jera akan dinning din Abi, Mummy tasa Rafi'ah ta dibar musu nasu a warmer, plate da cups Mummy ta dauko zata wuce part dinta, Jawad da fitowansa kenan yayi kasa da kansa ya ce "Ina Kwana" ta ce "lafiya Jawad, ya gajiya" ya ce "Alhamdulilah" daga haka ta wuce ciki, Mami sai hararansa take, bayan ta gama dibarwa Ikram abinci ta wuce part dinta ta rufo kofa, Jawad ya dawo kan dinning din ya zauna yayi sarving kansa ya hada tea, sai daya gama sannan ya mike ya nufi part din Maminsa, da sallama ya shiga parlor, Mami ta hade rai ganinsa taci gaba da bawa Ikram tea a baki, zama Jawad yayi yana kallansu ya ce "Take it yourself" ya karashe magana yana kallan Ikram, hannu tasa zata kar6i cup din a hannun Mami, Mami ta ce "Ina ruwanka to? Kai ka sani na bata?" Girgiza kai yayi yana kallanta ta ce "Then u mind ur words, babu ruwanka da abinda nayi niyya a cikin gidan nan" kansa ya kara saukewa kasa ya ce "Amma Mami yanzu Ilkram bazata sha tea da hannunta ba saikin bata, just because ta tashi da zazza6i, ita raguwar inane? shekara 17 fa" Hararansa kawai Mami take harya gama magana, ta ce "To saika hanani abinda nayi niyya tinda kaika haifeni, ko kishin uwarka bakayi ka bude baki ka gaishe da waccen matar, kana gani 'yar kanwata na ganina ina zirya ko sannu bata ce min ba, amma saboda kai kafi kowa ladabi ka gaishe da uwarta" shiru yayi baice komai ba, bayan few seconds ya ce "Kiyi hkr, amma dai kun fasa tafiya yau din?" Ta ce "Inafa tafiya Ikram ta tashi ba lafiya" a hankali ya ce "Allah ya sauwake" Mami ta ce "Yanzu ina zakaje?" silently ya ce "Court" ta ce "Saboda neman suna ko me?" Ya mike yana kallanta ya ce "May b i will just continue my work there, tinda sun bukaci hakan" ta6e baki tayi ta ce "A banza zaka musu aikin kenan?" Ya shafa kansa ya ce "No, ai dama sunce inna dawo zan iya ci gaba kona nema wani waje, end of d month zanci gaba da kar6an salary" beedsheet ta rufawa Ikram ta ce "Allah ya taimaka, Allah kuma yasa da gaske kake, danni yanzu lamuranka tsoro suke bani" murmushi ya danyi ya fita a parlorn ta bishi da harara.
Fitowa yayi a dakinsa cikin manyan kaya, sai kamshi yake ya dauka lab coat dinsa dake kan kujera ya daura akan kayansa, kaan dinning ya zauna yaga babu komai cikin warmers din, hakan yasa ya mike ya shiga daki ya dauko wasu files sannan ya nufi kofar fita hannunsa rike da key din mota, da sauri Jiddah tabi bayansa tana murmushi ta ce "Good morning Ya Yusuf" juyowa yayi yana kallanta ya ce "Morning Jiddah" idanta ne ya ciko tapp da hawaye, tayi kasa da murya ta ce "Dan Allah Yaya mena maka kace ka fasa aurena, ka fadamin koma menene Allah zan daina, i promise u Yaya" ta karashe magana tana goge hawayen idanta, duk jikinsa sai yayi sanyi, shima Allah na gani yana saan Jiddah but tinda Umma taki yarda tun farko ya janye jikinsa, hannunta ya kamo ya bata side hug ya ce "Keep quite" tayi shiru tana kwantar da kanta akan fadarshi taji ya ce "I luv u Jiddah, but i don't like some of ur attitude sometimes" dago kanta tayi tana kallansa ta ce "Na daina Yaya trust me" ya danyi murmushi ya ce "Then zaki aureni?" Ta daga masa kai ya ce "Kinyi alkawari bazaki kara yin abinda na hanaki ba?" Ta kara daga masa kai, ya sake murmushi yana kallanta ya ce "Kenan kinyi alkwari zaki zauna da wacce zan hadaku, but u are my first wife, she will come after u" turo baki ta danyi sannan ta daga masa kai, yayi patting bayanta ya ce "Then stop crying" zame jikinta tayi ta koma cikin gida ya bita da kallo, daga haka ya juya ya wuce parking lot. Da yamma liss Mummy ta sauke Rafi'ah a gida, bayan sun shiga duk da sauri take sai data labartawa Ummi Rafi'ah nada saurayi, Ummi batai wani mamaki ba sabida taga yadda take making calls, sai dai bata ce komai ba, Mummy ta mike tana kallanta ta ce "Na tilasta mata dai ta bani numbersa, tinda gobe ubanta zaizo sai a kirashi yazo suyi magana" kai kawai Ummi ta daga mata, daga haka ta rakata har paking lot kafin ta dawo ciki.
