ganinta ya tashi da sauri ya bude mata back seat yana ta murmushi ya ce "Kinsan turawa nawa na gani sun wuce daga fitar ki?" Rafi'ah ta danyi murmushi ta ce "To idan munje gida zan gayawa Ummi sai kuyi magana" ya sakar mata murmushi yana shafa keyarsa ya ce "Haba haba ai maganar bai kai aje gun Hajiya ba, ni ina ni ina wadannan turawan" Dariya ta danyi taci gaba da danna wayarta shi kuma yaja motar suka fita a clinic din. Suna isa gida Mustapha yayi parking ya fito ya bude mata door ya ce "A huta gajiya" ta ce "Nagode" daga haka ta nufi entrance din gidan, a hankali ta murda handle din kofar ta shiga, sai da zuciyarta ya buga ganin kallan da Ummi ta mata, ta saurin sunkuyar da kanta ta ce "Kiyi hkr, i just saw ur missed call now" Ummi ta dauke idanta a kanta ta maida kan TV ta ce "Take ur breakfast now, after all kizo" akan sofa ta ajiye ledan drugs dinta sannan ta nufi kan dinning ta dauka plate da serving spoon sannan ta bude warmer. Few minutes ta gama cakalar abincin data diba sannan ta dauka glass cup ta bude dispenser ta diba ruwa kafin ta koma parlor ta zauna, ledan drugs dinta ta jawo ta balla wanda take sha as usual sannan ta mike zata bar parlor. "Rafi'ah" sunanta da Ummi ta kira ne yasa ta tsaya, ta juyo da sauri ta ce "Ohh Ummi na manta kince idan na gama" daga haka ta koma gefen mahaifiyartata ta zauna, Ummi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Yanzun nan na gaya maki abu har kin manta Rafi'ah? Me yake daminki ne two days? Or are u sick this days?" Girgiza mata kai kawai tayi, Ummi ta ce "To Allah ya shiryeki, can u remind how many days baki kira Anty Halima kin gaisheta ba?" Turo baki ta danyi kafin ta ce "Ummi ce maki tayi bana kiranta?" Ummi ta mata dakuwa ta ce "Ko karya ta miki? I don't know what's wrong with u this days, gaba daya kinyi turning upside down" Rafi'ah ta sunkuyar da kanta ta ce "Wallahi is her fault Ummi, haka kawai sai tai ta min wata magana da bana so" Ummi ta dalla mata harara ta ce "Do as u wish, ko yayyankaki take banga dalilin rashin kiranta ba, duk duniya ina da wacce ta fita ne, 'yar uwata daya tak a duniya kiyi kusan sati baki kira kinji lafiyarta ba, idan baki kirata ba who will u call?" Shiru tayi ta dinga jujjuya ring din hannunta bata ce komai ba, Ummi ta mike ta ce "Abbanku ma yace baki kira kin gaishe shi ba" Murmushi tayi jin an anbaci Abbanta ta ce "Ai Ummi na fita very early today, da bazan manta ba" Ummi ta ta6e baki ta tattara plate din kan dinning ta wuce kitchen.
Phone dinta dake kan TV stand ta dauka tayi dialing number Abbanta, bugu biyu ya dauka hade da sallama bayan ta amsa ya ce "Good morning Mummy nah" ta dan langwa6ar da kanta ta ce "Morning Abba, how is work?" Ya ce "All fine Mamana, u missed school today why?" cike da shagwaba ta ce "Abba naje clinic yau fa kuma ni kadai na" Abba ya sauke ajiyar zuciya ya ce "This is not safe at all, ya za'ai ta barki ki fita ke kadai?" Shiru kawai Rafi'ah tayi tana jujjuya ring din hannunta, Abba ya ce "How many days baki kira Hajiya kun gaisa ba? She called me day before yesterday and yesterday too still complaining, meya hanaki kiranta ki gaisheta? cewa tayi ma ni nake hanaki zumunci da ita" ta turo baki ta ce "Abba dazu fa Ummi ma saida tamin fada, kuma kona kira Mummy sai tai tamin maganar aure as small as i am" Murmushi Abba yayi kafin ya ce "And that not the reason da zaisa kiyi sati daya baki kirata ba Mamana, remember she the only one of your mother's sister" a hankali ta ce "To" Abba ya ce "Not just To alone, idan baki kirata ba wallahi Abba zai manta da Mamansa yayi mata fada" ta danyi murmushi ta ce "Insha Allah Abba, when are u coming back Abba, muna ta missing dinka nida Abdul" cike da rarrashi Abba ya ce "Worry not Mamana, zan dawo ending week din nan insha Allah" ta ce "Allah ya kawo ka lafiya Abba" ya ce " Ameen, try and be taking ur drugs kinji ko" ta ce "Yanzu ma nasha Abba" ya ce "Good, we will talk ltr in the evening i have a lot to cover" ta ce "Allah ya tsare" ya ce"Ameen Mamana" daga haka yayi hanging call din. Kwanciya tayi akan sofa kafin ta bude