x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - KUKAN ZUCIYA

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 38354 words

Category: Tale Stories

Views 44

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
Ankul dawowa bayan yacemin karfe biyu zai dawo zama nayi na ɗakko wayata na kunna data nahau online hira muke da Yaya Fatima kiran Fahad yashugo wayan nawa da sauri na ɗaga cikeda shagwaɓa

Nace "Shine kayi zamanka har yanzu baka dawo ba bayan kace karfe biyu zaka dawo" ina jiyo sanda yai murmushi mai sauti

"Kina son nadawo ne, inna dawo maizan samu mai kika tanadarmin?"

"Na tanadar maka da komai,kuma ni tsoro nakeji nafison innayi motsi na ganka kusa dani hakan yana faranta min rai"

"Da gaske to gani nan a hanya" kashe wayan yayi saida yayi sallar La'asar a masallaci dake ɗan nesa da gidansa kaɗan sanna ya karasa gida.

Horn ɗin motarsa dana jiyo yasa na futa da sauri na buɗe masa get,yashugo da motar na maida gate ɗin na rufe na karaso wajan motar na buɗe masa murfin motar, yafuto yana dariya tareda sakani cikin jikinsa ya sumbatar bakina yace

"Kinyi kyau sosai besty bakiga yanda doguwan rigan nan tai maki kyau ba" sosai naji daɗin yabon da yai min hakan yasa na kuma shugewa jikinsa ahaka muka jera zuwa ciki, saida nakaisa har ɗakinsa na haɗa masa ruwan wanka ya shuga yana tsokanata inzo na tayasa wanka, na futo daga ɗakin da gudu ina dariya, Allah yasani kunyarsa nakeji banajin akwai wata rana da zatazo wacce zan iya tayasa wanka, ina nan falo zaune ya futa sanye da wando 3 kwata da farar t shart mara nauyi, kusa dani ya zauna ya jawoni jikinsa yana shafa gashin kaina

"Waini yaushe za'a daina jin kunyata saboda Allah ace wankama har yanzu da kaina nake baza'arinka yimin ba" rufe idona nayi alamar jin kunya ina dariya kasa kasa nace

"Nifa bazan iya ganinka ba kaya ba ajikinka ai kunya zanji" dafe baki yayi yana dariya kasa kasa

"Ok yanzu nagane laifin nawa ne, aiko yazama wajibi yau saina cire wannan kunyar dake tsakaninmu Allah yakaimu dare" murmushi kurum nayi tareda mikewa na kawo masa abinci na ajje bisa carfet dan nasan Ankul tun tuni bai fiyason cin abinci a dannig ba, sosai yaci abincin yana tsokanata inata dariya muna nan zaune muna hira har aka kira mangariba yafuta masallaci ni kuma na wuce ɗakina nai alwala.

Ankul bai shugo gidan sai wajan karfe takwas da rabi lokacin har nayi shirin kwanciya bayan nayi wanka na saka night wear na zuba humra sai tashin kamshi nake banji shugowar sa ba kasancewar harna fara barci sai mutum naji cikin bargo ya haɗe jikina da nasa, na buɗe baki ina shirin yin ihu ya saurin haɗe bakina da nasa, yanda yake kissing ɗina yasa jikina yaɗauki rawa Sosai yake min wasu kalar abubuwa wanda sam bansan dasu ba, gaba ɗaya yafuta hayyacinsa niko har sannan jikina rawa yake musamma sanda naji yana kokarin shuga jikina sosai nake kuka da rokonsa amma baimasan inayi ba saidai cak ya tsaya yana maida numfashi lokacin dayai kokarin shuga jikina J ɗinsa yaga tai wani irin kankancewa da sauri ya janye jikinsa daga jikina ya kwanta gefena yana maida numfashi, ban fuskanci komai saima zato danai ko rokonsa danake ne yasa ya tausayamin yafasa abinda yai niyya amma yanda naga yana numfashi yasa na kunna light da sauri tausayinsa ya kamani ganin yanda ya haɗa gumi aruɗe nace

"Ankul lafiya maiya sameka" janyoni yayi jikinsa tsawon lokaci yana cikin wani yanayi yanda idanunsa sukayi ja yasa na ruɗe na soma kuka,

"Ankul na amince gani kayi abinda kai niyya dani inda zaka dawo dai dai amma ni tsoro...hannunsa yasa saman laɓɓana alamar nayi shuru, hawaye naga sun zuba daga idanunsa yace

