mike ta ce "Abdul fa?" Ummi ta ce "Yana dakinshi" upstairs ta wuce tana murmushi ta ce "Let me see Abba first" tana shiga dakinsa ta sameshi yana zaune akan stool, Abba yayi murmushi ganinta ya ce "Is this my Mum?" Itama murmushi tayi ta zauna a kan carpet ta ce "Ina kwana Abba" ya ce "Lafiya kalau Mamana how are u and everyone?" Ta ce "All fine Abba, tare muka zo amma kanshi na ciwo shine ya wuce gida" Abba ya ce "Subhanallah, i will call him ltr, Allah ya sauwake" ta ce "Ameen" mikewa tayi ta ce "A huta gajiya Abba" ya ce "Alright Mother" tana fitowa a dakin ta shiga dakinta, yana nan yadda ta barshi sai kamshi yake, ta kwanta akan gadon tana murmushi ta ce "I missed u bed" daga haka ta mike ta fita a dakin ta sauko kasa. Abdul na gefen Ummi yana taya ta arranging papers, ya dan zaro ido ya ce "Anty" ta rungumeshi ta ce "Ya kake, tashi min a gefen Ummina" dariya Abdul ya dinga yi yana kallanta ya ce "Ai ke mun kyautar dake, yanzu ni kadai ne ko Ummi?" ta shafa kansa ta ce "Exactly Babana, tashi dai ka bata wajen tinda ita bakuwa ce" turo baki Rafi'ah tayi jin ance mata bakuwa, Side hug Ummi ta mata ta ce "So ya kuke, i hope everything is going fine?" A hankali ta Jinginar da kanta ajikin mahaifiyarta ta ce "Lafiya kalau, amma ba shida lafiya ne" Ummi ta ce "Subhanallah, meya sameshi?" Cike da damuwa ta ce "Ciwan kaine, dama fa akan da yamma idan yazo daukana zamuje gidan Mummy" Ummi ta ce "Ki bari next time sai kije kawai" a hankali ta ce "Toh, mai aiki kika dauka Ummi?" Ta ce "Ehh, ko karna dauka" Rafi'ah tayi murmushi ta ce "A'a ai aiki zai maki yawa" Ummi tayi murmushi tana shafa kanta ta ce "I hope bakya saan jikin ki nan" ta ce "Noo, da sassafe nake komai Ummi" Ummi taja hancinta ta ce "Good kici gaba da haka kinji first born, watarana zaki ga amfaninsa" a hankali ta ce "Insha Allah" daga haka ta mike ta wuce kitchen.
Da yamma Rafi'ah na zaune a dakinta duk ta shiga damuwa, ta kira Yusuf yafi a kirga amma ko daya baiyi picking ba, bude kofar dakin akai, tayi saurin juya kanta saboda idanta duk yayi jaa sakamakon kuka data yi, karasowa kusanta Ummi tayi ta ce "Idan bazaki tafi ba in kira Abbanki in fada masa, sau uku ina aiko Saudatu ta kira ki amma kinyi zamanki" mikewa tayi a hankali ba tare da kalli Ummi ba ta dauki Hijab har kasa cikin sauran kayanta sannan ta nufi hanyar fita, Ummi dake kallanta ta ce "Wait Fatima, wani abu na daminki ne?" A hankali ta girgiza kai, Ummi ta ce "Toh Allah ya kiyaye kije Mustapha ya kaiki, Abba kuma kya kirashi dan dawowarsa sai dare" slowly ta share hawayen daya sakko mata, ga zafin barin gida, ga damuwarta na halin da Yusuf yake ciki, gani take kamar yana nan kwance ba lafiya, cikin muryar kuka ta ce "Allah ya dawo dashi lafiya, na tafi" cike da tausayin Rafi'ah Ummi ta ce "Allah ya kiyaye" daga haka ta wuce dakinta. A hankli ta sauko a stairs din ta fita zuwa parking lot ta shiga mota, Mustapha yaja motar suka tafi, har sukaje gida ba tai magana ba, sai da yayi parking ta ce "Thank u" daga haka ta fito ta shige gate. Da sauri ta karasa entrance din