x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 3 - KUKAN ZUCIYA

  • 6001 words
  • 9000 words
  • Out of 38354 words

Category: Tale Stories

Views 38

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
faɗa mata na tabbata zata soka, kai kasan yanda ka haɗu kuwa ko wacce mace zatayi farin ciki ace namiji kamar kai mai tarin ilimi hankali da nutsuwa babban likita yace yana sonta na tabbata komai takeji dashi kafita, bama haka ba mazai hana kasami mahaifinta ka gaya masa kanason yarsa yabaka dama ka gana da'ita kaga shikenan in yayi na'am dakai itama dole tabi" kai kurum ya girgiza batare dayace komaiba yabar wajan.

Prince AMEEN Fu'ad lafiya yasauka airport na garinsu manyan motocin masarauta daya gani cikeda airport yasa ya dafe kansa cikeda damuwa yake takawa, Allah yasani baiso mai martaba yasan da dawowarsa ba shifa sam bayason rayuwar nan ko yaushe yana kusada sarki Allah ya sani baya ra'ayin sarautar nan, yana kokarin guje masu yaji muryar Chiroma yana dariya yace "Barka da zuwa magajin sarki" Fu'ad dafe kansa yayi🤦‍♂️ cikeda damuwa yake kallon Chiroma yace "Kaine ka gayawa Mai martaba yau zan dawo ko?" hmm yayi kwafa tareda cikin jibgegiyar motar da Sarkin mota ya buɗe masa, tafiyar yan mintuna takaisu gidan sarki, sosai ake murna da zuwansa musamman Deejah da Juhaina nan ya baje cikinsu sai surutu suke masa da kyar yasamu ya zille zuwa sashinsa na gidan mai martaban.

Kanol Usman na zaune cikin falonsa Fahad yai sallama cikeda ladabi yazauna saman carfet yana gaida Daddy sannan ya sunkuyar da kansa yana wasada yan yatsun kafarsa yafara magana muryarsa na rawa "Daddy daman ina son na ce" yanda yake magana a rarraɓe yasa Daddy yadakatar dashi da faɗin "Nutsu Fahad gayamin damuwarka kai tsaye yanda zakai magana da Amina kullum ina gaya maka karinkamin kallon nine yayanka ba Amina ba ina jinka" kasa Fahad ya kumayi da kansa kana yace "Daddy daman sonake kamin izini inason Su'ad sona gaskiyya inhar ka amince auranta zanyi! nafara zuwa kamin izini na nemi amincewarta" Daddy farin ciki ya lulluɓe zuciyarsa shi daman yadaɗe yana wannan hasashan cikeda farin ciki yace "Nabaka Su'ad Fahad na tabbata kai mai kaunarta ne, fatana ka rikemin ita amana kabata kulawa ko bayan raina! basai kayi mata magana ba kabarni da'ita kawai gobe insha Allah zanje karaye muyi magana da Baba Sunusi zan tsaida ranar auranku banason aja lokaci burina daman ako da yaushe naga na aurar da Su'ad kafin Allah ya karɓi raina kasan yanayin cutar danake fama da'ita ba lalle nasake shekara nan gaba a raye ba" Kanol yakarasa faɗa cikin damuwa "Insha Allah Daddy zama ka wuce hakan ai kanabin ka'idoji kuma kana kan magani" murmushi Kanol yayi tareda maida kansa saman kujera yana lumshe ido shi kaɗai yasan maiyakeji ajikinsa a jiya zuwa yau daya dawo Kano shi kaɗai yake jin matsanancin ciwon da cikinsa keyi.......✍🏻


07039793439
[6/4, 7:46 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA* 🌹


Story and Writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰


☀️ *First Class Writer Assosciasion* ☀️


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

5&6


Kanol yashuga ɗakin Ummi da murmushi a fuskarsa, Ummi dake tsaye jikin madubi tana shafa humra tajuyo cikeda mamaki tana kallonsa, ba kasafai ya cika shugowa ɗakin matansa ba kusan saidai su samesa a samansa, ajje humran tayi tazo kusa dashi gefan gado ta zauna, jawota yayi jikinsa suka kwanta saman gado yana dariya "Kanol da'alama yau kana cikin nishaɗi gayamin maiya saka farin ciki haka" sake rukota yayi jikinsa yana murmushi "Abin farin ciki yasamemu Dr yanzu Fahad yake gayamin yanason auran Su'ad harma nayi wayada Baba sunusi mun tsaida rana nan da sati huɗu masu zuwa gobe ma zanje karaye mu sake tattaunawa, ni uban ango shi uban amarya" Ummi da itama daɗi ya kumeta tasake kankame mijin nata tana faɗin "Kai naji daɗin zancan nan sosai Allah yasanya albarka amma Mami bata sani ba", "E sai gobe zan gaya mata na shuga ɗakinta naga sunyi barci itada ɗiyar tata" anan Kanol yai shirin kwanciyar barci Ummi tana mitar yatashi su koma samansa yace "Dan Allah Dr kibarni na kwana anan daga yau fa shi kenan bazan sake kwana anan ba" shuru tayi kawai taja masu bargo suka koma suka kwanta.