Har dare Ummi bata cewa Rafi'ah komai ba, ita kuwa tinaninta kawai aiki ne ya mata yawa saboda taga tana ta marking, bayan sallan isha ta sakko downstairs daga ita sai 'yar rigar baccinta iya gwiwa, kanta ba dankwali hannunta rike da phone dinta, tana zama ta kalli Ummi ta ce "Gobe Abba da wuri zai iso ko sai caan yamma?" ba tare da Ummi ta kalleta ba ta ce "Sai ki kirashi ki tambayeshi" ta dan turo baki ta ce "Amma Ummi ai zai gaya miki" tana rife bakinta phone dinta ya hau ringing ta kalli screen din tayi murmushi ganin Yusuf ne, daga haka ta mike ta wuce upstairs Ummi ta bita da harara. Cikin cool voice dinsa yayi mata sallma ta amsa, ya danyi murmushi ya ce "I am happy Babyluv, and it's all because of u" zama tayi gefen gado ta ce "What hapoend Dr" ya limshe idanuwansa kamar tana kllansa ya ce "Mummy just called me, tace Abba zai dawo gobe around 12 na rana" Rafi'ah ta dan zaro ido ta ce "Then what?" Yusuf ya ce "I will come and see him insha Allah, tace min ta mishi magana" kamar zatai kuka ta ce "Pls ka bari ba yanzu ba Dr" Yusuf yayi murmushi yayi hanging call din, dama kawai he just call to let her know, tashi tsaye tayi ta fara zagaye dakin, duk tabi ta rikice, wayarta ta dauka tayi dailing number Mummy taji not reachable, ta kara kiran na Yusuf still d same thing, kwanciya tayi akan carpet ta rasa ta ina zata fara tsayar da Yusuf, Allah na gani batasan hukuncin da Abba da zai dauka ba, jin an bude kofa tayi surin rife idanuwanta kamar me bacci, Ummi ta shigo ta dauko wasu takardu kan stool sannan ta fice a dakin, Rafi'ah ta sauke jiyar zuciya ta mike zaune ta buga uban tagumi.
