x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 9 - KUKAN ZUCIYA

  • 24001 words
  • 27000 words
  • Out of 38354 words

Category: Tale Stories

Views 39

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
bincike gidan sai sannan na tuna da Ameera na shuga ɗakinta amma naga wayam bako alamarta hannu na ɗora aka🙆‍♀️ na fashe da kuka ina faɗin "Wayyo Allah na shiga uku banga Ameera ba," nafaɗa ina rushewa da matsanancin kuka, duk yanda aka bincika gidan ba Ameera ba ogan yan fashin, C p yabar sauran yaransa suna tsoron gidan yayinda mu kuma muka wuce Hospital inda aka kai Uncle muna shuga dai dai an futo dashi daga ɗakin tiyata dan yankan yataɓa masa hanjinsa, bin gadon da'aka turoshi nayi da kallo ganin yanda fuskarshi tai haske yasa na fashe da kuka tareda rungume Mami, Ummi tace

"Ba kuka zakuyi ba mugodewa Allah dayasa aka kawosa asibiti da wuri da tuni mun rasashi amma yanzu da izinin ubangiji zai tashi nan da yan awanni" shuɗewar awanni Uncle bai farkaba nayi kuka na harna gaji Mami ta koma gidanmu, gefe guda kuma yan sanda na gudanar da bincike kan wanda yaturosu da kuma ɓacewar Ameera.

Wajan sha biyun ranar juma'a Uncle ya farka yana wata irin karkarwa da sauri na futa na kira Ummi kasancewar asibitun datake aiki ne,tare suka shugo da wani likitan, Uncle ya ruko hannuna cikin ciwo yake faɗin

"Su'ad kiyafemin mutuwa zanyi ina Ameera ina Mami, Ummi ga amanar Ameera nan na damka a hannunku kuriketa kar'a bawa dangin mamanta nabar maku ita duniya da lahira,Su'ad kiyi hakuri yau mutuwa zata rabamu fatana ko bayan raina karki manta dani kirinkami addu'a,Allah yabaki wani mijin wanda zai soki fiyeda son danake maki,naso ace nayi tsawon rai ta yanda zankula dake nabaki farin cikin rayuwa amma mutuwa zata rabamu kigayawa Mami tayi hakuri daman mu kaɗai muka rage yau gani nima zan tafi na barta😰"

Wata shakuwa da yayi can kuma sai aman jini, gaba ɗaya likitocin sukai kansa kowa da abinda yake masa har sannan hannunsa yana cikin nawa ni kuma na kifa kaina kan gadon dayake kai inata kuka duk da maganganunsa basuyi tasiri a zuciyata ba danni gani nake kawai zafin ciwo yasa yake waɗan nan surutun, salatin dayayi haɗe da kalmar shahada yasa na ɗago ina kallonsa idanunsa na kallon sama naji hannunsa dake cikin nawa yasaki, Ummi naga taja baya tana salati ɗayan likitan yaja farin kyallan dake lulluɓe jikin Uncle ya rufe masa fuska, ban fuskanci mai suke nufi ba saida naji ɗayan likitan ya kalli Ummi

Yace "Sai hakuri Dr kullu nafsin za'ikatul mot"

Ai bansan sanda na mike ba na rungumo Ankul da karfi nace "No!!! wallahi karyane! nace karyane ba Ankul ɗina bane yamutu kaine dai bakasan aikinka ba, na buɗe Ankul ina kallon fuskarsa "Kanaji ana maka sharrin ka rasu Fahad katashi ka shaida masu baka mutuba katashi nace Uncle Dan Allah besty ka tashi ka gaya masu kana raye" rukoni da'akayi yasa najuya ina kallon wanda ya rikeni Yaya Jabeer ne idanunsa sun kaɗa sunyi jawur ba kuka yake ba amma tabbas halin dayake ciki kwara ace kukan yake zuciyarsa zatafi samun sauki😰rungumesa nayi tareda fashewa da kuka

Nace "Dagaske wai da gaskene Uncle ɗina ya rasu, Yaya Jabeer ka karyata dan Allah ka karyata min Innalillahi wa'inna ilaiheer raji'un" Ummi ta ruko hannuna muka futa zuwa gida, su Yaya Jabeer suka tsaya zasu tawo da gawar Ankul.


