da "To". Kallansa Anty Amina tayi ta ce "Ko wanda kuka dauka aiki ne? Wanda ka bani labari" Abba ya ce "No, wannan wanda yake neman Rafi'ah ne" Wani katon abu ta hadiye hade da zaro ido bata dai ce komai ba, Abba ya fita a parlorn bayan yasa takalmansa.
Har bakin gate Ikleemah taje tace wa mustapha Abba yace a kaishi BQ, Mustapha ya bude kofar yana kallan Yusuf dake jingine jikin mota ya ce "Oga yace ka shigo" Yusuf ya shigo yana kallan Mustapha ya ce "Nagode fa" Mustapha nata washe baki ya ce "Bismillah" daga haka Yusuf ya fara binsa a baya, juyowa Ikleemah tayi suka hada ido da Yusuf, sai da kirjinta ya buga ganin yadda yayi kyau, ta dan saki murmushi ta juya, sai kuma ta fara tafiya slowly har suka iso dai dai da ita, ta sake kallansa cikin iyayi ta ce "Ina yini" ya ce "Lafiya kalau" daga haka ta shige apartment din Anty Amina, har bakin kofar parlorn Mustapha ya rakashi ya ce "Nan ne, zaka iya shiga" Yusuf ya gyada masa kai sannan ya murda handle din a hankali hade da sallama, Abba ya amsa shi cike da fara'ah ya ce "Bismillah", kan carpet ya zauna kansa a kasa ya ce "Ina yini Abba" Abba ya ce "Lafiya kalau, ya aiki" Yusuf ya ce "Alhamdulilah ka iso lafiya?" Abba ya ce "Lafiya kalau", shiru ne ya biyo baya, Abba ya kira layin Ummi bayan ta dauka ya ce "A kawo abinsha BQ" daga haka yayi hanging wayar, Abba na murmushi ya sake kallan Yusuf ya ce "Your name" Yusuf ya kara kasa da kansa ya ce "Sunana Yusuf",
Ikleemah na shiga parlornsu dama ta samu Anty Amina jikin window tana leken wanda zai wuce, Ikleemah ta zauna gefenta ta ce "Naga halittar ubangiji Anty, kinga kyansa kuwa?" Anty Amina ta ce "Ni dama nasan wannan santa yake" Ikleemah ta ce "Kinsan shi Anty? Wallahi na kamu da san shi" Anty Amina ta ce "Saurayin Rafi'ah ne, taab ai wallahi ba zatai auren jin dadi ba, sai tayi auran wahala tazo tana rokona na sammata abincin da zasu ci" Ikleemah dake kallanta ta ce "Anty wallahi kyakkyawa ne" Anty Amina ta ce "Yanzu tashi na hada miki fruits ki kai masa" cike da murna Ikleemah ta ce "Yauwa Anty, zan kare masa kallo" daga haka tabi ta zuwa kitchen.
Gajiya Ummi tayi da jiran Rafi'ah ta tashi ta haura sama, tana nan ta dukunkune a karshen gado tana rera kuka, Ummi ta dalla mata harara ta ce "Idan bazaki kai ba sai ki tashi kije ki fadawa Abban cewar baza ki iya ba" cikin kuka ta ce "Allah Ummi ni bazan iya ba, ni dai ki bawa wani ya kai" Ummi ta ce "Ni kikeso naje na kai kenan? Ai iyayin dayasa kika bari Anty Halima tasan shi, shi zaisa ki dauki hijab dinki ki kai masa ruwan sha" daga haka Ummi ta fice a dakin, Tashi Rafi'ah tayi ta leka ta window dinta ta hango motar Yusuf, hakan yasa ta kara fashewa da kuka ta zube a wajen, Ummi ne ta bude dakin ta dawo rike da wayarta yana ringing ta mikawa Rafi'ah ta ce "Sai ki fada masa bazaki kai ba" daga haka ta ajiye mata a kan gado ta fita. Tashi tayi a hankali ta shiga toilet ta wanke fuskarta sannan t fito ta bude press dinta ta dauko gogggen himar dinta har kasa tasa akan gown din jikinta,
Sai sauke ajiyar zuciya take ta sauko downstairs, Ummi ta nuna mata babban tray akan dinning ta ce "Gashi caan ki dauka" Rafi'ah ta dinga kallan kan tray din ganin drinks har kala 4 sai kankana a yayyanke cikin dan bowl da pineapple sai Apple a gefe, turo baki tayi ta dauka ta fita a parlorn Ummi ta bita da kallo harta fita.