lock din wayarta ta kira number Mummy, yana fara ringing ta dauka, Rafi'ah tayi kasa da murya ta ce "Assalamu alaikum" ba tare da Mummy ta amsa sallamarta ba ta ce "Ai dama ubanki kadai zaice ki kirani kiyi" Rafi'ah da mood dinta ya canza ta ta6e baki ta ce "Bafa ki amsa sallamar ba Mummy kuma ba Abba yace na kira..." kafin ta rufe bakinta Mummy ta ce "Keep that ur small mouth shut, inba iskanci irin naki ba kwana nawa baki kirani ba? Ko danni ba Zainab bace?" Rafi'ah ta bubbuga kafarta a kasa ta ce "To kiyi hakuri, ni wallahi zancen auren da kikeminne banaso shiyasa bana san kiranki" Mummy taja dogon tsaki ta ce "Aida dangin ubanki ne da yanzu kin ishesu da kira, kowa da dangin uwarsa yake fara alfahari amma banda ke saboda wauta ta miki yawa, inba hauka ba me suke muku wanda kuke jin dadin sa?" A hankali Rafi'ah ta ce "To kiyi hakuri, i know i hurt but that's not my intention, how will i not call u Mummy, bayan kinyi 1 month bakya kasar, wallahi ina missing dinki sosai" Ajiyar zuciya Mummy ta sauke kafin ta ce "Fine, ita kuma mahaifiyarki zan kirata tana tina muku cewa ni yayarta ce, ni kadai take dashi a duniyarnan tinda ba uwa ba uba" Dariya tayi a hankali ta ce "Ai munsani Mum, tana kuma gaya mana, ni maganar aure ne banaso kina min wallahi" Mummy ta ce "Bari dai na dawo kasar kafin komai, aure ko bakyaso sai kinyi shi tinda ba zama zamuyi tayi dake ba" Rafi'ah ta yatsine fuska ta ce "Ai Abba is not in support, SS2 fa kawai nake Mummy, why not idan na gama degree" Mummy ta ce "Allah ya kiyaye, kina gama secondary school zakiyi aure, shiyasa nake tina miki ki tsaida miji, shi kuma Abban naki idan bazai aurar dake ba sai ya bani ke tinda shi gani yake kamar labari kawai nake, indai ina raye sai dai ki karasa karatunki a gidan miji" Rafi'ah ta dan ta6e baki a hankali ta ce "Ai iyayena ma ba yarda zasuyi ba" Cike da masifa Mummy ta ce "Yimin bori dan ban haifa ba, da ace ina da 'ya'ya mai zaisa na saka miki ido Rafi'ah, ai a rashin babu ne" jin mood dinta ya canza yasa Rafi'ah yin dariya sannan ta ce "Just joking fa Mummy, kiyi hakuri" Mummy ta ce "Sai anjima zan kira idan na koma gida" bata jira cewar Rafi'ah ba tayi hanging call din.
Wajajen karfe 3 na rana Rafi'ah ta tashi daga nauyayyen baccin da yayi gaba da ita, ta mike a hankali ta shiga toilet tayi brush sannan ta doro alwala ta fito, hijabi har kasa ta saka sannan ta hau kan sallaya. Bayan ta idar tayi addu'a sannan ta cire hijab din ta dauka phone dinta dake kan gado ta fice a dakin. Tafiya take cikin quick light step har ta karasa saukowa daga stairs din, ta karasa cikin falon tana kallan Ummi dake marking papers din gabanta, saam bata kula da luvly brother dinta dake zaune akan dinning ba, bayan ta zauna gefen Ummi ya taso a hankali ya cire scarf din kanta, tayi tsaki ta juya tana kallansa ta ce"Ka dawo kenan ko?" daga haka ta kwace hulanta ta saka, tana juyawa ya kara cire mata yana dariya, kamar zatai kuka ta ce "Ummi wallahi zan zane Abdul, kiga abinda yakemin" Ko kallansu Ummi batai ba bare tayi magana, Abduljalal ya zauna gefenta ya dora hannunsa a shoulder dinta ya ce "How are u Anty nah, yau a school anata tambayan ki nace kinje follow-up Clinic" a hankali ta ce "Ohk". Bayan Ummi ta gama marking dinta ta dago tana kallan Rafi'ah da gaba daya tayi collapsing jikin Abdul tana kallo, Ummi ta dalla mata harara ta ce "Tashi ki zauna" mikewa tayi da sauri tana turo baki ta ce "To Ummi kice ya tashi na kwanta, mu 3 akan sofa daya" Ummi ta ce "Ke ki koma caan mana" ta make kafada ta ce "Ni kusanki zan kwanta" tana rife bakinta Abdul ya tashi ya nufi dakinsa yana murmushi ya ce "Na kar6i girman". Daga haka ta koma ta kwanta tayi pillow da cinyar Umminta, bayan few minutes Ummi ta ce "What did u told Abba in the morning?" Tashi Rafi'ah tayi tana kallanta ta ce "I haven't told him anythi..." Kallan da Ummi ke mata yasa tayi shiru ta sunkuyar da kanta, Ummi ta ce "This should be the last zamuyi abu baya nan ki kirashi ki gaya masa, sau nawa ina kaiki Clinic muna kar6an magani?" Tayi shiru still kanta na kallan kasa, Ummi ta ce"Talk