Har muka shuga mota ina kallon ɗakinda gawar Uncle ke kwance inajin wani irin kewarsa datake shugata, shikenan kuma na rabu da Uncle bazan sake ganinsa ba? na rasa Ankul kamar yanda na rasa Daddy na gaba ɗayama kukan yaɗauke na koma kamar wata mutum mutumi har sanda aka gama haɗa gawar Uncle aka kirani wai muyi sallama sosai nasawa zuciyata juriya nai masa addu'a da fatan Allah yasa aljannace makomarsa.

Kwanaki uku mukayi muna zaman makokin Uncle, har sannan ba labarin Ameera,abinda ya kuma ɗagan hankali kenan nakan shuga damuwa musamman idan natuna amanar da Ankul yabani hankalina yakan tashi, sosai yaya mukhatar yake tsaye kan case ɗin, kwanan Uncle goma da safe ina zaune a main falo aka kwankwaso kofa naje na buɗe yan sanda ne guda biyu mace da namiji iso nayi masu zuwa ciki na kira Ummi da Mami ɗan sandan ke magana

"Munzo daga stesion ne munason zamu tafida Amina matar Fahad zata amsa mana tambayoyi saboda zarginta da'ake dasa hannunta a kisan Fahad ɗin"

Zumbur Mami tamike tareda dafe kirji tana salati tace "Daman ance ku yansanda kun fiye sharri yau kuma sharrin naku kan ɗiyata ya sauka ni na raini abata nasan halinta bazata taɓa goyan bayan zalinci bama bare takai ga kisan kai, kutashi ku futar mana daga gida tunban farfasa maku kafafuwa ba"

Ummi ta dafa kafaɗar Mami tace "Kibari su tafi da'ita tambaya kawai zata amsa masu ta dawo", hannuna Ummi ta kamo tace "Gatanan kuje ni nasan ba hannun ta acikin kisan nan" Mami ciki ta shuge ta ɗakko wayarta ta kira kwamishina ko gaisuwar dayake mata bata amsaba tace "Tayaya zaka turo yaranka suzo su tafi da yata"

"Kiyi hakuri Mami bincike ne yabiyo ta kanta, yaran da muka kama sunce matarsa ce ta aikosu su kashe sa saboda bashi take soba aka aura mata shi, bincikenmu yatabbatar da Su'ad batason Fahad dole akai mata
Mami ajje wayarta tayi ta saka hijab tacewa yan sandan "Naji kuje zankawota da kaina amma bazata shuga motarku ba" ba yanda suka iya haka suka tafi nidai har sannan ina tsaye ina binsu da kallo zuciyata wani irin zafi takemin wanne irin sharri ne wannan maye alakata da yan fashin nan wanne laifi namasu da zasumin wannan babban kazafin, hannuna Mami taja tana

Faɗin "Karki damu Su'ad wallahi nasan sharri ne tayaya zakisa a kashe Fahad tabbas akwai wata a kasa kodai akwai wanda suka sami matsala da Fahad yaturo aka kashe sa yakeson ya ɗora maki laifin ba komai kiyi addu'a insha Allah komai zaizo da sauki".

Bayan munje duk yanda Mami taso subata ni mutawo tare ki sukayi saima sakayani dasukai, ina kallon Mami tabar stesion ɗin ranta aɓace, duk yanda muke zaton case ɗin yawuce haka dan gaba ɗaya laifin kisan ni aka ɗorawa tuni yan sanda sun turamu kotu, yan uwana sai shuge da fuce suke ganin anbada belina amma sam D P O yaki, ranar Monday muka fara halartar kotu, nanma ba nasara saima tarin tambayoyi dasuka rinkamin danma lauyana yana bani kariya sosai saboda kwararran lauya Mami ta ɗaukarmin, Alkali ya ɗaga shari'a nan da sati biyu ya kuma umarci yan sanda da lalle su nemu damo wanda ake zargin shiyasan wacce ta turosu dan yazo yafaɗi gaskiyya.


___________******____________


Fu'ad yadafe kansa dayaji yana sara masa saboda damuwa gaba ɗaya yana cikin damuwa, shirye shiryan tafiyar sa England dayake yasa bayama da nutsuwa, sam baida labarin rasuwar Fahad duk da yakan tunasa lokaci zuwa lokaci, yakanyi mamakin wai duk yanda suke da Fahad amma saisu share fin wata guda ba wanda ya kira kowa gaba suke ba kawai kowa yanjin nauyine duba da abinda yafaru, badan ransa yasoba Abiee yatakura masa lalle saiya tafi da Baraka yarinyar da yau watanta guda kenan amma bai taɓa sakata a idonsaba, yau da wuri ya shugo gidan saboda yanason yakaita amata shirye shiryan tafiya, wani cost zaije wanda zai shafe watanni takwas a london, wanka yayi yaci abincin daya shugo dashi sannan ya koma falo ya kwankwasa kofanta ya koma saman kujera ya zauna.

