x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 4 - KUKAN ZUCIYA

  • 9001 words
  • 12000 words
  • Out of 38354 words

Category: Tale Stories

Views 40

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Fu'ad ce masa ne "Muyi waya anjima Mami ta shugo zamuyi magana" kallon da Mamina kemin yasa jikina yin sanyi domin kallone na tausayawa a sanyaye nace "Mami wai Fu'ad ke cewa zai turo mai zance masa" shuru tayi alamar akwai abinda ke cin ranta, nasan Mami farin sani kusan shakuwar da mukayi da ita koda Ummi data haifeni bamuyi ba, hakan yasa na ruko hannunta ina cewa "Mami akwai matsala ko naga kina cikin damuwa" kanta ta girgiza tana kakalo murmushin yake tace "Kigaya masa yazo gobe suje karaye shida Shareef saiya sanar da Baba sunusi" kai kurum na girgiza kana nayi masa text na faɗa masa abinda Mami tace.

Washe gari kuwa karfe goma a kano tayiwa Fu'ad muna zaune nida Mami ya shugo da sallama daman yarigada yasaba kai tsaye yake shugowa gidanmu, gaisar da Mami yayi yana tambayar ina Ummi, Mami tabasa amsa da "Ummi tana asibiti jiya aikin kwana tayi kuma kaga har yanzu bata dawo ba" kafin Mami ta rufe baki Ummi ta shugo itada Jabir, zama tayi tana kallona "Ke ina kika saka wayanki anata kiranki baki ɗagaba, motana ta lalace a hanya inaso ki kaimin mota sai Jabir na kira nataso sa daga office" ni sai sannan ma na tuna da wayan tawa dana barota a ɗakina tun wajan tara rabona da'ita, Ummi da Mami suka wuce ciki kasancewar muna first falo ne, suna wucewa ciki Fu'ad matso kusa dani yana faɗin "Amarya ta" ni kunya ma yabani hakan yasa na rufe fuskata ina murmushi, zuwan Shareef yasa bamuyi wata doguwar hiraba suka wuce karaye Fu'ad yace yau zai koma saboda shirye shirye da suke jibi juma'a za'ayi sabbin naɗi a masarautar

Ummi ta kalli Mami tana faɗin "Mami yakamata ki gayawa yarki gaskiyar wasiyar da Kanol yabari lokaci yayi dazatasan komai, naga wannan dogon mai tsayi kamar falwaya zuruftun dayake mana a gida kamar saboda yarki ne yake yawan zuwa kuma na fahimci akwai soyayya a tsakaninsu" Mami haɗa hannuwanta biyu tayi alamar roko🙏"dan Allah Dr na rokeki mubar maganar nan wallahi Su'ad batason Fahad, Fu'ad takeso abata abinda takeso" Ummi mikewa tayi daga inda suke zaune ta soma tafiya tana faɗin "Narantse da girman Allah babu abinda zai hanani aiwatar da wasiyar da Kanol yabari saidai in mutuwa nayi!" tana gama faɗar haka ta wuce ɗakinta, kwana biyu gaba ɗaya na fahimci Ummi da Mami sun sami saɓani saboda yanda naga basawa juna magana daga gaisuwa ba abinda yake sake shuga tsakaninsu, tunda aka haifeni na taso indai har Ummi suna kano to plat ɗin abinci ɗaya sukeci da Mami amma yanzu sai naga kowa ya zuba abincinsa yana ci, in Mami tana ɗaki to Ummi tana falo sam basa zaman hira kamar can baya, banyi masu magana ba ina jiran su Yaya Jabeer da Uncle su dawo daga garinsu Fu'ad inda sukaje wajan bikin naɗin sarauta

Ranar juma'a bayan sallar la'asar ina zaune saman sallayata ina lazimi tun bayan mutuwar Daddy na ɗorawa kaina zama duk juma'a bayan sallar la'asar ina masa addu'a yaya Shareef ya shugo ɗakina jikinsa duk asanyaye yace "Su'ad kizo Baban karaye yazo" bayan sa nabi muka shuga tare, zama nayi kusada Mami ina gaida Baban Karaye kamar yanda muke faɗa masa, yan falon nabi da kallo Mamina ce sai Ummi da yaya fatima da bansan sanda tazo ba saiko yaya Sharif Uncle da Jabir daman basa nan suna garinsu Fu'ad.