gidan ta murda handle din kofar, still ta tsaya tana kallan Yusuf dake kwance yayi pillow da cinyar Jiddah, tayi saurin kauda kanta duk suka bita da kallo harta wuce part dinta, tana shiga ta turo kofar ta durkusa a wajen ta fara rera kuka, kusan awa daya tana zaune a bakin kofa kafin ta mike ta shige dakinta ta rufo kofa, tana nan zaune har akai magrib ta tashi tayi alwala tayi sallah har akai isha tana zaune akan sallayar, ta mike tayi isha sannan ta dauki towel ta shiga toilet tayi wanka, tana fitowa ta samu Yusuf a bakin gado yana zaune da laptop a gabansa, sauke kanta tayi ta nufi inda kayanta suke ta dauki night dress sannan ta koma toilet ta shirya, scarf ta saka bayan ta fito sannan ta karasa gefenshi ta zauna, a hankali ta ce "How are u now?" Ba tare daya kalleta ba ya ce "Better" tayi shiru tana kallansa, dago kansa yayi suka hada ido tayi saurin sauke kanta ta ce "Dan Allah kayi hakuri idan na maka laifi Doctor" girgiza kai ya danyi kafin ya ce "How many times zance miki bakimin laifi ba, ko kin daina fahimtar magana ne" hawaye ne tap a idanta jin yadda yayi maganar, cikin muryar kuka ta ce "U never shout at me, meyasa zakamin tsawa yau" hannunta ya kamo ta matso kusa dashi ya rungumeta very light, dan bai bari sun hada jiki sosai ba, ya ce "I'm sorry, i don't know what comes over me, haushin kowa nakeji yau, especially..." Shiru yayi yana rike da ita, ta dan sake shi tana kallansa ta ce "Ni ko?" Daga haka ta fashe da kuka, matsowa yayi ya kara rungumeta sosai ya ce "Bance ba, but haushi nakeji kawai" cikin kuka ta ce "Kayi addu'a mana" ya ce "Nayi" daga haka ya saketa ya kwanta akan gadon, share hawayen idanta takeyi tana kallansa ta ce "Or is it because nace matarka bata iya magana ba da safe?" Shi dai kallanta kawai yake, caan ya mike ya dauki pillow ya koma parlor ta bishi da kallo, duk yadda taso ta hakura karta bishi kasawa tayi, bayan 30 minutes ta leka parlorn ta sameshi saman kujera har yayi bacci, a nan wajen ta sulale ta fara kuka sosai.
Washegari da sassafe ta tashi ta hada masa breakfast sannan tayi wanka, tana shigowa dakin ta sameshi ya shirya, ta danyi kasa da kanta ta ce "Good morning" kai kawai ya daga mata, daga haka ya dauki briefcase dinsa da statescope zai fita ta ce "Breakfast din yana kan dinning" ya girgiza kai sannan ya fita a dakin, bin bayansa tayi har suka fito main parlor, ya gama saka takalmi sannan ya dauki komai nasa zai fita ta ce "Doctor breakfast din fa" ba tare daya kalleta ba ya fice ya rufo kofar, Jiddah dake zaune akan dinning ta sheke da dariya, duk yadda Rafi'ah taso kar tayi kuka amma hakan bai yuwu ba, ta fashe da kuka ta koma part dinta, jikinta har rawa yake ta zube aKan gado tana kuka me cin rai. Haka Rafi'ah taci gaba da hakuri, tin daga ranar duk maganar da zatai masa sai dai ya daga kai koya girgiza mata kai sai kace kurma, amma idan da Jiddah ne sukanyi hira wani lokaci, wani lokaci kuma zai kulata amma ba sosai ba, Rafi'ah kuwa babu abinda yake hadasu, yanzu a parlor ma yake kwana indai a dakinta yake, wani lokaci tayi kuka harta godewa