x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - LIFE PARTNER

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 73416 words

Category: Love Stories

Views 345

17 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
yayarta dake zaune a gefenta tana sauraronta, bayan ta dasa aya matar ta zaro ido hade da kundumo ashar ta ce "Baki fasawa yarinya baki ba? Ita har tana da bakin da zata kiraki da 'yar aiki? Wallahi tallahi Amina kinyi asara, ko uwarsu ce ta fada miki haka bakya tsigale taba ballanta wannan taniniyar yarinyar" Anty Amina ta ajiye glass cup din hannunta ta ce "Nifa Anty Rahama wani abun mamaki na gani that's why i totally forgot her speech, nifa tsohon saurayin Nusaiba na gani ya mata magana" Anty Rahama ta ce "Wacece Nusaiba?" Gyara zama Anty Amina tayi ta ce "Kawata da muka gama karatu tare, wallahi tana sanshi yana santa ingaya maki wata 'yar uwarsa ta shiga tsakani suka rabu, ni kuma dama fa.. Tin kafin nayi aure kyau yakemin, fatana dai ba saurayinta bane, wallahi Anty Rahama bakiga kyansa ba, kamar shi yayi kans... " tsawa Anty Rahama ta daka ta ce "Lallai Amina na yarda kin fara hauka, ina ruwanki da wani saurayi caan da mijinki" ta 6ata rai ta ce "Anty Rahama hauka kuma?" Ta ce "Hauka mana Amina, da kinsan irin tuggun da muka hada nida Umma akan Ya Muhammad ya aureki da baki fadi haka ba, ina gashi muna 'yan wansa na jini amma akace ya nemeni yaki, haka na hakura nayi wannan tsinannen auren da babu komai a cikinsa sai wahala, me za'ai da talauci Allah na tuba" Anty Amina sai kallanta take bata ce komai ba, Hakan yasa Anty Rahama ta kamo hannunta ta ce "Ko kin manta da Ummanmu da mahaifinsa uba daya suke, to haka mukaita kai kawo kauyen Masko har Allah yasa da kansa yaje ya sami Gwaggo Allah ya jikan rai yace yana sanki da aure, ke wahalar da muka sha wallahi bazai misaltu ba, amma gaki shekara 3 har yanzu ko 6ari baki ta6a yi ba" Anty Amina ta ta6e baki ta ce "To Anty kikasan ko shine baya ai... " katseta Anty Rahama tayi ta hanyar cewa "Kuul dama!!! da baya aihuwa ya haifi Rafi'ah da Abduljalal? Ki dai zauna dai, kina gani duk dukiyar nan su kwashe su barki da dan karamin fili" Anty Amina ta mike ta ce "To ai haihuwar ta Allah ce, duk magungunan da kike kawomin ina sha amma shiru har yanzu" Anty Rahama ta ce "Maza bani abinda zan samu in wuce na bar Umma ita kadai Ikleemah ta fice" daki Anty Amina ta shiga ba jimawa ta fito da sarkan gold ta mikawa Anty Rahama ta ce "Ga dai wannan" Anty Rahama ta washe baki ta ce "To barka, sai a siyar aci gaba da nema maki maganin haihuwa, ina dalili shekara 3 fa kenan babu labari" daga haka tayi kasa kasa da murya ta ce "Ni inaga ma wannan kishiyar taki ce tasa miki hannu, dan taga dake ake tafiya Abuja a barta a Kano" Anty Amina ta ce "Nima dai abinda nace kenan, amma koma menene yazo karshe" Anty Rahama ta nufi kofar fita ta ce "Muna nan dake zakiji labari, to nidai na tafi" Anty Amina ta daga mata hannu ta ce "To sai anjima" daga haka Anty Rahama ta fita ita kuma ta dawo ciki.