Murmushi Abba yayi bayan ya gama sauraron meaningful words din Yusuf ya ce "Amma iyayanka 'yan nan garin ne?" Yusuf ya ce "Ehh, sunan mahaifina Muhammad saraki, amma Allah ya musu rasuwa shida mahaifiyata shekara 7 kenan, akwai dai kanwar Mamana a unguwar Rimi, yanzu dai ina zaune ne wajen kanwar mahaifina da suke uba daya" Abba ya girgiza kai looking so sad ya ce "Allah ya musu rahama" Yusuf ya ce "Ameen".
Rafi'ah na zuwa dai dai apartment din Anty Amina Ikleemah ta fito rike da tray itama, fruits salad ne a gefe sai fanta da glass cup, Rafi'ah ta dalla mata harara ta wuce, itama harara ta dalla mata tabi bayanta, ajiye tray din Rafi'ah tayi ta bude kofar parlorn, Ikleemah ta shige da sauri, harara Rafi'ah ta bita da shi, daga haka ta dauka tray dinta ta shiga da sallama, a gefen Yusuf ta samu Ikleemah ta zauna wai tana gaishe shi, ta dire tray din hannunta ta juya ta fice a parlorn Yusuf ya dan saci kallanta, bayan sun gama gaisawa da Ikleemah ta mike tana ta rangwada ta fita a parlorn itama. Abba ya ce "Bismillah son, ga abinsha da abinci" Yusuf yayi kasa da kansa yana murmushi, bayan few seconds Abba ya ce "Kace kana aiki a Aminu kano TH ko?" Yusuf ya ce "Ehh" Abba ya danyi shiru kafin ya ce "But kasan class din da take a school?" Ya dirgiza kai, nan kwa yasan a SS2 take , Abba ya ce "To tana SS2 yanzu, sannan koda zatai aure sai ta gama secondary school, na kuma maka alkhawarin in har na gama bincikena zan baka auran Rafi'ah but on one condition" sai lokacin Yusuf ya kalli Abba sannan ya maida kansa kasa, Abba ya ce "Zata ci gaba da karatunta a gidanka" Ajiyar zuciya Yusuf ya sauke ya ce "Insha Allah Abba, nayi alkawari" Abba ya ce "To masha Allah, Allah yayi albarka, bari na amsa waya"
Yusuf ya ce "To Abba" daga haka Abba ya mike ya fita. Rafi'ah na komawa apartment dinsu ta wuce dakinta taci gaba da kukanta, abinda yake kona mata rai yadda Ikleemah keta washe baki tana kallan Yusuf, sannan shima yace mata bazai zo ba ya tashi ya zo, tana tina wadannn abu biyun saita fashe da kuka.
Har Abba y gama making calls dinsa ya shigo Yusuf ko abu daya baici ba, Abba ya ce "Baka ci komai ba Son" ya dan girgiza kai ya ce "I'm full Abba, na gode sosai Allah ya saka da alkhairi" Abba ya ce "Ameen, a huta gajiya" daga haka Yusuf ya fita a parlorn, very gentle ya dinga tafiya harya iso gate ya fita, ya shiga motarsa ya mata key ya bar layin, sai murmushi yake, kana kallansa kasan he's so happy.