Allah, wani lokaci kuma tayi hakuri amma ko kadanne saita zubar da hawaye, a haka har ta cika wata daya a gidansa duk ta kara ramewa tayi farii sosai saboda damuwa, kuma koda wasa bata gayawa kowa a gida ba. Ranar Saturday da yamma tana zaune a main parlor aka fara knocking, ta mike a hankali ta karasa kofar sannan ta bude, rungumeta Khairiyya tayi ta ce "Oyoyo Anty" itama rungumeta tayi tana kallan Ammi ta ce "Sannu da zuwa Ammi" Ammi ta shigo parlorn tana murmushi ta ce "Sannu Fatima" Rafi'ah na rike da hannun Khairiyya ta ce "Have a seat Ammi" Ammi ta zauna akan kujera, zama Rafi'ah tayi a kan carpet ta ce "Ina yini?" Ammi ta ce "Lafiya kalau Fatima, fatan duk kuna lafiya?" Ta ce "Alhamdulilah Ammi" mikewa tayi ta shiga kitchen Khairiyya ta biyota, abinci ta kai wa Ammi da fruits sai dambu da Mummy ta aiko mata jiya, bayan ta gama jere mata ta dauko fanta guda biyu da cups ta ajiye mata, Ammi ta danyi murmushi ta ce "Sannu da kokari" ita dai murmushi kawai take kanta na kasa, Khairiyya ta zuba abincinta ta fara ci, Rafi'ah na kallanta ta ce "Yaushe zaki zo mana hutu?" Khairiyya ta ce "Soon Anty, muna gama exams zanzo, jss3 zan shiga fa" Rafi'ah ta danyi murmushi tana kallanta ta ce "Masha Allah, i wish u all d best"
"Shiru Rafi'ah baku zo mana ba muma bamu zo ba" dagowa tayi jin muryar Ammi, with smile on her lips ta ce "Ammi ai yanzu baya dawowa da wuri sai yamma sosai shiyasa, kuma har weekend fita yake" kafin Ammi tayi magana aka bude kofar, ya shigo yana kallansu sannan ya nemi waje ya zauna, silently ya ce "Sannu da zuwa Ammi, ina yini?" Ta ce "Lafiya kalau, yanzu nake tambayarka ai, baka kaita ba kai baka zo ba muma kuma shiru" dan shafa kansa yayi yana murmushi ya ce "Wallahi Ammi aiki ne yamin yawa yanzu, amma insha Allah zamu zo" ta ce "To Allah ya kaimu" Khairiyya na kallansa ta ce "Yaya ina yini" ya ce "Lafiya Ammina, karfa ki cinye mana abincin mu" ta danyi murmushi ta ce "Ai Anty Fatima zata dafa maka wani" kallan Rafi'ah dake zaune ya danyi sannan ya dauke kai ya ce "Sai dai ke ki dafa min ai" ta danyi murmushi taci gaba da cin abinta, Yusuf ya ce "Ammi ke ba xaki ci abincin ba?" Ta ce "Alhamdulilah Yusuf na koshi" ya ce "Sameer ya tafi ko?" Ta ce "Ya tafi Dubai sai bayan wata biyu kuma" Yusuf ya ce "Ayyah, ya sameni a office jiya ai, so munyi sallama" ta ce "Haka yake cemin, shine nace ai yau bari nazo tinda kunki zuwa" cire hular kansa yayi ya ce "Zamuzo Ammi, Jiddah taje gida za tayi kwana biyu" Ammi ta ce "To Allah ya dawo da ita lafiya, na zata ai tana ciki ta ki fitowa ne" ya dan zaro ido yana murmushi ya ce "Never, ai ba zata jiki tayi shiru ba" Ammi ta ce "Hakan kake gani" daga haka ta kalli Khairiyya ta ce "To idan kin gama ciye~ciyen ki tashi mu tafi, dan idan magrib yayi driving wahala yake min" Yusuf ya ce "Har yanzu Ammi" ta ce "Har gobe kuwa Yusuf bana samun nutsuwa" daga haka ta mike, tashi Rafi'ah tayi ta ce "Mungode Ammi" Ammi ta ce "Ba komai, sai kunzo din" Khairiyya ta kama hannun Rafi'ah ta ce "Anty sai na zo hutun" Rafi'ah ta ce "Sai kinzo" Hijab dinta ta