sam bama haka da Uncle, ban taɓa masa kallon masoyi ba yanzun dai na faɗa soyayya wacce nake zaton zata wahalar dani danna ɗakko da zafi"
har muka gama lacture na futo zuciyata makale da tunanin bakon Uncle, zuciya da ruhi na ɗokin komawa gida nayi tozali da kyakkyawar fuskarsa mai cikeda annurin dake sanyaya zuciyata, wajan dana hango motar gidanmu na dosa kofar baya naketa kokarin buɗewa amma taki buɗuwa sai ta gaba dana ga anbuɗe min da sauri na shuga duk azatona Uncle ne saida na zauna ina buɗe jakata batare dana kalli wanda ke ciki ba nace "Uncle amma kayi saurin dawowa" jin baice min kala ba yasa na ɗago ina kallonsa, kallon kallo mukai ido cikin ido ni nafara ɗauke idanuna daga cikin nasa tareda sauke ajjiyar zuciya take wata kasala ta rufeni, nai saurin ɗora kaina saman seat na motar na lumshe idanuna ina jin yasoma tafiya da motar munyi tafiya mai nisa naji yayi parking gefan titi sai sannan na buɗe idanuna ina kallon sa, hannunsa duka biyun yana saman stearin motar yayinda ya ɗora kansa saman sitiyarin yana kallona da lumsassun idanun sa masu samin kasala kamar bayaso yasoma magana da muryar sa mai matukar daɗin ji da sauraro kamar baya so
"Ke bakya yiwa mutane magana saidai kirinka azabtar da zuciyar mutum!" da sauri na ɗago na sake kallonsa kashe min ido ɗaya yayi tareda ɗage gira, da murmushin sa daya doki zuciyata, bance masa kala ba saima gyara zamana danai "Kinsan yanda nakejin zuciya ta kuwa?" zuciyata bugawa take ko wanne bugun numfashi yana bugawa da sonki da kaunarki!, Su'ad hakika zuciyata tayi sartse da kaunarki ina sonki! ina sonki Su'ad!!, da sauri na ɗago ina kallonsa dan tabbatar da gaske bakon Uncle ne ke gayamin yana sona....✍️
Free book ne idan kinbi link baiyi ba kimin magana kai tsaye ta wannan lambar 07039793439 ki save Number ta da Mamie Yusuf Daboo
[6/4, 7:46 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA* 🌹
Story and Writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Assosciasion* ☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA
2-3
Kafin na gama tantance shin da gaske daga bakin Fu'ad maganar ke futowa na kuma tsinkayo miryar sa yana cewa "Ki tausayawa jaririyar zuciyata ki amshi soyayyarta na taɓa soyayya a can baya da wata wacce na mato a kanta kullum mafarkina da burina shine tazama matata ashe ita ba da gaske take sona ba yaudara ta take sai daga baya naji labarin auranta da wani bani ba! ni bana yaudara ba kuma nason a yaudare ni, mutum ne ni kaifi ɗaya idan nace E! to bazan taɓa canzawa ba nace a'a, Su'ad dan Allah karki yaudare ni in kinsan kinada wanda kikeso karki ɓoyemin zuciyata bata iya soyayya ba in inason abu haukan so nake masa So nake masa bana wasaba, kaunarki ta shugeni tun kallon farkon danai maki Su'ad"
Tsit nayi a zuciyata ina tunanin Shin wai wacce amsa zan bawa Uncle Fu'ad shin na amshi soyayyar sa kona ja aji, batare dana gama shawara da zuciyata ba najiyo ina magana "Ina sonka Uncle Fu'ad nima dan Allah karka yaudare ni ban taɓa soyayya ba banma taɓa yin saurayi ba ko yaushe idan wani yazo wajena Uncle baya bari ya kuma dawowa yace yafison nayi karatu mai zurfi kaima na roke ka muyi soyayyarmu cikin sirri karka bari ya sani!"
"Bakida matsala dani bazan taɓa bari Uncle ɗinki yasani ba nidai fatana ki soni sona gaskiyya! ina mai tabbatar maki auranki zanyi nan bada jimawa ba" sosai muke soyayya da Uncle Fu'ad munyi wata iriyar shakuwa musamman a waya mukan ɓata lokaci muna waya musamman cikin dare inda muke musayar kalaman soyayya, zuciya ta tuni ta narke a kaunar Fu'ad ta yanda nake jin inban aure shi ba bazan taɓa iya zaman aure da wani ba, gaba ɗaya na basa dukkan soyayya ta.
