x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - LIFE PARTNER

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 73416 words

Category: Love Stories

Views 338

17 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
aure kuwa sai dai yaga anayi" Anty Khadija ta ce "Sai fa kinyi da gaske kin kara cusa masa tsanar rayuwar aure, ni dama i just wanted to know ko yana da budurwa yasa na matsa masa, kuma na ganta, fara sool, gata yarinya da ita" Umma ta ce "Ina nan dake shida kansa zaice baya santa wallahi, banda shi ba ma yaji da ciwan dake daminsa zai jajibowa kansa soyayya, ai insha Allahu wannan yarinya itace ajalinsa" Anty Khadija tayi murmushi ta ce "Allah yasa, kinga idan ya mutu ai wancen tsohon zai daina mana maganarsa kowa ma ya huta" Umma ta ce "A juri zuwa rafi dai" kiran daya shigo wayarta ne yasa tayi shiru ta dauka wayar ta kara a kunne, bayan ta gama answering call din ta ce "Wai yaushe Jiddah zata dawo ne Umma?" ta ce "Duk sanda kika dawo da ita, dama bake kikace ta tafi a gidan ba" Anty Khadija ta ce "I'm thinking about something, why not muyi amfani da Jiddah ta hanyar rushe soyayyar Yusuf da waccen yarinyar" Umma tayi murmushi ta ce "Haka ma yayi" daga haka Anty Khadija ta mike ta nufi upstairs tana dialing phone number din Jiddah.

