x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 5 - KUKAN ZUCIYA

  • 12001 words
  • 15000 words
  • Out of 38354 words

Category: Tale Stories

Views 38

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
gangara gefan titi, Asibiti aka wuce dasu fu'ad da gaggawa ganin yanda jini ke zuba daga kan sarkin mota, Fu'ad ciwon hannunsa kawai aka wanke masa tareda saka masa bandeji, duk wannan abun gaba ɗaya zuciyarsa tana wajan Su'ad da har sannan yakejin sautin kukanta acikin kunnuwansa, kai tsaye gidan yayarsa Hadiyya yanufa acan yai wanka ya canza kaya ko abincin data ajje masa baici ba yafuce zuwa gidansu Su'ad baiko tsaya neman motaba, yahau adaidaita shidai kawai burinsa yaje ga Su'ad yaji damuwarta, baisha wahalar shuga gidanba kasancewar masu tsaron gidan sun ruga sun san sa.

kai tsaye garden yanufa inda suka saba zama da Su'ad ɗin saida yazauna saman kujera kana yakira lambarta ya shaida mata gashi nan cikin gidansu inda suka saba zama, da sauri takatse kiran ta futa da gudo ko mayafi bata saka ba, baisan da shugowarta garden ɗinba sabida idanunsa dasuke rufe haka kawai yakejin wata irin faɗuwar gaba wacce bai taɓajin irinta ba a rayuwarsa, kanta ta kifa saman cinyarsa tareda fashewa da kuka "Su'ad na gamaki da girman Allah ki gayamin abinda ke sakaki kukan nan dukkin ruɗani da kukan nan banda Allah yakiyaye mu ma da tuni ina lahira! Princess idan mutum yana cikin damuwa kuka bashine magani ba addu'a itake maganin komai"

"Nashuga uku Fu'ad kowa ya tsaneni a gidan nan gaba ɗaya sun juyamin baya Ankul sukeso baniba ashe haka rashin mahaifi yake na tabbata da Daddyna yana raye zai tausayamin yabani abinda zuciyata ke so, wai Ankul Fahad ne yake sona har'an tsaida ranar bikinmu maiyasa maiyasa ankul zaimin haka!" da sauri Fu'ad yasa hannu yadafe saitin zuciyarsa dayaji tai masa wani irin bugawa saboda yanda zancan yadaki zuciyar tasa, wani duhu yagani a idanunsa ganinsa yaɗauke na wucin gadi😥hakan yasa ya lumshe idanunsa yana karanto addu'a _Allahumma ajirni fi musibati wakalifni khairan minha, la'ilaha illah anta subahanaka inni kuntu minal zalimin_ ```Allahumma la sahala inlla....Su'ad ta amshe suka karasa tare, yai shuru kawai sabida yanda yakejin zuciyarsa ya tabbata inya buɗi baki kuka zaiyi shi kuma baison yayi kuka gaban Su'ad, jin shurun Fu'ad yasa taci gaba da basa labarin yanda sukai da baban karaye, gaba ɗaya ya shuga damuwa kansa ya kulle yama kasa cewa komai abu ɗaya daya sani shine ko sama da kasa zata haɗe bayajin zai iya hakura da Su'ad, "Fu'ad kayi shuru bakace komaiba dan Allah kanema mana mafuta ko kuma mu gudu mubar garin nan mutafi wata kasar musamu a ɗaura mana aure inyaso saimu dawo daga baya" buɗe idanunsa yayi akan fuskar Su'ad data gama ɓaci da hawaye shima idanunsa yayi jajir yace "Zaki bini da gaske zaki bini mu gudu sudan a ɗaura mana aure acan dangin babata inyaso saimu dawo" kanta tashuga gyaɗa masa mikewa yayi yana kallon agogo yace "kije kiyi sallar mangariba lokacin sallah yayi ki mana addu'a Allah yabamu nasara awannan yakin dake tunkaromu amma kisani tabbas ni nakine kema tawace ruwa da iska babu abinda zai rabamu nidake kamar hanta da jini ne rabamu zaiyi wuya, ki tattara komai naki da kikasan yanada mihimmanci inayin sallah zamubar gidan nan.....🙆‍♀️

Saura kiris a daina turasa ko ina zai ci gaba da zuwar maku ne a group ɗina na Kukan Zuciya real fans idan har kinsan da gaske kinason cigaba da bin book ɗin nan to maza yimin magana ta wannan lambar 07039793439 zanyi adding naki a group ɗin batare da kin biya ko sisinki ba🥰