*MUTUWA YANKAN KAUNA*

Lafiya kalau Kanol ya kwanta bayan yasha magungunan sa, amma cikin dare wani azababban ciwon ciki ya turnike sa sai murkusu yake tun yana iya daurewa harya tashi Ummi dake barci, ganin halin dayake ciki gaba ɗaya hankalinta yatashi ta gigice tama kasa basa taimako, Fahad taiwa waya sukazo shida Jabir suka garzaya asibiti, Su'ad da Mami basusan Kanol ba lafiya ba saida safe sukaje asibitin, lokacin yaɗanji sauki ba kamar sanda aka kawo saba, Su'ad na rikeda hannun Daddynta tunda suka shugo take hawaye shidai Kanol kallonta kawai yake yana girgiza mata kai alamar tai shuru, "Yi shuru Autata daina kukan haka nafa ji sauki Fahad yana shugowa zance ya sallamemu mu koma gida ko haka kike so" kai kurum Su'ad ta girgiza masa, shafa kanta yayi yana faɗin Allah yai maku albarka ya albarkace ku gaba ɗaya" shugowar Fahad yasa Kanol cewa "Yauwa maida Auta gida zamuyi magana da su Mami kici abinci ki wanka anjima saiki dawo ki tahomin da fatan dankali" kai Su'ad tasake gyaɗawa haka kurum takejin jikinta duk ba daɗi, jiki a sanyaye tamike zata futa, ta juyo tana kallon Kanol daya rike hannun Fahad duk da bata jiyo abinda Daddyn yake faɗa haka kurum take zaton maganarta yakewa Uncle ɗin"Ga amanar Su'ad nan na damka a hannunka itace karama kabata kulawa kabata duk wani farin ciki na rayuwa kada kabari ta koka ko bayan raina" Fahad yace "Insha Allah Daddy zanyi abinda kake so Allah yabaka lafiya" Ameen ya furta saman laɓɓansa kana muka fita daga ɗakin,

Kanol ya kalli Mami yana murmushi "Kuyi hakuri banjin wannan ciwon nawa na tashi ne! kuyafemin ga amanar yarana nan na damka a hannunku kuci gaba da basu ingartacciyar tarbiya kamar wacce muke basu ina raye, dan Allah kada kubari wani ruɗe na duniya yasa ku raba kanku kuci gaba da haɗe kanku kamar yanda kuke ayanzu, sannan Su'ad na bawa Fahad ya aureta ko bayan raina kuka canza ban yafe ba! da sauri Mami ta kalli Kanol "Abban Su'ad yazakace haka su yaran sukace maka suna son junansu shakuwa ce kawai fa a tsakaninsu ba soyayya, inma shi Fahad sonta yake to ita Su'ad tanada wanda ta..."Umarni na bayar lallene acikan burina ko bayan raina! "Kanol dan Allah kayi shuru cuta fa ba mutuwa bace, kabari inkaji sauki saimu tattauna" murmushi kawai yayi yana kallon Ummi data kasa magana hawaye kawai take, Kanol ya lumshe idanu yana faɗin "La'ilaha illallah muhammadan rasulillah" azabure Ummi ta ɗago tana kallonsa ganin yanda hannunsa dake cikin nata yasaki, wata kara tasaki haɗeda salati itama nan ta zube, dai dai shugowar Fahad daya dawo daga gida dan ganin yaya jikin Daddyn turus yayi ya tsaya bakin kofar ɗakin yama kasa shugowa, Mami ke salati tana girgiza Ummi datake zaton itama mutuwar tayi, "Fahad ka tsaya anan karaso ciki ka bata taimakon gaggawa Daddy yau Allah ya amshi abinsa, hasbinallahu wani'imal wakil" azabure fahad yashugo ɗakin yasoma tattaɓa Daddyn saida ya tabbata rai yayi halinsa kana yasa Mami ta ɗora Ummi saman gadon dake kusa dana Daddy yasoma bata taimakon gaggawa, a firgice ta farka dai dai shugowar Fatima da sai sannan taji Daddy bayada lafiya, ganin mutum lulluɓe da farin yadi yasa Fatiman ta buɗe yanayin dataga Daddy yatabbatar mata baya lumfashi luuu tayi baya zata faɗi mijinta ya rukota ta faɗa jikinsa tana fashewa da kuka, Fahad da kwamishina su suka jajirce kan gawar Kanol aka gama haɗasa suka ɗaukesa zuwa gida dan masa sallah akaisa makwancinmu na gaskiyya😰


