bayan few minutes ya fara karanto Al~qur'an kasa kasa saboda ya samu saukin abinda yake ji.
Bayan mintina kalilan ya mike ya fita parlor, zaune ya sameta a kan kujera tana kallo, ya zauna gefenta ya ce "What comes over u Jiddah? u just change all of a sudden" a hankali ta juyo tana kallansa sai kuma ta ce "Kaje wajen yarinyar ai nasani" ya kamo hannunta ya ce "What is ur evidence? Ina san ganinta kam banyi karya ba, but ai yanzu lokacinki ne, i can't leave u at this condition" harara ta balla masa ta zame hannunta cikin nasa, tana juya kanta ta fara hawaye, ya rungumeta ta baya ya ce "Sorry if i hurt u" juyo da ita yayi yana kallan fuskarta camly ya ce "This is our first day as couples Jiddah, pls don't let shaidan deceive u" a hankali ta kwantar da kanta akan kafadarsa tana sheshekar kuka, ya dinsha shafa bayanta yana rarrashinta, ita a duniya yanzu babu wadanda takejin haushinsu irin su Anty Khadija, idan ta tuna kullukan maganin da suka bata sai taji zuciyarta na zafi, itama yanzu dama ce ta samu kuma dole tayi amfani dashi, babu abinda zaisa ta yarda su shanye Yusuf ita ta tashi a babu, kara shigewa jikinsa tayi tana limshe ido, ya dan bubbuga bayanta ya ce "Are u not hungry?" ta girgiza masa kai, dago da kanta yayi yana kallan idanta ya ce "Why? Tin jiya bakici komai ba" ta sauke kanta a kirjinshi ta ce "I will eat ltr" ya kara dago kanta ya jawota jikinshi sosai ya ce "Then we will eat together ko?" Daga masa kai tayi, ya kai bakinsa kan nata ya fara bata hot and romantic kiss...
Horn Abi yayi Mustapha ya bude gate yana daga masa hannu, bayan ya shigo yayi parking sannan ya fito, da ladabi Mustapha ya gaisheshi sannan ya tambayi Abba, Mustapha ya ce "Bari a masa magana" daga haka ya nufi apartment din Anty Amina, ba jimawa Abba ya fito sukai musabaha, yana ta murmushi ya ce "U are welcome Honorable, bismillah ka shigo" daga haka suka nufi BQ, a parlor suka zauna sannan suka kara gaisawa, Abba ya ce "Bari a kawo maka abin sha" Abi ya ce "Alhamdulilah Engineer, ba dadewa zanyi ba i have an important meeting" Abba ya ce "Ohk ba damuwa, dama 'yan siyasa are always on meeting" Abi ya danyi murmushi ya ce "Dama wata magana ce ta kawoni, and i wish u will be happy with it" Abba ya ce "I hope so Honorable" Abi ya gyara babban rigarsa ya ce "Dama yau da safe d'an wajena Ahmad yazo min da magana ta cewa yana son 'yarka da aure, so shiyasa naga nazo na fara maka magana kafin komai" still Abba yayi yana kallan Abi with shock jin abinda yace, ya danyi murmushi ya ce "That is not a problem Honarable...
_08103810398_
*Hello everyone 🤗 i hope u are all fine? if so that's my wish 🥰 Many people suna complain akan na rage yawan page, but u too should notice that da ina page biyu ne yanzu kuma guda daya nake saboda yanayin time,so kunga page daya ai bai kai page biyu yawa ba, that is it 😇 sannan masu comment are like sisters to me, i luv u so much cus d comments are melting my heart billah, Allah ya bar zumunci yasa mu karu da juna 🤲🏻 ku huta lafiya* .