[6/4, 7:48 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹


Story and weitting by
Mamie Yusuf Daboo🥰


☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA


11&12

Su'ad ta ruko hannun Fu'ad daya juya zai tafi masallaci ya juyo yana mata murmushi kallon hannun nasa tayi tareda kafawa zoban hannunsa idanu, ahankali ta ciro zoban azurfar dake hannunta tasaka masa a hannunsa tana matukarji da zoban Ankul Fahad ya siyo mata shi awani zuwa saudiya dayayi, ta ciro na hannunsa tasaka a babban ɗan yatsanta tayi ko sa'a ya zauna ta kwantar da kanta saman kirjinsa

"Wannan zoban yazama zoban alkawari a tsakaninmu, alkawari mukayi da zuciyoyinmu matukar muna numfashi babu rabuwa a tsakaninmu duk rintsin da zamu shuga mu tabbata a kaunar junanmu, musa aranmu babu mai rabamu inba mutuwa ba!" Rukota yayi sosai ajikinsa ahankali

Yace "Na amince da duk abinda kikace insha Allah ni nakine ke tawace Ruwa da iska babu abinda zai rabamu ba rabuwa nidake" Ankul Fahad da tun futowar Su'ad yabiyo bayanta a ɓoye yanason yaga inda zata take wannan gudun kamar bata hayyacinta, ganin inda ta shuga yasa ya ɓuya jikin bishiya kasancewar garin yafara duhu yasa basu gansa ba amma shi yana ganinsu daga inda yake yanama jiyo duk maganganunsu, hawaye yake sosai dan bai taɓa zaton akwai soyayya tsakanin Su'ad da Fu'ad ba, a iya zaman fu'ad a gidan zai iya cewa bai taɓa ganin sunyi magana da ita ba saima harare harare, ashe soyayya suke suka mayar dashi wawa, ashe harare hararan dasukewa juna na soyayya ne yakasa ganewa, ahankali yafuto daga wajan ɓuyansa

Yace "Baku kyautamin ba tayaya kuka ɓoyemin wannan babban abin farin cikin, Su'ad azatona nine mutum na farko dazaki fara faɗamin abokina yana sonki, kaima Aboki duk laifinka ne daka gayamin kanason Besty wallahi da bazan taɓa fallasa sirrin zuciyata ba, ashe daman Su'ad ce budurwar da kullum kake gayamin kanasonta kake cewa kayi budurwa yar garinmu, ina mai tabbatar maku da na janye batun aurena da Su'ad na bar maka danna gano itace farin cikinka ni kuma fatana ako da yaushe inganku cikin farin ciki ina maku fatan alheri a rayuwar auranku!" yana gama faɗar haka yai gaba Fu'ad yabisa yana kiransa amma baiko waiwayo ya kallesa ba ya wuce cikin gida abinsa, kai tsaye ɗakin Mami ya wuce yasameta zaune saman gado tana lissafin kuɗi, zaman da yayi yasa ta kallesa tareda ajje abinda take

Tace "Fahad lafiya maiya sameka?" hawayan idanunsa suka zubo kan kyakkyawar fuskarsa "Mami ashe daman Su'ad da Fu'ad soyayya suke ban sani ba! Mami yaya zanyi da tarin soyayyar danakewa Aminatu yanzu haka zan hakura inaji ina gani in rasa farin cikina, mami bakiji yanda zuciyata take harbawa jinake kamar zan mutu" tausayin kaninta yakama ta ta sakko daga saman gadon ta zauna kusa dashi tareda dafa kafaɗarsa tana bugawa ahankali alamar rarrashi tama kasa cewa komai jitake kamar ta tayasa kukan amma ina bazatayi ba ta karyar masa da gwiwa matsayinta na babba ita zata karfaffa masa gwiwa wajan ganin ya jajirce yasawa zuciyarsa salama "Kayi hakuri sau tari abinda kakeso bashi ke zama alkhairi ba a rayuwarka kasawa ranka dama can Su'ad ba rabonka bace ka sadaukar da soyayyarka ga masoyanka guda biyu da kariga kasani farin cikinkinsu shine naka, inaso gobe kaje karaye ka gayawa baba sunusi ka janye batun auranka da Su'ad kafasa" haka tayita lallashinsa har zuciyarsa tayi sanyi yaji aransa yama hakura da auran ma gaba ɗaya zai zauna a haka ya karashe sauran rayuwar data rage masa.

