ido da ido mukai wanda hakan ya haifar min da wani bakon yanayi
Kyauda idanuna nayi daga cikin nasa ina danna wayata Mami nakira na shaida mata tayi bako
"Su'ad bako kuma ba Nura bane"
"E Mami wannan ya ce sunansa Nurein dariya Mami tayi kana ta ce yajirani gani nan a hanya"
Ajje wayata nayi saman kujera na kunna Aljazira ina kallon labarai, shuru nayi ina kallon labaran
Kallona yake yana ɗan murmushi ganin yanda nabada hankalina kacokan wajan kallon "Malama kinzo kin kunnawa mutane kallon saiki fassaramin abinda suke cewa danni dai ba fahimta nake ba"
Taɓe baki nayi ina cigaba da kallona bance komaiba
"Toki canza mana tasha inbazaki fassaramin ba"
Dafe kaina nayi nace "Nifa na gaya maka ban san mai suke cewa ba"
"Ai yanda kika zurawa tibi kyakyawar fuskar nan taki kawai yatabbatar min da kinsan mai suke faɗa" bai jira cewata ba ya ɗauki remote ya canza tasha, zanyi magana kenan Mami da Ameera suka shugo da ɗan tsallanta Ameera ta karaso wajena ta mikomin ice cream
Idanun Nurein akaina yake gaida Mami cikin girmamawa yace "Ma'ma tace nazo na karɓar mata sako wajanki"
"E munyi waya da'ita tace zakazo shiyasa da zan futa nabawa Su'ad ta ajjiye maka" ina kallon ya lumshe idanunsa yabuɗe su akaina, Mami tabasa sakonsa tai hanyar shuga ɗakinta
"Mami wannan Nuran fa bai sha ko ruwa ba balle lemun dana ajje masa"
Juyowa tayi tana kallonsa "Nura nanfa gida ne amma ko ruwa baka sha ba" shafa kansa yayi yana murmushi ya ce
"Mami nagode na koshi ne banjima da shan ruwa ba a mota na"
"Ummm to inma dai ta fulani kayi kai ka juyo" murmushi yayi yamike ya ɗauki ledan kayan da Mami tabasa ya tako zuwa kujerar danake kai yasa hannu ya ɗauki wayata yajima yana dannawa kana ya ce
"Maine pin ɗin faɗamin" yafaɗa da murya kasa kasa
"Nima ban sani ba" nafaɗa ina maida hankalina kan kallon danake, Amira yakira da hannusa suka futa tare da wayata a hannunsa, jimawa kaɗan Ameeran ta kawomin wayata tana dariya "Anty waifa tambayata yayi kinada saurayi,ni kuwa nace masa mijinki ya rasu" ta karasa faɗa jikinta a sanyaye
"Sai yace maki mai kuma" dariya yayi wai damancan da shi kika dace nama basa number ɗinki" wayana kawai na ɗauka na shuge ɗakina.
__________Hannu yabawa Chiroma suka cabke tareda rungume juna, Chiroma ya ɗauki Amina yana shafa kanta ya ce "Baby Su'ad ce yau a kasarmu kinzo kiga takwararki" harara Fu'ad ya zabgawa Chiroma tareda yin gaba ya shuge ɗaya daga cikin tawagar motocin da Mai martaba ya turo su ɗauki Fu'ad ɗin, ko cikin mota hira suke sosai shida Chiroma har suka karasa gida, a compound yasami Umma cike take da ɗokin ganin One boy ɗinta musamman daya sanar mata tare yake da Baby Su'ad, rungumesa tayi tana dariya ta shafa kansa tareda jan kumatunsa kamar wani karamin yaro ta ce
"Ah lalle nayi farin ciki da ganinka gaduk kanin alamu maman baby tana kulawa dakai sosai irin wannan kumatu haka" dariya yayi tareda bin bayanta zuwa ciki tana ɗauke da Baby Su'ad, kai tsaye sashinsa ya wuce yai wanka yaɗan huta har zuwa dare sanda Umma takirasa yazo suci abinci da mai martaba.