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._
_By FATIMA ✍🏻_
_35_
Abba ya danyi murmushi ya ce "That is not a problem if i didn't made promise to someone, na riga nayi wa wani yaro alkawari and i'm sorry to say so Honorable" murmushi Abi yayi ya ce "Don't think u did bad, cika alkawari ai abu ne me kyau, Allah yasa hakan shine mafi alkhairi" Abba ya ce "Ameen, Ameen" tashi Abi yayi ya ce "To yallaboi zan wuce, a huta gajiya" Abba ya bi bayansa with respect ya ce "Allah ya kiyaye a gaida iyali" Har mota Abba ya raka shi sannan sukai sallama, bayan ya shigo ya apartment din Anty Amina. Mami ce zaune a dakinta tana shirya kayanta cikin press, daga kai tayi dan ganin wanda zai shigo, Ikram ta zauna bakin gado ta ce "Mami kinga Ya Sadeeq ya kwacemin phone dina" Mami ta ce "Let him give u, ina Yayanku?" ta ce "Yana cin abinci a parlorn Abi" ta ce "Call him for me" tashi tayi ta fita a dakin, ba jimawa ta dawo ta ce "Yana zuwa" sannan ta juya ta fice. Few minutes Jawad ya shigo da mug a hannunsa yana jujjuya tea din da spoon, Mami ta ta6e baki taci gaba da abinda take, zama yayi a bakin gado ya ce "Gani" ta ce "Magana nakeso muyi" ya ce "Ohk i'm all ears" zama tayi tana kallansa ta ce "I want u to get marriage" da sauri ya dago kansa yana kallanta, ta ce "Yes, ka samo mata aure zakiyi" sauke kansa yayi yana kallan tea din hannunsa ya ce "Ohk" harara ta dan 6alla masa ta ce "Not just ok Ahmad, na gaji da zamanka a gidan nan, ga gidanka caan kaima kayi aure ka koma" a hankali ya ce "Insha Allah" tashi tayi taci gaba da abinda take shima ya mike ya fita a dakin ta bishi da harara. A hankali Jiddah ta mike a jikin Yusuf ta dauka scarf dinta ta saka, dago kansa yayi yana kallanta ya ce "Ina zakije?" Ta ce "Zan bude kofa, baka ji ana knocking ba?" ya ce "To ke zakije?" Zama tayi ta dan 6ata fuska ta ce "Ai nasan Anty Khadija ne" ya ce "Let me check" daga haka ya fito a dakin ta biyo bayansa, yana bude kofar parlor Anty Khadija ta shigo tana kallansu, Yusuf ya danyi murmushi ya ce "Welcome sis, have a seat" ta zauna akan 2 seater tana kallan Jiddah dake tsaye bayan Yusuf, a hankali ta zauna ta ce "Ina yini" Anty Khadija ta ce "Lafiya kalau, ya amarci?" Jiddah ta ce "Lafiya" Anty Khadija ta kalli Yusuf ta ce "Doctor ya amarci, ya kuma kwanan amarya?" A hankali ya ce "All fine" daga haka ya wuce daki. Yana shiga Anty Khadija ta kalli Jiddah ta ce "Dama sauran maganin nan na kawo miki, shine zaki hada shi dana bakin leda" tana rife bakinta ta ciro kullin magani ta mika mata, Jiddah ta dan yamutse fuska kafin ta kar6a ta ce "Ohk nagane" Anty Khadija ta ce "Yauwa, idan lokacin yayi zanyi alerting dinki" Jiddah ta daga mata kai ta ce "Ohk ba damuwa ki gaishe da Umma" Anty Khadija ta mike tana lankaya hand bag dinta ta ce "To sai anjima" daga haka ta fice a parlor Jiddah ta bita da harara hade da tsaki, jujjuya maganin ta dinga yi sannan ta ta6e baki ta mike ta cusa shi kasan cushion ta koma ta zauna, tana zaune taji Yusuf ya rungumeta ta baya, a hankali ya ce "What are u thinking?" Ta ce "Nothing" daga haka ya saketa ya dawo gefenta ya zauna, kwanciya tayi ta dora kanta akan cinyarsa tana kallan TV ta ce "Yaushe zan koma school" ya shafa kanta ya ce "Next week i think" ta ce "Allah ya kaimu" daga haka ta limshe ido.
Anty Amina ce zaune a parlor'n ta tana ta sheka dariya, Ikleemah ta fito a daki tana kallanta ta ce "Anty Lafiya?" Mika mata wayar Anty Amina tayi, Ikleemah ta dinga kallan pic din Yusuf da Jiddah na aure, duk sai taji ba dadi, ga wani haushi daya tsaya mata a wuya, ta kalli Anty Amina ta ce "Da gaske ne aure yayi?" Anty Amina ta kara shekewa da dariya ta ce "Aure mana Ikleemah, zanso naga fuskar waccen yarinyar" ta6e baki Ikleemah tayi, ita dai taji dadi ko banza Rafi'ah ta shiga kunci, ta wani bangaren kuma haushi taji, dan a yadda mafarkinta ya nuna mata ita kadaice mata a gurin Yusuf, ajiye wayar tayi ta koma daki tana jaan tsaki.
