x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - LIFE PARTNER

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 73416 words

Category: Love Stories

Views 334

17 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
samu sauki, dan kwana biyu ciwanta ya kan tashi but not that serious, hakan yasa tayi concentrating akan karatunta ta watsar da shi itama, duk da shi yana kokarin zuwa ya ganta amma saam bata wani sake masa yanzu, musamman yanzu da take shirin yin Waec dinta, Khairiyya ta kan zo gidan sosai wajen Rafi'ah, ko Yusuf ya kawota ko kuma driver ya suketa, sosai Rafi'ah take ji da yarinyar har cikin ranta. Bangaren Jawad kuma tin da aka saka bikin Rafi'ah ya daina zuwa gidan, kullum wajen aiki yake yini sai dare yake dawowa gida, idan ka ganshi zaka rantse bashi da damuwa, har wani kiba ya danyi ya kara haske, ya watsar da duk wani abu da zaisa ya shiga damuwa, Mami ma idan ya gaisheta da safe ya fice sai tayi bacci yake dawowa. Ba karamin tashin hankali Anty khadija da Ummanta suka shiga ba ganin maganinsu baya tasiri a jikin Yusuf, duk da dama malamin yace a hankali aiki zaiyi amma gashi dai babu changes tsawon wata 8, ita kuwa Jiddah tinda tayi 6ari ta shiga damuwa saboda har yanzu shiru ne babu alamun wani ciki a tattare da ita, suma suna nasu maganin ita da Auntyn sai dai suma babu abinda ya canza, dama da zarar Anty Khadija ta kawo magani Jiddah zata tattara tasa a handbag dinta idan ta fita school ta zubar a titi, haka ta dinga musu tin farkon bikinta har zuwa yau, wani lokaci idan ta tuna auran Yusuf sai ta fashe da kuka, haka zaiyi ta tambayarta amma ta masa banza. Anty Amina ma kullum taje gidansu sai an hado ta da magani, wani lokaci tayi amfani dashi wani lokaci ta ki, dan ita yanzu babbar damuwatarta bai wuce ta hana auren Rafi'ah ba, wannan karan da kanta ta kar6o magani tayi amfani dashi da sunan Rafi'ah ta bunne, bata ta6a shiga tashin hankali kamar ranar da aka kawo lefe ba, ko Jiddah batai haukan da tayi ba, yini tayi tana zarya a parlornta, karshe data kasa hakuri taje ta tono layoyin taga sunan nan inda suke, sake rufe wajen tayi sannan ta koma apartment dinta cike da damuwa, gashi Abba tinda biki ya rage saura sauti 2 ya dawo gida, baya bari ta fita ko ina saboda kullum Ikleemah sai tazo, watarana ta kwana watarana kuma ta tafi. Ranar Saturday Rafi'ah ta gama Neco, tsabar dadi ranar yini tayi tana bacci, washegari kuma Mummy ta taho da mai gyaran jiki aka fara mata, a BQ aka sauki matar saboda safe da yamma ake mata dilka, tin tana marmarinsa harta gaji, ga warinsa daya isheta, ji take kamar tayi amai wani lokaci, ana saura sati daya biki tana kwance a daki taji ana knocking ta danyi shiru sannan ta ce "Waye?" Abdul ya turo kofar ya ce "It's me, ana jiranki a BQ" tashi tayi tana turo baki ta zura himar dinta sannan ta fito a dakin zuwa downstairs, Ummi kadai ta samu a parlor, ta sunkuyar da kanta ta ce "Bacci nayi shiyasa ban fito ba" Ummi taci gaba da abinda take bata kulata ba, fita tayi ta wuce BQ, ta shiga parlor da sallama, Mummy ce da mai gyaran jikin a zaune suna magana, karasowa tayi ta zauna tana dan yatsine fuska ta ce "Wai yaushe za'a gama ne Mummy?" Anty Halima ta ce "Ranar da aka fara biki mana" kamar zatai kuka ta ce "Dan Allah daga yau a kyaleni banaso nikam, Allah ji nake kamar zanyi amai" harara Mummy ta dalla mata ta ce "Wallahi baki isa daga yau a daina gyaran jiki ba, ina laifin ranar Wednesday, Thursday ki huta friday a fara biki" tagumi Rafi'ah tayi tana kallanta kafin ta ce "Ni gaskiya i'm tired Mummy" Murmushi me gyaran jiki tayi cikin rarrashi ta ce "Kwana hudu fa kawai ya rage Amarya, ki kai hakuri kusan sati 3 ma balle kwana 4" dan turo baki Rafi'ah tayi ta cire hijabin jikinta sannan ta dauka zanin da take daurawa ta wuce daki.
