, yanzu haka yasa laptop a gaba yana kai" Abba ya girgiza kai baice komai ba, bayan ya gama shanye mago dinsa ya mike yana kallan Rafi'ah ya ce "Mamana Good night" ta dan turo baki ta ce "Night" Abba ya ce "What again, bakyaso na tafi ne?" Ta ce "Bayan gobe zaka koma kuma yauma saika tafi caan ka kwana" Abba ya ce "I'm sorry mother, i'm spending the night there, hope ba komai ko" daga masa kai tayi sannan ya kalli Ummi ya ce "Sai da safe Madam" ta ce "Allah ya tashemu lafiya" daga haka ya fita ya jawo musu kofar, Tashi Rafi'ah tayi ta dawo kusa da Ummi ta ce "Mummy fa yau saura sati 2 ta dawo ko?" Ummi ta ce "Hakane" Rafi'ah ta ce "I'm eager, cewa tayi fa gidanta za... " shiru tayi jin phone dinta na ringing, ta karasa wajen TV stand ta dauka wayar, Ummi dake kallanta ta ce "Who's that?" A hankali ta ce "Salmah ce, inaga maganar assignment din nan ne" daga haka ta nufi upstairs Ummi ta bita da kallo, tana shiga dakinta tayi picking call din ta kai kunnenta hade da sallama, on the other side Yusuf ya ce "How are u?" Ta zauna gefen gado ta ce "Fine, how is everyone?" Ya ce "Kowa lpy, hope kin isa gida safe?" Ta daga masa kai kafin ta ce "Sure" ya ce "Masha Allah" shiru tayi bata sake cewa komai ba, caan ya dan sauke ajiyar zuciya ya kira sunanta, silently ta amsa idanuwanta a limshe ya ce "When is ur marriage?" Rafi'ah ta zaro ido sai kuma ta ce "Aure kuma?" Ya ce "Ehh, ko baza kiyi inviting dina ba?" Ta danyi murmushi ta ce "Ba rana" Yusuf ya ce "Why, duk samarinki kice ba rana" dariya ta danyi har yana jiyota kafin ta ce "Nikam banida samari, im still young, SS2 fa kawai nake" ya bude eyes dinsa dake limshe ya ce "I disagree, kina da samari da yawa heart dina tamin searching na gani". Dariya
End Ads