*Su'ad*

Sauri sauri nake na kammala fatan dankalin da Daddy yace nayi masa ko wanka banyi ba haka kurum duk nakejin jikina yai wani irin sanyi, na zuba dankalin kenan naji wata faɗuwar gaba tareda kara haɗida salati kamar muryar Yaya Shareef nakeji shiyasa na futo daga kicin ɗin da sauri kamar zan faɗi na nufi compound na gidan inda nake jiyo hayaniya, nima salati na saki ina kamewa awaje ɗaya saboda abinda idanuna suka ganemin, wata irin girgiza nayi sai gani gaban motar na rirrike Uncle Fahad ina kuka kamar raina zai futa, Rukoni yayi sosai yana goge hawayan fuskarsa yama kasa cewa komai, hannuna yaja muka shuge cikin gidan ɗakinsa yakaini ya zaunar dani gefan gado shima ya zauna har sannan hawaye ke zuba daga cikin idanunsa yabuɗe baki zaiyi magana kawai yafashe da kuka, sosai yake kuka yanda yake kukan zakasan mutuwar ta taɓa masa zuciya, cikin kuka yake lallashina "Muyi hakuri! bamuda yanda zamuyi inama wani yana fansar wani dana mutu Daddy ya rayu, tabbas munyi babban rashi Su'ad dabazamu samu madadinsa ba" mikewa yayi ganin yanda na haɗe jikina waje ɗaya ina kuka dukkan ilahirin jikina karkarwa yake allura yake shirin yimin na ɗago ina kallonsa "Uncle mai zakamin allurar barci please dan Allah karkamin kabarni naga Daddy na nai masa kallon karshe nai masa addu'a", ajje alluran yayi muka futa falo tuni mutane sun fara taruwa, kasancewar juma'a ce ana idar da sallah a masallacin unguwarmu aka sallaci gawar Daddy munaji muna gani badan ranmu naso ba aka kai Daddy makoncinsa, mutuwar Daddy gaba ɗaya ta canzar rayuwata nazama wata slent sam ba rigimar nan dana saba bana komai sai karatun kur'ani dan tuni Mami ta takamin burki da yawan kukan danake, tace ba abinda zai amfanarwa Daddy saima azaba da zanja masa, Fu'ad yazo tun randa akayi matuwar dashi aka sallaci Daddy, yan uwansa ma sunzo sosai harda Umma da mai martaba, Abbi ɗinsa ne baya nan a waya yamin ta'aziya nai mamaki sosai yanda yan uwansa suka san dani, hatta babbar y'ar mai martaba Hidaya wacce ke auran sarkin garinmu saida tazo mana gaisuwa.

Rasuwar Daddy ta canza rayuwar jama'ar gidanmu baki ɗaya kowa yazama ustaz sai ahankali muka saba da rashin Daddy tuni kowa ya koma bakin aikinsa, yaya sharif ya koma kaduna inda yake aiki domin shima soja ne sai yaya Jabeer dake aikin banki nida Yazeed mun koma makaranta ni ina shekara ta biyu shi kuma yana shekarar karshe, duk fanni ɗaya muke karanta low.

