x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 22 - LIFE PARTNER

  • 63001 words
  • 66000 words
  • Out of 73416 words

Category: Love Stories

Views 332

17 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
nan?" Ikleemah ta daga mata kai sannan ta bata hanya ta huce, bayan sun shiga ta turo kofar ta ce "Tana ciki bari na mata magana" daga haka ta haura upstairs Anty Khadija kuma ta nemi waje ta zauna. Da sallama ta bude dakin ta shiga, Anty Rahama dake kwance tayi saurin tashi zaune ta ce "Ikleemah bance karki hawo bane, kina ganin yadda ake fama amma ke bakyajin magana" karasawa tayi gefen mahaifiyarta ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, dafe kirjinta tayi a hankali ta ce "Ammi kirjina, wayyo Allah na" cike da damuwa Anty Rahama ta rungumeta ta ce "Allah zai baki lafiya Ikleemah, amma menene na haurowa bayan kinsan nima yanzu zan sauka" silently ta ce "Anty Amina ne tayi bakuwa" Anty Rahama ta ta6e baki ta ce "Koma wacece karki kara yin gangancin haurowa ba tare dani ba, bazaki kwala min kira ba" tana rife bakinta Anty Amina ta shigo dakin da phone dinta a hannu, karasawa wajensu tayi ta ce "Subhanallah, lafiya dai ko?" Anty Rahama ta ce "Ina lafiya Amina, daga kinyi bakuwa wai ta hauro sama kiranki, tana gani jiya sai da muka koma asibiti aka bamu wasu magungunan" Hannun Ikleemah Anty Amina ta kama ta ce "Haba Leemah, so kike ki kara jawo mana wani abun ne, ai yau kam jiki yayi kyau, maza muje kasa a dafa miki abinda kikeso" dagata tayi suka nufi kofar fita Anty Rahama tabi bayansu, a hankali suka dinga saukowa a stairs din saboda Ikleema, bayan sun shigo parlor Anty Amina ta dinga kallan Anty Khadija dake zaune tana danna wayarta. Kwantar da Ikleema tayi akan kujera ta zauna ta ce "Sannu da zuwa" Anty Khadija kallesu ta ce "Yauwa sannu" zama Anty Rahama tayi ta ce "Wa kike nema?" Anty Khadija ta danyi murmushi ta ce "Fatan an gama biki lafiya" harara Anty Rahama ta balla mata ta ce "Malama kinyi kuskure, ai ba anan akayi auran ba da zaki zo mana ban gajiya" murmushi Anty Khadija tayi ta ce "Nasani, nazo ne muyi magana da matar gidan nan" Anty Amina dake kallanta ta ce "Wace irin magana?" Anty Khadija ta gyara zama ta ce "To da farko sunana Khadija Bello, nice yayar Yusuf wanda ya auri 'yar gidan nan" dan murmushi Anty Amina tayi, bata san Anty Khadija ba amma tanajin labarinta dan ita tayi sanadiyyar raba Yusuf da Nusaiba, a hankali ta ce "Sannu da zuwa Hajiya Khadija, bari a kawo maki abin sha" daga haka ta mike, cikin saurin Anty Khadija ta ce "No, No, karki damu, ba zama nazo yi ba, nazo ne daman muyi magana, nasan kina daya daga cikin makiya auran nan" Anty Amina ta koma ta zauna tana kallan yayarta ta ce "Aiba ni kadai ba, kinga dani da yayata da 'yarta da Ummanmu da wasu daga cikin danginmu duk ba so muke ba, dalili kuwa shine basu dace ba, ga kuma cuta dake cin yarinyar" Anty Khadija tayi crossing legs dinta tana jijjiga key din mota ta ce "To kun samarwa kanku mafita?" Anty Rahama dake kallanta ta ce "Tukunna dai" juyowa Anty Khadija tayi ta kalleta sannan ta ce "Tukunna fa kika ce?" Anty Rahama ta ce "Ehh, bakiga muna da marar lafiya ba, wannan yarinyar da kike gani sanadin auran nan ta shiga