x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - KUKAN ZUCIYA

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 38354 words

Category: Tale Stories

Views 41

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
mace dake gidan mijinta nasan irin son da Fahad yake maki kema kuma kinsan hakan kawai soyayya da kauna ce suka rufe maki idanu kika kasa tantance Aminci zaki zaɓa ko kauna"

"Na zaɓi Aminci nabar Kauna da Soyayya bari nahar abada bazan sake soyayya ba nayi banji da daɗi ba nabarta har karshen numfashi na, ki gayawa Fahad a maidani gida ni naji sauki"

*Ina bawan Allah Fu'ad*

Yana futa a gidan yatare nape ko gaya masa inda zai kaisa baiyi ba ya kifa kansa saman kafafunsa shi kaɗai yasan maiyake ji a zuciyarsa, saida suka hau babban titi kana mai nape ɗin

Yace "Ranka yadaɗe ina muka dosa" batareda Fu'ad yaɗago ba yabasa amsa da

"Fara kaini Atm dake kusa na ciri kuɗi sannan ka karasa dani airport" basu jima suna tafiya ba mai nape ya faɗa masa gasu a Atm Fu'ad yafuta yacuro kuɗi sannan suka cigaba da tafiya, suna isa airport ya saka hannu a aljihu ya ciro dubu huɗu yabawa mai nape ɗin

"Yallaɓai ɗari biyar ne kuɗinka" hannu kawai yaɗaga masa batareda yace komaiba yasoma tafiya har ya shuge cikin airport ɗin mai nape ɗin na kallonsa, haka kawai yaji tausayin bawan Allah daga gani yana cikin damuwa "Allah ya magance maka damuwarka yahaɗaka da farin cikin duniya dana lahira yabaka duk abinda kake nema" mai nape yafaɗi haka yana share hawayan fuskarsa rabonsa dan gidansa tun bayan sallar azahar ya futo nema ko abinda iyalansa zasuci da rana bai basu ba mashin ɗinma ba nasa bane na haya ne, gida ya koma yabawa matarsa dubu biyu yace suyi cefane sannan ya cigaba da aiki, Fu'ad yana shuga airport ɗin baisha wahalar samun jirgi ba saboda yasaba da ma'aikatan wajan a recepsion ya zauna kasancewar sai nan da minti goma sha biyar jirgin zai tashi, shirun dayayi tunanin Su'ad yake har sannan yana jin ihunta sanda take faɗin _"Fu'ad come back please"_ ya share hawayan idanunsa yazaro glass daga aljihunsa yasakaya a fuskarsa suka ɓoye jan da idanunsa sukayi.

Anty Jameela wacce guguwa tai sama da ita bata ajjeta ko ina ba sai gaban wata yar karamar bukka wacce a ido idan ka ganta bazaka taɓa zaton ko kaza zata iya shiga ta zauna ba bare mutum, bukkar ko kofar shiga babu amma tana tsayawa a gaban bukkar ta buɗe ta shiga da sauri tana kwalawa bokan kira harta zauna gaban sa inda ya bayyana "Ranka ya daɗe gashi na aiwatar da duk abinda kace" karɓar abinda ta mika masa yayi tareda wurgasa ya shuge cikin wata kwarya wacce abin yana shuga kwaryan takama da wuta, wani ihu Boka yayi tareda kecewa da dariya

Yace "Burinki ya cika Fu'ad zai zama yanda kike so kallesa nan" lekawa Anty Jameela tayi cikin yar tukunyar dake gaban bokan zaune taga Fu'ad a wani waje da'alama recapsion na filin jirgi ne fuskar nan tasa ba walwala, ɗagowa tayi tana kallon boka bakinta har rawa yake wajan faɗin.

"To maiyakeyi anan ɗin? kuma ina zashi tsoro nakeji karya bar kasarnan ban gama aikinba"