Da daddare Rafi'ah na zaune a parlor tana shan tea Abba ya shigo parlor, ta mike a hankali ta kar6a ledan hannunsa ta ce "Sannu da dawowa Abba" ya ce "Yauwa Mamana, how are u?" Silently ta ce "Fine Abba" daga haka ta wuce kitchen, ajiye ledan hannunta tayi ta ce "Ummi, Abba ya dawo" daga haka tayi saurin ficewa dan ma kar a sata aiki, Ummi ta bita da harara sannan ta wanke hannunta ta fito parlor. Rafi'ah na shiga dakinta taga missed call din Yusuf har 7, kafin ta sake kira wani kiran ya shigo, a hankali tayi picking ta kai kunne, ya ce "Where have u been Baby?" ta ce "Bana kusa ne" ya ce "I'm outside" toh kawai tace sannan tayi hanging call din, babban himar dinta ta saka har kasa, sai kamshi take ga fatar jikinta dake sheki, ko powder babu a fuskarta amma tayi bala'in yin kyau, ta jima a tsaye tana rike da staircase, gashi tana san fita amma kuma su Abba na parlor, ganin call din Yusuf na kara shigowa tayi karfin hali sannan ta sauko ta nufi kofa, Ummi dake yayyanka Apple ta dago tana kallanta ta ce "Ina zakije?" Tsayawa tayi cikin cool voice ta ce "Waje" daga haka ta bude kofar ta fita, as usual yana tsaye jikin motarsa yayi folding hannu, Yusuf ya dan zaro ido ganin yadda ta canza sosai, gaba daya street light din ya haskata, ta sauke kanta tana wasa da fingers dinta ta ce "You're welcome" ya ce "Thank u wife, kinga yadda ki kai kyau kuwa? anya nima bazanje amin ba" boye fuskarta tayi tana murmushi ta ce "Kai ai namiji ne" ya ce "To ai banaso ki fini kyau" dariya ta danyi ta ce "How are u?" Ya shafa gashin kansa yana kallanta ya ce "I'm fine love, ya jikin ki, ina bakya damuwa sosai" kai ta daga masa sannan ta ce "Ehh" ya ce "That's good" bude mota yayi ya ciro IV card da yawa cikin bakin leda da kuma key ya mika mata ya ce "Take this, key din na gidan ne" ta kar6a tana murmushi ta ce "Thank u, ai basu tambayi key ba" ya ce "Mummy ta tambaya dazu, ki kai mata" kai kawai ta daga masa, ya ce "To ya kamata ki shiga gida, dare yayi" ya karashe mganar yana kashe mata ido daya, murmushi tayi kawai ta ce "To, saida safe" ya ce "Alright Baby" daga haka ta shige ciki shi kuma ya koma mota yayi reverse sannan ya bar layin. Anty Khadija ce zaune gaban Umma duk sunyi jugum har abin tausayi, Anty Khadija ta mike tana kallan Umma ta ce "Nifa gani nake kamar Jiddah yaudararmu take bata amfani da duk wani magani da muke bata, inba haka ba yau wata kusan 9 labari bai canza ba" Umma ta ta6e baki ta ce "Haka dai kika gani Khadija, idan hakane ta ina zata so a mata kishiya? dole dai tana amfani da magungunan nasara ce babu, gobe kuwa zan koma inji ya ake ciki" Anty Khadija ta sauke ajiyar zuciya sannan ta ce "To Allah ya kaimu" daga haka ta fice a dakin. Karfe 12 na dare Rafi'ah ta tashi ta danna wayarta dake gefenta, missed call din Yusuf ta gani guda 3, ta danyi murmushi ganin text dinsa a saman wayar ya rubuta "I love you" hasken wayar ta kunna sannan ta shiga toilet ta dauro alwala ta fito ta shimfida sallaya ta tada sallah, har kusan karfe 3 kafin