[7/29, 6:47 AM] Zarah: https://m.facebook.com/Zamaniwritesassociation
*_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_By FATIMA ✍🏻_
_27~28_
Washegari bayan sallan asuba Rafi'ah ta sauko downstairs ta shiga kitchen, yunwa takeji bata wasa ba, dan rabanta da abinci tin jiya data dawo a school, cup ta dauka ta debi ruwan zafi sannan ta hada tea, ta bude fridge ta dauko bread ta zauna kan kujera ta fara sha, bayan ta gama ta dafa indomie tasa a warmer sannan ta koma upstairs, tana kokarin bude dakinta Ummi ta fito, ta dan sunkuyar da kanta ta ce "Ina kwana" Ummi ta ce "Lafiya, what did u want for breakfast?" Dago kanta tayi tana kallan Ummi ta ce "I already cooked indomie" Ummi ta ce "To aje a shirya" wucewa tayi cikin dakin tana fadin "Insha Allah". Yusuf ne zaune a parlor yana shan tea, sai kiran number Rafi'ah yake amma taki picking, ya danyi murmushi ya ajiye phone din a gefensa dai dai nan Jiddah ta sauko da plate a hannunta, sai side bag dinta da laptop, ta ajiye plate din akan dinning ta karasa gefensa ta zauna, juyowa yayi yana kallanta ya ce "Good morning madam" ta dan kalleshi ta ce "Ina kwana" ya ce "Lafiya, jiya baki tsaya munyi hira ba why?" Ta6e baki tayi ta ce "Bayan kai kake bani labarin waccen yarinyar" Yusuf ya dan zaro ido ya ce "To kiyi hkr, yanzu dai yaushe zamuje gidansu ku gaisa" ta dalla masa harara ta mike ta ce "Ba dai dani ba" kamo hannunta yayi ya ce "Dake mana, bari na gaishe da Umma sai mu fita na ajiyeki a school" ta danyi murmushi tana kallansa, shima din kallanta yake, ya sauke murya kasa a hankali ya ce "U look beautiful Jiddah" ta dan boye fuskarta a bayan laptop ta ce "Kaima kayi kyau Yaya, but jiya kafi kyau" sake hannunta yayi yana murmushi ya ce "U wait me here" daga haka ya wuce upstairs. Da sallama ya shiga dakin Umma, tana zaune gaban mirror taci tsadadden lace, sai powder take shafawa, ta juyo tana kallansa ta ce "Yauwa Yusuf dama yanzu nake cewa Khadija ta maka magana kafin ka fita" zama yayi yana kallanta ya ce "Ina kwana Umma" ta ce "Lafiya kalau, zanje gidan Hajiya Saratu, idan ka tashi a aiki ka biya ka daukoni" a hankali ya ce "To, kenan bada mota zaki fita ba?" Ta ce "Ehh, Khadija zata saukeni yanzu" ya ce "To insha Allah" daga haka ya mike ya fita a dakin. Yana saukowa ya samu Jiddah tsaye tana jiransa, ya dauka key dinsa da lab coat yana kallanta ya ce "Let's go" daga haka tabi bayansa suka fita, hira sosai Jiddah ke masa har suka iso school dinsu, yayi parking yana kallanta ya ce "Study hard Jiddah" ta danyi murmushi ta ce "Insha Allah Yaya" daga haka ta daga masa hannu ta fita a motan. Sadeeq ne ya fito a part dinsu yana jaan trolley, ya dan kalli Jawad dake zaune shiru a parlor ya ce "Good morning" Jawad ya dago yana kallansa ya ce "Morning" daga haka ya limshe idanuwansa ya jingina kansa jikin sofa, bayan few seconds Ikram ta fito, ta dan tsaya tana kallan Yayansu kafin a hankali ta ce "Yaya" bude idanuwansa yayi yana kallanta ta ce "Ina kwana" ya ce "Lafiya, how are u feeling?" Ta ce "Naji sauki, Mami tace ka sameta a ciki" da kai