Baba Sunusi yayi gyaran murya yana faɗin "Alhamdulillah shekaran jiya wani yaro yaje wajena shida Shareef yagayamin yanason nai masa izini zai turo iyayansa su nema masa auran Aminatu Su'ad kamar yanda kuke faɗa,na tambayesa yataɓa sanar da Kanol kafin rasuwar shi yace min a'a nace masa yaje zan nemesa, abinda baku saniba shine adaran da Kanol zai rasu munyi waya yake gayamin yabawa Fahad auran Su'ad harma ya tsaida rana wata biyu! Allah baiyi zai gani ba, amma ni zan cika masa burinsa daya mutu yana fata, bazan taɓa canzawa ba!" yana gama faɗar haka yafuce daga falon murmushi Ummi tayi tana faɗin "Fenally", kwantar da kaina nayi saman kafaɗar Mami na fashe da kuka "Wayyo Allah na shuga uku wallahi bazan auri kanin babata ba bansonsa banason Fahad wallahi Fu'ad nakeso *wayyo zasu rabani da rayuwata farin cikina shine zaɓina hasken idaniyata hasken rayuwata* rasa Fu'ad daidai yake da katsewar numfashina wayyo na shuga uku ni su'ad nafaɗi haka ina ɗora hannuna aka🙆‍♀️ na fasa uban ihu tareda bajewa akasa ina kurma ihu kamar wata sabuwar yar bori, Yaya Fatima ta mike a fusace tayo kaina zata dakeni, da sauri na makalkale Mamina ina cigaba da ihun kukana waini ko zasuji tausayina su lallaɓa baban karaye ya janye, "Yaya daman nasan bazakiji tausayina ba saboda ke anbaki wanda kike so dan anga Daddy na baya raye shine za'ace yabawa Uncle ni, wallahi bana sonsa bakisan zafin rabuwa da masoyi ba shiyasa zaki dakeni maimakon ki tausaya min," Mami ta jani jikinta fuskarta fal damuwa tace "Yi shuru babyna daina kukan haka bawanda ya isa yai maki dole matukar ina numfashi Fahad ɗin zai dawo yasameni ne inbai janye batun auran nan ba bani ba shi!" sai sannan naji sanyi a raina na kwantar da kaina saman kafaɗarta ina sauke ajjiyar zuciya har barci yayi awon gaba dani.


Jingine yake jikin bishiyar sab sab data kawata wajan iska na kaɗawa a hankali yajima a wajan ya kaɗaice kansa, gaba ɗaya bayason hayaniya ko kaɗan shiyasa yazame daga cikin sauran mutanan dasuka rage a gidan dan tuni wasu sun tafi tunda angama naɗin harma anyi walima, wayarta yaketa faman kira tana ring amma ba'a ɗagaba, tun daga nesa Juhaina take hango Fu'ad a nan rayuwarta ta duniya ba namijin datake so samada Yarima Fu'ad hankalinta duka yana kansa shiyasa ma takasa kula ko wanne saurayi amma shi ta lura sam hankalinsa baya kanta kwanakin nan takejin raɗe raɗin wai yana son wata yarinya a kano, ahankali ta karaso wajan tana murmushi bishiyar dake kallon wacce yake jiki taje ta tsaya tana faɗin "Yaya Turaki ashe kana nan anacan cikin gida ana nemanka, Umma tace nazo nan tasan bazaka wuce nan ɗin ba" batare daya daina danna wayar dayake dannawa ba yace "Kice gani nan zuwa" ɓata rai Juhaina tayi kana tace "tace kafata kafarka" fara tafiya yayi tabisa da sauri danya fita sauri kasancewarsa dogo shiyasa yakeda sauri, saida ko yarugata shuga sasin Umman, yasami Umma da Anty Jamila matar Abbi ɗinsu baiko kalli inda Antyn takeba ya zauna kusada Umma ya ɗora kansa saman kujera ya lumshe idanu ahankali yace "Umma duk bana cikin nutsuwata wani iri nake jina kamar wanda zan rasa wani abu arayuwata!" Umma ajjiyar zuciya tayi ahankali tana kallon Fu'ad tace "Al'ameen ba abinda zai sameka sai alheri wannan nauyin da'aka ɗaura maka ne yasa kakejin haka, kazama jarumi mana kaida ke shirin zama sabon sarki😹" murmushi yayi tareda mikewa ya wuce sashinsa dake cikeda abokansa ciki harda Fahad, Anty Jameela kwafa tayi tareda girgiza kai tana bin Fu'ad da kallo wanda yai burus kamar bai ganta ba, fuuu ta fuce daga falon ranta na suya da watsin da fu'ad yayi da ita, tabbas saita basa mamaki tayi alkawari saita lalata rayuwarsa saitayi silar da zai rasa duk wani farin cikinsa harma da sarautar da ake son naɗasa dan wannan turakin da aikai masa taga alamar sharar fage ne.