Su'ad idar da sallarta kenan tana zaune saman dadduma tana azkhar Ummi tashugo ɗakin ta zauna gefan gadon su'ad ɗin ahankali tafara magana da sigar lallashi "Su'ad kiyi hakuri ki ɗauki kaddara kisa aranki auranki da Fahad babu fashi naga wannan dogon yazo mana gida, bansan dame yazo ba amma inaji ajikina kamar da abinda kuke kullawa, yanzu dan Allah bakiji kunyar Mami ba agabanta kike nunawa ɗan uwanta baki sonsa ke bakisan kara ba, tunda aka haifeki take ɗawainiya dake koni dana haifeki bansan wahalarki ba, ita komai tasamu ke dukkan takardun kadarorinta sunanki ne komai ta samu Su'ad burinta akoda yaushe tasaki farinciki ashe kodan wannan bazaki so ɗan uwanta ba, inda watace bazata taɓa goya maki bayaba amma dayake kaunar datake maki daga zuciyarta ne haka ta zaɓi farin cikinki akan na ɗan uwanta, koma ba wannan ba ashe bazaki iya cikawa Daddynki wasiyarsa ba daya bari, dan Allah amatsayina na wacce na haifeki na rokeki daki hakura da Fu'ad ki rungumi kaddararki Fahad insha Allah bazakiyi nadamar auransa ba zakiyi farin ciki" tunda Ummi tafara magana Su'ad ke kuka gaba ɗaya Ummi tagama kashe mata jiki amma yaya zatayi da zuciyarta kan abinda takeso, ita bata taɓa son Ankul ba batajin kuma zata so shi, bare takaisu ga aure, to inta auri Fahad maita aura, kanin Mami zuciyarta tabata amsa tayaya zata iya zaman aure da wanda takewa kallon kanin mahaifiyarta, koda ta auri Fahad batajin zata iya basa kulawar da mace take bawa namiji ina zatakai kunyarsa, batasanma Ummi ta futa a ɗakinba sai data ɗago kanta da niyyar tayi magana kana taga ɗakin ba kowa sai ita, Fu'ad massages yayi mata ya koma asibiti wajan sarkin mota za'ayi masa karin jini.

Washe gari Ankul sassafe yaɗauki hanyar karaye karfe goma acan tayi masa bai wani jima ba ya juyo kai tsaye asibitinsu ya wuce bai biyo gida ba, tinda yazauna a office ɗinsa yakasa aikata komai ko feshan ɗinsa Dr hafis yaturawa su, Dr hafis daya tashi ya shuga office ɗin Fahad harya zauna fahad baisan yashugo ba saida yasa hannu yataɓa sa kana ya kallesa da sauri yana ajjiyar zuciya kamar wanda yai kuka.


"Amma bakada lafiya kwana biyun nan naganka sai'a slow" Fahad ya ɗora kansa jikin kujera ahankili kujeran ke juyawa dashi yace "Lafiya kalau nake kawai inada damuwa ne akan Su'ad" Dr Hafis dariya yayi "Su'ad Su'ad ko yaushe dai maganarka akanta nagaya maka kafaɗa mata awuce wajan katsaya kana kallon ruwa sai kwaɗo yayi maka kafa tukunna" sauke numfashi Fahad yayi tareda futar da iska mai zafi daga bakinsa

Yace "Na nawa kuma asheni ina zaune yaron nan Fu'ad yagama siye zuciyarta" nan dai Fahad yasanarwa da Dr Hafis komai "Kabar damuwa kayi addu'ar neman zaɓin Allah hakan zaifi wannan damuwar da kake ciki wacce zata iya haifar maka da ciwo" godiya yayiwa Dr sannan suka mike suka futa tare dan tuni lokacin tashinsu yayi.

Fahad koda ya koma gida wayar Fu'ad yakira yajima bai ɗaga kiranba sannan ya ɗaga.

"Aboki kana inane ko ka koma"

"A'a ina kano asibiti jiya wajan tahowarmu motarmu ta faɗi sarkin mota yabugu aka kaganshi a kwance tun jiya ba cigaba ɗazu naiwa mai martaba magana yasoma shirya masa tafiya cairo anjima jirginsu zai tashi" Fahad wanka kawai yayi ko abinci bai ciba ya wuce wajan Fu'ad wanda tun a wayar dayaji muryarsa yasan yana tare da damuwa, sanda yaje kallo ɗaya yamasa yaga yayi wani zuru zuru shidaman haka yake yanzu ne damuwa zata saka sa rama kilama nan gaba kaɗan saiya kwanta zazzaɓi bayan sun kai sarkin mota airport suka juyo Fahad dake tuki ya kalli Fu'ad daya ja uban tagumi kansa kurum ya girgiza yana faɗin