kwance take jikin Ummi tana ta faman sauke ajiyar zuciya, Ummi ta kamo hannunta tana kallan idanta ta ce "How are u daughter?" A hankali ta ce "Da sauki" Ummi ta gyara mata scarf din kanta ta ce "Allah ya baki lafiya", bude kofar dakin akai Abba ya shigo Abdul na biye dashi, suka karasa kan gadon suna kallanta cike da tausayi, jikinta Abba ya ta6a ya ce "Mamana, ina ke maki ciwo yanzu?" Silently ta ce "My chest Abba, amma kadan kadan yake" Abba ya durkusa dai dai fukarta ya ce "Soon zai daina Mamana, zanje gida na dawo me zan kawo maki?" Ta danyi smiling sannan ta ce "Shawarma Abba" ya shafa kanta ya ce "To Insha Allah" Abdul ya kamo hannunta na hagu yana kallanta ya ce "Get well soon Anty, Allah ya baki lpy me daurewa" kallansa tayi trying hard to control herself ta ce "Thank u love" limshe idanuwanta tayi dan ita kadai tasan abinda takeji deep down, damma da aka mata alluran ya rage mata radadi da ciwo, Abba ya kalli Ummi ya ce "Lie her down and pray Madam, after then itama tayi sallah tayi addu'a sosai kinji Mamana?" Kai ta gyada masa ta ce "To" Ummi ta kwantar da ita ta ce "Allah ya kiyaye, amma Abdul kar ya dawo ya zauna kawai tinda kaima komawa zakayi ai" Abba ya ce "Me zai hana muzo tare mu koma, ai shima yanaso yaga condition dinta" Ummi ta ce "To sai kun dawo" daga haka suka fita ita kuma ta shiga toilet danyin alwala. Yusuf ne zaune a office din Dr. Aryan, bayan ya mishi bayanin abinda ya kawo shi Dr. Aryan ya ce "Allah ya sauwake" daga haka ya kira Dr. Hisham ya sanar masa yadda sukai, on the other side Doctor yace ya kar6a test din nasa sannan ya rubuta masa sabbin magani, after yayi hanging wayar ya kalli Yusuf sannan ya ce "Let me have the test" Yusuf ya mika masa test din, bayan ya duba ya ce "Allah ya sauwke, bari nayi ma wata patient injection idan na dawo saina rubuta maka drugs din, nasan by now she's awake" Dr. Aryan ya karashe maganar yana kallan agogon dake manne a bangon office din, mikewa Yusuf yayi dan sauri yake ya wuce gida, gaba daya he looks so tired, Dr. Aryan ya ce "Can't u wait?" Yusuf ya ce "Let me have the injection saina mata i'm also a medical doctor" daga haka ya ciro ID card dinsa ya mikawa Dr. Aryan, kar6a yayi yaga sunansa, asibitin da yake aiki da year din daya fara aiki sai field dinsa daga karshe, murmushi Dr yayi ya ce "Masha Allah, ashe ina tare da babban likita ne, nice to meet u Yusuf" daga haka ya mika masa allurar Yusuf ya fara hadawa, Dr. Aryan ya kalleshi still smiling ya ce "Me yasa amma baka za6i field din cardiologist ba {Likitan Zuciya}, kodan ciwanka ma?" Yusuf yayi murmushi ya ce "Not interested, and self medication is not allowed" Dr ya ce "Kuma hakane, Allah ya sauwake, let me get the drugs for u, room dinta shine na kan corner, probably room 4" Yusuf ya ce "Ohk" daga haka yaci gaba da hada alluran. Ummi na fitowa a toilet ta kalli Rafi'ah data juya baya sannan ta dauki sallaya tayi hanyar fita, a hankali Rafi'ah ta ce "Ummi ina zakije" tsayawa Ummi tayi ta juyo tana kallanta ta ce "I want to pray outside Rafi'ah, ina nan corridor ko kinasan wani abu?" Girgiza kanta ta hauyi ta ce "No" daga haka ta limshe idanuwanta Ummi kuma ta fita.