Fu'ad can bedroom ɗinsa yashuge yana sake kiran layin Su'ad haka kurum yakejinsa wani iri muryarta yakeso yaji kozai sami nutsuwa, wannan karon bugun farko ta ɗaga muryarta a sanyaye ta masa Allah yasa alkhairi da addu'ar Allah yataya ruko "Princess naji muryarki ba dai dai ba" kamar zatayi kuka take faɗin "Barci nayi na gaji shiyasa kaji muryata haka" sake gyara kwanciya yayi yana faɗin "Ban yarda ba indai kina cikin damuwa kema kinsan ina ganewa faɗamin kawai maike faruwa" fashewa tayi da kuka, gaba ɗaya ya ruɗe harda tashi zaune yadafe kai🤦‍♂️ "Oh Baby gayamin maike damunki inbaki gayamin ba billah yanzu zan kamo hanyar kano batare da kowa yasani ba" shagwaɓe murya tayi "Banida lafiya zazzaɓi nake tun safe Ummi taki kulani Mami kuma bata nan bare ta kaini hospital" komawa yayi ya sake kwanciya "Raguwa zazzaɓin kikewa kuka tonan da watannima haihuwa zaki, wacce tafi zazzaɓi wahala, kisha ko paracetamol ne anjima zan kiraki naji yaya kikeji" kai kurum ta girgiza masa saboda wani tausayinsa daya mamaye zuciyarta tayaya zata bari a rabatada Fu'ad wanda yai soyayya akaro na farko baiji daɗiba yanzuma ace bazai sameta ba, ai wallahi ko sama da kasa zata haɗe koda tsiya koda tsiya tsiya sai an aura mata Fu'ad idan suka ki kuwa wallahi guduwa zatayi tashuga duniya dadai ta auri Uncle wanda takewa kallon kanin uwa.


Fu'ad da Fahad da dare suka shirya cikin koriyar shadda wacce Fu'ad ya ɗinka masu, sosai sukai kyau komai nasu iri ɗaya suka saka sai suka futo kamar wasu twince inka gansu inba saninsu kayiba zakace uwa ɗayace ta haifesu saboda kamanni dasuke ɗanyi kaɗan saidai Fu'ad dayafi Fahad fari da tsayi, Fahad ba fari bane can shidai baza'akirasa da baki ba hakaza baza'ace masa fariba yanada tsayi kaɗan amma saboda yanada kiba saita shanye tsayin nasa, Suna hakimce a bayan mota yayinda Sarkin mota kejansu, har zuwa G R A gidansu Fu'ad yazo gaida mahaifinsa dayazo garin jiya da dare basu sami haɗuwa ba saboda hidama dasuke da mutane, Anty Jameela suka samu a falo taci uban kwalliya tana hakimce tanacin Apple, Fu'ad ko kallon inda take baiyi ba kai tsaye ya wuce sashin Abbi ɗinsa, ya mugun tsanar matar nan tunda take ƙazabtar masa da kanwarsa guda ɗaya tilo dayakejin duk duniya bayada sama da'ita yana matukar ji da Deejah akanta zai iya rabuwa da komai indai zatayi farin ciki, Fahad dakebin Fu'ad da kallon mamaki yace "Amma naga kamar Anty Jamila muka wuce a Falo ko bamu gaidata ba" taɓe baki Fu'ad yace "Saime to dan bamu gaidata ba haifarmu tayi!" karaf maganar a kunnan Antyn dake shirin shugowa sashin murmushi tayi tareda laɓewa har suka gama gaisawa da Abbi saida taji suna sallama kana tai saurin ɓuya a bayan labule saida suka futa ita kuma ta shuga, Washe gari sassafe Anty Jamila taiwa Abbi karyar zataje gidansu yajirata ta dawo bazata jimaba zata dawo saisu wuce Kaduna inda can Abbi ke aiki, bata doshi gidan nasu ba kai tsaye hanyar wani daji ta yanka a motarta tajima tana gudu a motar nan cikin jejin kana ta sauka a motar da jingina tareda rufe idanunta tasoma karanto wasu ɗalasimai kafin tarufe bakinta wata iriyar guguwa mai karfi tayi sama da ita🙆‍♀️🏃‍♀️🤭