Ranar Friday da yamma Rafi'a na zaune a dakinta tana tilawa Abdul ya shigo rike da phone dinsa ya na "Mummy want to talk to u" ta kar6a wayar ta kara a kunne hade da sallama, Mummy ta ce "I don't really know the essence of ur phone Fatima, why is it always off? Haka saurayinkin yake kiranki yaji ko yaushe a kashe" Abdul ya sheke da dariya harda kwanciya, turo baki kawai tayi kafin ta ce "Ni Islamiyya zan tafi ai mun gaisa" Mummy ta ce "Kika kashemin waya wallahi sai ranki ya 6aci, daga tambaya zaki taramin mutane wani wai islamiyya, Allah yasa Madina zaki taho" Qur'an din ta ajiye gefen bed side drawer ta mike tsaye, Mummy ta ce "To dama next week zan dawo, nace bari na fada da wuri dan ranar dana sauka dake zan wuce gidana" kallan wayar kawai Rafi'ah take with confusion ta ce "I will just go and see u Mummy, Abba ya hanani barin gida" Mummy taja tsaki ta ce "Sai na gani ai, na ta6a jin yadda ake hana diya taje wajen yayar uwarta, shekara nawa ina naci ya bani ke baiban ba na hakura, sai dan kwana uku zuwa hudun da zakimin zai hana, da anyi magana yace ba lafiya kike dashi ba, ai yanzu kam we have to drop a very big thank to God, Zainab tacemin bai fiye tashi ba yanzu ko?" daga mata kai tayi kamar tana gabanta sannnan ta mikawa Abdul wayarsa ta ce "To Allah ya kawoki lpy" Mummy ta ce "Alright sai anjima" daga haka tayi hanging wayar.
Dai dai lokacin Ummi ta bude kofar dakin, ta dinga kallan Rafi'ah dako uniform din boko bata cire ba, gashi har ana shirin islamiyya, Ummi ta ce "Why haven't u remove ur uniform Fatima?" A hankali ta ce"I slept off bayan na dawo, yanzu zanyi shirin islamiyya" Ummi ta ce"Hope u are not sick?" Girgiza mata kai tayi ta ce "Noo, stress ya sani bacci Ummi" ta ce "Ohk, Abba yana hanya fa" tayi wani tsalle hade da kara ta ce "Are u serious Ummi?" Ta daga mata kai ta ce "Sure, ya kiraki bai sameki ba" gaba daya she can't hide her happiness, ta rungume Ummi cike da shagwa6a ta ce "Almost 2 months fa banga Abba ba Ummi, amma dai muma 2 months zai mana ko?" Ummi ta zameta a jikinta ta ce "I don't know" Rafi'ah ta zauna gefen gado ta ce "Is he alone?" Ummi ta dalla mata harara ta ce "U can call him and ask" turo baki tayi ta tashi ta fara cire uniform dinta ta ce "Ai nasan waccen matar saita biyoshi" Ummi dai bata kula taba ta kalli Abdul dake kwance kan gadon Rafi'ah ta ce "Kai ba zaka je islamiyyan bane?" Ya mike yana kallanta ya ce "Zanje Ummi" ta ce "Oya do fast is after 4 now" daga haka ta fice a dakin yabi bayanta shima. Har Abdul ya shiya ya dinga jiran Rafi'ah a mota bata fito ba, ya kalli Mustapha dake kallan film din india a wayarsa ya ce "Let me check on her" daga haka ya koma cikin gida, a parlor ya samu Ummi tana tasa turaren wuta, ta juyo tana kallansa ta ce "Baku tafi bane, karfe 4 da rabi fa" ya tsaya yana kallanta ya ce "Anty isn't out fa Ummi" ta ajiye kwaskon hannunta ta nufi stairs ta ce "The only thing Rafi'ah can do fast is to sleep, in dai bacci ne tana kwanciya bata kara minti daya" tana bude kofar dakinta ta sameta a gaban mirror tana ta fama da trouser dinta ta kasa daure tazuge, dama mostly Ummi ke daura mata ko Abdul, itama ta koya amma yau gaba daya ta rasa kan abin ta masa kulli yafi hudu, dago kanta tayi tana kallan Ummi kamar zatai kuka ta ce "Help me pls Ummi, i can't do it, tin dazu yaki zama, my neck is even aching" Ummi taja tsaki ta karasa gabanta ta durkusa tana gyara mata ta ce "Keep shut now before i give u a dirty slap, when was the last time na koya maki daura abin nan" kamar zata fashe da kuka ta ce "Ummi ni kasawa nayi, I'm just trying my best but na kasa daurawa" mikewa Ummi tayi bayan ta gama daura mata ta ce "Wear your hijab and come out now" ta dauka zulelen hijab dinta har kasa ta saka sannan ta lankaya side bag dinta da qur'an ke ciki ta biyo bayan Ummi, bayan sun sauko ta bata light hug ta ce "Pls Ummi kiyi ma Abba hug dina kafin na dawo na mishi wani" Ummi ta dalla mata harara ta wuce kitchen, murmushi tayi ta fita a parlo'n ta wuce parking lot, bayan ta shiga motar Abdul ma ya shiga, Mustapha ya juyo yana kallanta ya ce "Wani film din india nake kalla Hajiya Rafi'ah, yarinyar yadda kikasan ke, komai naki take, ita fa har takalmin makaranta mahaifiyarta take saka mata" dalla masa harara Rafi'ah tayi ta shiga turo baki, hakan yasa yayi shiru yaci gaba da tukinsa, dan yasan yau babu me ta6a Rafi'ah tinda Abba yake hanya, in kwa aka ta6a ta har abinda aka mata tin tafiyarsa saita juye masa, shima Abdul shiru yayi ganin irin 6ata ran da tayi, bayan few minutes ta ce"Ai duk kaika fada mishi" Abdul ya zaro ido ya ce "I'm not the one sis, have u forgotten he said... " toshe kunnuwanta biyu tayi, cikin tsawa ta ce "I don't want to hear anything pls" shiru yayi ya juya kansa gefe, yasan by this time kam sunyi late kuma ana duka, shi kuwa tinda ta masa shouting bazai kar6a mata duka ba yau.
Mustapha na parking suka fita yaja mota ya barsu a wajen, Abdul ya nufi gate din ya tura, zaro ido tayi ganin students a compound ana ta dukan lattee, Abdul ya danyi murmushi ya shige ciki tabi bayansa, duk gaba daya ta gama tsorata sai numfashi take saukewa daki daki, ga idanuwanta da suka fito alaman tsoro, bayan an yiwa kowa Abdul ya mika hannunsa aka masa guda hudu ya wuce, Rafi'ah da duk ta rude ta ce "Pls don't leave me Abdul, pls help me kaji dan Allah" ko ya juyo ya kalleta ya shige ciki abinsa, Malamin ya daure fuska yana kallanta ya ce "Kawo hannunki" ta ce "Ai Abbana yazo ya fadawa Malam Ahmad kar ana dukana, bani da lafiya wallahi" wani kallan rashin mutunci ya mata ya ce "Ai kowa ma ba lafiya ce dashi ba, ki kawo hannunki na dakeki ki wuce aji an fara kar6an hadda" ta dukunkune one side ta ce "Pls let me go, i promise not to come late again, dan Allah kamin hakuri" Tinkarota malamin yayi ta fasa kara jikinta ya hau rawa, har idanta ya cika da kwalla ta dago tana kallansa ta ce "For God sake na roke ka". Muryar wani malami sukaji yana cewa "Wannan ai mahaifinta yazo tin shigarsu islamiyya ya sami headmaster, ai ba'a dukanta Malam Umar" ko kallansa Malam Umar baiyi ba ya ce "Su sauran 'ya'yan da aka daka ba mutane bane, dan meyasa zaku ware ta ace baza a ta6a taba, ni ba ruwana da ubanta koshi waye dukanta zanyi wallahi" Malam Sadeeq ya ce "Ba batun 'yar wani bace Malam, indan haka za'a bi ai rabi da quarter ba dukansu za'ai ba, ina maka bayani ne akan akwai dalilin da yasa ba'a dukanta" ganin ko kallansa baiyi ba yasa ya wuce ya barsu a wajen, sai lokacin hawayen idanta suka gangaro kasa, ya daka mata tsawa ya ce "Bani hannunki kona miki a jiki ki wuce" girgiza masa kai ta hau yi ta saita kofar gate ta fita a dari da sittin.
Cikin saurin ya taka birki yana fadin innalillahi, itama gaba daya ta tsoruta jira kawai take taji an kade ta, jin shiru yasa ta bude hijabinta a hankali tana kallan gabanta, sai kuma ta sunkuyar da kai ta kasa magana, Yusuf ya fito a motar sanye da lab court, daga gani yanzu ya tashi a clinic, ya dinga kallan Rafi'ah da kanta ke kasa ya ce "U again" ta dago da sauri jin muryarsa, suna hada ido ta saukar da kanta kasa, ya matso kusa da ita ya ce "U haven't forgot the other incident right?" Ta girgiza kai a hankali ta ce"It isn't my fault that time, shine yazo ya bigeni without me knowing and baiyi horn ba" ya danyi murmushi yana kallanta ya ce "Yau fa?" ya karashe magana yana shafa beard dinsa, ta kara sunkuyar da kai ta ce "I'm sorry it wasn't intentional, and dukana za'ai" Yusuf ya dan zaro ido ya ce "Who?" Ta ce "Malam Umar" ya kalli gate din islmiyyar sannan ya kalleta ya ce "Why?" Kamar zata fashe da kuka ta ce "Is because i'm late" ya ce "And why did u came late?" Sai lokacin ta dago kanta tana kallansa ta ce "Na kasa daura tazugen wandona shin... " zaro ido tayi da sauri taja baya, sai a lokacin ta lura saam bai dace ta fada masa haka ba, ya danne dariyar dake cinsa ya ce "Then what?" Ta fara kame kame ta ce "Noo i slept off.... Yes i slept and... And i woke up very late..Very late i swear"
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_7~8_