"Ba'inda zaije gidama zai dawo yana kano daga gidansu wata yarinya yake wacce yake masifar so, nasoma ace itace zata mana aikin nan so ba yanda zanyi yarinyar tanada addini sannan babarta a tsaye take akanta da addu'o'i sau uku ina tura aljanu na suna dawomin da konan nan jiki shiyasa na haɗa aikin da tsohuwar budurwarsa Suwaiba duk yanda zakiyi kiyi dan ganin yaje legos sun haɗu da'ita dan itace cika makon aikin mu, ya cilla mata kullin magani wannan ki tabbatar yasha a cikin lemu zamu saka masa a zuciyarsa ya zarto nan gidanki ke kuma kina zuwa kije sashinsa ki buɗe lemu ki zuba a ciki dazaran yasha zance yakare" "To boka ina godiya amma inna buɗe lemu na zuba wani abu ai zai nuna alamar an buɗe"
"Baki yarda da aikinmu ba, kenan kina shakku akai" da sauri ta girgiza kanta alamar A'A kafin tayi wata magana taji an watso ta wajan bukkar ta zura takalmanta ta soma tafiya sai da tayi nisa kana ta juyo fili ta gani fetal ba alamar bukkar ta ɓace ɓat🙆‍♀️

Prince rai ɓace ya sauka a garinsu, kai tsaye G R A ya wuce gidan mahaifinsa bayason a masarauta asan yadawo yasan halin mai martaba da sakawa zuciyarsa damuwa akan lamuransa shiyasa bai doshi gidan ba so yake saiya dawo dai dai tukunna, can kasan ransa yana son zuwa masarauta yaga Umma amma ji yake kamar ana fisgarsa zuwa gidan Abie.

Anty Jameela ta gama zuba maganin kenan a cikin lemu ta futa shi kuma ya shugo gidan, haka kawai yaji kamar wanda ake jansa zuwa sashinsa inda baima cika zama ba, yana shuga ya buɗe fridge ya ɓalle murfin lemu yakafa kai yasha bako bisimillah😰kuskuren dayayi kenan, wani irin juya yaji kansa yanayi hajijiya ta ɗebesa luuuu yafaɗa saman kujera ya soma barci,

Alhamdulillah Su'ad ta sami lafiya harta koma gida mun bar hospital na daina kuka a fili na rashin Fu'ad sai KUKAN ZUCIYA danake na goge komai na Fu'ad daga wayata kama da lambar sa hotunan sa duk wani abu da nasan zai tuna min da Fu'ad, ganin hankalin Su'ad ya kwanta yasa Mami da Ummi suke ta shirya shiryan bikin Su'ad da Fahad, haka shima Fahad tuni yasai sabon gida anan sharaɗaG R A katon gidane daya cikasa da kayan alatun more rayuwa duk wani abu dayasan Su'ad tanaso saida ya zuba a gidan a ɓangare guda ba karamin lefe ya haɗaba kamar wanda baisan ciwon kuɗi ba haka yake kashe su har saida Ummi tai masa magana, Mami da yaya Fatima sukaje suka dawo da santin gidan Yaya tasami Su'ad wacce yanzu batada inda take zama samada ɗaki sabida karta ga Fahad, har sannan banajin sonsa kawai zanyi biyayya ne "Kinga gidanki kuwa kamar na wata yar shugaban kasa gaskiyya ba karamin so Uncle ke maki ba, da mukaje faɗi yake Fatima dan Allah kalli gidan nan kiga in akwai abinda kikasan Su'ad tanaso wanda bansa ba dan Allah ki faɗamin nasaka" taɓe baki nayi ina juyawa yaya baya

na ce "Daman zai faɗi haka mana tunda yasan yariga yagama da rayuwata, yarabani da farin cikina"mirmushi Yaya tayi ta futa daga ɗakin, tana aikawa da Su'ad harara

Wasa wasa sai gashi yau alhamis saura kwana biyu ɗaurin aurena da Fahad har sannan bansakejin ɗuriyar Fu'ad inata dai saka idanu zuwansa tunda yace zai zo ɗaurin auranmu nasan tabbas zaizo ɗin, ba wani taro za'ayi sosai ba kuma ma ɗaurin auran a karaye ne shiyasa tun ranar juma'a da yamma Mami dasu yaya fatima sai wasu matan yayun ummi suka wuce karaye.