ya amsa mata sannan ta koma ciki, ya mike ya shiga part dinsu hade da sallama, a parlor ya samu Mami tana ta zuge Jakar kayanta, ya zauna yana kallanta ya ce "Gani" bayan ta gama zuge jakar ta dago tana kallansa ta ce "Dama na yanke shawara ka koma gidan Kawu Audu kafin na dawo" ya dago da sauri yana kallanta ya ce "Why Mami?" Ta masa wani kallo ta ce "Is an instruction i'm giving u Ahmad, idan ka dama ka tsallake karka bi" ya sauke kansa kasa baice komai ba, Mami ta ce "I'm just spending two weeks there, idan ka tattara kayanka ka tafi banasan ka sake lekowa gidan nan sai idan na dawo, dan ba zaka zama driver din matar ubanka ba" ba tare daya dago kansa ba ya ce "But what if Abi call me" harara ta galla masa ta ce "Wannan kuma ya rage naka" daga haka ta mike tana gyara zaman sarkan Gold dinta ta yafa veil dinta ta fito, jawo trolley dinta yayi yabi bayanta har zuwa parking lot, Sadeq ya kar6a yasa a boot, karasawa yayi wajen motar yana kallan Mami ya ce "Allah ya tsare" ta ce "Ameen" Ikram na kallansa ta ce "Yaya till we come back" ya daga mata hannu sannan ya koma cikin gida bai tsaya yaga tafiyarsu ba. Da yamma Rafi'ah na shigowa dakinta ta ga phone dinta na haske, ta dago wayar tana kallan screen din, ganin Yusuf ne tayi dan karamin tsaki ta ajiye wayar, daukan laptop tayi ta fito a dakin, ta zauna kan kujera tana kallan Ummi ta ce "Abba yace idan anyi hutu zan bishi Abuja" Ummi ta kalleta kafin ta ce "Ba inda zakije" dan zaro ido tayi tana kallan Ummi ta ce "Nifa ba ruwana da matarsa, kawai inasan zuwa ne" ba tare da Ummi ta kalleta ba ta ce "Waya ce maki tare zasu koma?" Ta bude hannayenta alamar bata sani ba ta ce "Kawai nayi tinanin tare zasu koma ne" Ummi ta dan harareta ta ce "Saboda ke kika haifeshi ko?" dariya ta farayi ta ce "To ai dama ni mamanshi ne" Bude kofar parlorn akai Abdul ya shigo da sallama, Ummi dake kallansa ta ce "Why are u in a hurry?" Ya wuce dakinsa da suri ya ce "Ummi akwai match" Rafi'ah taja tsaki ta ce "Akwai wahala dai, wahalalle kawai" da shirinsa na zuwa ball ya fito, sai kamshi yake kayan kuma sun masa kyau ba kadan ba, Rafi'ah ta ce "Yanzu zai dawo duk doyi" ko kulata baiyi ba ya dauka table water a fridge ya fice, few minutes da fitansa Mustapha yayi knocking, Ummi ta ce "Waye?" Mustapha ya ce "Nine Hajiya, wai Yusuf ne yake sallama da Rafi'ah" sosai kirjin Rafi'ah ya buga, ta dan zare ido tana kallan Ummi kafin ta sauke kanta kasa, Ummi ta ce "Kace tana zuwa" Mustapha ya amsa da toh sannan ya juya, kallan Rafi'ah Ummi ta sakeyi for the second time ta ce "Wa kika cewa Yusuf zaizo yau?" Ta dan kara zare ido ta ce "Wallahi Ummi i don't know he's coming, nima bansan zaizo ba" Ummi ta mike ta ce "This should be the last, banasan haka, idan zaizo u let me know" a hankali ta amsa da toh, Ummi ta ce "Sai ki tashi kije ai" ta mike duk jikinta a sanyaye ta haura sama, wayarta ta dauka taga 16 missed call dinsa sai text messages guda 5, ajiye wayar tayi ta dauka veil dinta ta yafa sannan ta sauko, walking slowly ta fita a parlor tana turo baki harta fita gate.