Ina kwance cikin ɗakina Uncle Fahad yashigo yasha kwalliya cikin shadda ruwan zuma ya ɗora farar rigar su ta likitoci a saman kayan sa hannunsa na rikeda wayoyinsa ahankali yake bubbuga fulon danake kai, buɗe lumsansun idanuwa na nayi wanda suka rune da barci turo baki gaba nayi tareda gyara kwanciya ta "Ni maizan maka wai Uncle?" kallon agogo yayi yana nunamin "Kalli mana na makara fa tun ɗazu ke nake jira baki futo ba" saida na kuma gyara kwanciyya ta sannan nace "Yau banida lacture kaje kawai" ina kallonsa yafuta yanamin wani kallo da ako yaushe shi nake gani akan fuskarsa harya fuce yana murmushi.
Karar shugowar sako cikin wayata yasa na tashi ina dubawa dan azatona Uncle Fu'ud ne ilai kuwa shine yake sanar dani yana garden mu haɗu acan, a gurguje na shirya ina kallon agogo sha biyu saura kwata, harna futo na koma na sako rigar sanyi saboda wani sanyi danaji anayi ga iska tana busawa, ahankali nake takawa har na shuga garden ɗin tun daga nesa na hangosa ya haɗe sosai cikin kananun kaya jan wando sai farar shart daya ɗorawa rigar sanyi mai haɗe da hula itama ja mai farin layi layi wayarsa yake dannawa harna karaso baisan nazo ba saida nayi gyaran murya, a hankali ya ɗago kyawawan idanuwansa yanamin wani shagalallan kallo mai haɗe da murmushi, ni gaba ɗayama Fu'ad mamaki yake bani yanda yake wani narkemin in muna tare, kiran daya shugo wayarsa ya katse masa maganar dayai niyar yi yana mirmushi yai picking call ɗin, banji mai a kace a ɗaya mangaranba sai shi danaji yana faɗin
"Oh Khady ba haka bane kinsan dai yanda muke dake, ina kano akwai abinda ya rikeni shiyasa ban dawo ba amma ina hanya gobe indai haka zai faranta maki rai" bai kara cewa komai ba yakashe wayar yana kallona ganin yanda na haɗe rai, "Ran hukuma ya daɗe wannan fuskar shanun fa" kwafa nayi ina gyaɗa kai nace "Wacece Khady?"
"Au shine abin fushin Khady kanwa tace mu biyu kaɗai mahaifiyarmu ta haifa, kafin Allah yai mata rasuwa ina matukar ji da Khady kasancewar bata da kowa a kasar nan mahaifiyarmu yar kasar sudan ce ta haɗu da mahaifina Alhaji bello a jami'a lokacin yana malamin makaranta a jami'ar su sunyi soyayya sosai dashi kafin maganar aure ta shuga tsakani, kakana wanda ya haifi Abbunmu shine sarkin garinmu su biyu jal ya haifa shiyasa yake matuwar son ya'yansa da basu duk abinda suke so shiyasa a sanda yaji labarin soyayyar Abbi da Ummu takanas yatashi zuwa Sudan bai dawo ba saida ya tabbatar an ɗaura masu aure sannan yabaro su acan yadawo, shekara biyu da auran Allah yaiwa mai martaba rasuwa hakan yasa Abbi suka dawo nageria lokacin ina ɗan shekara ɗaya, ankai ruwa rana akan naɗin sarauta inda majalissar sarki suka zaɓi Abbi shi zai maye gurbin mahaifinsa sam shi dama can baya ra'ayi sarauta, cikin dare ya lallaɓa sukabar gida shida Ummu dani ba'a sake jin labarin suba saida aka naɗa kanin Abbu ɗinmu sannan suka dawo, shekarata goma sha biyar lokacin muna secaundry nida Fahad aka haifi Khadija nayi murna sosai lokacin da muka koma gida muka tarar Ummu ta haihu, nida Fahad mun shaku sosai shakuwarmu tasa ko hutu akai tare muke tafiya gidanmu muyi rabin hutunmu acan sannan muje gidansu mu karasa hutun a can shakuwarmu ta zarce Abota tazama aminta, a shekarar da muka gama Secaundry Allah yaiwa Ummuna rasuwa sakamakon haihuwa datazo yi Allah baisa zata haifi abinda