Watan Daddy ɗaya da wani yammaci ina zaune falo na biyu wata mata tayi sallama ta shugo duka shekarunta bazasu wuce ashirin da biyar ba yanda take wani kalle kalle yasa nima nake kallonta kamar na santa amma na manta inda na santa, ta zauna saman kujera kamar bataso tacemin "Hajiya Amina tana nan kuwa?" kamar nace mata bata nan ganin tambayar rainin hankalin dataimin mutanan dake takaba ina zasu futa wata unguwa, bance mata komaiba na mike na shuga ciki danna kira Mami, tare muka futo da Mami da Ummi jin danai Mami tace "A lale da zuwa Zainaba daman kece?" ɗan shuru tayi kana ta gaida su mamin, jin danai ance Zainaba yasa na gane inda nasanta matar Uncle Fahad ce wacce suka rabu dashi shekaru biyar kenan, Ummi ke tambayar ina "Ameera yammata yanzu nasan ai ta girma" bata bawa Ummi amsaba sai dariya da tayi kawai tana nan har Uncle Fahad da yaya Jabeer suka dawo, ko zama Uncle baiyi ba bayan sun gaisa tai masa gaisuwa ya wuce ɗakinsa, bin bayan sa nayi yana tsaye cikin ɗaki harya fara rage kayan jikinsa yarage daga shi sai dogon wandon shadda sai farar singileti yana kokarin cire dogon wandon ni kuma nayi sallama na shuga kai tsaye, jin sallamata yasa ya juyo yana kallona yaɗan ɓata rai yana cewa "Banace ki daina shugomin ɗaki kai tsaye haka ba, kina fara neman izini tukunna" nidai bance masa komaiba na zauna gefan gado ina cewa "Uncle wai maiyasa bazaka maida Zainaba ɗakintaba kodan Ameera ma dake tsakaninku" ɓata rai yayi yana kallona ya ce "Kintaɓa ganin inda mutum yazauna da makiyinsa" turo baki gaba nayi ina cewa "Tayaya masoyi zai koma makiyi baka sonta daman ka aureta harda yara" zama yayi nesa dani kaɗan yadafe kansa yana magana.

"Bantaɓa son Zainaba ba, Mahaifinta wan mahaifi nane shiya ɗauramin aure da ita nazauna da'ita zaman amana, duk da inada wacce zuciyata keso tun tana jaririya amma haka na danne son na zauna da Zainaba da zuciya ɗaya, ashe itada mahaifinta suna da wata manufa akaina, mun haifi yaranmu guda biyu Abdallah shine babba sai mariya damuke kira da Ameera saboda sunan mahaifiyata dataci! acan baya bayan matuwar mahaifina yayan babanmu ya auri innarmu ashe shi da biyu ya aureta saboda ya kwace duk dukiyar da Abbanmu yabar mana nida Mami, Innarmu ta gano haka saita gudu garinsu ta damkawa mahaifinta duk kanin takardun kadarorinmu sannan ta dawo gane ba komai a wajanta da baba yayi yasa ya rinka wulakanta ta har Allah ya amshi ranta!😰 bayan rasuwarta kakanmu yabamu duk wasu takardunmu Mami ta adana mana, wata rana bayan aurena da Zainaba na dawo daga hospital ranar agajiye na dawo gajiya tasa bana kojin yunwa, ina zama takawomin abinci nace mata banajin yunwa ta ajjiye sai zuwa anjima zanci, bata ɗauke abincinba ta shuga ɗakinta, dai dai sannan Ameera da Abdallah suka dawo daga school, Abdul daman bayada juriyar yunwa yaro ɗan shekara goma jakarsa kawai ya ajje yacemin Uncle Abinci zanci nazuba masa abincin da Zainaba ta kawomin lomarsa uku yafara dafe ciki yana murkususu kafin wani lokaci kumfa tafara futa daga bakinsa ihun yaron yasa Zainaba futowa daga ɗaki ganin halinda Abdallah ke ciki yasa ta kwala ihu tana kallona Fahad abincin dana kawo maka kabasa banbi ta kanta ba na ɗauki Abdul da abincin zuwa Asibitinmu kafin najema rai yayi halinsa Abdul ya rasu😰na bincika abincin saina gano guba a ka saka, bayan ankai Abdul gidanmu na gaskiyya na tsare Zainaba da tambaya anan take gayamin Babanta be yakawo guba yace tazubamin a abinci naci na mutu dansu gaje duk dukiyar da Abbanmu yabar min ni kuma jin haka yasa na saketa saki uku kar naje wataran cikin dare da burma min wuka ta kasheni" Shuru nayi kawai ina bin Uncle da kallo tabbas nasan lokacin da Abdul ya rasu amma banzance ga dalilin rasuwarsa ba" jiki sanyaye na bar ɗakin nasa na koma nawa ɗakin na kwanta lamo ina tunanin lamarin duniyar nan

HAJIYA JAMILA
Harara tabi Fu'ad da ita sanda suka gama gaisawa ya haura sama inda Abbinsa yake mikewa tayi daga inda take zaune tabi bayansa cikin sanɗa ta tsaya a bakin kofa ta saka kunne tana so ta juyo maganar da zasuyi da safiyar nan....✍🏻