Zainaba zaune gaban mahaifinta dake cin tuwo, saida tajira ya gama ci sannan tace "Baba waiya maganarmu ne ta Fahad wai haka zanyita zama nifa indai ba gidansa ba wallahi bazan sake aure ba, kuma zuwan danaima rannan na gano wata babbar masifa dake shirin faruwa damu domin na gano son Su'ad a cikin idanun Fahad" Baba ya bushe da dariya yana faɗin "Wannan shine kuskure na karshe da Fahad zaiyi idan har yasake ya sake aure Allah ne kaɗai zai fuddashi daga tarkona amma badai mutumba"😂dariya Zainaba tayi tana jinjinawa Baban nata ganin ashe shima har yanzu hankalinsa nakan Fahad ɗin "Ai baba basai kayi komaiba ni kaɗaima na ishi Fahad inada tarin abubuwan dana tanadar masa matukar yai kuskuran auran wata batare daya maidani ɗakina ba...✍️


Inkinsan kinason karantawa kuma zakina yin commeny to maza yi save ɗin wannan lambar 07039793439 da Mami Yusuf Daboo kimin magana zanyi adding naki a group ɗina🙏
[6/4, 7:46 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹


Story and weitting by
Mamie Yusuf Daboo🥰


☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

9&10


Fahad cikeda kewar Su'ad yashugo gida kwana biyun nan dayayi babu ita ba karamin ɗaga masa hankali yayi ba musamman jiya zuwa yau gaba ɗaya taki ɗaga kiransa a waya, kai tsaye ɗakin Mami ya shuga ganin ba kowa a falon sai hanne mai aiki, Su'ad na kwance kan gado ta lulluɓa da katon bargo jiya zuwa yau ita kaɗai tasan mai takeji a zuciyarta batajin zata iya hakura da soyayyar Fu'ad data gama mamaye mata dukkan zuciyarta, ɗakin shuru ba motsin komai saina zubar ruwa dayake jiyowa daga bathroom, harya juya zai futo azatonsa Su'ad ɗince ke wanka, jiyowa yayi jin saukar numfashin mutum a bargo janyo bargon yayi tareda saurin zama gefan gadon a ruɗe yake faɗin

"Besty bakida lafiya ne" taɓa jikinta yayi yaji zafi sosai dafe kansa yayi yace "Kinsan kina zazzaɓi kikazo kika lulluɓa da bargon nan kinaso kimin asara ko" kallon inda yake banba saima tsaki da naja tareda juya fuskarta na daina ganinsa, hawa yayi saman gadon sosai yana matsawa kusada niba hasale nace "Ka futar mana daga ɗaki Fahad banason ganinka banason sake ganin fuskarka" dafe kai yayi🤦‍♂️cikada damuwa ya sauka daga gadon yana kallon Su'ad da mamakin maganarta, futowar da Mami tayi daga bathroom yasa ya kalli Mamin yace "Mami maiya sami Besty naji tana magana kamar wacce aljanu suka taɓa"

Mami jingina tayi da kofar bathroom tana kallon Fahad da duk damuwa ta bayyana karara a fuskarsa tausayin ɗan uwanta yakamata tasani ba karamin so Fahad yakewa Su'ad ba saidai yayi sake yayi wasa da damarsa tuni wani yariga sa shuga zuciyar Su'ad "Fahad maiyasa zakamin haka? taya zaka sami Kanol ka gaya masa kanason Su'ad waya gaya maka haka ake soyayya ina mai umartar da lalle ka janye batun auran nan domin yata tanada wanda takeso har sunyi alkawarin aure" da sauri ya zauna gefan gado saboda jirin dayaji yana kokarin kayar dashi, "Mami tayaya zan hakura da soyayyar da zuciyata ta rayu da'ita samada shekara ashirin! inason Su'ad banajin akwai wani namiji a duniyar nan daya fini kaunarta, itace rayuwata zuciyata gaba ɗaya itace ni" yakarasa faɗa hawaye suna biyo kuncinsa "Fahada na rantse da Allah koda son Su'ad zaiyi ajalinka saika barta, inba haka ba babuni babu kai kaje kanemi wata yar uwar bani ba!" tana gama faɗar haka ta koma bathroom saboda wani kuka dake kokarin taso mata na tausayin ɗan uwan nata guda ɗaya jal daya ragemata anan duniya, Fahad kallon Su'ad yayi wacce ke kuka kamar ranta zai futa jin maganganun su Mami wai ita yaya zatayi da ranta shin Aminci zata zaɓa ko kauna, sosai kukanta ke taɓa zuciyar Fahad jiri na ɗibansa haka ya fuce daga ɗakin zuwa nasa ɗakin ko takalminsa bai cire ba ya kwanta saman gado tareda fashewa da kuka.