wannan hali" Anty Khadija ta kalli Ikleema sannan ta ce "Allah ya kyauta, to muma dai ta bangarenmu basan auren muke ba, taya za'ai shekara daya da auran 'yar uwata ya mata kishiya, kishiyarma yarinya karama da bata san ciwan kanta ba, to ni ba dogon magana nazo yi ba, harka ce ta samu yadda zakuji dadi muma muji dadi, idan kun yanke shawarar ga card dina da komai ajiki" tana rife bakinta ta dauko card din ta ajiye akan kujera sannan ta mike ta ce "Sai anjimanku" Anty Amina ta ce "Allah ya kiyaye". Tana fita Anty Rahama ta kalleta ta ce "Anya kuwa yayarsa ce? Naga basa kama" Anty Amina ta ce "Ba iyaye daya suke ba, inaga a gidansu ya girma, amma kinsan mubi matarnan komai zai tafi dai dai" Anty Rahama ta ce "Nima naga alamun nasara, amma kinsan baza su so Ikleema ta shiga gidan ba" Anty Amina ta ta6e baki ta ce "To shine autan maza? Mu dai idan Rafi'ah zata fito na har abada ai ko ba komai mu mukai nasara, wallahi Ikleema ki kwantar da hankalinki namiji sai kin zama amma ki manta da Yusuf" shiru Ikleema tayi tana kallan Anty Amina, caan ta danyi murmushi ta ce "Na hakura Anty indai itama xata fito, wallahi a yanzu bani da burin daya wuce naga ta gama wulkanta" Anty Rahama ta ce "Gaskiya mu yarda kawai, kuma idan auran ya 6alle sai dai kinga tai ta zama a gida, daga nan suyi rayuwarsu muyi tamu" Anty Amina ta dauka card din tana kallan address din gidan ta ce "Zanje gobe na sameta nima" Anty Rahama ta ce "Bari naje na kira Umma na fada mata komai, daga haka ta mike ta wuce sama tana murmushi.
Gently ya dinga daga kafarsa yadda baxata ji footsteps dinsa ba, juyowa yayi yana kallan Rafi'ah dake kwance akan kujera, mistakenly kafarshi ta bugi center table tayi saurin mikewa tana kallan parlor, komawa yayi bayan kujera da sauri ya buya, ta dinga bin parlorn da kallo jin motsi, mikewa tayi ta leka bayan kujerar suka hada ido, ta turo baki ta koma kan kujera ta kifa kanta ta fara kuka, with lots of disturb ya tashi yana murmushi ya zauna gefenta ya ce "Yanzu fa zan dawo, i just want to buy something akan junction" kwace hannunta daya rike tayi ta ce "Nasan ai wajen matarka zakaje" jawota yayi jikinshi ya rungumeta ya ce "Noo, zan samo mana lunch ne" ta kara turo baki ta ce "Ni bazanci irin na jiya" ya shafa bayanta ya ce "What do u want then?" A hankali ta ce "Egg and bread with tea" ya ce "Meyasa kike shan tea da rana" ta ce "Ni ko yaushe ma idan inasan sha" ya ce "To bari na hada miki" daga haka ya kwantar da ita akan kujera ya fita a parlor, kamshi yaji a kitchen hakan yasa ya nufi nan, Jiddah ce tsaye a gaban gas tana soya kwai, ya rungumeta unexpected tayi saurin juyowa, suna hada ido ya manna mata kiss a kumatau ya ce "How are u, dazu da safe naje na samu kina bacci" ta ce "Fine" daga haka taci gaba da abinda take, yana rike da ita harta gama ta kashe gas din, a hankali ta ce "Zan wuce parlor na ka sakeni" ya danyi murmushi yana kallan egg din hannunta ya ce "Nima zanci" ta hade fuska ta ce "To muje parlor" ya ce "Noo, sai dai ki zuba min nawa" kallansa ta dingayi kafin ta sauke kanta, ya ce "Bazaki bani bane?" Ta ce "Nifa banci komai ba tin safe gashi yanzu karfe 2 ne, kuma idan na zuba maka baxai isheni ba, dama kai zaka ci saina baka, amma