dauka akan kujera ta saka sannan tabi bayansu, har mota suka rakasu, Yusuf nata murmushi har suka tafi, juyowa yayi zai koma cikin gida suka hada ido, sai da kirjinta ya buga tayi saurin dauke kanta, ita tama manta raban da yayi mata murmushi ko magana, kusan sati uku da kwanaki kenan, sai daya shige ya rufo kofa sannan ta shiga itama. Da dare Yusuf na kwance a parlor ta fito sanye da Hijab ta zauna gefensa, a hankali ta ce "Doctor" ya bude idanuwansa yana kallanta, ta ce "Gobe zanje follow up clinic, maganina ya kusan karewa" sauke idansa yayi a kanta ya ce "Wa zai kaiki?" Sai yau ya mata magana bayan sati uku da suka wuce, ta kauda kanta gefe hawaye taap idanta ta ce "Cab" maida kansa yayi gefe ya limshe ido, ta tashi ta koma daki tana goge hawayen idanta, dama tasan yanzu duk duniya ba wanda ya tsaneta kamar Yusuf, babu abinda yake 6ata mata rai irin rashin magana da yake mata, fashewa tayi da kuka ta jawo wayarta akan drawer zata kira Mummy, kawai kuma ta fasa ta gefar da wayar a kasa, kuka sosai take tana kiran sunan Abbanta, da tasan haka rayuwar aure yake da tin tini bata yarda da Yusuf tayi aure ba, gaba daya yanzu ta tsani kanta da komai nata, cikin kuka ta ce "Nina jawowa kaina, Ummi dan Allah ki yafemin, bansan haka zai faru dani ba, i'm tired with this misrable life na gama gajiya" shiru ta danyi jin an bude kofar dakin, ta dago kanta a hankali ganin wanda zai shigo.
*Gashi harda na jiya 🤗 Sorry for keeping u waiting.*
_08103810398_
[8/11, 1:23 PM] Zarah: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._
_By FATIMA ✍🏻_
_42_
A hankali Jiddah ta tura kofar dakin ta rufe, ta kama kugu tana murmushi ta ce "Dama duk macen da tasan inda yake mata ciwo bai dace ta shigo gidan wata ba, gashi kin shigo banda azaba babu abinda kike sha" kwashewa da dariya tayi tana tafa hannu, Rafi'ah ta kauda kanta tana share hawayen idanta, Jiddah sake cewa "Gara ki tattara naki ya naki kibar mana gidanmu kafin abu yayi tsanani, dan yanzun nan ya gama gayamin ya tsaneki fiye da kowa a duniya" tana fadin haka ta juya ta fice a dakin. Tsabar bakin ciki kasa kuka tayi ta kifa kanta akan gado numfashinta yana neman sarkewa, a hankali ta jawo wardrobe din dake gefenta ta dauko drugs dinta, bayan ta balla ta mike ta dauki guntun pure water ta hadiye maganin, komawa kan gadon tayi ta kwanta tana addu'a ko zata samu saukin abinda take ji. Washegari da tinda ta tashi ta gama abinda za tai ta shirya tana jiran Yusuf saboda clinic da zata je, shiru yana dakin Jiddah ko lekowa baiyi ba, Rafi'ah na zaune a parlor Jiddah ta fito da plate din abincin a hannunta, sai rakwarkwasa take tana murmushi, bayan ta ajiye plate din ta koma part dinta tana dariya, shiru har bayan azahar Yusuf bai fito ba, Rafi'ah dake kwance ta jawo phone dinta tayi dialing number Ameera, yana shiga ta dauka ta ce "Amarya, how are u?" Cikin sanyin murya Rafi'ah ta ce "Fine, where are u now?" Ameera ta ce "I'm at home, do u need something?" Limshe ido Rafi'ah tayi ta ce "I want to see u Khadijah" Ameera ta ce "To bari nazo yanzu" hanging wayar