*Thank u so much for the calls and du'ah, ubangiji Allah ya biya maku bukatanku na alkhairi aduk inda kuke, i so much appreciate the way u people cares, especially when reading ur messages, na gode sosai da sosai* 🥰
[7/29, 6:47 AM] Zarah: *_...شريك حياتي..._*
_{MY LIFE PARTNER}_
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
_By FATIMA ✍🏻_
_25~26_
Washegari da safe Ummi na kitchen Abdul ya shigo cikin shirinsa na makaranta, ya dafa kafadarta ya ce "Good morning mother" ta ce "Morning, how are u?" Ya ce "Fine" Ummi ta ce "Go and take your breakfast" ya ce "Anty bata fito ba Ummi? And It's almost time" Ummi ta juya ta fita a kitchen din bata ce komai ba, upstairs ta wuce ta shiga dakin Rafi'ah, ta sameta gaban mirror ta gama shirinta tana zaune da dan karamin hijab dinta a hannu, strictly Ummi ta ce "Idan baza kije school din ba Abdul yayi wucewarsa" ta mike a hankali tana kallan Ummi ta ce "Na gama" Ummi ta ce "If u like keep sitting" daga haka ta fita a dakin taja mata kofar. Kamar wacce bata da jini ta zira hijabin sannan ta dauka school bag dinta, har zata fita taga phone dinta dake kan gado tana haske, dago wayar tayi tana kallan screen din, ta6e baki tayi ta kashe wayar ta jefa cikin press hade da jaan karamin tsaki. Tana saukowa downstairs ta samu Abdul har ya gama breakfast dinsa, ta ajiye school bag dinta sannan ta zuna ta hada tea ta fara kur6a, kana kallanta kasan a dole take sha, duk abinda take Ummi na kallanta sai dai bata ce komai ba, bayan tasha half ta mike ta haura stairs ta shiga dakinta, phone dinta ta kunna sannan tayi dailing number Yusuf, yana dagawa ya ce "Why are u not picking my calls Fatima?" Cikin fishi ta ce "Pls don't come to my house i beg u, dan Allah karka zo, i'm begging u for the sake of Allah Dr" fashewa da kuka tayi bayan ta dasa aya, Yusuf dake saurarenta ya danyi murmushi ya ce "But do u want me to break the promise i made to ur Mummy? Or what do u want me to do? so kike nace bazan zo ba kenan, she will take me non serious Rafi'ah, maganar neman aure fa ba wasa bane" sassauta kukanta tayi ta ce "Dan Allah karka zo nikam, if not i will pretend i don't know u" shiru yayi na few seconds kafin y ce "It's ok, bazan zo ba, nasan abinda zance mata, stop crying and wipe ur tears" tayi shiru tana goge idanta da bayan hannunta, ya ce "Kin goge?" Ta daga masa kai, ya ce "Baza kije school bane?" Silently ta ce "I'm going now" ya ce "Ohk safe, say your du'ah and cool down your heart, babu abinda zai faru" ta danyi shiru sai kuma ta ce "Ba kace ka fasa zua ba?" Ya ce "To kije school idan kika dawo zamuyi magana" ta ce "Ohk" daga haka tayi hanging wayar ta ajiye ta fito, tana saukowa a stairs taji Ummi na cewa Abdul "Ku tafi abinku, idan yaso ta hau cab" turo baki tayi bayan ta karaso ta dauka school bag dinta da 500 din da Ummi ta ajiye mata a gefen jakar sannan ta fice a parlorn.