wallahi bazan hada abinci wata banza taci ba" Yusuf ya matseta a jikinshi ya ce "Yanzu dai bazaki bani ba kenan" ta ce "Na fada maka ai" ya ce "Zanje eatery na siyo mana abinci yanzu sai mu kara" make kafada tayi ta ce "Nifa bazata ci abincina ba" kin saketa yayi saima kansa daya kwantar a wuyanta, Tana kokawar kwacewa Rafi'ah ta shigo kitchen din, hakan yasa tayi collapsing a jikinshi tana dallawa Rafi'ah harara, ko kallansu batai ba ta wuce ta dauko flask da mug ta fito a kitchen din, kasa hada tea din tayi ta tsaya rike da mug din a hannunta, jin motsi yasa tayi saurin bude flask din zata debi ruwa Yusuf ya ce "What are u doing?" Kin kulashi tayi ta zuba ruwanta sannan ta rufe ta dauka liptopn akan dinning ta saka a ciki, daukan mug din tayi zata wuce part dinta ya riko hannunta ya ce "Sugar fa" juyawan da zatai ta zubo ruwan zafi a kafarta, ta saki kara ta jefar da cup din ya tarwatse a wajen, da sauri Yusuf ya dagata ya ajiyeta kan kujera yana kallan kafar, Jiddah ta dinga hararansu tana murguda baki, cikin rarrashi Yusuf ya ce "Sorry dear, bari na gyara wajen muje mu siyo abinci" hawayen idanta ta share ta ce "Bayan kasa na xubar da tea dina" dariya ya danyi jin ta kirashi da tea, ya san ko me za'ai ba iya sha zata tai ba, ya dagata suka nufi part dinta ya ce "Keda baki da lafiya menene naki na hada tea kuma" a hankali ta ce "Ba kabarni da yunwa ba kaje wajen matarka, meyasa bazan hada ba" ta turo baki ta kwanta akan kujera, murmushi yayi ya fita a parlor ya share inda mug din ya fashe sannan yayi mopping wajen, karasawa yayi gefen Jiddah ya ce "Zamuje eatery me zan kawo maki" girgiza masa kai tayi ta ce "Ni banasan komai" ya bata light kiss ya ce "I know u like shawarma, ita zan siyo maki" bata ce masa komai ya koma part din Rafi'ah, a tsaye ya sameta harta sa hijabi, ya ce "Bafa dake zanje ba" cushion din gefenta ta wurga masa ta ce "Kuma saina bika, ai jiya ma daka fita baka dawo da wuri ba" ya danyi murnushi ya ce "Zance naje ai jiya" ta kara turo baki ta nufi kofa ya bita da kallo yana murmushi, baisan meyasa idan yana tare da ita baya gajiya da kallan abubuwanta ba, key din mota ya dauka ya fita, a parlor ya sameta tsaye tana jiranshi, tayi saurin kama hannunsa ta ce "Harda yawo ma zamuje ko Doctor" ya ce "Eh" rungumeshi tayi tana murmushi ta ce "When are we coming back?" Ya ce "Till night" ta danyi tsalle ta ce "Yess" daga haka suka fita zuwa parking lot Jiddah ta bisu da harara. Sai lokacin Anty Khadija ta koma gida, bayan tayi parking ta shiga parlor da sallama, Umma dake kallanta ta ce "Sai yanzu" ta ce "Ehh na biya clinic ne" Umma ta ce "To ya kukai?" Anty Khadija ta ajiye veil dinta akan kujera ta ce "Kamar dai yadda Malam ya fada hakan take, suma inaga da abinda suka kulla a kasa, shine ya hadu da wanda muke ya kasa bada result me kyau, gaskiya Umma sun mungun tsanar yarinyar" Umma ta danyi murmushi ta ce "Barka, kinga yanzu haduwarmu dasu, zasu bar komai a hannunmu, sai muyi yadda mukaga dama" Anty Khadija ta ce "Hakane, kuma Umma baza suyi tinanin sake wani abun ba, balle su toshe mana hanyar namu aikin" Umma ta danyi dariya ta ce "Dama Malam yace min bamu kadai bane" daga haka Anty Khadija ta mike ta haura upstairs.