Yaya Jabeer wanda yafuto daga ɗakin Ummi kasancewar tare suke da Fahad basusan da zuwan baban karaye ba sai yanzu daya dawo Ummi ta faɗa masa komai, turus yaja yatsaya sanda ya shuga ɗakin Fahad ya gansa kwance yana rizgar kuka kanar wanda akace masa Mami ta rasu, gaba ɗaya Jabeer ya kiɗime ɗago Fahad ɗin yayi yana faɗin "Uncle lafiya kake kuka haka?" ruke Jabeer yayi "Jabeer kataimakeni yaya zanyi da zuciyata Su'ad bata sona tace bazata aureni ba!" Jabir dafe kansa yayi shi dariyama Fahad ɗin yaso basa hakan yasa yace "Shine zaka tsaya kana wannan kukan sai kace wanda akaiwa mutuwa wallahi kaji na rantse matukar ina raye Su'ad batada wani miji inba kai ba barima kagani"

Mikewa yayi ya fuce daga ɗakin zuwa na Mami baiko kula da Mami dake zaune gaban madubi ba ya janyo Su'ad daga saman gado wacce ke faman kuka har lokacin, fuskarta ya ɗauke da mari "Ashe bakida hankali bansani ba! ke harkin isa kifaɗawa Uncle magana toki sani auranki da Uncle ba fashi saidai in an kaiki ki mutu!"
"Jabeer agabana kake dukan yata ko mutuwa tana kunyar idon mahaifi fa" ta tashi ta rungume Su'ad tana lallashinta.

Fu'ad yafuto daga fada kenan yau tun safe suna tareda mai martaba yana futowa Fahad yafara kira yaji yaya sukaje gida amma har wayan tagama ring bai ɗagaba hakan yasa ya kira lambar Su'ad wacce rabon dasuyi waya tun jiya da dare gashi yanzu har karfe uku na rana yasan yayi laifi yana zaton hakan yasa bata ɗagaba har kiran ya katse saida ya shuga sashinsa ya cire rawanin kansa ya ajje saman kujera ya zauna kana ya sake kira, Su'ad tana gani kiran harya katse bata ɗagaba saboda batasan yaji muryarta yanaji zai san kuka take hankalinsa zai tashi ita kuma batason damuwar sa, ganin kira yanata shugowa yasa ta ɗaga tana kokarin saita kukan dake shirin kwace mata amma ina ta kasa musamman dataji yace "Hubbina inata kira kinki ɗagamin waya ko" kukane mai sauti ya kwace mata shuru yayi yana sauraron kukan nata dayakejinsa har tsakiyar kansa "Princess kinada damuwa amma kinki gayamin haka mukayi dake! damuwarki damuwata ce dan Allah gayamin maike damunki tun jiya kike kukan nan Mamin bata dawo ba?" kai ta gyaɗa masa kana tace "Fu'ad muna cikin matsala kayi mana addu'a Allah yasa mu kasance da juna" mikewa tsaye yayi tareda ɗaukar rawanin sa a hannu yafuta bayan ya kashe wayan yana kwaɗawa Sarkin mota kira, ko rawanin nasa bai mayar ba ya shuge mota yana bawa sarkin mota umarnin yai gudu sosai soyake suje kano nan da awa awanni gudu sosai Sarkin mota keyi amma Fahad gani yake kamar ba gudun yake ba ji yake kamar ya karɓi tukin gaba ɗaya ya lulluɓe sarkin mota da masifa faɗa yake masa kamar zai ari baki baiyi aune ba ji kake kiiiiii sitiyarin motar ya kwace motar ta daki wani gini dake gefan titi tafara hayaki

Fu'ad ya runtse idanunsa saboda azabar dayaji na glass daya shuga hannunsa, ɗayan hannunsa yasa yazare glass ɗin yana lumshe idanu saboda azabar daya sha, ganin motar na kokarin kamawa da wuta yasa ya tattara duk kanin karfinsa ya daki murfin motar yabuɗe yafuta da sauri tareda jawo sarkin mota daya soma futa a hayyacinsa saboda buguwar dayayi a kansa, Fu'ad ya raba rawaninsa biyu ya ɗaurewa Sarkin mota kansa daya soma zubar da jini shima ya ɗaure hannunsa dake masa wani azababban zugi, dai dai sannan motar yan sanda tazo wajan domin kiransu da wasu jama'ar dake gefan wajan sukayi tun sanda sukaga motar ta
End Ads