ta kwanta anan kasa nan da nan bacci ya dauketa, washegari ya rage saura kwana 4 biki, 'yan uwan su Ummi sun fara sauka a gidan maza da mata, ba karamin tashin hankali Anty Amina ta shiga ba, dan a cewar malaminta ko taron bikin baza'ai ba, gaba daya ta shiga damuwa har wani rama takeyi gashi ta kasa nutsuwa, kusan kullum sai kaji Abba na mata fada. Da sallama ya shigo dakin hannunsa rike da makullum mota, ya zauna bakin gado yana kallan mahaifiyarsa ya ce "Mami gobe fa zan tafi Cyprus" tashi tayi ta zauna tana kallansa ta ce "Ai na zata ka fasa tafiyan da naji ba kai magana ba" ya dan shafa gashin kansa ya ce "Ehh, da ba yanzu bane, to amma sun kirani ne" Mami ta ce "To Allah ya kaimu, da yushe zaku tashi?" Ya ce "Karfe 10 na dare, idan na kwana a Abuja sai mu wuce" ta ce "To Allah ya kaika lafiya, kana dawowa kayi auranka kaima ka zama mutum, ga masu cuta ma suna aure ballantana lafiyayyu" shiru yayi kansa akan wayarsa yana dannawa, Mami ta ce "Wannan karan bakasan kilishi ne? naji bakai maganar ba" dagowa yayi yana kallanta ya ce "Inaso" daga haka ya mike ya fita sannan ya ja mata kofar. Direct part din Mummy ya shiga da sallama, ya zauna akan kujera yana kallan TV, fitowa tayi tana kallansa ta ce "Jawad kaine?" Ya ce "Ehh" dan raban daya shigo mata harta manta, sai dai idan sun hadu a parlorn Abi su gaisa, Mummy ta dauko masa malt da cup sai ruwa ta ajiye masa a gabansa ta ce "Dan kai yanzu ka zama bako Ahmad, bama ganinka baka ganinmu" murmushi ya danyi yana shafa gashin kansa ya ce "Aiki ne Mummy" ta ce "Haka dai kace, kaikam idan ka zama shugaban kasa sai dai muyi hakuri da kai, kullum aiki aiki baya karewa, ai naga a court dinma ana hutu ko?" Murmushi ya sakeyi ya ce "Zan tafi Cyprus ne gobe" Mummy ta sake baki tana kallanshi ta ce "Cyprus Ahmad?" Ya ce "Insha Allah" ta ce "Amma kasan zan aurar da Rafi'ah ko?" A hankali ya ce "Ehh, amma kiyi hakuri daga court din ne suka nemi a turani, wata biyu zanyi a caan" Mummy ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ai shikkenan, Allah ya taimaka ya kuma bada sa'a, bari na aike ka ka kai musu sako" daga haka ta shiga daki tana fadin "To dambu kake so ko meat pie zan maka sai kana soyawa?" Fitowa tayi da envelop a hannunta ta mika masa ta ce "Dan Allah ka kai musu yanzu Jawad, tin dazu nake kiran Abduljalal yazo ya kar6a baizo ba gashi yamma ta kusa" very gentle ya mike ya dauki malt din yana kallanta ya ce "To saina dawo" ta ce "Ka gaishe su, baka fadi me zan makan ba" ba tare daya kalleta ba ya ce "Dambu nakeso" ta ce "Ba damuwa" daga haka ya fita a parlorn Mummy, Sadeeq kadai ya samu yana cin abinci, ya wuce shi ya fita a parlor ya nufi parking lot, yana kunna motar ya danna horn, gate man ya bude sannan ya fitar da motar bayan ya amsa gaisuwar mai gadin, yana fita yayi parking ya bude envelope din, kananun IV card ne aciki na kamu na Mummy tayi organizing, ya ciro guda daya yana kallo, bayan ya gama karantawa ya maida ciki ya rufe sannan ya tada motar ya bar kofar gidan.