now, how many times? Ya kirani dazu yana ta fada na barki kin fita ke kadai, ba Mustapha nace ya kaiki ba? shekara 17 ace bazaki iya zuwa ki kar6a common drugs ba, i still don't like yadda Abba yake treating dinki wallahi, nayi magana harna gaji, wallahi Abdul ya fiki iya abubuwa, ya dawo kamar shine gaba dake, when will u change Rafi'ah fisabililliah?" Sai lokacin hawayen idanta ya sakko, wallahi har zuciyarta ba wai ta fadawa Abba dan yayi fada bane. Bayan hannunta tasa ta share hawayen idanta sannan ta dago ta kalleta ta ce "I'm sorry, and insha Allah i won't repeat such thing again" Ummi ta ce "Better, kin kira Anty Haliman ne?" Ta kara turo baki ta ce "Na kirata dazu, nifa wallahi kice mata ta dainamin zancen aure inba hakaba zan daina kiranta duka duka kowa ma ya huta" Ummi ta ce "To menene damuwanki da zancen aurenta? Wallahi koda wasa kar naji kin daina kiranta, banda shashanci irin naki auran za'a miki yanzu? Ki bita kawai a hankali" Rafi'ah ta share guntun hawayenta ta ce "Kuma harda cewa wai nafisan dangin Abba da ita, ni meye ruwana dasu banda gaisuwa daya zama dole" Ummi ta ce "Ki daina min hawaye dama, koma me zata fada u have to listen, ita kadai nake dashi duk duniya, bayan ni baku da wata uwar data wuce Anty Halima" a hankali ta ce "I know Ummi but ni banason yadda Mummy take abu sometimes, komai sai tayi magana haba" Ummi ta ta6e baki ta ce "And i asked u to cook kikaje kika nemi gado kika hau bacci ko?" ta yatsine fuska ta ce "Zanyi yanzu" Ummi ta ce "It's impossible in jira sai kin gama baccinki na jaraba kafin kiyi abinci, na gama rice kije ki rakasa stew din and if u like pls let it burn" daga haka Ummi ta mike ta dauka scripts dinta ta haura upstairs.
Kitchen ta wuce ta gauraya stew din sannan ta fito ta wuce upstairs zuwa dakinta, Hijabs dinta guda 3 ta dauko duk color daya sannan ta sakko, Abdul ta samu yana zaune yana cin banana, ta karasa kusanshi ta ce "Abdul pls help me and wash my Hijabs, kaga gobe zanje school kuma Thursday akwai hadda" ya juyo yana kallanta ya ce "Let me finish watching this match, i will wash ltr" ta shagwa6e fuska ta ce "Haba Abdul, kawai kaje ka zuba ruwa a washing machine kasa liquid detergent shine sai anjima that's all it's fah" ya ce "Anty banfa ce bazan wanke maki ba, wai ma meyasa ba kisa an kai laundry ba" ta zaro ido ta ce "Da Mustapha sai yayi sati bai kar6o kayanba ni inada Islamiyya jiranshi zanyi, just tell me idan baza kai ba" tashi yayi ya kar6i hijabs din yana kallanta ya ce "Is that all?" Ta bashi light hug ta ce "Thank u dan kanina me kama da Mummy" daga haka ta fashe da dariya, yaja tsaki ya ce "Ni bana kama da ita, kiba ne kawai kamar ita" bin bayanshi tayi har backyard tana ta dariya ta ce "Allah kuna kama" ya ce "That's what people said, amma ai ni bana fada irinna Mummy, jiya fa dana kirata we spent more than 1 hour muna waya, duk kuma complain takemin a kanki" a wani balcony dake wajen ta zauna ta ce "Na kirata ai yau, ta daiyi fada kam, ni dama idan ta gama Umranta ta dawo Nigeria ta wuce Bauchi mu huta" Abdul yayi dariya ya ce "Gidansu anan kice su wuce Bauchi" ta ta6e baki ta ce "To gidanta kam sai bayan wata wata zan ringa zua". Haka sukaita hiran Mummy har kayan ya gama turning ya tsaya, ta kalli Abdul ta ce "Dan Allah kayi spinning Abdul" ya ce "Komai zan maki ne wai" ta ce "Pls, kaga Salma Umar kaninta har nails dinta yake yanke mata idan yayi tsayi, kaga nima yayi tsayi zaka yankemin ko Abdul dina" Murmushi sosai yayi ya tashi ya fara kwashe hijabs din, duk duniya bayan Abbansu da Umminsu ba wanda ya keso sai luvly sister dinshi, he hate seeing her crying, he hate seeing her unhappy, duk wani abu a duniyar nan da zaiyi turning dinta upside down baya sonsa, wani lokaci ji yake inama lalurar da Allah ya dora mata ya dawo kansa. Ji yayi kawai ta tashi a firgice, ya juyo yana kallanta ta ce "What's that Aunty?" Kamar zatai kuka tana kallansa ta ce "Oh my God, it's burnt, it's brunt i know, Allah na manta dashi ne" daga haka ta zura da gudu tayi hanyar kitchen Abdul ya bita da kallo yana kyalkyala dariya.