Yau ya kama sati 2 da bikin Rafi'ah, tin sassafe ta tashi ta shirya saboda Yusuf ya mata alkawari zai kaita gida yau, sosai tayi kyau ta yafa veil dinta akai, gefenshi ta koma ta zauna ta ce "Doctor" ya dauke kansa akan laptop ya juyo yana kallanta, ta ce "Pls na kwana mana kaji" dan zaro ido yayi ya ce "I can't sleep here without u, sai dai idan zaki bari jibi kwanan Jiddah sai kije ki kwana" kwantar da kanta tayi akan kafardarsa ta ce "Banaso" ya ce "To ba kwana, da daddare zan dauko ki" a hankali ta ce "Na yarda to, kuma sannan ni..." Shiru tayi ta fasa cewa komai, ya bata side hug ya ce "Now tell me, me zaki ce?" A hankali ta ce "Matarka ta daina shiga harkana tinda bataso mu zauna lafiya, kagani dazu na jona ruwa a kettle shine ta juyemin, hakama jiya ta daukemin Apple dina akan dinning kuma nayi magana tace wai in kwata idan zan iya" shiru yayi yana kallan lips dinta dake motsi, ta kai hannunta kan botton din rigarsa ta ce "Kuma Ummina tace karna sake nayi fada da ita, so kace itama ta daina min haka" bakinshi ya ajiye akan nata ya ce "Ai jiya na mata fada sosai, bazata kara ba" ta ce "To ai yau..." Shiru tayi jin bakinshi cikin nata, tayi saurin janye fuskarta ta matsa a gefensa ta ce "Ba yanzu zamu tafi ba" jinginar da kansa yayi akan gado ya limshe ido, kamar zatai kuka ta ce "Karfe 9 fa yanzu Doctor" bude idanuwansa yayi ya kamo hannunta ta dawo kusa dashi ya ce "Zanyi missing dinki Baby, i so much luv u, banasan naji bakya jikina" daga haka ya rungumeta tsam tsam a jikinshi, cikin rarrashi ta ce "I will miss u too, but ni kam ka tashi mu tafi" ya danyi murmushi ya ce "Tona tashi" ta kama hannunsa ta ce "Let's go" kashe laptop din yayi ya dauki phone dinsa da key din mota sannan suka fita. Jiddah na zaune a parlornsa tana shan tea, ya ce "Zan kaita gida na dawo" ta juya musu keya bata ce komai ba, har zasu fita ta ce "To meye damuwana da sai ka gayamin, aikin banza kawai" Rafi'ah ta juyo da sauri jin abinda ta fada, sai kuma tayi shiru, Yusuf ya bude kofar suka fita, yana jiwo tsakin da tai amma baice mata komai ba, har sukaje parking lot baiyi magana ba, bayan sun shiga ya tada motar Rafi'ah ta kamo hannunsa ta ce "Dan Allah ka daina fishi Doctor, i apologize on behalf of her" juyowa yayi yana murmushi yaja hancinta ya ce "I'm not angry dear" ta ce "But you're not smiling" ya ce "Ai nayi" ta ce "Ai saida nayi magana" shiru yayi ya danna horn gateman ya bude sannan suka fita, bayan sun hau titi ta dan kalleshi ta ce "I'm soryy to say ur wife doesn't have manners of talking".