[8/4, 2:59 PM] My Imaan: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_

*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._

_By FATIMA ✍🏻_

_37_

A bakin gate yayi parking as usual, dashboard ya bude ya dauko chequebook da biro yayi rubutu sannan ya yage paper din yasa a pocket dinsa, wani dan karamin box ya dauko sannan ya dauki envelope din ya fito a motar ya rufe, gently ya karasa bakin gate din ya tura sannan ya shiga, few people ne a tsakar gidan kowa da abinda yake wasu na zaune akan mat, wasu kuma nata backyard ana girki, wasu manyan mata ne akan tabarma suna zaune sai hira suke, kana kallansu kaga dangin su Ummi ne sai kanwar mahaifiyarsu da ita kadai ta rage musu wacce suke kira da Gwaggo, ko ba'a fada ba kamanni sun nuna, tsugunawa Jawad yayi ya ce "Ina yinin ku" a tare duk suka amsa da fara'a ya mike ya shiga cikin gidan, Ummi ce zaune a parlor da wasu mata biyu, ya zauna akan carpet yana murmushi, Ummi ta ce "Is it you Jawad? Dama kana nan?" murmushi yake yana gyara hulan kansa ya ce "Ina nan Ummi, aiki ne ya min yawa yanzu" ta ce "To Allah ya taimaka" ya ce "Ameen, ya hidima?" Ta ce "Alhamdulilah, let me get something for you" daga haka ta mike, gaishe da sauran matan yayi suka amsa masa, ba jimawa Ummi ta fito a kitchen da warmers a hannunta ta wuce parlorn Abba, bayan ta fito ta ce "Ka shigo ciki Ahmad" tashi yayi a hankali ya wuce parlorn Abba ya zauna akan carpet ya fara danna wayarsa. Shigowa Ummi tayi ta zauna ta ce "Kaci abincin ko, bari Rafi'ah ta kawo maka kunu, ko baka sha?" kansa ya dan sauke kasa ya ce "Ina sha, amma dai na koshi da abincin" Ummi ta ce "To bari a kawo maka kunun" daga haka ta fita a parlor. Upstairs ta wuce ta shiga dakin Rafi'ah, a kwance ta sameta tana waya, tayi saurin hanging wayar tana kallan mahaifiyartata, Ummi ta ce "Kije ki dauki kunu ki kaiwa Jawad, yana parlorn Abbanki" a hankali ta mike ta dauki himar dinta ta saka sannan tabi bayan Ummi ta fito, tana saukowa ta wuce kitchen ta dauko flask din sannan ta shiga parlorn Abba, very gentle ta karasa gabansa ta ajiye flask din, suna hada ido tayi saurin dauke kanta ta nemi waje ta zauna gefenshi, a hankali ta ce "Ina yini" ya ce "How are u?" ta ce "I'm fine" ya ce "Ya shirye shirye?" Kanta na kasa ta ce "Alhamdulilah" daga haka ta mike ta fita a parlor ya bita da kallo. Mug ya dauka ya bude flask din sannan ya debi kunun ya saka cube din sugar guda 2 sannan ya dauka spoon ya juya ya fara sha a hankali. Few minutes ya gama sannan ya ajiye cup din, Ummi ne ta shigo parlor daukan abu, ya danyi kasa da kansa ya ce "Ummi zan tafi Cyprus gobe insha Allah" dagowa tayi tana kallansa ta ce "Tooh zaka kara nisa kenan, daga wajen aiki ne suka tura ka?" Ya ce "Ehh" ta ce "To Allah ya tsare hanya, ya dawo da kai lafiya, are u staying long?" Ya ce "Noo, just 2 months" ta ce "Aida yawa Jawad, Allah dai ya taimaka ya tsare" ya ce "Ameen", daukan abinda zata dauka tayi sannan ta fita a parlor, so yake yace mata yana san yaga Rafi'ah amma ya kasa, gashi he is eager to go home.