Baraka dake zaune gefan gado tayi tagumi, zumbur ta mike jin bakon lamari yau wacce bakuwa suka samu a gidan har take bugo mata kofa, plate shoe ɗinta ta zura tareda yafa ɗan kwalin doguwar rigar dake jikinta ta futo, ba karamin faɗuwa gabanta yayi ba ganin Fu'ad a hakimce saman kujera da wannan ranar, kallo ɗaya yai mata ya ɗauke kai yana taɓe baki, shi baiga amfanin wannan auran da'akai masa ba, waya gaya masu yana son farar mace shi sam arayuwa baya bukatar mace fara, kuma taɓe baki yayi ganin yanda ta zauna kasan carfet saida yamike sannan

Yace "Ki shirya akwai wanda zai kaiki kiyi pascort" ɗakinsa ya shuge ya kira direbansu na office yace yazo zai aikesa, yana zuwa ya haɗata suje ayi mata abinda yakamata, ba karamin haushi Baraka tajiba, ta kudurci aniyar saita cusawa Fu'ad soyayyarta kota halin kaka bata taɓa ganinsa ba sai yau akallo ɗaya kuma datai masa ta kamu da mugun sonsa ayan kwanakin dasuka rage masu ta fara futowa ta sabarwa kanta zaman falo wani bin tana nan yake shugowa tai masa sannu da zuwa amma ko kallon inda take bazaiyi ba zai shuge ɗakinsa, sosai take shuge masa har ɗakinsa takan shuga in yana ciki musamman da safe ta gaidashi, yau tana shuga tasame sa kwance ya kifa cikinsa yana sauke numfashi ya haɗa ubangumi duk da fankar dake yi a ɗakin, karfin fankar ta kara tareda kunna A c cikeda karfin hali ta hau saman gadon tana masa sannu, janyota kawai yayi jikinsa atake yafara aika mata da sakonni, bata wani tsaya jan aji ba tabada kai bori yahau😹 dan itakam daman ta jima tana son zuwan wannan ranar duba da shekarunta ayanzu zasu kai ashirin da tara zuwa talatin amma ta kame kanta zata iya rantsuwa da Allah babu wani namijin daya taɓa koda rike mata hannu, ba karamar azaba tasha ba a hannun Fu'ad dan da zafi zafi yake gabatar da komai bako alamar tausayawa, saima daya sami nutsuwa ne yaɗan tausaya mata ganin yanda lokaci ɗaya jikinta yai sanyi sosai bathroom ya shuga ya tsabtace jikinsa sannan ya haɗa mata ruwa zafi yace taje ta gyara jikinta kafin ta futoma har yayi barci, murmushi tayi ganin yanda yake sauke nimfashi ahankali ta sumbaci laɓɓansa ta fuce daga ɗakin tana murmushi, tun daga wannan ranar Baraka ta koma ɗakin Fu'ad da kwana bai hanata ba saima farin ciki dayai da hakan,ahankali suka saba saidai har sannan baya sakar mata fuska zata iya rantsewa bata taɓa ganin dariyarsa ba, dama shi can bayada fara'a tun bayan rabuwarsa da Su'ad sai abin yai gaba ga kuma damuwar wannan aure da'aka kakaba masa, ranar alhamis jirginsu ya ɗaga zuwa birnin londan, ko cikin jirgi tana lafe ajikinsa tayi barci ta tashi har jirginsu ya sauka, Usman abokinsa yazo tararsa saida yakaisa har gidan dazai zauna kana ya koma gidansa yakawo masu abinci shida tasa matar.


__________Ranar da muka koma kotu ta cika fiyeda zama na farko yan sanda kuma sunzo da damo wanda ya gudu a daran, sosai yakafe kan lalle nina sakasu kashe Ankul abinda yaja hankalin mutane sosai, Alkali na shirin yanke hukunci lauyana da baisami zuwa ba sai sannan ya turo kofar kotun yashugo yana neman afuwar alkali.