Yusuf na gama hada alluran ya fito a office din Dr. Aryan sannan ya nufi room din da Rafi'ah take, da sallama ya shiga room din ya karasa kan gadon, tana kwance ta juya bayanta idanta a limshe, ya karasa dab da ita ya leka fuskarta, zaro ido ya danyi yana kallanta surprisingly enough, jin kamar motsi a bayanta yasa ta bude idanuwanta ta juyo a hankali, ta zaro ido silently ta ce "who i'm i seeing?" Zama yayi a gefenta ya ce "How are u now?" Ta ce "Much better, how did u know i'm here?" Ya danyi murmushi ya ce "My heart told me u are here" ta saki murmushi me kyau ta ce"It's impossible" ya ce "Bakisan idan zuciya na san ganin abu tana searching ta gano in yake ba?" Ta danyi dariyar daya bayyana with teeth dinta kafin ta ce "So ita ta kawo ka kenan?" Ya ce "Sure! Yaushe kika samu attack" ta fara wasa da fingers dinta ta ce "Immediately i entered my house, so i slept to rest, kawai kuma sai na farajin somehow heartburn" Yusuf dake kallanta tin tini ya ce "Allah ya kara maki lpy, are u sure u are taking ur drugs?" Ta daga masa kai ta ce "Ina sha" daga haka ya mike ya ce "I'm giving u an injection now" ta dan matso bakin gadon ta mika masa hannunta, daga hannun rigar yayi yana kallanta ya ce"Kina tsoron Allaura ne?" Ta danyi smiling ta ce "Not that much, amma fa kar kamin da zafi" yana ta dariya ya goge wajen da spirit sannan ya caka alluran, ya dinga kallan fuskarta to see her reaction, sai ma yaga batai wani raki ba, cotton wool ya saka mata a wajen sannan ya ce "Sorry, insha Allah da safe zan shigo na gaisheki" ta ce "Ohk, thank u" ya daga mata hannu ya nufi hanyar fita, kafin ya bude kofar Ummi ta bude ta shigo, ya danyi kasa da kansa with full of respect ya ce "Ina yini Umma" Ummi ta ce "Lafiya kalau" daga haka ya fita a dakin ita kuma ta shigo tana kallan Rafi'ah da har ta sake kwanciya ta ce "Magani aka baki ne?" Ta girgiza kai ta ce "Injection" Ummi ta ce "Tashi kiyi sallah sai na hada maki tea ki sha" daga haka Ummi ta daga ta suka shiga toilet.
Da sallama Abba ya shigo parlorn yana kallan Anty Amina dake zaune, ta amsa masa sallamar ranta babu dadi sannan ta ce "Inata kiran wayarka baka picking" Abba ya zauna yana kallanta ya ce "The phone isn't with me, Rafi'ah ba lafiya anyi admitting dinta dazu, so gobe da safe kije ki duba ta" ta dan hade rai ta ce "Zanje gida fa, banje na gaishe da Umma ba, kuma dama akwai abinda tamin inaso kaja mata kunne" Abba ya dago yana kallanta ya ce "But nace maki tana asibiti ko? And goben make sure kinyi branching kin gaisheta" bata ce komai ba ta wuce kitchen ta dauko masa ruwa da cup ta ajiye a gabansa sannan ta koma daki ya bita da kallo ganin fuskarta kamar an kunna wuta. Washegari wajajen karfe goma Anty Amina tazo asibiti, duk ranta a 6ace yake dama ba dan Abba ba da ba zuwa za tayi ba, a hankali ta bude kofar ta shiga ko sallama babu, kan kujera ta zauna tana kallan Ummi ciki ciki ta ce "Ina kwana" Ummi