Folding hannayensa yayi yana kallan idanta ya ce "This is not strictly true" ta saukar da kanta kasa a hankali ta ce "It's true" murmushi me kyau yayi ya dan matsa gefe kafin ya ce "To ki shiga ciki" ta noke kafada ta ce "No, i'm going back home" ya ce "Why?" Ta ce "Yace zai dukeni to" ya danyi murmushi yana shafa tulin gashin dake kansa ya ce "To muje na kar6a maki" ta dan zaro ido ta ce "Are u serious?" Ya ce"Sure let's go" ta saki wani daddaden murmushi tabi bayansa suka shiga gate din. Ba kowa a compound din sai sound din karatun student, ya juyo yana kallanta ya ce "where is ur class?" Ta nuna masa upstairs da hannunta ta ce"A sama ne" bin staircase din yayi da kallo kafin ya fara takawa tabi bayansa. Suna hawa ta nuna masa class dinsu, ya shiga da sallama ya mikawa malamin hannu, ita dai Rafi'ah na tsaye bakin door tana kallansu, bayan sun gama magana Yusuf yayi masa godiya sannan ya fito, a dai~dai bakin kofa ya tsaya yana kallan Rafi'ah ya ce "U can go in, and kicewa Umma a dinga saka maki robber a wando ba tazuge ba" tayi saurin rife fuskarta da hijab dinta, ya danyi murmushi a hankali ya ce "Bye bye" daga haka ya nufi stairs ya fara sakkowa, Yana fitowa ya shiga motarsa yasa mata key ya wuce.
Minti 10 ya kaishi gida, yayi horn gate man ya bude sannan ya shiga yayi parking, fitowa yayi ya bude back seat ya dauko laptop dinsa da lab coat sannan ya nufi entrance din gidan, da sallama ya shiga parlon fuskarsa hade da murmushi as usual, Jiddah ta taso da sauri ta kar6i laptop din hannunsa tana farfara ido ta ce "You are welcome Ya Yusuf" shi dai kallanta kawai yake da mamaki, ta turo baki ta ce "Ya Yusuf ba magana kuma" sauke idansa yayi a kanta ya ce "Thank u, when did u came back?" Fuskarta dauke da murmushi ta ce "In the morning" Ya ce "U are welcome" daga haka ya wuce dakinsa tabi bayansa, kan bed ya nuna mata ta ajiye masa laptop din sannan ta juyo tana kallansa ta ce "Yaya" ya ce "I'm all ears?" Ta ce "What will u eat" juya kansa yayi gefe baice komai ba, ta dinga kallansa kafin ta ce "Or are u not hungry?" Sai lokacin ya sauke ajiyar zuciya ya ce "I just need a cup of tea" ta ce "Alright, bana hada maka" daga haka ta nufi kofar fita ya bita da kallo.
Jiddah na hada tea tana ta murmushi Anty Khadija ta shigo kitchen din, strictly ta dinga kallanta kafin ta ce "Wa kike hadawa tea da la'asar din nan" Jiddah ta juyo tana murmushi ta ce "Anty Khadija Ya Yusuf ne ya dawo, and he want to take a cup of tea" Anty Khadija taja dogon tsaki ta karasa gabanta ta dauka cup din tea din ta zubar cikin sink kafin ta kama kunkuminta tana kallan Jiddah eyes into eyes ta ce "Ubanwa yasa ki hada masa tea?" Sauke kanta tayi kasa ta ce "Anty Khadija naga yanzu ya dawo a Clinic kuma yana bukatar kulawa tin safe... " bige bakinta Anty Khadija tayi ta ce "Keep quite before i give u a dirty slap, kawai daga ganin sarkin power sai miya tayi zaki, an gaya miki kulawa dashi kika zo yi" Murguda mata baki Jiddah tayi kafin ta ce "To ke ina ruwanki dani, nifa gaskiya bazaki takuramin ba wallahi, ki fita a harkata kawai, idan ba haka ba duk abinda na miki ke kika sani" daga haka tayi wucewarta fuuuuuu ta barta tsaye a wajen. Mamaki sosai ya kama Anty Khadija ganin abinda Jiddah ta mata, har yaushe bakinta ya bude da zata na fada mata maganganu irin haka, ta sauke ajiyar zuciya kafin ta fita a kitchen din tayi hanyar stairs.