Yace "Ya mai girma mai shari'a inason na gabatar da shaidata wacce zata tabbatar da ba Amina Usman Karaye bace tai wannan kisan kan"

Alkali yace "Kotu tabaka dama"

Ganin Amira danayi yan sanda sun shugo da'ita ta tsaya tana kuka kamar bazata ce komai ba, gaba ɗaya bata cikin nutsuwarta har saida alkali yai mata magana ta nutsu tayi magana sannan tafara magana

"Sunana Mariya Fahad Aliyu, ranar alhamis tara gawata da misalin karfe biyu na dare ina kwance a ɗakina naji tsayuwar mota a bayan gidanmu labulan ɗakina na ɗaga na lega windo dai dai sannan wannan ta nuna ɗaya daga cikin yan fashin ya hauro gidan namu yabuɗewa sauran gate suka shugo, yanda naga bindugu da wukake a hannunsu saiya tsorata ni hakan yasa nai amfani da wayar Anty na dake hannuna na kira Mami yayar mahaifina ina kuka na sanar mata yan gashi sun hauro gidanmu, Mami saboda tsabar kiɗimewa bata kashe wayar ba ta futa tana sanarwa da Ummi halin da'ake ciki, Ummi ita ta kira C p Mukhter tagaya masa, anan na kashe wayar ganin Mami bata kashe ba, sanda yan fashin suka shugo gidan ɓuya nayi can gaban gado ina jiyo abinda ke faruwa a falo amma tsoro ya hanani fitowa, sanda yan sanda suka shugo gidan wannan ta nunana damo ya shugo ɗakina ganin zanyi ihu ya toshe min baki, ya yage net ɗin dake jikin windon ɗakina wanda ya futo ta waje ya jefani sannan shima ya diro ya jani muka faɗa wani babban rami dake bayan gidanmu, wani yakira a waya bayan yaga wucewar motar yan sandan yazo ya ɗaukemu suka kaini wani gida suka kulleni a ɗaki sau ɗaya wani bawan Allah yake kawomin abinci da rana mai gadin gidanne yace yanajin tausayi na zai taimakamin na futa.
Ranar danayi sati a gidan mamata taje ta gayamin ita ta tura su damo su kashe Abbana dan tagaje dukiyarsa dan Allah na rufa mata asiri nace bazan iya rufe wannan asirin ba anan ta umarci damo da lalle in dare yayi nima ya aikani inda babana yatafi...🙆‍

Comment and share

Eid Mubaraka my lovely fans🥰😍❤️🌹
[6/9, 7:02 AM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹


Story and writtin by
Mamie Yusuf Daboo🥰


☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA


23&24

Ranar nayi kuka sosai sai dare wanda ke gadin gidan yazomin a tsorace yace na biyosa, tare muka gudo daga zariya da mukazo kano ya dankani a hannun yan sanda anan CP yaganni ya ɗaukeni zuwa gida na gaya masa komai yanda yafaru sai yau nazo nan domin na shaidawa duniya cewa ba Anty bace ta kashe Daddyna ba Ummana ce" tana zuwa dai dai nan ta fashe da kuka tareda zubewa a kasa Ummi ta ɗauketa suka tafi da'ita asibiti nan take Alkali yawanke ni sannan ya yankewa Zainaba da su Damo hukuncin kisa ta hanyar rataya mahaifiyar Zainaba dake cikin kotun itada Zainaba ganin yanda yan sanda suka kama Zainaban yasa ta yanke jiki ta faɗi nan take rai yayi halinsa.

Mami kuka take sosai jikinta sai karkarwa yake yaya Jabeer ya riketa zuwa motarsa muka shuga zuwa gida, sosai masoyana suke ta zuwa tayani murna,wasa_wasa saiga Mami ta kwanta ciwo kamar bazata tashi ba kwananta biyar a asibiti sannan taji sauki aka sallamota.

Rayuwa nake wata irin rayuwa mara jin daɗi kullum cikin kuka muke nida Ameera musamman in mukaga hoton Ankul dole tasa Mami ta ɗeɓe duk hotunansa dake cikin gidan, karatuna naci gaba namaida hankali sosai wajan zuwa makaranta cikin shekaru biyu na kammala natafi low school.