*Attention pls 🙏🏻*
*This is to inform u that i may not be able to be updating everyday, I'm still in school so sai ranar da kuka ganni kawai, but i promise u that i will try my best to be entertaining u insha Allah, so expect no date of posting, u can see me any day/time. Sannan littafin bana kudi bane na wanda ke da ra'ayin karanwa ne 🥰*
*The page is dedicated to Fadila Madaki* 😍
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_
_5~6_
Anty Khadija ce zaune a babban parlon su da glass cup a hannunta tana shan exotic, lokaci~lokaci ta kan daga kanta ta kalli series din da ake a TV, bayan ta shanye na cikin cup din ta dago kanta tana kallan mahaifiyarta dake zaune a gefenta ta ce "Umma bafa kice komai ba?" Cike da damuwa matar da aka kira da Umma ta juyo tana kallanta, Anty Khadija ta ce "Dole ne fa Umma mu tashi tsaye, wallahi tallahi Yusuf ya kawomin budurwarsa har office dina, i'm still in a state of shock Umma, wai Yusuf da budurwa, lallai kam this is impossible wallahi" Umma ta ajiye remote din dake hannuna ta juyo tana kallan Anty Khadija, sai lokacin ta samu damar motsi, ta kirkiro murmushin takaici ta ce "Ba sai yayi auren ba idan shi yake da iko, indai ina raye rayuwar Yusuf ba zata ta6a kyau ba wallahi, sai dai ya kare rayuwarsa a haka, idan yaso ciwan zuciyar ya kashe shi" daga haka ta mike ta fara haurawa stairs, Anty Khadija taci gaba da chewing gum dinta ta ce "Atoh, indai ba'a dau mataki ba kam komai zai lalace" daga haka ta dora kafarta daya akan daya taci gaba da shan exotic dinta.
kasa dago kanta tayi tana ta wasa da fingers dinta, sai bayan Ummi ta gama mata fada ta ce "Pls don't let me angry again, wallahi zan manta da baki da lafiya na miki duk abinda naga dama" a hankali ta ce "Kiyi hakuri" Ummi ta ce "Ki wuce ki gyara kan dinning" tabi ta gefe a hankali ta wuce zuwa parlor ba tare data bari sun hada ido da Ummi ba. Karfe 8 bayan an idar da sallan isha Yusuf ya shigo parlor, milk shadda ce a jikinsa ta sha aiki, tayi masifar amsar jikinsa kamar dama saboda shi akayi ta, kallo daya Umma ta masa ta dauke kanta, ba yabo ba fallasa ya dan saki fuska ya ce "Sannu da gida Umma" a hankali ta ce "Sannu" Anty Khadija ta ce "Doctor sai yanzu?" ya ce "Wallahi Anty, nayi meeting ne shiyasa na dawo late" ya karashe maganar yana cire lab coat din jikinsa ya nufi dakinsa, Anty Khadija ta bishi da harara kasa kasa ta ce "Wicked man" Umma ta ce "Not only wicked" Anty Khadija ta ta6e baki looking into her mother's eyes ta ce "Ni wallahi Umma a duniya idan akwai wanda na tsana ya biyo bayan Yusuf, duk da nunawa nake ina san shi ina kaunarshi amma bakiga da yadda nasa ya kawomin budurwarta saba" Umma ta harari kofar dakinsa ta ce "Yanzu haka ma wajenta yaje zaice wani meeting yayi, indai ina raye kaida farinciki kunyi sallama,