dake hadawa Rafi'ah tea ta ce "Lafiya" Anty Amina ta ce "Ya mai jiki" Ummi ta ce "She's getting better", bude kofar toilet Rafi'ah tayi ta fito, towel kadai ne a jikinta ta karaso ta zauna akan gado tana turo baki, ganin hararan da Ummi ke mata yasa ta danyi kasa da murya ta ce "Good morning" Anty Amina ta mike tana kallan Ummi ta ce "Sai anjima" daga haka ta bude kofar ta fita. Verseline Rafi'ah ta shafa sannan tasa riga da wando ta koma kan gadon ta kwanta, tinaninta Ummi zatai mata fada amma kuma sai taga akasin haka, Ummi ta mika mata tiree me dauke da tea sai bread da chips a gefe ta ce "Tashi kici abinci" Mikewa Rafi'ah tayi ta kar6a tiree din sannan ta faracin abincin, few minutes ta gama ci ta ajiye sannan ta goge hannunta da tissue ta kwanta, waya Ummi ta mika mata ta ce "Ga Anty Halima, jiya ta kira kinyi bacci" kar6an wayar tayi ta kara a kunne ta ce "Mummy" from the orther side Mummy ta ce "Daughter how are u?" a hankali ta ce "Da sauki sosai" Mummy ta ce "To adai dinga kiyayewa, ni dama hankalina bai kwanta ba da kikace zaki raka waccen matar shopping, wallahi badan kar Muhammad yace ina shiga hurumin gidansa ba da babu inda zaki, muka sani ma ko ita ta jawo miki ciwan ya tashi" dariya Rafi'ah tayi ta ce "Sai bayan fa mun dawo Mummy" taja tsaki ta ce "Ke dai kibar mace Rafi'ah, mata akan kishi babu abinda basayi, bari dai na dawo kasar fuskarki ma ba zata gani ba" Rafi'ah ta ce "To Allah ya kaimu" ta ce "Ameen" daga haka ta mikawa Ummi wayar. Bude kofar dakin akayi Yusuf ya shigo da sallama, Ummi ta amsa tana kallansa, ya karaso ciki ya dan tsuguna ya ce "Ina kwana Umma" ta ce "Lafiya kalau" ya ce "Ya mai jiki?" Ta ce "Da sauki, sai godiya" daga haka ya ajiye babban bakin ledan dake hannunsa ya dan kalli Rafi'ah data takure waje daya ya ce "How are u feeling?" A hankali ta sunkuyar da kanta ta ce "Da sauki" daga haka Yusuf ya juya ya ce "Allah ya sauwake, sai anjima" Ummi ta ce "To mungode Allah ya saka" daga haka ya fita ya rife kofar. Ummi ta kalli Rafi'ah ta ce "Who is he?" Dago kanta tayi ta ce "Doctor ne, shine ai wanda yamin injection jiya da daddare" Ummi bata sake cewa komai ba ta nemi waje ta zauna, Gwalalo ido Anty Khadija tayi ta ce "Yusuf nake gani a nan? Naga jiya yace yazo ya kar6i magani, in fact ai ba nan ake zuwa ba" ta wuce Nurse din da suke magana tare tabi bayan Yusuf, cikin few minutes ta karaso shi ta ce "Malam meya kawoka nan? Meyasa bakaje aiki ba?" Yusuf ya juyo yana kallanta ya ce "Nazo na duba abokina ne baiji dadi ba" Anty Khadija ta ce "To bari naje na ganshi, kaga ai zaiji dadi" daga haka ta nufi room din da Rafi'ah take, cikin sauri ya tare ta ya ce "Aiba dole saikin je ba, baima sanki bafa" Anty Khadija ta tsaya tana kallansa, ta karasa bakin kofar da sauri tasa hannunta akan handle din kofar zata bude Yusuf yayi saurin janye hannunta ya ce "Why won't u mind ur own business? Nace maki baima sanki ba".

