you wallahi" na faɗa a fili hawaye na kwaranyowa daga cikin idaniyata, gogewa nayi naci gaba da kwalliyata na kammala na ɗakko doguwar rigar Shadda na saka ina kokarin ɗaura ɗan kwali Ameera ta shugo
"Wow Anty na ina zaki haka irin wannan kyau haka Allah bakiga yanda kikai kyau ba" sai kuma tayi shuru jikinta yai wani irin sanyi ta zauna gefan gado taja tagumi tana kallona
"Anty kwalliyar nan taki saita tunamin da Abbana Allah sarki ubangiji yajikanka Abba" sai kawai ta kwanta saman gado tana kuka "Anty shikenan ni marainiya ce banida uba uwa tana can gidan yari, Anty dan Allah ki kaini gidan naga Ummana kafin a zartar mata da hukuncinta" zama nayi kusada Amira zuciyata babu daɗi jinake kamar na tayata kukan
"Kiyi shuru Meera insha Allah gobe zamuje kiga Zainaba daina kukan dan Allah nima karki sakani kuka, ko yaushe ina gaya maki kirinka min kallon uwa mahaifiya ga Yaya Jabeer nan shizai zame maki tamkar Uncle dan Allah kidaina kuka inmun tuna Uncle addu'a zamuyi masa ba kuka kinsan haka Mami ke gaya mana ako yaushe"
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA
31&32
Wanko idanunta Amira tayi ta fito, ni kuma na mike na daga labule ina kallon compaund dai dai sanda naga shigowar motar Fu'ad gidanmu, murmushi nayi tareda gyara fuskata nacewa Ameera ga Uncle dinta can yazo taje ta shigo da shi sitting room, jiki a sanyaye ta fita ina nan zaune har zuwa sanda tadawo tacemin Fu'ad ya ce naje
"Kije kicewa Hanne takaiwa baki abincin dana hada sitting room ta hada da lemu da ruwa suna cikin freezer" batacemin komai ba ta fice bayan yan mintina nabi bayanta dai dai zan shiga Hanne ta fito hannunta rikeda kudi yan dubu dubu sai murmushi take tana dariya tacemin
"Kinga yallabai Fu'ad ne yabani"
Dariya nayi tareda cewa "an gode" nashiga da sallama yanda Fu'ad yakafeni da idanuwa har abin yaban kunya zama nayi kasan carfet ina gaida abokinsa Usman dasuka zo tare, fuskarsa sake yake amsamin gaisuwar banko kalli inda Fu'ad yake ba kaina a kasa bansan sanda yabaro inda yake zaune ba yadawo gafda ni ya zauna saida naji maganarsa tamkar maiyin rada a cikin kunne na sannan na dago muka hada ido, kashemin ido yayi salon dayayi yasani dariya tareda saurin rufe idanuna da hannuwana ina dariya
"Kinyi kyau sarauniyata, ina godewa Allah dayasa inada rabon auranki ashe inada sauran farin ciki a rayuwata, dan Allah budemin fuskarki nayita kallah inajin dadi"
kaina nai saurin sawa cikin kafafuna ina dariya sosai dan bakaramin dariya Fu'ad yaban ba daman can shi mutum ne mai barkwanci bare yanda yake magana da wata murya mai dadi da fisgar hankalin mai sauraro
"Uhmm bazaki dago na kallekin ba?" ko rowar fuskar akemin?" tona kuwa gode bari na koma inda na fito" yafada yana mikewa tsaye, da sauri na dago ina kallonsa da murmushi a fuskata, komawa yayi ya zauna, shaf yama manta ba su kadai bane a dakin saida ya zauna sannan ya ga Uthman dake ta zafga loma, hararar sa Fu'ad yayi yana fadin "Malam maine haka kuma ya za'a kawo abu danni kai kuma ka zage kana cinyemin"
"Ai naga ba shine a gabanka ba love kake yi niko bazan iya barin wannan delicious din ya wuce ni ba,kasan wannan best food ɗina ne bana filakonta ko a gidan sirikai nai, ni zanso ma a gaggauta ayi bikin nan kullum ina gidanka amarya tana hadamin wannan hadin dan tunda nakecin gurasa a rayuwata bantaba cin mai daɗi kamar haka ba"Usman yana gama fadar haka ya dauki flask ya fita dashi yana fadin "Bari a kaiwa su sarkin mota suma su fara taba abincin amarya kafin tazo"dariya Fu ad yayi tareda jin jina kai
Zama ya gyara tareda cewa "Amarya wanne event kike shirya mana lokaci yana tahowa fa"
"Bazanyi komai ba walima kawai zanyi shima a cikin gidan nan ba'a wani waja ba"sun jima suna tattauna yanda bikin nasu zai kasance sai gafda mangariba sanna suka tafi.