ke cikinta ba suka koma tare! munyi kuka kamar bazamu daina ba nida Khadija da Fahad, awannan yanayi Abbansu Fahad ya ɗaukemu yakaimu Rasha karatau acan mukayi karantu likita, bamu taɓa komowa gida ba har saida muka kammala karatu watanmu biyu da dawowa nan ma Allah yaiwa Abban su Fahad rasuwa, nadawo na samu Abbunmu yayi aure kawar Ummu wacce tunda tazo nageria batada aminiya sama da'ita, sosai take azabtar da Khadija ni kuwa daman ba zaman gidanmu nake ba ko yaushe ina tareda mai martaba kanin mahaifina acewarsu nine yarima mai jiran gado saboda mai martaba bayada ɗa ko ɗaya ya'yansa duka matane, shiyasa ko yaushe muna tare, awannan lokacin Fahad yayi aure ni kuma na wuce Canada inda naci gaba da karatu bayan na kammala na sami aiki acan shekaruna goma acan ban sake waiwayar gida ba inadai bincikar rayuwar Khadija wacce nasa matar mai martaba Umma ta ɗauketa ta maidata wajanta, Umma nada kirki ita kullum mukewa kallon uwa mahaifiya wacce bata ɗauki lamarin mu da sauki ba, ko kafin rasuwar Ummu akwai aminta mai karfi tsakaninta da Umma idan bakasani ba ka ganmu tareda Umma bazaka taɓa zaton ba ita ta kawomu duniya ba duk da wasu na mata kallon da wata munufa take nuna mana so". Sosai Fu'ad yabani tausayi ganin yanda yake goge kwalla tabbas rashin uwa babban rashine daba kowane ke ganewa ba sai wanda yarasa tashi Cikeda tausayawa nake kallonsa nama kasa cewa komai, kiran sallar damukaji yasa muka mike atare zuwa cikin gida, da yaya shareef naci karo abakin kofa ya harɗe hannu yana kallona fuskarsa babu walwala yace "Ke meke tsakaninki da AMEEN Fu'ad" ɗan ɗagowa nayi na kallesa yasake haɗe rai yana kallona nace "Ba komai kawai naje garden ne nagansa shine fa mukayi hira" wucewa yayi da'alama daman masallaci zashi ganinmu dayai tareda Fu'ad yasa ya tsaya tambayata, kai tsaye ɗakina na wuce wanda ke manne dana mami na, kasancewar ina priod yasa banyi alwalaba na kwanta saman gado.
Alhaji Usman karaye shine mahaifina haifaffan garin karaye ne, makarantar allo yakawo sa cikin garin kano inda bayan yasauke kur'ani ya shuga makarantar boko, wanki da guga yake shiya rikesa harya kammala pramary da sceundry, anan karatun nasa ya tsaya saboda awancan lokacin ba abune mai sauki ba shiga jami'a kusan sai kanada hanya sannan zaka samu shuga, Alhaji Usman ya haɗu da wani tsohon soja dayake kawo masa wanki sun saba sosai ta yanda har gidansa yakanje anan ne yake gayawa Genaral Aliyu cewa yana son shima yazama soja amma bayada hanya, haka Genaral ya shuge masa gaba harya sami damar tafiya makarantar horar da sojoji dake kaduna, bayan kammalawar sa aka tura sa aiki can jos, Genaral yaɗauki babbar yarsa ya aurawa Usman, Allah ya jarabci Alhaji usman dason matarsa Amina wacce keda tsananin biyayya gatada kirki, Alhaji Usman yataka mukamai na soji da dama ya zauna a garuruwa sosai, shekarunsu goma da aure da matarsa Amina amma bata taɓa haihuwa ba, ko kaɗan hakan bai damesa ba saboda son dayakewa Amina bayajin zai iya haɗata zama da wata ɗiya mace, gwaggo mahaifiyar Kanol Usman ita ta takura masa lalle saiya kara aure inba hakaba wlh saiya saki Amina, cikin haka Allah yahaɗa kanol da Dr Baseera Wali wacce ke aiki a babban asibitin kasa dake JOS, ya nuna sha'awar auranta saboda ya lura itama tanada saukin hali, watan Baseera goma a gidan Kanol ta haifi yarta mace kyakkyawa mai matukar kama da'ita ranar suna yarinya taci sunan Gwaggo waton Fateema, shekara biyu tsakani Baseera tasake haihuwar ɗa namiji Jabeer sannan Shareef daga nan haihuwar ta tsaya mata har sannan hajiya Amina bata haihu ba, ko kaɗan rashin haihuwar bai dameta ba ta dogara ga Allah tasani shike bada haihuwa, iyayanta ma saida suka jima kafin suka haifeta tana scoundry sannan aka haifi FAHAD