Da sauri da sauri Anty Amina ta tattara magungunan da suka kar6o wajen malaminsu tasa a handbag dinta, duk ta haddace yanda akace tayi, Ikleemah dake kallanta ta ce "Wai Anty Amina tafiya zakiyi?" Ta ce "Ai ina wanka tafiya zanyi ikee, kinga yace da wuri zai taso, jirginsu karfe 9 zai tashi, to ina Abuja ina Kano a tafiyar jirgi" Ikleemah ta mike ta ce "To kona biki ne?" Anty Amina ta ce "Tambayi uwarki idan zata barki, banaso muje tayi ta damuna a waya ki koma, idan zama zama" Ikleemah ta kalli mahifiyarta dake zaune gaban TV, Ikleemah ta ce "Mami bazan bita bane?" Anty Rahama ta ce "Idan kinaso, ni Umma nakeji idan kika tafi, inna fita ita kadai kenan zata zauna" jin haka yasa Anty Amina ta dauki handbag dinta ta shige dakin Umma dan tasan dama ba bari zatai taje ba sai dai idan Umma tayi magana. Tinda Rafi'ah taje school zuciyarta ke bugawa, gashi dai Yusuf yace bazai zo ba amma duk jinta take wani iri, babu yadda Ameerah batai ba amma taki fadin abinda ke daminta, koda akai break a class ta zauna bata fita ko ina ba, ana tashi kuwa Mustapha yazo daukansu, Abdul dake kallanta ya ce "Are u sick Anty?" Ta girgiza kanta ta shiga mota, Mustapha yaja motar yana murmushi ya ce "Hajiya karama Abba ya iso tin sha biyu saura" da sauri ta dafe kirjinta ta ce "Ai nasan zai zo" daga haka ta kwanta ta limshe ido, suna isa gida yayi parking a waje ya ce "Hajiya ta aikeni kasuwa, amin afuwa" Abdul ya ce "Ba komai" Rafi'ah ta dauki school bag dinta ta fito tabi bayan Abdul, ba kowa a parlorn da suka shiga, Abdul ya fara hawa stairs itama tabi bayansa, da sallama Abdul ya shiga parlorn, Ummi ta amsa masa, ya karasa gefen Abba yana murmushi ya ce "Sannu da hanya Abba" Abba ya kama hannunsa yana murmushi ya ce "How are u Son, ya karatu?" ya ce "Lafiya kalau Abba" ciki ciki tayi sallama ta shigo parlorn, kasa zuwa ta rungume Abba tayi just like she used to, ta zauna gefen Ummi kanta a kasa ta ce "Sannu da dawowa Abba" ya danyi murmushi yana kallanta ya ce "How are u Mamana?" a hankali ta ce "Fine" daga haka ta mike ta wuce dakinta. Bayan Abdul yayi sallan azahar ya dawo wajen Abba sukai ta hira, Ummi ta mike ta shiga dakinta saboda bacci da takeji, Rafi'ah dai tinda ta kule a daki bata fito ba har akai la'asar, jin ba muryar su Abba yasa ta fahimci sun fita masallaci, kamar 6arauniya ta sauko downstairs ta debi abinci sannan ta dauki bottle water ta koma sama da sauri, tana gama hawa suka hada ido da Ummi dake tattara cushions tana daurawa kan sofa, sauke kanta tayi ta shiga daki ta rufe kofarta. Ummi ta zauna akan kujera tana kallan TV, ba jimawa Abba yayi sallama, Ummi ta amsa tana kallansa, zama gefenta yayi yana kallan TV ya ce "Halima ta kirani wai yaran nan me neman Rafi'ah zaizo, shine ya kirani yanzu" Ummi ta juyo da sauri tana kallansa, dama tin dazu take jira ya mata maganar baiyi ba, with surprise ta ce "Zaizo kuma?" Abba ya ce "Eh, tinda ya bukaci hakan ai baza'ayi discouraging dinsa ba, let him come" Ummi ta ce "Kenan dai aurar da Rafi'ah za kai yallaboi" ya ce "Idan har nayi bincike na gano ba matsala why not? Tinda da bata sanshi ba zata hadashi da wani nata ba" Ummi ta sauke ajiyar zuciya ta ce "Ni gaskiya i'm not in support, ina laifin idan ta gama secondary school, saurin me ake shekarunta fa 17 ne kacal a duniya" Abba ya juyo yana kallanta ya ce "I know she's 17, kinga Zainab a zamanin nan idan yarinya ta nuna aure takeso then let her, dan bamusan me zai faru ba Allah ya kiyaye, and I'm not saying zan aurar da ita immediately, no..till when she finish her secondary school" Ummi bata ce komai ba sai ajiyar zuciya data sauke, bayan mintuna kadan Abba ya mike yana kallanta ya ce "Bari na shiga apartment din Amina kafin ya karaso" ta ce "A dawo lafiya" daga haka ya nufi downstairs.