"Masha Allah my Son ka girma amma wannan baturiyar tazo kenan bazata koma ba" mai martaba yafaɗi haka yana nuna Baby Su'ad dake kwance saman cinyarsa tana wasa da rawaninsa
Fu'ad zama yayi kasan carfet yana murmushi yake gaida mai martaba dake amsawa fuskarsa sake, tare suka ci abincin suka gama sannan suka gangara hira anan Mai martaba ke cewa Fu'ad
"Al'ameen banason zamanka acan wata kasa nafison zamanka nan kusa dani kullum shekaruna daɗa ja suke girma yana daɗa kamani, ko yaushe mutuwa zata iya ɗaukata in baka kusa akwai matsala, kasani akwai masu harin kujerar nan ni kuma nafi aminta dakai, shiyasa nayi magana da Ummanka akwai babban fili dana sai maka tun kwanaki kadawo ka gina asibiti ka zauna kusa dani hankalina zaifi kwanciya"
Fu'ad shafa sumar kansa yayi wacce ke kwance luf tasha gyara ya ce "Allah yaja da ranka ina godiya amma ni nafison zaman wata kasa can hankalina yafi kwanciya idan ina nan yakan tunamin da abubuwa da yawa waɗanda sun kasa goguwa a zuciyata" yafaɗi haka da raunanniyar murya.
Umma murmushi tayi cikeda tausayi dan tun sanda taji sunan yarinyar Ameen ta tabbatar da har sannan da sauran soyayyar Su'ad a zuciyar Fu'ad "AMEEN Kayi hakuri kamanta komai kadawo kasarka da zama hakan zaifi maka"
"Insha Allah zan dawo Umma" yafaɗi haka yana mikewa dan zuwa cikin gida yagaida sauran matan mai martaba.
Girgiza kai Umma tayi tareda faɗin "Narasa wanne irin so Ameen kewa yarinyar nan ba yakasa mantawa da ita kullum addu'a nake masa amma kamar tiri kalli yanda ya koma da Fu'ad mutum ne mai faran faran ko yaushe fuska a sake amma ni rabon danaga dariyarsa harna manta"
Murmushi kawai Mai martaba yayi ya mike zuwa sashinsa, duk yanda Fu'ad yaso ya zo kano wajan Fahad abin ya gagara ko yaushe suna tare da mai martaba in anka gayyaci mai martaba zuwa wani taro saiya turasa shida Chiroma gaba ɗaya ya gaji shifa saboda haka bayason zaman bare yafi kaunarsa zaman nesa fiyeda gida.
Babban wajene mai kunshe da sashi sashi daban daban wanda ya danganci mata kama da wajan gyaran jiki shagon ɗinki daya tara manyan teloli da sukasan ɗinki yasansu, kayan costumeties, komai da mace ke bukata zaka same sa awajan gefe kuma ga babba wajan cin abinci da babban event, wajan na mami ne bata jima da buɗesa ba nike kula da ɓangaran gyaran jiki na mata wanda aka zuba ma'aikata sosai waɗanda sukasan aikinsu, sosai wajan ya karɓu a wajan mata musamman na yankin mu dama kewaye, sauri nake zan koma gida saboda yamma tayi lokacin tashina yayi, banzo da mota ta ba driver ne yakawoni dan haka na futo bakin titi ina jeran nape, wata mota harta giftani tayo baya ahankali glass ɗin motar yake sauka mamallakin motar ya leko kansa yana murmush ya ce
"Hajiya Su'ad yammata kwana dayawa ko nemana bakya yi"
Ni dariyama yabani ko akanme zan nemesa daga gani ɗaya danai masa to in nemesa ince masa me, buɗemin kofa yayi yana faɗin
"Zomu tafi gidan dama na nufa Ma'ma ta aikeni wajan Maminki" haka kawai naji bazan iya yimasa musu ba na shuga, tare muka shuga gida da Nurein hakan na lura ba karamin daɗi yayiwa Mami ba, wasa wasa saiga shakuwa ta shuga tsakanina da Nurein harya fara bayyana min asirin zuciyarsa tun ina sharesa amma yawan nacinsa yasa na amshi soyayyar sa, kamar da wasa muka fara soyayay mai zafi harta kai ga muna batun aure.