Alhaji Muhammad Sageer shine mahaifin Yusuf, babban dan kasuwane sannan yana da tarin dukiya, Alhaji Muhammad mutum ne mai san mutane da taimakon talakawa, matarsa kwaya daya tak me suna Aisha, shekararsu 5 da aure sannan ta haifi Yusuf, tin daga lokacin ya dauki san duniya ya daurawa Yusuf, idan kanaso kaga 6acin ransa to ka ta6a masa only son dinsa a rannan ne zakaga 6acin ransa kaca~Kaca. Watarana suka dauki hanyar Kaduna dan zuwa ziyarar 'yan uwa da abokan arziki, a hanyarsu ta dawowa sukai hatsari Allah ya kar6i ransa da matarsa, a lokacin Yusuf nada shekara 15. Tin daga ranar kanwar mahaifin Yusuf ta kar6eshi, zama na rashin dadi Yusuf yake a hannunta, daga haka har ta kafe ta tsare duk wani gadon Yusuf ya dawo hannunta, gashi ba komai take masa ba, kai kace ba da dukiyarsa take shanawa ba, itama mijinta ya mutu sai 'yarta kwaya daya Khadija, tin daga lokacin bata kara aure ba, itace waccen kasa gobe wannan, ta sayi gidaje da dama bayan na gadon Yusuf, daga haka ta tsunduma cikin kasuwanci, kan kace kwabo kudi sai kara haka6a yake, sai dai Yusuf ba abinda ya karu da kudin duk da kudinsa ne, karatun likitanma da yayi a Dubai mijin kanwar mahaifiyarsa ce ya biya masa, bayan ya tafi itama Umma ta biyawa Anty Khadija tayi karatunta a kasar Cyprus, kusan a tare suka dawo, suka kuma fara aiki a tare sai dai kowa inda yake aiki da ban ne.
Jiddah 'ya ce agun kanin mahaifin Khadija, shekararta 20 kacal a duniya, gidansu yana nan kusan su Anty Khadija, tinda Yusuf ya nuna yana santa Anty Khadija ta koreta wai sai ta koma gidansu saboda ba gidan ubanta bane, watan ta kusan 5 bata gidan, sai yanzu ta kirata ta bata hakuri saboda dawowanta zai mata amfani wajen 6ata soyayyar Yusuf da Rafi'ah a yadda ta dauka soyayya suke.


*😃 sorry ina busy wallah, ziyara nake kota ina, but i promise akwai update gobe insha Allah.*


_08103810398_
[6/9, 11:00 AM] Teemarh: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️
_We are here to Educate, Motivate and Entertain our Readers_
〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️〰️

*BY FATIMA* _{Real~Teemarh}_

_9~10_

Anty Khadija na gama hawa upstairs ta wuce dakin Umma, nan ta samu Jiddah ta gama fada mata duk abinda ya faru, cike da masifa Anty Khadija ta ce "Ubanwa kika murgidawa baki?" Jiddah ta 6ata rai tana kallan Umma ta ce "Kingani ko Umma, ni kenan kullum sai taita takuramin, what's her business with me?" Anty Khadija ta nuna ta da yatsa ta ce "Sai in kakkaryaki wallahi na zubar da abin banza"
End Ads