Tashi Ikleemah tayi daga kwancen da take ta fito parlor, ta buga uban hamma tana kallan Anty Amina ta ce "Anty ki bani 500 dan Allah naje shago" Anty Amina ta ce "Uban me zaki siyo harna dari biyar Ikee? Ni kinga duk kudadena sun kare, kwanakin da nayi a gida duk uwarki ta yasheni, saboda haka bani dashi" Ikleemah ta ta6e baki ta ce "To bani 200, kati fa kawai zan siyo dan Allah" Anty Amina ta juyo tana kallanta ta ce "Ke nima 200 ce daukeni ki siyo katin" tana rife bakinta Abba ya shigo, hakan yasa Ikleemah ta shige daki tana kunkuni.
Tsaye yake gaban mirror yana daura wristwatch dinsa a hannu, sosai yayi bala'in yin kyau sai kamshi yake, bakin yadi ne ajikinsa me laushi, ko a ido ka kalla kasan me tsada ne sai wane da wane, kayan sun matukar kar6enshi kasancewarsa farine shi tass, kallan gashin kansa yayi yana murmushi, raban da ya rage gashin kansa kusan shekara kenan, sai dai ya taje ya shafa mai, amma yau shine yaje aka rage masa gashi, sai ya ga ya kara kyau ma, key din motarsa da phone dinsa ya dauka sannan ya zira well purnished half shoes dinsa, ba kowa a parlor dan duk mutanen gidan na sama, ya fita ya jawo musu kofar sannan ya wuce parking lot ya bude motarsa ya shiga, yana horn gateman ya bude mishi ya fice a gidan. 10 minutes ya kawo shi cikin GRA, ya duba street name din to confirm ko layin ne, daga haka ya danna kan motar cikin layin, gida biyu ya wuce kafin ya fara tinanin na ukun ne kona hudu, ya dinga kallan gate din ko zaiga an fito amma shiru, hakan yasa ya bude motar ya fito yayi knocking gate din, mutumin na budewa Yusuf ya ce "Sannu Baba, dan Allah tambaya nake" mutumin ya ce "Allah yasa na sani yaro" Yusuf ya ce "Gidansu Abduljalal nake nema, nasan dai nan layin ne amma kuma ban gane gidan ba" mutumin ya ce "Allah sarki kace gidan Alhji Muhammad, yana da yarinya wata fara doguwa me suna Rabi'ah ko?" Yusuf ya danyi murmushi jin yace Rabi'ah ya ce "Nan ne Baba" kamo hannunsa Mutumin yayi ya nuna masa next house ta dayan side din ya ce "Ga caan gidan yaro" Yusuf ya zira hannu a pocket dinsa ya ciro 2k yasa masa a hannunsa ya ce "Godiya nake Baba" cike da fara'ah Mutum ya ce "Na gode yaro, ubangiji ya biya maka bukatunka na alkhairi" "Ameen" kawai yace ya shiga motarsa ya karasa bakin gate din su Rafi'ah yayi parking, fitowa yayi walking slowly sannan ya karasa gate din yayi knocking, Mustapha ya bude kofar yana kallan Yusuf, hannu ya mika masa ya ce "Nazo wajen Abba ne" Mustapha ya ce "To bari a sanar masa" daga haka ya juya ya nufi apartment din Anty Amina. Ikleemah ya samu tana zaune a balcony tana danne dannen waya, Mustapha ya ce "Dan Allah 'yammata kicewa Alhaji ana sallama dashi a waje, idan ya tambaya kice saurayi ne, me farar mota" Ikleemah ta mike ta bude kofar falon, bayan ta shiga ta tsaya bayan kujera ta ce "Abba wai ana sallama da kai" ya juyo yana kallanta ya ce "Waye?" Ikleemah ta ce "Mustapha dai yace saurayine me farar mota" Abba ya mike yana duba phone dinsa ya ce "And he didn't call me, je kice ya shigo a kaishi parlon BQ" Ikleemah ta juya ta fita bayan ta amsa