"Duk kabi kasa damuwa aranka kalli yanda kayi wani ziru zuru kamar wanda yatashi daga jinya" murmishi Fu'ad yayi yana kallon Fahad dayaci gaba da faɗin "Ni naruga nabar maka Su'ad harma naje karaye munyi magana da Baban karaye kasan girman ka awajena ya wuce na auri abinda kake so tabbas dan son Su'ad ina sonta tun randa tazo duniya naji banida wata mata inba itaba!" Fu'ad yaɗago kansa yana kallon Fahad kana yace

"Bazan iya auran abinda kakeso ba aboki kai kafi cancanta daka aureta saboda kafini sonta, kai karayu da kaunarta ni kuma yan watanni nayi a soyayyarta dan haka bazan iya auranta ba ni na bar maka bazan aureta! ajje ni gidan Anty Hadiyya" mirmushi Fahad yayi yanabin Fu'ad da kallon tausayi

Yace "Bazan ajjeka ba da gidanta kake sauka naga inkazo kano ko kwana nawa zakai muna tare sai wannan karon ashe daman har mace takai girman da zata raba amintarmu" lumshe ido Fu'ad yayi yana murmushi

Yace "Su'ad tayi kaɗan ta rabamu muje ni daman banson naje gidanne ta ganni ta shuga damuwa banson damuwarta ko kaɗan" Fahad baice komaiba yaci gaba da tukinsa "Inason nasai kayan sawa banzo da shirin kwanan garin nan ba sai gashi ina shirin yin na biyu"

"Wanne kaya kuma zaka siya, ga nawa nan nasan zasuyi maka saidai tsayinko" kallon juna sukai sai kuma suka fashe da dariya atare suka furta "Maika tuna" nan ma dariyar sukayi kamar basune a damuwa ba Fahad yace "Natuna rayuwarmu ta scaundry inban wanke Uniform ɗina ba na saka naka su Moha suyita tsokanata saboda yanda rigan ke sakkomin har kusan kasa oh rayuwa kaga yanda muke da Moha kamar baza'a rabuba amma tunda muka kammala school bamu kara ganin juna ba ko yana raye" har sannan murmushi bayyane kan fuskar Fu'ad yace "Allah nima nakasa mantawa da Moha koya zama sojan ko yaya oho Allah dai yasake haɗamu wata rana" har suka karasa cikin gida suna hira, gidan shuru kamar babu kowa da'ace da ne da tuni koba yaran gidan zaka samu Mami da Ummi a falo suna hira amma damuwa yanzu tasa kowa zaman tunani a ɗaki shiyasa ba wanda yasan da zuwan Fu'ad gidan.

Karfe huɗu baban karaye yaiwa gidan tsinke tunda ya zauna yakewa Mami faɗa wai ta zuga ɗan uwanta yaje ya gaya masa ya fasa auran Aminatu "To kisani wallahi koda zan ɗaura aure gobe da safe Fahad yasakomin ita da dare to saina ɗaura aidai na cika wasiyyar ɗan uwana kuma ku sani na maida ɗaurin auran nan da kwana shida ranar asabar mai zuwa aure babu fashi!" yagama faɗansa ya tafi ko gaisawa basuyi ba, Ummi daɗi taji sosai nan take tasoma kiran waya tana sanar da bikin Su'ad asabar, Fahad jiki a sanyaye yamike daga wajan yakoma ɗakinsa anan yasami Fu'ad kwance kan gado yana kuka kamar wani mace dan gaba ɗaya yana jiyo faɗan baban karaye daga inda yake saboda yanda yake maganar cikin faɗa da fusata

"Fahad maiyasa banda sa'a a soyayya kowacce mace naso bana samu abaya naso Suwaiba kamar hauka amma ta yaudareni yanzu naso Su'ad wacce itama ke sona kamar ranta amma kaddara ta rabamu Fahad mai nayiwa soyayya take azabtar dani haka nagama soyayya bazan karaba!" mikewa yayi yana yiwa Fahad sallama ba yanda Fahad bai lallashi Fu'ad ba kan yazauna zuwa safiya sai yabi jirgi ya koma amma yakafe har yakai kofar futa daga falon farko na gidan yaja ya tsaya jin Su'ad na kiran sunansa kallo ɗaya yayiwa fuskarta bai sake kallonta ba saboda yanda zuciyarsa ta tsinke