Cikin satin shirye shiryan biki Mami ketayi ta gefe guda kuma ta zage tanamin gyaran jiki na musamman irin nasu na yan maiduguri cikin kwana uku kamshi yakama jikina ko giftawa nayi a waje sai anji kamshe barema ace na zauna a waje, saida biki yarage saura sati guda sannan Mami ta fara ɗirkamin magani wanda acewarta na sanyi ne Anty Fatima gaba daya tadawo gida saboda shirye shirye daman gidanta ita kaɗaice Yaya Mukhtar yana legos wani aiki, itama sosai ta tisoni a gaba da nata magungunan wani bin inna sha kaina har ciwo yake amma kona faɗa basa tsayawa fasawa Mami kam na gefe sai dai tayita mana dariya in taga yanda ake dirama dani wajan shan maganin
Ayau gidansu Fu'ad suka kawo kayan lefe gidanmu Anty Jamila sai harare harare take tana sakin magana ba wanda ya kulata sai Mami dan tunda suka shigo gidan take wani cika tana batsewa tareda harare harare kaya suka jibgo sosai kamar ba gobe Momy matar wan Ummi itace ta soma yaba kayan tana faɗin "Kai kaya sunyi masha Allah Ubangiji yabada zaman lafiya" Anty Jamila dake wani shu'umin mirmishi ta ce
"Kaya kam gasu nan sunyi kyau kamar bana bazawara ba"wani banzan kallo mami tayi mata tana faɗin
"Aifa kam da babbar budurwa ai kwara karamar bazawara da Minal har nawa take banda ma kaddarar mutuwa da mai zai hada Minal da zawarci ga...."Hajiya dan Allah ayi hakuri mu rufe taro da salatin annabi" Umman mai martaba ta fadi haka dan tsaida maganar, saida suka tafi a mota Umma taiwa Anty Jamila tas takuma ce ko a biki bata bukatar ganinta a gidanta tunda ita ba'a zaman lafiya da ita, bakaramin shaka Anty jamila tayi ba ganin yanda Umma ke yarfa ta a gaban matan waziri, hakan yasa ranta yaɓaci ta sake cin alwashin ganin bayan auran nan na Fu'ad.
Bangaran Fu'ad shiri yake sosai makeken gida mai kyau da tsari part biyu mai martaba ne ya mallaka masa gidan bakaramin dadi yaji ba Baraka ya dauka sukaje gidan ta gani yace tazaɓi sashin dayai mata iri dayane sai dai ɗaya yafi ɗaya girma hakan yasa taɗau babban acewarta saboda baki tunda itace uwar gida ko yan uwansa na Sudan ne sukazo a wajanta zasuna sauka, Mami da Momy da Anty Fatima suka zo sukaga sashin Minal ɗin sun yaba sosai, saura kwana huɗu biki Baraka ta tare a gidan dayai mata mugun kyau manyan kudi Fu'ad yakashewa sashin dan kawai ya farantawa Baraka dayake matukar ganin girmanta dan sanda yagaya mata zai kara aure yayi zaton zata tada hanakalinta tayi masa hauka irin wanda wasu matan keyi in mazansu zasu kara aure amma Allah sanya alkahiri kaɗai tace masa, yaso yayiwa Su'ad komai kamar yanda yayiwa Baraka amma Mami tace sun gode basai yayi komaiba ko cokalinsa basa bukata zasu saka komai.
Saura kwana uku ɗaurin aure Mami dasu Mommy sukaje bare suka shiryawa su'ad ɓangaranta komai yayi dai dai inji Anty Fateema ba karamin kudi suka kashe ba kowa so yake ya faranta mata kasancewarta karama a cikinsu.
Ranar alhamis akayi walima gida ya cika sosai dangi ta ko'ina sunxo yan karaye ma tun jiya da yamma suka zo kowa sai farin ciki yake da nishaɗi, Mami da kanta tai deccoresion ɗin wajan da zamuyi walima wanda yai matukar kyau mai ban sha'awa kowa ya kalla sai ya yaba, karfe biyar saura Amarya tafuto sanye cikin shiga ta mutumci less ne marun ajikinta sai plate shoe ta sanya dogon hijab ɗinta har kasa, fuskarta bawata make'up hoda kurum ta shafa sai kwalli da man leɓe sai fuskar tata tai kyau sosai ta zauna a inda aka tanada dan ita, malama Rabi'atu Yusuf ta gabatar da lacca ɗinta mai taken gidan Aurena, sai gaf da mangariba aka tashi bayan an kama amarya aka raba manyan bag wanda aka saka turaran wuta da humra da lallenmu na gargajiya,akaci akasha aka rufe taro da addu'a da kuma fatan zaman lafiya ga amarya da ango.