Rafi'ah tayi ta share hawayen idanta ta koma ta kwanta. Bayan minti 15 taji ana knocking, ta mike ta fita a dakin, tana bude kofar Ameera ta rungumeta ta ce "I missed u friend, how are u?" Murmushi kawai Rafi'ah tayi ta kama hannunta ta ce "You're welcome" daga haka suka shiga part dinta, har dakin Rafi'ah ta shiga da ita suka zauna, Ameera dake kallanta ta ce "Kinyi rama and kin kara fari, is anything wrong?" Tare hawayen idanta takesan yin amma hakan bai yuwu ba, ta rungume Ameera ta fashe da kuka ta ce "I'm tired Ameera, na gaji da zaman auren nan kuma" zaro ido Ameera tayi tana kallanta ta ce "What are u saying Rafi'ah? Indai matsalar Jiddah ce ba sai kin shiga harkarta ba" Rafi'ah ta hau girgiza kai cikin kuka ta ce "No it's Doctor, Ameera bansan da wani ido zan kalli Ummina na fada mata na gaji da auren Yusuf ba" kara fashewa tayi da kuka ta sulale kasa ta zauna akan carpet, Ameera ta sauko itama tana kallanta ta ce "Pls explain further, ban gane abinda kike fada ba". Share hawayen idanta tayi ta ce "Ameera Doctor ya tsaneni, tin satina biyu a gidan nan nake ganin ba dai dai ba, baya min magana, baya cin abincina, baya min komai da kika sani, ko dakina baya shigowa yanzu" daga haka ta fashe da kuka ta turo baki ta ce "Wannan ma shiya dama ai, ni babban damuwana daina min magana da yayi, i'm in pain Ameera, my heart is always beaten, it hurts me morethan u know Ameera" ganin yadda take kuka yasa idan Ameera ma ya ciko da hawaye, gaba daya ta shiga damuwa itama, ko a mafarki bata tinanin Yusuf zaiyi abinda Rafi'ah ta fada ba, amma gashi a zahiri tin aure na wata daya matsaloli iri iri, lallai yau ta yarda maza abin tsoro ne.
Share hawayen daya gangaro mata tayi ta dago Rafi'ah dake kuka kamar ranta zai fita ta ce "Have u tell anyone?" Rafi'ah ta girgiza kai ta ce "Noo, dan Allah karki fadawa kowa banasan hankalinsu ya tashi, and beside that inasan mijina, no matter how zan zauna dashi har karshen rayuwata" Ameera ta shiga share mata hawayenta ta ce "No Fatima, u have to tell someone ko zaki samu mafita, u can't be hurting yourself this much, bayan haka ma bakya tinanin ciwanki ya tashi" Rafi'ah ta rungumeta ta ce "Dan Allah promise me u won't tell anyone, Khadija kar ki bari wani yaji zancen nan, pls keep my secret only u Ameera" fashewa ta karayi da kuka jikinta na rawa, Ameera dake kuka itama ta ce "Ohk i promise u that i will keep this secret alone, amma meya kamata muyi yanzu?" Rafi'ah ta saketa ta fara goge hawayen idanta ta ce "U help me praying Ameera, nasan dai tinda nake ban ta6a cutar wani ba, so Allah ba zai bari a cuceni ba nima" Ameera ta ce "Insha Allah zan taya ki da addu'a, kuma zaki cinye wannan jarabawar da yardar Allah" Rafi'ah ta share mata idanta ta ce "Nagode Ameera, dama inasan in baki hand card dina na asibiti, sai ki kar6omin drugs dina, zan kira Doctor Hisham na gaya masa" Ameera ta ce "Ohk ba komai zan kar6o maki yanzu" tashi Rafi'ah tayi ta dauko hand card dinta cikin jaka ta mikawa Ameera ta ce "Zakiga office dinsa da sunansa a jiki, zan kirashi sai na masa bayani"