"Daman kana gidan nan ban sani ba yaushe kazo"
"Ɗazu muka shugo da Fahad yanzunma tafiya zanyi" yafaɗi haka yana cigaba da tafiya da ɗan gudu take binsa saida yafuta compound sannan ya tsaya "Zantafi Su'ad kiyi biyayya ga iyayanki duk ɗa nagari yana son ganin farin cikin iyayansa kisa aranki daman can Allah bai kaddara zamuyi aure ba! iyakarmu soyayya kimanta dani ki rungumi mijinki Fahad zakiji daɗin zama dashi fiye dani insha Allah zan dawo ran asabar wajan ɗaurin auranku" kam ta kame waje ɗaya jin maganganun Fu'ad bata ankare ba taga Fu'ad yana shirin fita daga gidan wani ihu ta saki tareda faɗin Fu'ad Come back please!!! ta zabura zatabi bayansa taji an riketa duk da idanunta a rufe suke da ɓacin rai tasan wane saboda jin kamshin sa datayi "Kasakeni Ankul kasakeni nabisa kana kallo farin cikina zai tafi" gaba ɗaya Fahad jiyake kamar yayi kuka ganin yanda jikin Su'ad ke ɓari kamar mai shirin tada aljanu🤭"Saketa Fahad" Ummi dake kallonsu tun ɗazu ta faɗi shiko sake kankameta yayi danshi yafara tunanin ba lafiyarta kalau ba "Kasake ta nace! tabisa suje can ta nemi wasu iyayen su ɗaura mata aure da shi saboda ke bakisan tawalkali ba, shi yana namiji ya iya tafiya yabarki ya gaya maki gaskiyya amma kin kasa ɗauka saboda idaninki sun rufe da makauniyar soyayyarsa" Fahad baiyi aune ba sai kawai gani yayi Su'ad ta sulale ta faɗi kasa tana wani irin numfashi daba shi ba hatta Ummi dake faɗa saida hankalinta yatashi, Mami da sauri tayi kan Su'ad tana faɗin

"Shikenan kun kashe min ita ku bakuda asara ni kuka cuta Su'ad dan Allah kitashi ke kaɗai nakeda ita ke nake kalla ako da yaushe naji sanyi a raina ke kika maye min gurbin da a kullum ke damuna a zuci Aminah...😥
[6/4, 7:48 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹


Story and weitting by
Mamie Yusuf Daboo🥰


☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
S ANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

12&14


Fahad ya kinkimi Su'ad yasata a mota gaba ɗaya hankalinsa yatashi asibitinsu ya wuce da'ita Dr Hafis ya karɓeta ruwa ya jona mata tareda mata alkurai harya samu tadawo normal tai barci, Hafis yadafa kafaɗar Fahad yace "Agaskiyya kubi yarinyar nan a yanda takeso abokina nasan duk akan maganan nan ce dan Allah abarta kasan yanda jininta yai mugun hawa kuwa, wallahi kuka cigaba da kuntata mata zaku iya rasata gaba ɗaya"

Fahad yadafe kansa cikeda damuwa ya ce "Dr narasa yanda zanyi Baban karaye yadage kan maganar nan halin yanzuma fa harya tsayar da rana gaskiyya inaga barin garin nan zanyi inkomai ya dai daita na dawo" "Kaje ina?" yaji muryar Ummi tana faɗa tareda shugowa ɗakin "Wallahi kasani ko mutuwa Su'ad tayi sai an ɗaura auran nan an kaita gidanka inyaso daga gidanka a wuce da'ita kabari, Mami ko kallon inda Ummi da Fahad da suke magana batai ba gaba ɗaya hankalinta naga Su'ad ganin yanda take sauke nunfashi a hankali yasa hankalinta kwanciya.

Da kuka sosai Nafarka lokacin ɗakin ba kowa sai Yaya Fatima Ummi da Mami sun futa, Yaya Fatima ta hararw ni kamar zata kaimin duka cikin masifa ta ke faɗin "Su'ad yanzu abinda kika zaɓarwa kanki kenan mai Fu'ad yakeda shi wanda Fahad bashi da? dan Allah ki kwantar da hankalinki ki rungumi kaddararki, a rayuwar nan fa kowa kika gani da kalar kaddarar sa" Kuka nake sosai nace "Na hakura da Fu'ad tunda harya iya karya alkawarinmu yatafi yabarni bayan munyi alkawarin duk runtsi duk wuya muna tare amma ya iya tsallake ni yatafi ya barni na hakura Yaya na karɓi zaɓin Daddy na zan cika masa burinsa bayan ransa zan tabbatar da wasiyyar sa daya barmin koda kuwa hakan na nufin tarwatsewar zuciyata da tabbatuwar kunci a rayuwata,"

"Insha Allah ma bazakiyi kunciba a gidan Fahad zaki samu farin ciki da walwala fiyeda kowacce
End Ads