After 15 minutes Rafi'ah ta shigo parlor, sai data dan tsaya ganinsa dan a tinaninsa ya wuce, ta sunkuyar da kanta ta wuce dakin dake parlor, ba jimawa ta fito da wani dan bucket a hannunta, Jawad ya ce "Idan kin gama kizo" juyawa tayi ta kalleshi sannan ta fita ta kaiwa Gwaggo bucket din ta dawo, a hankali ta karasa inda yake ta zauna, ya mika mata envelope din ya ce "Mummy ta bayar a baki" ta kar6a sannan ta ce "Thanks" daga haka ya ciro box din da cheque ya mika mata ya ce "And this is for you" ta dago ta kalleshi sannan ta kar6a, kallan cheque din ta dinga yi, ta kara kallansa ganin 100k ajikin cheque din, sauke kanta tayi kasa ta bude box din a hankali, ta dan zaro ido ta ce "Azurfa?" Ya daga mata kai ya ce "I hope it will size you?" Murmushi tayi ta fara zira ring din a hannunta na dama, ta juyo hannun tana kallansa ta ce "Yayi kyau sosai, thank u so much" kallan dogayen fingers dinta kawai yake, ta cire ring din ta maida shi box dinsa sannan ta ce "I'm so much greatful, nagode sosai Allah ya saka da alkhairi" a hankali ya dago yana kallanta ya ce "I know u have more than that, so no need to say thanks, and i'm wishing u a happy marriage life, try your best and be the best wife ever" a hankali ta ce "Insha Allah" still looking at her ya ce "Gobe zan tafi Cyprus bazan samu daurin auran ki ba" duk jikinta sanyi yayi ta ce "Allah ya kiyaye, ya kaika lafiya" ya ce "Ameen" daga haka ya mike ya dauki key din motarsa, tashi tayi tabi bayansa har suka fito a gidan, ta rakashi har mota tana mishi Allah ya kiyaye, silently ta tsaya a bakin mota ta ce "I'm lost of words Ya Jawad, nagode sosai da sosai, Allah ya saka, i'm happy with the gift" murmushi ya danyi ya ce "Ba komai, thanks too" rife motar tayi sannan ta shiga gida shi kuma ya tada motar ya bar layin. Tana shiga compound Gwaggo ta ce "Shine angon ne Fatima?" Turo baki tayi tana kallan kakartata ta ce "Ba shine bane fa Gwaggo" Gwaggo ta ce "To shi wannan din waye? angon baizo ya gaishe niba fa, baisan kanwar kakarki tazo bane" dariya ta danyi ta ce "Keda zamu tafi tare, ai an maki dakinki" daga haka ta wuce ciki ta barta a tsaye.
Washegari da sassafe Jawad ya gama shirinsa na tafiya Abuja, daga caan karfe 10 na dare zasu tashi zuwa Cyprus Mami na tsaye ta gama hada masa komai ta ce "Yanzu sai kaje Abujan zaka karasa kenan?" Ya ce "Ehh" ta ce "To saura karkaje ka gaishe da mutanen gida, nasanka yanzu zaka ce aiki ya maka yawa" murmushi ya danyi ya ce "Ai a caan zan sauka tinda yau zan wuce" ta ce "To Allah ya kiyaye, ya kuma tsare hanya" ya ce "Ameen", Sadeeq ne ya fitar mishi
End Ads