Da sallama Anty Khadija ta shigo dakin, Umma ta amsa sannan tayi hanging wayar da take ta ce "Khadija kin dawo ne?" Ta ce "Na dan jima ma ina daki ne" Umma ta ce "Kin kaiwa Jiddah maganin dai baki manta ba ko?" Zama tayi a bakin gado ta ce "Na kai mata, kinga a hankali a hankali aiki zaina tafiya" Umma ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To saura kuma ke, dama jira nake na gama da Yusuf, ki fito da miji kema kiyi auranki" Anty Khadija ta dan ta6e baki ta ce "Umma kenan" Umma ta ce "Ba batun Umma kenan ba, shekararki fa 37 Khadija, ga Yusuf da yake 35 yayi aure ai yanzu kam kema sai ki tafi" Anty Khadija ta ce "Zan tafi ai, akwai lokaci" Umma ta ce "To Allah ya kaimu, ga Jiddah me 25 ma tayi auranta" tashi Anty Khadija tayi tana kallan Umma ta ce "Nifa har yanzu ban samu wanda raina ya kwanta da shi ba, ni inasan mijin da yake da Kudi na gani na fada, kyau, kuma wanda zai soni kamar ya mutu" Umma ta ce "To Allah ya kawo miki" ta ce "Ameen" daga haka ta fice a dakin. Rafi'ah ce zaune a gefen Abdul tana kallan yadda yake limshe ido yana juyi, ta kamo hannunsa ta ce "Abdul ko zaka ci abinci?" Ya girgiza kai, juyawa Rafi'ah tayi tana kallan Ummi ta ce "Ummi yaci abinci dazu ne?" Ummi dake kallansu ta ce "Yaci, ku fita waje ko zai dan sake" Rafi'ah ta kama hannunsa ta taimaka masa ya mike sannan suka nufi kofa Ummi ta bisu da kallo, tin dawowan ta a islamiyya bata tashi gefen Abdul ba, da yayi motsi zata tambayeshi koda abinda yake so, kana kallan Rafi'ah kasan ba karamar damuwa tayi akan rashin lafiyar luvly brother dinta ba. Ummi ta sauke ajiyar zuciya sannan ta mike ta wuce upstairs. Kujera Rafi'ah ta ajiye musu a balcony suka zauna, lokaci lokaci ta kan bashi labari ko kuma ta nuna mishi abu a waya duk dan ya dan sake, kuma alhamdullilah hakan ya masa dadi sosai, juyawa tayi jin footsteps a bayansu, ganin Ikleemah ce yasa ta juyo taci gaba da bawa Abdul labarin da take,
"To shi dama mutumin shi kadai mamanshi ta hai..." Shiru tayi ganin Ikleemah ta tsaya akansu ta kama kugu, Rafi'ah ta kauda kanta ta ce "Malama Lafiya?" Dariyar karfin hali Ikleemah ta fara yi kafin ta ce "Nazo ne na miki jaje game da abinda ya faru" Rafi'ah ta ce "Wane abu kuma?" Ikleemah ta kara fashewa da dariya ta ce "Wai kina nufin baki da labarin auran Yusuf?" Sosai zuciyarta ya buga, ta juya kanta taki kallan inda Ikleemah take, Ikleemah ta ce "To sai ayi hakuri a nemo wani, dama nasan wahalar banza kike Yusuf ba tsarar auranki bane" tashi Rafi'ah tayi cikin fishi ta ce "Mind your words Ikleemah, meye hadina dake daza ki dinga min irin wannan maganar" Ikleemah ta ce "Ai dama bance na hada abu dake ba, Allah ma ya kiyaye in hada jini da dangin cuta" tass, tass, ya sauke mata mari biyu a kumatun ta, Ikleemah ta zaro ido tana kallan Abdul dake tsaye a gabanta yana huci, yayi pointing dinta da yatsa ya ce "This should be the last zaki kira mu da dangin cuta, and idan cutan ne ai daga familyn ku ta fito, and let me keep this warning to u, Antynah isn't ur mate, u stay far away from her, idan ba haka ba u will know the bad side of me" yana kai karshe ya dauki wayar Rafi'ah ya wuce cikin apartment dinsu, kai kace bashi ke nishin rashin lafiya yanzu ba, daga Ikleemah har Rafi'ah kallansa suke, Rafi'ah ta wuce ciki itama ta bar Ikleemah dafe da kuncinta a tsaye.
Tana shiga ta samu ba kowa a parlor ta wuce dakin Abdul ta murda handle din ta shiga, tsaye ta sameshi gaban mirror da towel a hannunsa, strictly ta ce "Why did u slapped her?" Ba tare daya kalleta ba ya ce "Because she insulted u" Rafi'ah ta ce "Don't u ever try to slap her again, bata girmeka bane? or are u stupid" baice komai ba saima kayansa daya fara cirewa, ta ce "Kuma kasan Abba won't take it likely ko? Yanzu da abinda ya faru da wanda bai faru ba zasu fada mishi, so kake kullum yana yiwa Ummi fada, zai ce fault dinta ne" idanta taap cike da hawaye ta karashe maganar, ita babbar damuwarta bai wuce fishin Umminta ba, shiyasa yanzu komai zai faru ta hakura zata shanye akan Abba yayi wa Umminta fada, rungumeta da taji yayi ne yasa ta dawo daga tinanin data tafi, Abdul ya kai hannunsa idanta ya ce "Pls don't cry sister, insha Allah babu abinda zai faru" a hankali ta ce "But u slapped her Abduljalal, why?" Bayanta ya hau bubbugawa calmly ya ce "Not when they're insulting u sis, bazan iya ganin ana insulting dinki nayi shiru ba, bama zagi ba, wallahi ko kallan banza aka miki bazan bar mutum ba, did u know how much i luv u Aunty?" Rungumeshi itama tayi tana murmushi ta ce "Idan kana sona ta kaida abinda banaso" ya ce "Ohk" daga haka ta sakeshi ta fita jin an bude kofar parlor.