"Bazan iya maki komai ba Su'ad bansan iya tsawon lokacin dana ɗaukaba batare dana gano cewar bani da cikakkiyar lafiya ba nidai nasan har sanda muka rabu da Zainaba lafiya ta kalau" sam ban gane inda zancan nasa ya dosa ba hakan yasa gaba ɗaya hankalina ya kuma tashi aruɗe nace

"Bakada lafiya Ankul tashi to muje hospital kona kira Dr Hafis yazo ya duba ka"

"Ba rashin lafiyar jiki nake nufi ba kalli nan" yafaɗi haka yana nunamin J ɗinsa, kallon inda ya nunamin ɗin nayi da sauri na runtse idona saboda gamon danayi, Fahad yana murmushi yace

"Buɗe idonki ki kalleni ki gane rashin lafiyar danake nufi ya zamuyi" yanzu kam nagano abinda yake nufi

"mu gayawa Mami nasan zata samo maka magani"
"A'a karmu gayawa kowa mubar wannan sirrinmu ne, zan nemi magani bansan da matsalar bama da tuni nasamo magani, wannan yazama sirri nidake karki gayawa kowa dan Allah"

"Haba Ankul tayaya zan iya gayawa wani wannan matsalar ai tamuce dagani sai kai" rungumoni yayi jikinsa har barci ya ɗaukeni baiyi barci.

Fahad dayaga Su'ad tayi barci tashi yayi yai wanka ya gyara jikinsa ya ɗakko system ɗinsa ya soma binciken magani daya dace ya sha.

Tun sanyin safiyar lahdi yaketa shirya kayansa cikin trabiling bag fuskarshi fal da damuwa ga kansa dake masifar sara masa saboda damuwa idanunsa sunyi jawur sosai kamar wanda yai kuka,kofa yabi da kallo ganin tayi motsi cak ya tsaya yana bin Khadija data shigo ta zaune kan sofa ta fashe da kuka "Yaya Prince yanzuma tafiya zaka kuma yi ka barni ni ɗaya?" Khady ta faɗa cikin kuka sosai, rigar hannunsa ya jefa saman bed da sauri ya tsugunna gaban Khady yasaka hannunsa cikin nata yanaji inama shine yake wannan kukan inama shima zai iya kukan nan ko zuciyarsa zata masa daɗi "Khady yi shuru dan Allah ba laifina bane laifin Abie ne na gaya masa bana son tafiyar nan amma ya kafe dole wai saina fara aiki a asibitin legus nima zanso ace an barni nan na rinka ganinki ko yaushe amma insha Allah na maki alkawari zan rinka zuwa duk karshan mako please Khady ki daina kukan nan" cikin kuka Khady ta gyaɗa kanta tana bin ɗan uwan nata da kallon tausayin rasa masoyiya da yai, Khady da Juhaina daketa rawar kai tare suka raka Prince har filin jirgin sama saida yatafi sannnan suka dawo gida, a legos gida da motar hawa asibitin dazai fara aiki dasu suka basa kai tsaye yafara aikinsa ba ruwansa da sabgar kowa indai ba hospital zai je ba to bazaka taɓa ganinsa a waje ba kullum yana gida kamar mace,

Sauri sauri yake shirin futa bayason makara saboda karfe tara yanada feshen ɗin dazaiwa c s, takwas saura ya shuga hospital ɗin tun daga resepsion yake amsa gaisuwar ma'aikata yanda suke basa girma kai kace shine mai asibitin a mutumche yake amsa gaisuwar saidai fuskar nan tasa tamke ba ko ɗigon fara'a haka yake haka suka saba ganinnsa shiyasa basu wani damu ba.
Bai tsaya a ko'ina ba sai kofar katon office ɗinsa tamkar falon wani gidan saida ya zauna saman kujera ya sauke ajjiyar zuciya tareda cusa hannuwansa duka biyun cikin gashin kansa yana fuzzar da iska mai zafi daga bakinsa, shirye shiryan shuga tiyata yafara yi ta hanyar canza kayan jikinsa ya shuga ɗakin tiyatan.