_08103810398_



[8/10, 8:46 AM] Zarah: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_41_

Shiru Yusuf yayi ya ci gaba da driving dinsa, bayan few minutes ta dan kalleshi sannan ta ce "I'm sorry if i hurt u" still baice komai ba, sai bayan minti uku ya ce "Not at all, i don't feel like talking anymore" jinginar da kanta tayi jikin kujera ta limshe ido, har sukaje gida babu wanda ya kara magana a cikinsu, a kofar gida yayi parking yana kallanta ya ce "Come down" ta ce "Why not kayi parking a ciki to?" Ya girgiza mata kai kawai, ta ce "But Abba zaiyi magana yana nan fa" ba tare daya kalleta ba ya danna horn, bayan Mustapha ya bude gate din ya shigar da motar sannan yayi parking. Fitowa tayi tana kallansa ta ce "Bari na fadawa Ummi tare muke" ya girgiza mata kai, kamo hannunsa tayi cike da damuwa ta ce "My Doctor is anything wrong with u? Kona maka laifi ban sani ba" limshe idanuwansa yayi ya ce "Uhm~uhm, baki min komai ba, kawai naji banasan magana ne, may be..." Shiru yayi ya bude idanuwansa yana kallanta, ta kai hannunta face dinsa ta ce "May be what?" ya girgiza kai ya ce "I'm having Headache kuma haushi nakeji" murmushi tayi ta rungumeshi ta ce "Allah ya baka lafiya" a hankali ya ce "Ameen" tana dago kanta ta hango Anty Amina da Anty Khadija suna tahowa, sai shewa suke suna tafawa, yadda take kallansa shima Yusuf haka yake kallansu, har suka karaso inda suke Rafi'ah na rike da hannun Yusuf dake zaune, ta dan sunkuyar da kanta ta ce "Ina kwanan ku" Anty Khadija ta washe baki tana kallanta ta ce "Amarya har kin fara fita ne?" Kafin tayi magana Anty Amina ta ce "Haba sati biyu fa, ai yaci ace tazo taga mutanen gida" Anty Khadija ta karasa wajen motar tana kallan Yusuf ta ce "Bashi da lafiya ne?" Rafi'ah da kanta ke kasa ta dan sake hannunsa ta ce "Ehh, kanshi ne yake ciwo" sai lokacin ya dago kansa yana kallansu ya ce "Good morning" a tare suka amsa gaisuwar, Anty Khadija ta ce "To Allah ya sauwake" daga haka suka nufi inda motarta take, murya caan ciki ta kalli Anty Amina ta ce "Kingani ko, alamu sun nuna abin ya fara aiki, aina fada miki daga yau komai zai dai dai ta" Anty Amina ta kamo hannunta ta ce "Gaskiya babu abinda zan iya saka miki dashi Khadija, Amma dama nayi alkawarin idan komai ya dai daita akwai filina da zan mallaka miki, nasan dai watakila kinfi karfinsa amma ai kyauta da dadi" Anty Khadija tayi murmushi tana kallanta ta ce "Gaskiya naji dadi sosai, yanzu dai ki koma komai ake ciki zan kira ki" Anty Amina ta daga mata hannu sannan ta koma apartment dinta ba tare data kalli inda su Rafi'a suke ba, dago kansa yayi ya ce "Move, zan rife kofar i'm going home" ta marairaice ta ce "Baza ka gaishe su ba?" Ya girgiza kai ya ce "Some other time, i can't stay here" matsawa tayi ya rufe kofarsa sannan ya tada motar yayi horn, juyawa tayi duk jikinta a sanyaye ta nufi apartment dinsu, tana hawa balcony ta juyo taga harya fita a gidan, bell ta danna sannan taja gefe ta tsaya, bayan minti 2 aka bude kofar, kallan budurwar data bude kofar tayi sannan ta shiga parlorn, Rafi'ah na murmushi ta rungume Umminta dake zaune akan kujera, Ummi ta shafa bayanta ta ce "How are u daughter?" a hankali ta dago tana kallan Ummi ta ce "I'm fine Ummi, ina Abba?" ta ce "He's upstairs" daga haka ta
End Ads