Yana tsaye jikin motarsa yayi folding hannayensa, har ta karaso ta tsaya a gefensa murmushi yake, ya sauke ajiyar zuciya ya ce "Thank God u came out, how are u Baby?" ta juya kanta gefe bata ce komai, ya ce "Pls talk Fatima, or have i wronged you?" Juyowa tayi ta dalla masa harara, Yusuf ya shafa gashin kansa yana kallanta ya ce "Did..u just eye me Rafi'ah?" ta sake jujjuya idanuwanta tana turo baki, ya ce "Ohk, if that would cool your heart keep eyeing me" shiru tayi bata ce komai ba sai jujjuya ring dinta take, ya danyi murmushi ya ce "Kin gama hararan nawa kuma kin hakura?" ta daga masa kai, ya ce "Good, how are u then?" girgiza kanta ta hauyi a hankali, nan da nan idanta ya ciko da ruwa, Yusuf ya ce "What happened again Rafi'ah, or are u sick?" Ta girgiza masa kai ta ce "I'm not sick, is just u that offended me yesterday" zaro ido Yusuf yyi yana kallanta ya ce "But u just finished eyeing me, ba kin rama ba" ta turo baki tana goge hawayen idanta ta ce "To dan meyasa kake kallan Ikleemeh data kai maka abinci" with surprise Yusuf yake kallanta, ya ce "Who's she?" Ta ce "Jiya bata kai maka abinci ba" har lokacin kallanta yake da mamaki ya ce "To kiyi hakuri insha Allah i promise i won't smile at her again" kanta na kasa tana ta jujjuya ring dinta, ya ce "To kimin murmushi" ta noke kafada, ya ce "Dan Allah Rabi'ah ta" ta dago tana kallansa ta ce "I'm not Rabi'ah" ya danyi dariya ya ce "Haka wancen mai gadin yace min, wai sunanki Rabi'ah" sai lokacin ta danyi murmushi ta ce "That's how he used to call me" ya ce "Then can i contribute" ta kara dariya ta ce "So u want us to fight again?" Yusuf yayi dariya ya ce "Noo, and we are not fighting Allah ma ya kiyaye" a hankali ta ce "Ameen" tana dariya. Zaune yake a parlor yana ta jujjuya tea din hannunsa da spoon saboda yayi sanyi da wuri, Mummy ce ta fito a part dinta tasha lace me kyau, sai kamshi take bugawa, kana kallanta kaga babbar Hajiya, Jawad ya dan sunkuyar da kansa ya ce "Ina yini" ta ce "Lafiya kalau Jawad, su Mami sun tafi ina bacci bamuyi sallama ba" da kai kawai ya amsa, ta ce "Are you not eating food? Gashi fa akan dinning" ya juya yana kallan kan dinning sannan ya ce "I will eat ltr" ta ce "To shikkenan, zanje gidansu Rafi'ah sai dare zan dawo" ajiye glass cup din yayi akan center table ya ce "Let me drop u" Mummy ta ce "A'a ka zauna kasha shayinka Jawad, u don't have to worry zan iya driving ai" bin bayanta yayi yana murmushi ya ce "A'a zan kaiki Mummy" ta tsaya tana kallansa ta ce "To karna baka wahala anjima kuma" ya ce "A'a zan daukoki ai ba abinda nake" Mummy ta ce "To shikkenan muje" ya bude mata back seat ta shiga sannan ya zagaya seat dinsa yayi wa motar key, bayan sun hau titi Mummy ta ce "Abi yace kaci gaba da aiki ko?" Ya ce "Ehh" ta ce "To Allah ya sanya alkhairi" a hankali ya ce "Ameen" yana rife bakinsa phone dinsa ya hau ringing ya dan juya ya kalla screen din, ganin Mami ke kira yasa wayar a silent yaci gaba da driving dinsa.
'Yar karamar yatsarta ta mika masa ta ce "then let's bet" Yusuf dake dariya ya ce "You will soon get used to the idea... So i won't bet on it" Rafi'ah ta danyi dariya ta ce "Kaji tsoro" shima dariyar yake ya ce "No, i'm not scared, but u know what?" tayi saurin girgiza masa kai, ya ce "When ever i marry you, you will stop wearing veil" ta dan zaro ido