__________Ahankali yafuto daga cikin tsadaddiyar motarsa fuskarsa ba ɗigo annuri, yajima tsaye nan jikin motar yana kallon cikin gidansa, kafin ya saka hannu yaɗau jakar Laptop ɗinsa ya saɓa a kafaɗarsa yafara takawa a cikin compound ɗin, har zuwa tsakiyar falo, da gudu wata kyakkyawar yarinya da bazata wuce shekaru biyu ba ta futo daga ɗaki ta ɗanesa cikin muryarsu irinta yara tace "Papi welcome back" lumshe idanu yayi tareda sumbatar kumatun yarinyar

Yace "My Princess yaya gida" futowa tayi daga ɗakinta tayi kwalliya sosai cikin kananun kaya riga da wando wanda suka matukar amsar jikinta, kokarin shugewa jikinsa take yaɗaga mata hannu, ya ɗauki yarsa suka wuce ɗakinsa, dage kai Baraka tayi tanabin mijin nata da kallo tarasa gane kan wannan bahagon mijin nata shekaru uku kenan da auransu amma babu wata shakuwa a tsakaninsu bata taɓa ganin dariyarsa ba sai ranar data haifa masa Baby taga yana murmushi sanda yagaya mata yasawa yarinyar Aminatu Su'ad kowa da Su'ad yake kiran yarinyar amma shi yabi ya kakaba mata Princess tarasa wanne irin so Fu'ad yakewa Princess indai yana gida to yana tare da'ita harta kwana tare suke da'ita ko ita sai yayi sati bai haɗa makwanci da'ita ba indai ba bukatarsa ce takawosa ba,

Wanka yayi yafuto yana goge ruwan jikinsa da karamin tuwel Princess ya kalla wacce ke zaune saman gado tana game a wayarsa murmushi yayi yanajin kaunar yarinyar tana kara shugarsa, lumshe idanu yayi yana tuna farkon haɗuwarsa da Su'ad irin soyayyar dasukayi har zuwa kallon karshe dayayi mata ranar ɗaurin auranta da Fahad, da sauri ya zauna gefan gado yadafe kansa yana sake tuna rayuwarsa tunta yarinta shida Fahad yatuna yau shekaru uku kenan ba wanda ya nemi a wani acikinsu, da sauri ya ɗakko tsohon sim ɗinsa na nageria ya saka cikin wayansa yai copy ɗin lambar best freind kamar yanda yai save ɗin numbar, yakira yafi sau goma amma maganar ɗayace lambar bama ta aiki, sake dafa kansa yayi ya kira Abokinsa Usman bayan sun gaisa yace

"Usee asamarmin jirgi inda dama zuwa gobe nakeson sauka a nageria"

Dariya Usee yayi yace "Turaki ikon Allah yau kuma nageria tai kira kenan kaida madam ko kai ɗaya?"

"Nida Princess banda Mamanta"

"Angama mai girma turaki"

Ko Baraka bai gayawa tafiyar ba sai sanda zasu tafi airport yace "Zamu tafi gida da Princess ba daɗewa zamuyi ba bana tunanin zamu wuce one week"

Rau rau tayi da idanu kamar zatayi kuka tace "Ni wanne laifi nayi dabaza'a tafi dani ba, shekara uku fa rabonda naga mamata"

Batare daya kalleta ba yace "Ni tawa mamarma mutuwa tayi samada shekaru rabona da'ita yaya nayi saike da kullum sai kinji muryanta kuna vidio call kina ganinta"

Tana kallo jirginsu yatashi tana hawaye ta tare texzii tahau zuwa gida zuciyarta kamar zata fashe saboda bakin cikin Fu'ad ita kam sam bazata taɓa ɗorar da farin cikin aure ba babu wata soyayya a rayuwar auran nasu share hawayanta tayi tana faɗin "Anty Jamila duk ke kika jamin dan haka nima bazan taɓa baki haɗin kai wajan cikar burinki"

__________Jin ana kwankwaso kofa yasa na mike da sauri na buɗe dan daman zaman jiransa nake, tsayawa yayi a bakin kofar ya harɗe hannuwansa a kirji ganin an buɗe kofar yasa ya shugo da sallama saida ya zauna na kawo masa lemu da ruwa, bai sha ba saima wani kallo dana lura yana bina dashi, ganin na kamasa yana kallona yasa ya ɗauki wayarsa ya waske yana dannawa.

Binsa nayi da kallo dan ganinsa saiya tunamin da Ankul ɗina ba kaɗan ba suke yanayi da Uncle ɗin dande wannan yafi Uncle tsayi, sanye yake cikin kananun kaya blue jeans da black shart katse shurun namu nayi ta hanyar faɗin "Nura ko"

Kallona yayi yana wani taɓe baki kana yace "No Am Nurein"

"Ok Mamin bata nan taje nan zoo road amma ina zaton tana hanya ni sakon data bani tace nura zan bawa kai kuma kace Nurein so inaga ba naka bane"

ɗagowa yayi yana kallona karaf idanunmu suka sarke cikin na juna kallon
End Ads