Anty Jameela na murmushi ta damkawa Suwaiba rafas ɗi nyan dubu dubu guda uku "Ga somin taɓin kuɗin aikinki nan bazan baki sauran ba sai aiki ya kammala"

Murmushi Suwaiba tayi daɗi takeji sosai a ranta da ganin wannan uban kuɗin wai duk nata ne hakan yasa tace "Bakida damuwa Hajiya aiki kamar angama sane gobe insha Allah tun safe zanwa garin legas tsinke na ruga naga inda yake da gidan dayake zaune abu ɗaya zaki bani makullin gidan"

"Au kinga na manta wallahi gashi" tamika mata makullin bayan ta ɗakkosa daga jakarta, mikewa Suwaiba tayi tana wani juyi kamar tana gaban mijinta🤭dariya Anty Jameela tayi bayan taga futar Suwaiba daga ɗakin, harda tsallanta na murna gobe iwar haka burinta ya cika an ɓatawa Fu'ad suna shida sarautar saidai yagani anayi💃

Fu'ad tunda yashuga asibiti bai futo ba sai tara na dare gaba ɗaya agajiye yake jin kansa, ta restaurent ya biya yayi take away sannan ya wuce gida wanka yafara yi saboda gajiyar daya kwaso, jiyake inama yanada mata tabbas yau da saidai su raba gajiyar nan, abincin yaci yaɗan hau online bai jima ba yafara jin barci haka yasa ya kashe datan ya wuce bedroom.

Dare yayi sosai ahankali take juya kanta cikin barci kafin ta farka a firgice tana salati, salatin datayi shiya tashi mai martaba dake kusa da'ita yana barci, a kiɗime ya farka yana tambayar "Asiya lafiya naganki haka maiya sameki wani abune ya faru?"

"Lafiya kalau ranka ya daɗe amma wani mafarki nayi, hankalina yatashi anya ko One boy yana lafiya" Mai martaba maida kansa yayi ya kwanta tareda lumshe ido kana yabuɗesu akan matar tasa "Lafiya kalau ɗanki yake ɗazuma saida mukayi waya dashi lokacin yana hospital yace bai koma gida ba" Umma sakkowa tayi daga kan gadon ta shuge toleit mai martaba yabita da kallo yana sakejin son matar tasa uwar gidansa yana sake shuga ransa musamman ganin yanda ta damu da lamarin Fu'ad ko yaushe batada magana saita Ameen yayi kaza ko yaranta data haifa bayajin tana yiwa so kamar yanda takewa Fu'ad, da Khadija duk da sauran matansa suna zargin son datakewa Fu'ad badan Allah bane dan tana ganin nan gaba shine sarki shiyasa take sonsa, shidai yasani ba haka bane son datakewa Fu'ad tun yana yarone sau tari Ummu kafin ta rasu tasha bata Fu'ad ya jima awajanta shiyasa suka shaku sosai, Umma tafuto ta shimfiɗa dadduma ta tayar da sallah tana rokon Allah yakare mata ɗanta ya nesantashi daga abinda tayi mafarkin yasamesa yanzu, sanda ta gama addu'o'inta ta shafa ta koma ta kwanta sannan ta lalubi wayarta taga karfe 03:44 am lambar Fu'ad ta buga tajima tana ring sannan yaɗaga aɗan tsorace yake tambayar Umman lafiya

"Lafiya kalau One boy kawai cewa nayi bari na tashi ɗana ya ribaci daren nan da koda raka'a biyu ce ta nafila" dirowa yayi daga kan gadon yana murmushi yace

"Na gode Ummana na mike kuwa alwala ma zanyi nayita sallah daga nan har safiya ina rokon Allah yakarawa Ummana lafiya da nisan kwana tayita bani kulawa har zuwa taga jikokina" dariya Umma tayi ta kashe wayar ta shige jikin mijinta tana murmushi, Fu'ad bai koma barci ba sai bayan sallar asuba daya dawo daga masallaci ya koma barci bayan yayi karatun kur'ani izifi uku yai azkhar sannan yakoma ya kwanta,dan yau bazai shuga hospital ba sai huɗu na yamma.

Karfe shida dai dai jirginsu Suwaiba ya sauka a garin legos ikko ikon Allah cunkus ɗakin tsumma😹itada kawarta ne hotal suka kama suka ɗan huta bayan sallar mangariba Suwaiba ta wuce gidan Fu'ad, ta tarar baya nan hakan yasa tasa makulli ta buɗe karamar kofar shuga gidan ta shuge ciki ba kunya, ɗakuna biyu ta gani cikin falon ta murɗa handling na kofa ɗayar tajita a rufe hakan yasa ta nufi ɗayar tana murɗawa ta buɗe ta shuga, wanka tayi ta shirya cikin wasu shegun kaya kanana masu masifar kyau da fusgar hankali, ta feshe jikinta da kalolin turarukanta da wanda Anty Jameela tabata wanda ta karɓo daga wajan boka🤭

Takwas dai dai Fu'ad yashugo gidan bakinsa ɗaukeda addu'ar shuga gida harda sallamarsa kamar wanda yabar mutum a gidan, ajje ledan abincinsa yayi saman kujera yana shirin shuga ɗakinsa yaji an rungumosa ta baya ba karamin tsorata yayi ba saboda shidai yasan shi kaɗaine agidan, bai ankare ba yaji an soma shafa jikinsa ana kokarin ɗora hannu kan J ɗinsa, afusace ya jiyo yana karanta ayatul kursiyyu domin azatonsa gamo yayi saidai wazai gani inba gizo idanunsa sukai masa ba Suwaibace wannan a fusacen dayake ya danki wuyanta yana faɗin

"Malama maiya kawoki gidana maiya sake dawo dake rayuwata bayan yaudarar da kikamin saboda kin maidani sha sha sha shine yanzuma kika dawo ki yaudare ni?",

Suwaiba da idanunta suka furfuto tafara hango mutuwa saboda yanda ya rike mata makogwaro tace "Ka sakeni zangaya maka wanda ya turoni" bai saketanba saima kara rike mata makogwaro dayai idanunta dayaga ya firfito tana kakarin mutuwa yasa ya wurgata ta bugu da kujera tasaki ihu bai tausaya mata ba yasa kafa yatake hannunta

"Zaki gayamin ko saina haɗaki da hukuma" kanta take girgizawa tama kasa magana sabida azabar da hannunta da kanta keyi,wayansa ya ɗakko ganin yana shirin kiran yan sanda yasa ta magantu

"Anty Jameela ce ta turoni na shugo rayuwarka muyi rayuwa na zama karuwarka saboda batason kazama sarkin bare" dafe kansa yayi ya koma saman kujera ya zauna kamar kuma wanda aka kunna yamike ya fara jan kafafun Suwaiba bai tsaya da'ita saida yakaita kofar gate can waje ya wurgata ya koma ciki ya ɗebo sauran kayanta ya watsa mata

"Wannan yazama na farko kuma na karshe dazaki kuma shugomin gida, ki gayawa wacce ta turoki insha Allah nafi karfinta itada duk wani sharrinta, kar nake kallonta a tafin hannuna,harya juya zai koma ciki yadawo yamika mata hannu

"Ina kika sami makullin da kika buɗemin gida"

"Anty Jameela ta bani a sashin Abie ɗinku ta ɗakko" murmushi mai ciwo Fu'ad yayi yamika mata hannu

"Bani makullin" tamika masa yakoma ciki yana sauke ajjiyar zuciya.....✍️

Saura kiris pages su daina fitowa na daina posting ɗin book ɗin nan a kowanne group sai group ɗin Kukan zuciya real fans indai har kinsan kinason cigaba da bin labarin nan to masa yimin magana ta wannan lambat nai adding ɗinki a group 07039793439
[6/4, 7:48 PM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹


Story and writtin by
Mamie Yusuf Daboo🥰


☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

17&18



Dakyar Suwaiba ta koma hotal ɗin data sauka saboda wani azababban ciwo da wuyanta yake mata lalle ta tsallake rijiya da baya a irin rikon dayai mata tabbas zai iya kasheta tasan inya kasheta yakashe banza saboda ba wani gata ne da ita ba, iyayanta bawasu masu hali bane tasan kasar nan tamu anaji ana gani sai a rufe maganar tunda shi ɗan manya ne bakaramar nadama tayi ba data bari kawarta ta ruɗe ta harta karɓi wannan aikin na Anty Jameela datake ganin bashida wani wuya.

Yau da nishaɗi muka tashi kasancewar sunday ne Uncle yana gida bai fita hospital ba kamar yanda muka saba tare muke komai na gidan yanda Uncle yake kula dani yasa gaba ɗaya nama manta da Fu'ad gaba ɗaya na mallakawa Uncle zuciya na, bayan munyi sallar azahar wanka mukayi tare muka fito danning zamuci abinci, ina sanye cikin doguwar rigar atamfa A shape wacce ta matukar zaunawa a jikina ni kaina nasan nayi kyau saboda yanda nayi kiba na kara haske, ga wani ɗauri danayi sosai Uncle ya yaba da kwalliyar tawa sai bina yake da kallo, jerowa mukai zuwa wajan danning ɗin ina tsokanarsa ina dariya tare mukaci abincin kamar yanda muka saba ciyar da juna, falo muka koma ya kunna kallo ni kuma na kwantar da kaina saman cinyarsa ina shirin barci, buga kofar da'akai yasani mikewa zanje na buɗe kofar

"Besty keda kika soma barci ki zauna ni na buɗe" harara nai masa irinta masoya nace

"Saidai ayi riga rigayan zuwa"kafin na rube baki yatafi da sarsarfa nima na take masa baya ya rigani zuwa saidai ganin waɗanda suke bakin kofar yasa shi yin turus kunya duk ta kama sa ganin kayan dake jikinsa Mami suka shigo falon da sallama itada Ummi a
kunyace yadawo falon yana wani sinkuyar dakai kamar wanda yaiwa sarki karya🤭

Ina jikin Mamina na makalkaleta Ummi sai bina take da kallo nasan itama cewa zatayi nayi kiba, danko ni nasan ba karamar canzawa nayi ba, Mami data kasa daurewa tace "kai masha Allah Dota ɗita nayi murna sosai Allah ubangiji ya inganta nasan wannan kiba bata haka nan bace mai dalili ce da'alama nakusa samun jika" da gudu na mike na shuge kichin na kawo masu lemu da cake Allah yasa inada abinci hakan yasa na haɗo masu dashi, Ankul yana gama gaisawa dasu ya koma ciki danba karamar kunya yajiba yanda suka gansa.

Su Mami sunjima sosai sai bayan sallar mangariba suka tafi.

Anty Jameela na tsaye gaban dinning tana shiryawa Abie abinci da lamun dayasha magungunan data amso a wajan boka, wayarta dake ajje kan dinning tashuga ruri ganin Suwaiba ce mai kiran yasa ta saurin ɗagawa tareda jan kujera ta zauna, jin abinda Suwaiban ke faɗa mata yasa ranta yaɓaci bata jira futawar Abie ɗinba ta wuce ɗakinta ta kule can ciki bayan ta dannawa ɗakin key
Wayan boka ta kira tana sanar masa abinda Fu'ad yamata

"Kinga ki futa hanyar yaron nan ba abinda zamu iya akansa tsaye yake kan addu'a da azkhair gashi yana yawan karatun kur'ani gefe kuma ga watanan datake kara masa addu'ar kariya, kinsan aljanu nawa natura suna dawomin nikam na futa hanyar yaron nan bazai kassarani ba"

Anty Jameela ranta ɓace ta futo daga ɗakin nata saurin saita kanta tayi ganin Abiee zaune bisa dinning yana aikawa cikinsa lemu, zama tayi kusada shi tana kara masa sannu da hanya, saida yagama cin abinci yabita da kallo

"Narasa maiya zaunar dake agarin nan kinki komawa kaduna" taɓe fuska tayi

"Ni kawai garin yafuta araina nafison zaman nan kaima kabar aikin nan ka dawo nan ka amshi sarautarka" murmushi yayi kawai yana danna wayarsa.

"Niko Alhaji nace maizai hana yaron nan Ameen asama masa wata a aura masa shekarunsa kullum daɗa ja suke yakasa ajje iyali"

"Kamar kin shuga raina abinda yake cimin rai kenan ko jiya nai masa magana amma sai cewa yayi shi bayanzu zaiyi aure ba shekarunsa fa yanzu Talatin da shida, inaga zanyiwa mai martaba magana a haɗasa da Juhaina ta wajan mai martaba" da sauri Anty Jameela tace

"Ai kuwa karkayi haka yarinyar nan rannan naji suna hira da Khady tana faɗa mata ɗan wazirin gombe ke sonta" shuru yayi baice komaiba, jin alamun bazai sake cewa komaiba yasa Anty Jameela tace

"Ni badan kar'ace naso kaina ba sai nace inba damuwa a haɗasa da Baraka kanwata kaga itama taki futar da wani tsayayye suje can su sasanta kansu" nan ma shuru Abiee yayi baice komaiba sai can yace

"Tabbas kinyi hange mai kyau gobe zan tura makama su tambaya mana inta amince ni banida damuwa da Ameen lamarinsa yafara bani tsoro aure zan masa saidai kawai atura masa matar legos" yana gama faɗar haka yamike yafuta.

Washe gari tana ganin Abiee yafuta itama ta fuce zuwa gidansu gargaɗin Baraka tayi akan indai aka tambayeta tanason Fu'ad ta
End Ads