*SHARIK HAYATI*

Dedicated to Maryam Shehu 🧡

_08103810398_
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_15~16_

Kiran da CMD yayi wa Anty Khadija yasa ta juya tana hararan Yusuf ta bar wajen, sanyayyar ajiyar zuciya ya sauke hade da limshe ido sannan ya juya ya fita shima, direct parking space ya nufa ya shiga motarsa ya bar clinic din. Misalin karfe 5 na yamma akai discharging din su Rafi'ah, bayan an gama kai komai mota Abba ya shafa kanta looking into her eyes ya ce "Sannu Mamana, i hope u are not feeling any pain?" Ta daga masa kai tana gyara wuyan hijabinta ta ce "Ehh Abba" ya kalli Ummi dake nade bedsheet din kan gadon ya ce "Let's go Madam" ta ce "Ina fitowa yanzu, akwai sponge dinta a toilet da sauran abubuwa zan dauko" Abba ya kama hannun Rafi'ah suka fita a dakin, sai sannu yake mata har suka isa mota, ya zaunarta a back seat ya durkusa daidai fuskarta yana murmushi ya ce "What do u want to eat?" Ta mayar masa da murmushi ta ce "Nothing Abba" ya shafa fuskarta ya ce "In siya maki Shawarma, i know u like it" ta zaro ido tana dariya ta ce "Abba bayan a asibiti shawarma nayi ta ci, nidai a'a banaso" ya ce "To me kikeso?" Ta ce "Dan~wake, nasan Ummi zata dafamin idan muka koma" Abba ya zaro phone dinsa a aljihu ya ce "Let your stepmother cook, kinga muna zuwa idan kikai wanka sai kici" ita dai murmushi kawai tayi tana kallan Abbannata, yana fada mata bai jira cewarta ba ya kashe wayarsa, Ummi na karasowa ta shiga front seat Abba ya zagaya mazauninsa yaja motar suka tafi. Cikin 15 minutes suka isa gida, Mustapha ya bude gate suka shigo, bayan Abba yayi parking ya fito yana kallan Rafi'ah dake kokarin bude kofa ya ce "Let me get the food for u" ta daga masa kai tana satan kallan Ummi, suna hada ido tayi saurin sunkuyar da kanta, Ummi dake kallanta ta ce "Which food?" Rafi'ah ta rife kofar motar ta ce "Dama Abba ne yace wai tamin dan wake" Ummi ta ta6e baki ta nufi entrance din gidan, tana danna bell Abdul ya bude yana mata sannu da dawowa, daga haka ya wuce ta ya rungume Rafi'ah yana patting bayanta ya ce "Welcome home dear" ta shafa bayansa itama ta ce "Thank u bro" daga haka ya kama hannunta suka shiga ciki, suna shiga ta kwanta kan sofa tana limshe ido, Ummi ta ce "Get up Rafi'ah" ta dan turo baki ta ce "I just want to rest Ummi i'm not sleeping" Ummi ta ce "Won't u bath?" ta ce "Ba yanzu ba" Ummi ta dagata ta ce "Tashi kije kiyi wanka" tashi tayi dan ba yadda zatai ta wuce upstairs. Cikin fishi Abba ya shigo farlon ya zauna, kana kallansa kasan ransa a 6ace yake, kallan direction din inda yaji footsteps yayi, Ummi ta ajiye flask din hannunta akan dinning ta ce "What are u taking for dinner?" Abba ya girgiza kai ya ce "Ki hadawa Mamana abinda tace tana so, i think tea is ok for me" ba tare da Ummi ta kalleshi ba ta ce "Dama ban jira tamin ba ai, na riga na gama komai ruwa kawai nake jira ya tafasa" Abba ya juyo yana kallanta, ganin ta koma kitchen yasa ya mike ya nufi mosque danyin sallan magrib, ba jimawa Rafi'ah ta sauko cikin sleeping dress dinta iya knees, Ummi ta juyo tana kallanta ta ce "Have u pray?" Ta ce "Yes" Ummi ta ce "Abincin yana kan dinning, and after all ki tabbar kinyi combing gashinki" Rafi'ah ta shafa gashinta dake daure da ribbon tana kallan Ummi ta ce "Dan Allah kimin" Ummi ta dalla mata harara ba tare da tace komai ba. Anty Khadija ce
End Ads