Yaran gidan Kanol sun taso kansu a haɗe bazaka taɓa gane cewar Baseera ce ta haifesu ba, Baseera suna kiranta da Ummi yayinda Hajiya Amina sukr kiranta da Mami, shekarun Shareef goma Ummi tasake haihuwar ya mace ranar suna yarinya taci sunan Hajiya Amina suke kiranta da Su'ad ba karamin gata Su'ad ke samuba awajan Mami itace komai nata kusanma awajanta take sai shan nono ke kaita wajan Ummi koda aka yaye Su'ad gaba ɗaya Ummi ta barwa Mami Su'ad, Fahad kanin Mami ba karamin so yakewa Su'ad ba ko yaushe yana tareda ita, shekarun Su'ad goma sha biyu Fahad ya auri yar wan babansa bayan rasuwar mahaifinsu Genaral Aliyu, Kanol Usman da Ummi yanzu haka suna zaune a kaduna inda Ummi ke aiki shima Kanol acan yake aiki, Mami da yara suna zaune a kano saboda Su'ad dake makaranta da kuma su yaya Jabeer dake aiki, tuni anyi bikin Yaya Fateema tana auran babban ɗan sanda suna zaune anan kano.
Su'ad dake shirin yin barci taga shugowar Fahad ɗakinta, saida ya zauna saman stool kana
Yace "Naga abincinki baki ciba, Ummi tace yau gaba ɗaya bata ganki ba ina kikaje" turo baki gaba tayi dan in tana gaban Uncle ɗin nata gaba ɗaya narkewa take ta koma karamar yarinya, shi kuma yayita biye mata tana zuba masa shagwaɓa da shiririta "Nifa Uncle yau ba kalar abinda nakeso ba akayi, kuma ai Ummi tasan bansan kunun gyaɗa da doya shine tayi ni bazanci komaiba yau" tafaɗi haka tana gyara kwanciyarta, "Wacce irin maganace haka Besty amma dai kinsan banson ki zauna da yunwa ko yanzu fa har karfe biyu bakici komai ba, kinga tashi gayamin mai kike son ci saina saka a siyo maki" da sauri na mike na zauna saman gadon ina murmushi kafin nace "Nifa Uncle kawai ka kaini nayo take away chips nakeson ci da shawarma sai meat pie da Peach mai sanyi" dafe kansa yayi yana kallonta kafin yace "Oh Su'ad nagaji dayawa yau mutum biyu naiwa cs yanzu haka gudowa nayi nazo na huta kuma ki sani na sake futa, bari kawai nabawa Seteven yasiyo maki" komawa tayi ta kwanta tana ɓata rai ahankali take mita "Shikenan kaje ka kwanta ɗin aidaman nasan basona kuke ba yan gidan nan ace na wuni banci abinci ba amma ba wanda ya damu dani, dan anga Mami da Daddy basa nan ne aida ko shi nasan zai kaini naci abinda raina keso" Fahad zama yayi gefan gadon yana cewa "Kinga bafa wani abun damuwa bane wane yace maki bamu damu dake ba, yanzu dai bari naje nayi wanka nazo na kaiki kici abinda ranki keso, kema ai kinsan bama haka dake farin cikinki ai shine nawa koba hakaba yar Uncle" yafaɗi haka yana kashe mata ido ɗaya, gabanta ne yai wata irin faɗuwa saboda ganin kallon dayake mata wanda baida maraba da irin wanda Fu'ad ke mata ako da yaushe, Bayan yayi wanka yazo suka fita tare basu wani jimaba suka dawo gida
Su'ad tare suka shugo gida da Uncle Fahad, shike rike da ledojin da tayo siyayya, tsakiyar falon ta baje taci wancan taci Ummi da yaya shareef na kallonta ba wanda ya kulata harta gama ta wuce ɗakinta.