Da yamma ina zaune nida fadila yar wan ummice kawata ce sosai tun yarinta haka kawai nakejin faɗuwar gaba wacce narasa ta maice na ɗora kaina saman kujera ina jiyo Fadila tana waya dasu Mami kamar daga sama naji kamshin turaransa ban buɗe idona ba har sanda naji sallamar Ankul wanda ko tantama babu nasan tare suke da Fu'ad, ilaiko muryarshi najiyo yana gaisawa da Ummi data futo daga ɗakinta, muryarsa fes kamar bayada wata damuwa, banbuɗe idonaba har saida na tabbatar da sunbar falon zuwa sashin Ankul sannan na buɗe na ɗauki wayata na shuge ɗakina inajin yanda kirjina da kaina suke bugawa "Ameen maiyasa maiyasa zakazo ayanzu so kake ka hanani karasa biyayyar danake shirin yiwa mahaifina kanason tarwatsa zuciyata ne" kwanciya nayi lamo har sanda naji wayata tana kara koda bansan wake kiranba amma na tabbata Mami ce dan ring ɗinta daban yake a wayana

"Dota kinci abinci kuwa"

"E!" nabata amsa ina sauraron abinda zatace.

"kaiwa Ankul wayanki zamuyi magana na kira tasa baya shuga ko baidawo ba?"

Inama zan iya yiwa Mami karya danace mata bai dawo ba, amma bazan iya ba dole na mike nabi hanyar zuwa ɗakinsa, da sallama na shuga suna zaune su biyu da'alama magana suke mai mahimmanci ganin yanda hannunsu yake sakale cikin na juna, banko kalli inda Fu'ad yake ba namikawa Ankul waya nace "Mami ke kiranka, bansan maita gaya masa ba nidai ina tsaye naga ya fuce da sauri ko wayar tawa bai bani ba, na fara tafiya zanbar ɗakin naji Fu'ad ya ruko hannuna, na juya ina kallonsa hawaye na zarya a fuskata na tausayinsa ganin yanda ya zabge lokaci ɗaya kamar wanda yai jinya banyi aune ba kawai naji na fashe da kuka hannu yasa ya toshe bakina murya kasa kasa

Yace "Princess rufa mana asiri so kike Ankul ɗinki ya jiyomu" da sauri yasa hannunsa a cikin jakarsa ya ciro karamin akwati mai ɗan karan kyau yasakamin a hannuna ya koma saman gado ya kwanta ni kuma na futa daga ɗakin da sauri, banga Ankul ba da'alama baya gidan.

Ankul kai tsaye gidan Baban su Zainaba ya wuce, har ɗakin baban yashuga yazauna yana gaida Baban dake masa wani kallo kamar zai kai masa duka.

Yace "Yanzu gobene ɗaurin auranka amma ka kasa zuwa ka gayamin sai yayarka ce take gayamin saboda bakuda zumunchi kun rainani ko saboda ni banida kuɗi, to bazan wakilceka ba kaje ka nemi wani bani ba" taɓe baki Fahad yayi tareda mikewa ya ajje masa ledar ɗinkin da Mami tace yakawowa Baban sannan yace

"Badamuwa Baba inma bakaje ba bazan rasa wanda zai wakilceni ba barema da kaina zan iya karɓarwa kaina aure" yana gama faɗar haka yafuce daga ɗakin, dai dai sannan Zainaba tashugo ɗakin a ruɗe ita bata taɓa jin zancan auran ba sai yanzu innarta ke sanar mata, zubewa tayi gaban baban tana rusar kuka

"Wallahi baba ka cuceni kaine kayi silar rabani da Fahad gashi yanzu inaji ina gani zaiyi wani auran ka kasa taɓuka komai😰kilama tazo ta haifi namiji shi kenan dukiyar da muka sakawa rai tabar tamu"

Dariya Baba yayi kamar wani sabon kamu ya zira hannunsa a aljihu yafuto da wani kullin magani yana nuna mata yace

"Kalli wanan ɗazu na samosa a wajan wani malami badai gobene ɗaurin auran ba to yanda aka kaimasa amarya haka za'a ɗakkota kedai ki zubamin idanu kawai inada abinda nake kullawa"

Sosai Zainaba take murna dajin maganar da Baban yafaɗa hakan yasa ta koma ɗakinta zuciyarta fes da farin ciki.

*RANA BATA KARYA*

Tun sassafe samarin gidanmu suketa shirin tafiya karaye dan shaida ɗaurin auran Aminatu da Fahad, sosai Fahad yake cikin farin ciki marar musaltuwa kallo ɗaya zakayi masa ka gano farin cikin dayake ciki, yana sanye cikin Fara kal ɗin shadda yasha malum malum shugarsa shida Jabeer iri ɗaya ce, ko'ina ka hangosa baki buɗe sai zuba murmushi yake duk sun shirya Fu'ad kawai suke jira yagama shiryawa su wuce, Tsab yagama shirinsa yafuto yana gyara zaman rawaninsa suka jero shida Fahad zuwa wajan da motocin dazasu shuga suke.

Ina tsaye baki window ina leka compound burina kawai na saka sa a idona nai masa kallo na karshe, irin kallon danasan har abada bazan sake masa irin kallon ba.

Da sarsarfa yake tahowa kasancewar su Fahad sunyi masa nisa dan harsun shuga mota shi ya tsaya amsa waya, binsa nake da kallo yanda yayi kyau cikin bakar shadda ya ɗora malum malum ta farar shadda wacce akayiwa aiki a gaban rigar da bakin zare, rawaninsa da takalminsa harma da agogon fatar dake hannunsa duk bakake ne, kamar wanda akace ya juyo muka haɗa ido cak ya tsaya yanamin murmishi tareda ɗagomin hannu yaci gaba da tafiya, murmushin da nakejin har abada bazan taɓa mantawa dashi ba kasancewarsa na karshe da yayimin ina kallo ya shuga motarsa wani yaja wanda nake zaton tare sukazo saboda kayan gidan sarauta dana hango a jikinsa da'alama dogari ne,komawa nayi na zauna gefan gado tareda jan tagumi, ina nan zaune har barci ya ɗaukeni ban sani ba saidai farkawa nayi naji gidan yakaraɗe da hayaniya na buɗa ido da sauri na sakko daga gado dai dai da shugowar Fadila tana murna da faɗin yarinya bani tukwaici nagaya maki wata magana...✍️

07039793439
[6/4, 7:48 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹


Story and writtin by
Mamie Yusuf Daboo🥰


☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

*Na gaisheku ƴan group ɗin KUKAN ZUCIYA comment ɗinku na sani nishaɗi wannan page ɗin gaba ɗaya nakune kuji daɗinku*

"Wanne abu zaki gaya min da har saina baki tukwici nasan dai cewa zaki an ɗaura min aure da Fahad koba haka zaki faɗa ba" ban jira Fadila ta ce komai ba na faɗa bathroom na kunna famfo ruwa na zuba na fashe da matsanancin kuka "Shikenan shikenan yanzu na zama mallakin Uncle haba kaddara mai yasa zaki mana haka maiyasa zaki rabani da farin cikina wayyo Allah wayyo zuciyata wayyo Ameen" ta karasa faɗa da karfi tareda nemar waje na zauna na fashe da matsanancin kukan takaicin rashin Prince Ameen,
Mami gaba ɗaya hankalinta na gida hakan yasa ana gama ɗaurin aure itada Momy matar wan Ummi suka juyo gida, Ba wani shagalin biki akai ba sabida yanda bikin yazo ba shiri ga kuma rasuwar Daddy dako wata biyu bai yi ba, da mangariba Mami da sauran tsirarun ƴan uwa suka mika ni gidan Fahad, gidan da nasa a raina zan tabbata ina Kukan Zuciya a cikinsa, basu wani jima ba aka tafi aka barni daga ni sai halina tunda muka shiga gidan nake kuka ta cikin mayafin daya lulluɓe min duka jikina basu jima da tafiya ba uncle ya shigo, sallamar dayai tayi dai dai da bugawar zuciyata wanda yai sanadin dana kuma fashewa da kuka ya zauna kusa dani ya buɗe mayafin daya lulluɓe ni yana murmushi saidai annurin fuskarsa lokaci ɗaya ya kau, ya saki mayafin jiki sanyaye, bai cemin uffan ba haka nima bance masa, nadai lura jikin Uncle yai matukat sanyi ganin ya fita yasa na kwanta kan gadon ina kuka sosai, Fahad mai saukin hali kullum kalaman lallashi yake bina dashi musamman ganin naki sakin jiki da shi, kyautatawar Uncle a gareni yasa nabar kukan fili na rashin masoyi na koma kukan zuciya, Uncle na matukar kokari sosai ganin ya kwantar min da hankali komai na gida shi yake yi tun bana sakin jiki da shi harna ware na saki jiki muka koma kamar da sanda muna gida, har sannan mikin son Ameen Fu'ad na nan ɓoye cikin zuciyata nakan tina dashi a kullum nakan kuma so nasan a wanne hali yake yanzu ina yawan ɗaukar wayar Uncle a ɓoye nayita kallon hoton Fu'ad ina kukan zuciya wani bin sai nayi kamar zan kira lambar sa sai kuma na tina haramcin hakan na ajje wayar na ɓuya a ɗaki nai kuka sosai tareda addu'a Allah ya cire min sonsa a zuciyata, sanda hutun da aka bawa Uncle a wajan aiki ya kare ya koma aiki randa yatafi sai naji gidan shuru kewar gida ta kamani gashi muna hutun school,


Zaune suke gaban malam na gangare wanda yasha uban rawani da malum malum kamar malamin gaske, Zainaba tana kuka take cewa "Dan Allah malam ka taimakamin inason mijina, gashi ya sakeni har saki uku, ya auri wata, sonake yasaketa yazo yamaidani acusa masa tsanarta sosai yaji nan duniya ba warda ya tsana sama da ita ya korata gidansu da takardar saki uku" malam ya zana wata kasa dake gabansa ya girgiza kai ya ce

"Auran nan babu rabuwa aciki duk wanda yace zaija to komai zai iya faruwa dashi sannan kema babu sauran zama ke dashi sai dai kizaɓi abinda kike so bayan wannan"

"Malam ka taimakeni!"

Ungo wannan yamika mata wani kullin magani yace "Ki zuba sa a inda kika tabbatar zai taka koya tsallaka, inhar kikayi haka to ba abunda zai iya yiwa matar tasa zai zama fanko awajanta ita kuma zata kasa jurewa harta kai ga ta nemi saki, bayan yasaketan kizo ki gayamin zansan yanda za'ayi sai'a maida auran naku" cikeda murna tabasa kuɗin daya butaka ita kuma ta dawo gida ta tisa baba agaba akan ya kira Fahad yace yana son ganinsa yanzu, lokacin Uncle na shirin barin office dan haka ya shaida ma Baba da gashi nan zuwa yanzu insha Allah, Da gudu Zainaba tashugo cikin gidan tun ɗazu tana tsaye kofar gida tana jiran zuwan Fahad tun daga nesa data hango motarsa ta dawo gidan ta kunce kullin maganin daga gefan zaninta ta zuba sa a kofar ɗakin Baba, mahaifiyarta data futo daga ɗakinta tabita da kallon tuhuma "Zainaba mai kikeyi haka a kofar ɗaki ba sallamar Fahad nakeji ba, waima maine wannan a hannunku" Baba daya leko daga ɗakinsa yace.

"Kefa mairo kin fiya saka ido ina ruwanki da maine a hannunta ke Zainabu cewa Fahad yashugo ina ciki"

Fahad yashugo da sallama yana gaida Innah mairo fuskarta cikeda fara'a take amsa masa gaisuwar, yana shuga ɗakin Baba Zainaba tayi wani tsalle tana murna harda taka rawa, a kasa ya zauna yana gaida Baba, ta inda yake shuga bata nan yake futa ba faɗa yake sosai

"Yanzu saboda rashin zumunchi irin naku ace kayan abinci ma bazaku iya saimin ba saina roka kuna kallon halin danake ciki aikima ya gagareni amma bazaku rinka tausayamin ba wannan ba halin ubanku bane, ubanku mutumin kirki amma kaida yar uwarka mahaifiyarku tashuga tsakani na da ku"

Fahad dariya ma abin yabasa daya tuna ko karshan wata saida Mami tagaya masa ta turawa Baba kayan abinci, shine yanzu zai zo yana masa mita "Ayi hakuri baba ban zaci wanda Mami takawo harya kare ba yanzu bari naje zan aiko maka dasu"

"Basai ka aiko ba kabani kuɗin kawai nasiya da kaina" mikewa Fahad yayi yana murmushi yafuta, mota yaje ya ɗebo kuɗi ya kawo wa Baban sannan yafuta, har sannan Zainaba tana zaune kofar ɗakin daɗi ya kume ta ganin har sau biyu yana taka maganin.

Yau sosai nakejin nishaɗi hakan yasa da wuri na kammala abinda zanyi nai wanka ina zaune gaban madubi na gama tsantsara kwanliya wacce najima banyi irinta ba tun kafin rasuwar Daddyn mu, doguwar rigar material nasa wacce takama jikina tamin kyau sosai na feshe jikina da turere mai kamshi, na gyara gashina dayasha kalolin mayuka sai kamshi yake da kyalli, ban ɗaura ɗan kwalinba na ajjesa saman kujera ina kallon agogo karfe huɗu saura kwata, mamaki nake maiya hana
End Ads