Tinda Abi ya turo Sadeeq ya kira shi ya kasa nutsuwa, ya dinga kai kawo yana tinanin abinda zaije yaji, bayan minti 10 Sadeeq ya kara knocking dakin ya shigo, tsayawa yayi yana kallan yayan nasu ya ce "Abi yana jiranka fa Yaya" kai ya daga masa sannan ya bi bayansa suka fita, parlor ya fita ya zauna akan carpet yana kallan Abi ya ce "Sannu da dawowa" Abi ya ce "Yauwa son" shima shiru yayi ya rasa ta ina zai fara masa bayani, caan dai ya dago yana kallan Jawad da kansa ke kasa ya ce "Naje gidan su Fatima dazu, sai dai kuma the answer wasn't funny saboda an riga da an yiwa wani alkawari, so u don't worry son, kayi fatan Allah yasa haka shine alkhairinka, ya kawo maka wata da ban" tinda Abi ya fara magana Zuciyarsa take bugawa non stop, a hankali ya ce "Ameen" daga haka ya mike ya nufi dakinsa just trying to control himself, yana shiga dakin wasu hawaye masu zafi suka sauko masa, yayi saurin gogewa saboda raban da yayi kuka harya manta a rayuwarsa, ya zauna bakin gado ya kama kansa yana karanto addu'o'i, bayan few minutes aka bude kofar dakin, dagowa yayi suka hada ido da Mami, yayi saurin sauke kansa ya ce "I'm having headache"
[8/3, 7:09 AM] My Imaan: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers._
_By FATIMA ✍🏻_
_36_
*THE PAGE IS DEDICATED TO THE WHOLE MEMEBERS OF ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* 💞
Shiru Mami tayi tana kallansa kafin ta ce "Since when?" Ba tare daya kalleta ba ya ce "Two hours ago" juyawa tayi ta fita a dakin, ba jimawa ta dawo da bottle water sai cup hade da panadol, zama tayi gefensa ta 6alla masa maganin ta mika masa sannan ta zuba masa ruwa a cup ya hadiye, mika mata cup din yayi ya ce "Thank u" Mami ta kar6a sannan ta mike ta ce "U rest first, idan bai daina ba sai muje clinic" kai ya daga mata sannan ta fita a dakin ta jawo masa kofa. Bayan sati daya da bikin Yusuf, Rafi'ah na kitchen tana kwashe shinkafa cikin warmer wayarta ya fara ringing, ta fito cikin nutsuwa ta dauka wayarta sannan ta koma kitchen Ummi ta bita da kallo, picking call din tayi hade da sallama Yusuf ya ce "How are u Baby?" a hankali ta ce "I'm fine" ya ce "Good, zanzo yau da yamma" dan murmushi tayi me kyau tana gyara zaman phone din a kunnenta, dan tinda yayi aure sai yau zata ganshi, waya dai kwana 3 da aure suka farayi, cikin cool voice dinsa ya ce "Or are u not happy? I missed u more than u know Baby" cikin sanyin murya ta ce "I also misaed u Doctor" ya ce "Worry not u will see me insha Allah" murmushi tayi ta ce "Allah ya kaimu" ya ce "I will call u ltr when i'm home, ina driving" toh kawai tace sannan tayi hanging call din tana murmushi. Bayan ta gama komai ta wuce upstairs zuwa dakinta ta tattaro hijabs dinta na hadda ta wuce backyard ta saka a washing machine, tana zaune tana chat da Ameera harya gama sannan ta dauraye tayi spinning ta fara shanyawa, tana gamawa taji anyi parking mota, lekawa tayi taga Mummy na shirin fitowa, ta karasa da gudu ta rungumeta tana murmushi ta ce "You're welcome mother" Mummy ta shafa kanta ta ce "Thank u daughter" handbag dinta Rafi'ah ta kar6a sannan suka wuce ciki.
Haka Rayuwar Rafi'ah ya kasance watarana dadi watarana kunci, babu abinda yake daga mata hankali face idan ta kira Yusuf Jiddah ta dauka, dan dole haka ta dinga avoiding call dinsa ko zata