Idan har kin tabbatar kina son cigaban labarin nan kuma zakina yin comment to maza yimin magana ta wannan lambar nai adding ɗinki a group ɗin da nake posting:. 07039793439
[6/4, 7:46 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹


Story and weitting by
Mamie Yusuf Daboo🥰


☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA


7&8


kunnanta ta saka a jikin kofar ta fara jiyo maganarsu "Abbi barka da safiya" Fu'ad ya faɗi haka yana tsugunne gaban mahaifin nasa
"Barka dai Ameen jiya Mai martaba ke sanarmin za'a tura manya su shiga maganar auranka da Su'ad nayi farin ciki sosai My son na godewa Allah dayasa zanga wannan lokaci Allah yasa albarka"
can kasan makoshi Fu'ad ya amsa da Ameen kafin ya jiyo Abie din dayaci gaba da magana "Takawa ya gayan yanason buɗe maka hospital akwai babban fili da Takawa ya baka kyauta za'a fara aikin gininsa kwanan nan"
"Abie nidai bana ra'ayi buɗe hosoital ɗina ason raina a barni na koma canada naci gaba da aiki dasu ko kuma a barni a hospital ɗin gwammanati"
"To bazan hanaka ba amma dai kayi magana da Takawa sannan gidana dake nan baya nake ga a gyara sa saika zauna anan ko?"
"Abie nifa gaba ɗaya bana son zaman kasar nan dan Allah basai an gyara inda zan zauna ba kawai zan fara zama a part ɗina na masarauta kafin na gama shirye shiryan komawa canada"
"To yanda kace"
"Abie bari na koma sai munyi waya kenan?"
"Haka ne jirgin yamma zanbi na koma" hannu Daddy ya mikawa Fu'ad sukai musabaha kafin daga bisani sukai sallama, da sauri Anty Jamila ta fara sakkowa daga step ɗin tana haɗawa bibbiyu ta sakko da sauri ta faɗa ɗakinta tana zagaye sa, da sauri ta ɗauki wayarta ta lalumo wata lamba bugun farko aka ɗaga batare data amsa sallamar da wacce aka kira tayi ba ta fara masifa tana magana cikin faɗa faɗa "Hajiya Nafisa anya bamu gama barci ba kuwa to yaron nan aure zai" da sauri wacce aka kira da hajiya Nafisa ta tashi zaune daga kwance da take tana zabga salati "Aure ai kuwa matukat ba ƴaƴanmu zai aura ba to kuwa tabbas Ameen zai tabbata ba aure wacce mai tsautsayince ta kinkimowa kanta wannan gingimeman aiki?"
"Ban sani ba amma dai a kano take ya zama wajibi mu mike tsaye mu kara kaimi wajan ganin hakanmu ya cimma ruwa"
"To yanzu Hajiya Jamila yaushe zaki shigo kizo mu leka wajan na gangare"
"To kinsan Alhaji na gari ama dai inya tafi zan zo muje bamuga ta zama ba" sallama sukayi Hajiya Jamila ta ajje wayar har sannan tana jin zuciyarta ba daɗi

SU'AD
Na gyarawa kwanciyata saman gado ina kara manna wayata da jikin kunnena ina jin jerin kalaman soyayyar da Fu'ad ke faɗa min masu saka duk kan ilahirin jikina kara amsar soyayyarsa, kai hakika Fu'ad karshe ne yakai matuka a soyayya gaba ɗaya ya mamaye zuciyata bana iya kallon ko wanne namiji kallo na soyayya inba Fu'ad ba, "Kinyi shuru kin barni inata zuba ko, Su'ad lokaci yayi da zamu bayyana soyayyarmu kowa ya sani a gidanku, ni dama tuni kowa yasan da zamanki, ɗazu mai martaba yake cemin yanason shugowa kano tambayarmin auranki" zaro idanu nayi kamar yana kallona na ce "Uncle Fu'ad karatunafa gaskiyya banason barinsa kai kuma nasan ba zaman kano zakayi ba" "Mai zanyi a kano Canada nakeso mu wuce ana ɗaura auranmu kinga sai ki cigaba da karatunki acan" murmushi nayi tareda kallon kofa jin motsin shugowa da sauri na kalli kofar a tsorace danna zaci Uncle ne amma sainaga Mami ce bata tambayeni dawa nake waya ba dan tuni tasan da soyayyarmu da
End Ads