.......Hajiya Jameela tunda suka koma gida take cika tana batsewa saboda abinda Umma tai mata ba kramin kona mata rai yayi ba, Abbie baya gari yana Abuja gaba ɗaya watan nan bai zauna a bare ba yana can ayyuka sun masa yawa har ana ya gobe ɗaurin auren Fu'ad baizo bare ba.
Da sallama ya shugo falon saida yaiwa kansa mazauni a ɗaya daga cikin manyan kujerun dasuka kawata falon sannan ya ɗago ya kalli wacce ke zaune a falon kana yace "Anty Jameelah ina wuni" wani kallon banza ta wurga masa tareda girgiza kai ta lura tunda Fu'ad yadawo kasar nan ya raina ta banda ya rainata har ita zai kalli idanunta ya rinka kiranta da Anty Jameela koda yake ba laifinsa bane laifin Baraka ne saboda ita ke kiranta haka tasan a bakinta yaji, Fu'ad na murmishi ya ce "Nace ba dan Allah idan Abbie na ciki ki sanar mas nazo"
Wani dogon tsaki Anty Jameelah taja kana ta ce "Lalle Aminu wuyanka ya isa yanka ina matsayin matar babanka kake kiran sunana gatsal haka, saboda baka da kunya ni zan maka magana da mahaifin naka?"to nima ban gansa ba." tana gama faɗar haka ta wucerta ɗaki,
Mirmushi yayi tareda danna wayarsa ya karata da kun nan sa yayi sallama bayan sun gaisa da mahaifin nasa yake tambayarsa "Abie har yanzu baka zoba gashi gobe ɗaurin aure fa"
Abie na dariya ya ce "Dole sai nazo nayi zaton tunda ga maimartaba ni basai nazo ba tunda ko nazo ɗan gayya nima zanzama"
"Abba kazo, aurena fa yanzu saika ki zuwa bikina?"
"Ameen baka da kunya ni kake gayawa bikinka" Fu'ad yana dariya ya ce
"Abba kaifa abokina ne da mai Martaba ne shine bazan iya faɗa masa haka ba"
"Shikenan zanzo goben mu haɗu a kano can naga za'a ɗaura auran nima zaman nan ya isheni ga tarin ayyuka ga Jameela taki zaman Abuja narasa zaman me take anan?"
Fu'ad a ransa yace zaman samin ido mana amma a fili saiya waske da cewa "Abie aure kawai zaka kara anan kai zamanka da amaryarka anan ita kuma taci gaba da zaman nan ɗin"
"Ba ruwana idan taji wannan maganar taka zaku kwashi yan kallo" Abie ya katse wayar yana dariya.
BARAKA
Duk yanda takeso ta jure takasa yau tunda gari ya waye takejin xuciyarta ba daɗi daurewa kawai take ganin gidan nata yasoma tara baki, zuciyarta ce ta wani irin bugawa ganin fitowar Fu'ad cikin shiga ta alfarma, yana sanye cikin dakakkiyar shadda mai sheki da walwali kallo ɗaya zakayiwa shaddar kasan bata kananun kudi bace saboda yanda take maiko da ɗaukar idanu ga wani kamshi datake fiddawa na musamman, hula takalmi agogo duk kansu jajaye ne, bakaramin kyau yayi ba kai bazaka ce yanada aure ba har yana da y'a, yanda yake washe hakora yana dariya shi kaɗai ma ya isa ya bayyanar maka da tsantsar farin cikin dayake ciki, gaisawa yake da yan uwan Baraka harya karasa bedroom ɗinta inda take zaune ta zabga uban tagumi saida ya zauna kusa da ita yana mirmishi ya ce
"Yadai wife naganki wani iri?" bakaramin jarumta tayi ba waja maida hawayan dake kokari xubo mata tace
"Banjin daɗi kaina na ciwo kaɗan kaɗan"
"Oh sorry wife kisha magani ki kwanta ki huta and karki sawa kanki damuwa please" batare daya sake duban inda take ba yamike ya fice daga room ɗin,yana fita ta kife a kan gadon ta fashe da kuka mai tsima zuciya...✍🏻
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng