x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - KUKAN ZUCIYA

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 38354 words

Category: Tale Stories

Views 46

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads
sashin Abbansa yasan yanzu acan zai tadda Mamansa, ilai kuwa kamar yanda yazata ɗin tana sashin suna tareda Abba sunacin abinci saida yajira suka gama kafin yafara magana

"Abba daman akwai wacce nake zuwa wajanta to sai akace na turo manya shine nace bari na gaya maka"

Mama ta kama baki alamar mamaki tace "Ikon Allah daman wai kanada budurwa Nurein amma baka taɓa zancanta ba dani harna fara magana da innarku saude a haɗaka da Halima ɗiyarta wace wannan kuwa"

"Ma'ma Su'ad sunanta yar kawarki Mami" mug ɗin hannunta datake shan yoghourt ne ya suɓuce ya faɗi tana kallonsa da mamaki

"Yanzu Nurein duk yammatan dake garin nan karasa wazaka aura sai bazawara kana saurayinka" mur yasha kamar bai taɓa dariya ba yana kalon Abbansa dayai shuru yana kallonsu

"Abba ai auran bazawara ba haramun bane ko?" yatambayi Abban nasa

"Hakane Nurein ba haramun bane sunna ce ma, nayi farin ciki da faruwar hakan gobe zan yiwa Alhaji islama'il magana sai suje"

"Yauwa Abba na gode Allah ya kara girma"

"Kai saurareni kajini da kyau, na rantse da Allah ko bayan raina ka auri yarinyar nan ban yafe ba! bandama rigima irintaka ina kai ina ita shekara nawa ka bata yarinyar ma da'ake zargin ita ta kashe mijinta..."kinga ya isheki haka kai Nurein jeka ciki" Abba ta inda yake shuga bata nan yake futa ba tas ya wanke maman ya tashi ya shuge ɗakinsa, itako kwafa tayi ta koma nata ɗakin tana zagayan neman mafuta.

Chiroma da computer ɗinsa yai amfani ya cire tsaron dake cikin wayar Su'ad yabawa Turaki, ahankali yake duba wayar harya shugo wajan sakonni sosai yasha mamakin irin zafafan sakonni da Nurein ke aikowa da Su'ad itama bata sanya wajan maida masa da martani, kansa yaji ya sara masa tareda wani irin bugawa da kirjinsa yayi har saida ya dafe wajan, duk Chiroma yana kallonsa baice komaiba dan yanada labarin soyayyar sa da Fu'ad, wanka Fu'ad yashuga ya futo ya shirya cikin bakar jallabiya mai gajeran hannu ya nufi sashin Umma, yanda yake tafiya cikin sanyin jiki yasa Umma take kallonsa da tausayawa harya zauna kujerar kusada ita yana gaidata

"Al'ameen ashe abokinka Allah yai masa rasuwa ɗazu Chiroma ke gayamin daya shugo nan Allah yai masa rahma"

"Ameen Umma yanzuma zuwa nayi nace a shirya Baby Su'ad zamuje kano dana ce sai friday zan shuga saboda case ɗin waɗanda suka kashe sa, amma bazan iya bari har sai zuwa juma'a ba"

"Ok tana ciki tareda Juhaina inagama tai mata wanka tun ɗazu" mikewa yayi ya shuga ɗakin Juhaina, tana zaune gefan gado kusada ita Baby Su'ad ce tana wasa da teddy da sallama ya shuga ɗakin ya zauna saman kujera yana kallon Juhaina datai kasa da kanta, da gudu Baby Su'ad tazo ta faɗa jikinsa ya rungumeta yana kallon Juhaina yace
"ɗago ki kalleni magana zamuyi ta fahimta, batun yau ba nasan kina sona ajiya naso na faranta maki ta hanyar auranki amma wani dalili mai karfi ya gifta wanda yasa na fasa, nasan kinsan labarin Su'ad da irin son danake mata jiya naje garinsu na samu mijinta ya rasu, zan maye gurbinsa zan auri Su'ad a wannan karan insha Allah ina sonta! wani irin so nake mata wanda bantaɓa yiwa wata ɗiya mace ba a duniya son danake mata yasa bazan iya haɗata dake ba, Baraka ma bansan yanda zanyi da'ita ba! idan kinada wani dayake sonki ki basa dama yafuto idan kuma babu ina neman alfarmar ki karɓi tayin soyayyar da Chiroma yai maki"

Da sauri ta ɗago tana kallon Fu'ad har sannan idanunta na zubda hawaye tace "Shi kenan na hakura dakai amma kasani zuciyata tana sonka! nabaka zaɓi ka zaɓarmin Chiroma ko Abdallah ɗan sarkin gombe"

Shuru yayi yana nazari kana ya ce "Ke wanne yafi kyanta maki arai ke zaki zauna da abinki bani zan zauna maki ba tayaya zan maki zaɓi"

"Nazaɓi Abdallah inaso nai naisa dakai bazan iya auran Chiroma ba saboda nasan ko yaushe kuna tare zan rinka ganinka akai akai wanda hakan zai iya haifar min da matsala"

"Shi kenan zanyiwa mai martaba magana ki faɗawa Abdallah ɗin yaturo a tsaida rana kawai" mikewa yayi ya futa, Juhaina tabi bayansa da kallo yana futa ta kifa kan gadon ta fashe da kuka, shi kenan Su'ad ta rusa mata burinta, batajin zata taɓa son yarinyar nan da yaya Turaki ke matuwar so sai tayi duk wani abu datasan zai bakanta mata rai a duk ranar data shigo gidan...


07039793439
[6/11, 9:46 AM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹


Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰


☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA

27&28


Ashe batada rabon auran Turaki ta leko ta koma yayi mata😰kuka take sosai har Umma ta shugo ta sameta, faɗa tai mata sosai tariga tasan son datakewa Turaki.

Shi kuwa a nasa ɓangaran shirinsa yake hankali kwance yau jinsa yake cikin wani irin nishaɗi wanda yajima baijisa a cikiba gefe kuma ga kewar Fahad datake damunsa, a haka yagama shirinsa cikin bakin materi'al mai ɗigon fari, ya kafa hula zanna bukar wacce aka ɗinkata da bakin zare sosai shugar tai masa kyau yasha naɗin rawani baki, cikin kwanciyar hankali da nutsuwa yake tuka motarsa Baby Su'ad na zaune gefansa tana shan ice cream ɗin daya sai mata a hanya, surutu take masa shi sam hankalinsa ba'a kanta yake ba yanaga Su'ad hangota yake da tunanin yanda zasu kaya a karo na biyu shin zata amshi soyayyarsa ko zata ki, a yanda ya fahimceta jiya kamar ta manta da shi Nurein yake ko wa shine a gabanta, tabbas a wannan karon jiyake komai zai faru saidai yafuru amma bazai taɓa bari ta kuɓuce masa a wannan karon ba.

Yau tun safe banida aikinyi sai barci tun goma na safe danai break nasake kwanciya saboda gidan ba kowa saini kaɗai sai hanne mai aikin gidanmu, ina sanye cikin kayan barci dogon wando da riga iya cinya sai hula dana saka akaina barci make sosai sonake na huta kafin huɗu na yamma na shiga shagonmu yau Mami ce acan nasan kuma zuwa yamma zata dawo ni na karɓeta wajan ba laifi sosai muke samun costomer masu zuwa gyaran gashi wasu kuma kunshi ko kitso dan wajan ba abinda bamayi harda kwalliyar amare.

Cikin barci naji ana dukan kofata a hankali, buɗe idona na kalli agogo 11:45 am dirowa nayi daga kan gadon ina turo baki da jin haushin wacce ke bugomin kofa ta katsemin barcina mai daɗi nasanma hanne ce, hakan yasa na buɗe kofar idanuna rufe nake magana ina mika da'alamar barcin bai isheni ba

"Dan Allah hanne maine haka ina barci na mai daɗi harda mafarki kikazo kika tasheni" nakarasa faɗe ina mika tareda buɗe ido zaro idanu nayi😳 ina komawa da baya ganin wanda ke tsaye a bakin kofar cikeda mamaki na ce

"Fu'ad lafiya da safiyar nan?" da gudu wata kyakkyawar baby tazo tarikeni cikin muryarsu ta yara tace "momma kicewa Papi ya maidani wajan Nani na nidai banason nan" rungume yarinyar nayi koba tambaya kamanninta kaɗai sun tabbatar minda yar Fu'ad ce ɗagowa nayi ina kallonsa naga yanda ya kafeni da idanunsa kallona yake bako kiftawa, da sauri na kalli jikina kama hannun yarinyar nayi muka koma cikin ɗakina, nauyayyar ajjiyar zuciya ya sauke ya juya ya koma main falo ya zauna.

Ina shuga ɗaki wanka na faɗa agurguje na futo na bar Baby ita kaɗai cream kawai na murza na zura doguwar riga na tareda hijab na ɗauki Baby muka futo, sosai ta lafe ajikina na ɗago fuskarta ina mata murmushi na ce

"Ya sunanki?"

"Aminatu Su'ad Ameen" lumshe idanuna nayi sakamakon wani daɗi daya ziyarce ni ko tantama babu Fu'ad sunana ya sakawa yarsa.

Wani abu naji yatokaremin a kirji wanda babu ko tantama nasan kishine kenan wata ya aura bayan mun rabo, ashe daman zai iya auren wata inba niba, hamdala nayi a zuciyata tunawa da nayi yanda narinka masa addu'ar Allah yabasa wacce tafini kila Allah ne ya amsa addu'ata yabasa wata, saida na zauna kujerar nesa dashi kaɗan na ɗora Baby a kan cinyata sannan na kwalawa Hanne kira takozo da saurinta

"Hanne kawomin abinci na bawa Baby na tasha hanya ki haɗomin da yoghourt bamai sanyi sosai ba"Baby na ai zakisha yoghourt ko?" na faɗa ina kallon fuskar Baby Su'ad

"Kin manta dani ne?"

"Maizan maka to kaje matarka ta baka" nafaɗi haka ina shafa kan Baby da naji ta shuga raina sosai jinta nake kamar nina haifeta, wasu hawaye suka zubomin dana tuna da tunifa nizan haifi yarinyar nan, da'ace Uncle yanada lafiya da tuni nima kila na haifi kamar wannan,

"Subhanalla wannan hawayan fa, nifa ba kuka nazo kiminba zuwa nayi mu dai daita kanmu sonake na aureki nan bada jimawa ba, Su'ad kamar yanda kika sani abaya haka yake har yanzu soyayyarki tana nan cikin zuciyata"


"Dakata Fu'ad kamanta duk wata soyayya da mukai dakai abaya yanzu babu ita a zuciyata bana sonka bazan iya auranka ba alhalin kanada wata matar wacce nasan ita kafara so kafinni"


"Kema kinsan ba wacce nakeso nan duniya inba keba, kalli Baby Su'ad dake hannunki kawai zai tabbatar maki da kaunar danake maki, dan Allah ki ajje batun wata matata kizo mu sasanta kanmu muyi aure shine burinmu"

Wallahi kaji na rantse bazan aureka ba, tuni na samu wanda nakeso kuma zan aura bazan taɓa yaudararsa ba" ina gama faɗin haka na saɓa Baby a kafaɗa na wuce danning da'ita nabarsa nan zaune, na kula ba karamin haushi yaji ba nan yabarmin Su'ad yai tafiyarsa nayi zaton zai dawo ya ɗakketa amma har yamma shuru harsu Mami suka dawo suna tambayata ina na sami yarinya nagaya masu yar Fu'ad ce.

Fu'ad afusace yabar garin yanajin wani bakin ciki dayazo ya tokare masa a kirji harshi Su'ad zata kalla ta ce bazata aure shi ba, bayan ɗimbin soyayyar dasukayi abaya tun a hanya yafara jin zazzaɓi zazzaɓi da wani ciwon kai da kyar ya karasa gida, wasa wasa saiga ciwo ya kwantar dashi wani irin Zazzaɓi yake mai zafi da ciwon kai mai tsanani, shi kaɗai yake jinyarsa a ɗaki ko mutanan gida basu san bayada lafiya ba sai ranar da Baraka suka sauka a kasar itada Usman da matarsa, gidan mai martaba suka sauka Umma tai mata izinin shuga sashin Fu'ad ɗin bayan taci abinci ta ɗan huta.

Yana kwance lamo kan gado ta shugo ɗakin da sallama, ɗago kai kurum yayi yana kallonta baice mata komaiba yamaida kansa ya kwantar saman fulo, da sauri ta zauna kusa dashi ta taɓa jikinsa taji zafi zau gaba ɗaya ruɗewa tayi

"Abban Su'ad bakada lafiya daman kake zaune kai ɗaya a ɗaki" batajira cewarsa ba ta futa da sauri zuwa sashin Umma ta sanar mata, tare suka dawo ciki hankali tashe Umma ta kira sarkin mota Usman shiya ruko Fu'ad saboda gaba ɗaya jikinsa ya saki bayada wani kuzari, yanda kirjinsa ke bugawa yafi komai ɗaga masu hankali.

Baby Su'ad tana wajena yau kwannanta huɗu kenan mun shaku sosai kasancewar batada wuyar sabo, kullum tanamin zancan Papi zai zo yaɗauketa, dariya nake mata nace kin gaji da zama dani saita girgiza kai alamar a'a, tun ina zuba idanun ganin Fu'ad har nasoma fargabar maiya hanasa dawowa duk da daman na lura ba karamin kular dashi nayi ba, har sannan ba waya a hannuna sau tari data Mami nake amfani data tambayeni ina tawa ce mata nayi a makaranta ta faɗi ban ganta ba, yau satin Su'ad ɗaya a gidanmu tunda ta tashi take kuka ita wajan Papi zata ita nakaita wajan Papinta, jin kukan yayi yawa yasa Mami tace na shirya na maidata garinsu da mamaki nake kallonta na ce

"Mami ni ina nasan wani garin su inma nasa garin nasan gidanne?"

"Ga Shareef nan yana gari ki shirya ya kaiku" ba yanda nayi haka na shiryawa Baby kayanta dana sai mata da tarkacan kayan wasanta, muka doshi garin su Fu'ad tunda muka ɗauki hanya gabana yake faɗuwa haka kurum nakeji ajikina kamar akwai abinda yasami Fu'ad shiya hanasa zuwa ko kuma fushi yayi dani, Allah yasani har yanzu ina son Fu'ad amma banajin zan iya auransa saboda yanada mata son danake masa yasa bazan iya zama dashi yanada wata matar ba, inata wannan tunanin barci ya ɗaukeni har muka isa gidan sarki, bamu sha wahalar shuga gidan ba saboda ganinmu da sukayi da Baby Su'ad, sarkin mota yafara ganinmu ya washe baki yana dariya ya ce

"Hajiya barka da zuwa, kunzo kuma gidan basa nan yanzu Umma ta futa asibitin da Turakin yake" da sauri na ɗago na kalleshi muryata tana rawa na ce

"Baba maiya sami Fu'ad ɗin?"

"E to nadaiji ance ciwon damuwa ne" sarkin mota shiya mana jagora zuwa hospital ɗin

Fu'ad na zaune jingine da fulo Usman yana gefansa ransa a ɓace sai masifa yake "Akan wata banza can kake neman kashe kanka dan tace bazata aureka ba saime, ni ban taɓa ganin irin wannan mahaukacin son ba, basu baka ita ba tana budurwa yanzuma data zama bazawara sai sun tsaya suna ja maka rai kamar itace..."Ya isheka Uthman kasan abinda zaka rinka faɗawa Su'ad itace rayuwa ta ruhina, wallahi a wannan karan na rasata mutuwa zanyi na gaya maka damuwata ne danka taimaka min baka zauna kana gayamin maganganun dazasu karamin ciwo ba, so ba karya bane na tabbata kasan mainene so tunda auran soyayya kayi! Su'ad koda ace ta tsufa mijinta ya rasu wallahi zan iya auranta a ko wanne yanayi take ita nakeso ba wani abu na jikinta ba *itace burina* idan nasameta banida sauran wata damuwa, dan Allah na rokeka kaje ka lallaɓamin ita ta daure ta aureni dan Allah" Fu'ad yafaɗi haka yana saka hannunsa cikin na Usman🤝

Jikin Uthman yai sanyi yana bin ɗan uwan nasa kuma aboki da kallo yama kasa magana sai kafesa dayai da idanu yana kallon yanda hawaye ke zubowa daga idanun Fu'ad hannunsa yaruko zaiyi magana sallamar mu tasa yai shuru da sauri na isa gaban gadon cikeda damuwa ganin yanda Fu'ad yai wata iriyar rama ya kara fari kamar wanda ba jini a jikinsa, ganina dayayi tsaye a kansa yasa ya ce

"Kagani ko Uthman kana kallo tafara min gizo ko Aboki gayamin kodai na haukace ne ita nake gani a gabana dan Allah Uthaman karka tashe ni daga wannam barcin danake ka barni na dawwama tare da ita a cikin mafarki na, hannu ya miko min alamar na matso kusa da shi, ban matsan ba saima komawa gefe danai nasoma kuka

"Kaima mutuwa zakayi kabarni kamar yanda Uncle yatafi ya barni, nifa wasa nake maka ko yanzu ka shirya na amince zan aureka indai hakan zaisa ka farin ciki, kasani ina sonka! inason ganinka cikin farin ciki da walwala kwanciyar hankalinka shine nawa", lumshe idanu yayi tareda maida kansa saman fulo ya kwanta yana mikomin hannu, hannuna nasa cikin nasa ya janyoni na faɗa jikinsa yasa hannayansa ya rungumeni yana sauke numfashi, muna a wannan yanayin har bamusan sanda Uthman ya futa ba, da sauri na janye jikina daga nasa tuna cewa hakan haramunne, Allah yayi hani da haka da sauri na fara furta Astagafirillah na koma can gefansa na zauna ina kallon sa, ya rame sosai sai uban haske daya kara.

"Zubamin abinci yunwa nakeji"

Basket ɗin dake ajje saman fridge na ɗakko na buɗe warmars na zuba masa fatan dankali dayasha hanta da alayyahu sai tashin kamshi yake, na mika masa plate ɗin amma sai yaki karɓa sai hannu yasa ya ɗauki spoon ɗin yafara ɗiban abincin ahankali yana ci ni kuma ina rike da plate ɗin abincin, muna a haka ta shugo da sallama, kyakkyawar maca ce fara kakkaura, tana rikeda da Baby Su'ad sai dariya take mata, take gabana ya faɗi daga gani ba tambayya na tabbata wannan ce matar Fu'ad mahaifiyar Baby Su'ad, zama tayi kusa dashi tareda taɓa jikinsa ta ce

"Dear yaya jikin naka?"

"Da sauki" yabata amsa a takaice yaci gaba da cin abincin nasa, ɗagowa nayi na sake kallonta itama ni take kallo tana aunamin harara.

"Princess bani ruwa" Fu'ad da muryar maras lafiya, atare muka mike da ita na rigata isa gaban fridge saboda yafi kusa dani, ruwan gora na ɗakko masa na ɓalle masa murfin na basa a hannu ya kafa kai ya shanye ruwan tas, plate ɗin abincin na ɗauke wanda shima yaci dayawa na ajje sa saman fridge bayan nasa wani plate ɗin na rufe.

Yanda ta shugo ɗakin cikin nutsuwa da kamala haɗe da cikakkiyar sallama yasa na maida hankali ga dattijuwan matar wacce nake zaton bazata wuce shekaru hamsin da biyar ba zuwa sittin, yanda naga fadawa na take mata baya ga yammata biyu atare da'ita ɗaya na rikeda hand bag ɗayan kuma na rikeda wayoyinta, hakan yasa na gane itace Umma matar mai martaba, hannuna ta ruko tana murmushi ta ce

"Sannu da zuwa Su'ad ɗin Fu'ad yanzu sarkin mota yake gayamin kunzo kun kawo baby Su'ad"

Kasa na zame ina gaidata cikeda girmamawa, hannu tasa ta ɗagoni ta maidani gefan gado na zauna.

"One Boy yaya jikin, sai kuma ga Sweet heart tazo cuta ta warke"

Murmushi kurum yayi sai sannan Umma taga Baraka dake zaune can gaban gadon kan kujera,

"Ran uwargida ya daɗe yaushe kika zo, na baroki a gida kin rigani zuwa,kodan na tsaya duba marassa lafiya a genarel hospital" Baraka murmushi kurum tayi taci gaba da danna wayarta, Umma katuwar dadduma ta shimfiɗa ta zauna nima ta umarceni dana zauna ta zubomin abinci, kasa cin abincin nayi sai danna wayata da nake, shugowar Dr yasa na mike zan futa, dan tun ɗazu nake zuba idanu naga ta inda Yaya Shareef zai ɓullo amma shuru gashi har anfara kiran sallar la'asar, futa nayi ina lalubansa amma babu shi babu alamunsa ko matarsa ma bata inda ya ajjeta, cikeda damuwa nake danna lambarsa harta shuga bugun farko yaɗaga yanamin dariya.

"Yah Shareef ina kaje ne?naga baka compound na hospital ɗin"

"Waini kike tambayya toni kin ganni nan a abuja nafi minti talatin ma da sauka"

Shar shar idanuna suka zubo da kwalla "Yaya zakamin haka ka barni a garin mutane katafi ka barni yanzu yaya zanyi na koma gida?"

"Kinga kwantar da hankalinki motata ma tana nan garin jirgi nabi saboda kiran gaggawa na samu daga office, Umman mai martaba ita tace na barki gobe su Mami zasuzo
End Ads