AMEEN sosai yakejin daɗin zaman Kano tun washe garin randa yazo yacewa Yunus ya koma gida inzai komo zai biyo jirgi ko fita zaiyi shi kaɗai ke fita a motar FAHAD sau biyu yana kaiwa HIDAYA ziyara suyi hira sosai yai wasa da yaranta sannan yadawo gidansu Fahad kusan baida matsala da kowa a zamansa na gidan, sosai Ameen keson rayuwa irin haka ta ba ruwan kowa da kowa ba kamar suba a masarauta ko ina zaka kana tareda rakiyar fadawa shi yasa ya kwashe sati biyu a garin kano kafin ya saka ranar tafiya,
karfe goma na safiyar Ranar Lahdi Fu'ad yagama shirinsa na komawa garinsu, har sannan baiga futowar Su'ad ba, har sun gama sallama da Ummi sun futa compound yanata waige waigen inda zaiga Su'ad ta fito harya shiga mota yahangi futowarta lokacin Fahad na kokarin tasar mota, da sarsarfa ta karaso wajan tareda buɗe back seat ta zauna, Fu'ad ya sauke wata nauyayyar ajjiyar zuciya wacce har Fahad ya kallesa batare dayace komai ba ya juya yana kallon Su'ad
"Daman kinada lacture amma baki shirya da wuri ba sai yanzu, bayan nagaya maki karfe goma zankai Fu'ad airport" cuno baki tayi gaba kana ta ce "Aini dai rakaka zanyi banason zaman gidan nan gaba ɗaya su Ummi basa son gani na dan anga Mami bata nan kowa baya kulani kaima duka ka canza min yanzu ba ruwanka dani ko kaɗan baku rike amanar da Mami ta baku ba Allah ma yasa yau Mami da Daddy zasu dawo" Fahad tasar motar yayi batare dayace komai ba ya girgiza kai kawai yana yaba rigima irinta Su'ad yafara tafiya gate man ya buɗe mana kofa muka futa, saida Fahad ya fara tafiya saman kwalta sannan na futo da wayana na kunna data sakon Fu'ad shiya fara shugowa na buɗe da sauri ganin yana online
_"Princess kinyi kyau! bakiji yanda naji zuciyata ba dana ganni cikin mota zan bar gari batare dana ganki ba"_
_Tayaya zan bari farin cikina yatafi batare dana sake ganin saba zanyi kewarka_ ɗagowa yayi yana kallona ta madubin motar yakashe min ido tareda murmushi mai narkar da zuciyar masoya, haka mukaita musayar zafafan kalamai nida Fu'ad har muka karasa airport ɗin, zama mukayi muna jira sai nan da minti goma sha biyar jirgin da zaije garinsu zai tashi, Uncle Fahad ya zuba mana ido yana murmushi yace "Duk kun ɗauki waya kunata chat kun manta dani awajan, Su'ad dawa kike chat ne?" FAHAD ya aika mata da tambaya yana kokarin leka screen na wayar tai saurin kifa wayar a kan cinyarta kana ta basa amsa
"Da Ameerah" Fu'ad ma wayar ya ajje suna ɗan taɓa hira har jirginsu yatashi raina duk ba daɗi haka muka koma gida.
Da yamma ina zauna inda nasaba zama na cikin gidanmu wata yar rumfa ce da'aka kawatata da shuke shuke kala kala wajan yanada daɗin zama ga iska dake kaɗawa, kamshin wajan kawai ya'isa yaja hankalin mutum ya zauna, Uncle Fahad ne yakaraso wajan cikeda damuwa yaja kujera ya zauna kusa dani yajima yana kallona batare da yace komaiba na kula yana cikin damuwa hakan yasa nace "Uncle lafiya kake kuwa" ajjiyar zuciya yasauke a fili tareda saka hannunsa ya shafi sumar kansa kana ya ce "Besty ina cikin damuwa sosai, wata yarinya nakeso amma narasa ta hanyar da zanbi na faɗa mata ina sonta, tsoro nakeji gani nake kamar bazata soni ba, besty bani shawara bakiji yanda zuciyata take kaunar yarinyar ba" saida nayi dariya sosai sannan nace "Wacce mai sa'ace wannan da har Uncle ɗina yake shayin gaya mata yana sonta! kasan me kafuto kawai ka