__________Ashirye ya futo cikin da kakkiyar shaddarsa ruwan zuma kallo ɗaya zakayiwa shaddar kasan bata kananun kuɗi bace wani kyalli take da walkiyya mai ɗaukar idanu hannunsa ɗaure yakeda agogo na zallar fata baki, yakafa hular tangaran ta zauna das akan nasa kafafunsa na saye cikin tsadaddan takalmi Haf shoe baki mai matukar kyau, tunda yafuto Jakadiya take binsa tana masa kirari dariya ta bashi sosai yanda take zuzuta sa saida yadara wanda hakan yasa Umma dake zaune a falon ta ce
"Lah yau wacce rana Turaki yana dariya gaskiyya jakadiya nabaki dubu hamsin" guɗa jakadiya tayi wacce tasa Turaki ya toshe kunnansa yana murmushi ya kalli Juhaina dake zaune gefan Umma tayi tagumi tareda zubawa Turakin idanu ba karamin kyau yayi mata ba yau nan take wani abu ya tokare kirjinta, Turaki zama yayi a kusa da'ita ganin yanda ta kafesa da idanu ya ce
"Autar Umma lafiya kike kuwa irin wannan kallon kamar baki sanni ba" taɓe baki tayi tareda mikewa ta shuge ɗakinta faɗawa saman gado tayi ta fashe da kuka, tarasa yaya zatayi da soyayyar Fu'ad ta kasa son ko wanne namiji shi kaɗai takewa wani irin so, wayarta ta ɗauka ta kira lambar Khady tana kuka take cewa
"Deeja na kasa jurewa soyayyar Yah Yarima zata kashe ni yaya zanyi ina zansa kaina naji daɗi, inata kokarin ganin na manta da soyayyarsa amma yau ganinsa ya tada min tsohon mikin son sa daya jima yana addabar zuciyata, nayita nuna masa ta hanyoyi daban daban acan baya amma yakasa ganewa"
"Juhaina ya kikeso ki maida mana hannun agogo baya, ya zakiyi da Abdallah kuma wanda kika amshi soyayyarsa dan Allah ki manta da wani Ameen sauran wata" Khady ta faɗa ranta ɓace
bayanta Turaki yabi ya tsaya bakin kofa yana jiyo maganganunta da khady shuga yayi ciki ya zauna gefan gado saida ya zauna ɗin sannan ta gansa da sauri ta kashe wayan tana maida kanta saman fulo
"Tashi ki gayamin da gaske sona kike mai yasa kike sona?"
Sake ɓoye fuskarta tayi cikin fulo, ganin baza tayi magana ba yasa yamike tareda faɗin
"Shi kenan ni zanje kano na dawo anjima zanzo saiki faɗamin da gaske kike sona zaki aure ni?"
Fucewa yayi daga gidan har zuwa inda tawagar fadawa suke waɗanda zasuyi masa rakiya zuwa kano, zai biya ta masarauta yakai sakon mai martaba.
Sai bayan sallar La'asar Turaki ya shuga gidanmu dake tarauni mai gadi bai tsaya tambaya ba yabuɗe masu get tawagar motocin guda biyar suka shuga ciki, Turaki ya shuga main falo da sallama, gidan shuru kamar ba kowa saida yasake sallama sannan hanne mai aiki ta futo, murmushi tayi dan ta ganesa saidai jikinta yai sanyi sosai dan ganinsa saiya tuna mata da Uncle Fahad mutumin kirki,gaishesa tayi sannan ta wuce ciki ta sanar da su Ummi zuwansa tare suka futo da Mami ya zube kasan carfet yana gaidasu, tuni hawaye yafara wanke fuskar Mami Ummi dake ciccin magani ta ce
"Fu'ad sai yau Allah yakawo ka kai mana gaisuwar Fahad samada shekaru uku da rasuwarsa"
Arazane yaɗago yana kallon Ummi muryarsa tana rawa ya ce "Ummi ban gane ba mai kike faɗa haka ina Fahad"
Mami da har tafara kuka ta ce "Fahad Allah yai masa rasuwa wata biyar da bikinsa yan fashi suka shugar masa gida suka kashe sa"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, la'ilaha illallah muhammadan rasulilla"abinda Turaki yake iya faɗa kenan kafin yafashe da matsanancin kuka..
07039793439
[6/10, 7:37 AM] maman sauban: 🌹 *KUKAN ZUCIYA*🌹
Story and writtin by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Assosuciasion*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of Tha Nation
MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYA
AIMANAH
YANAYIN RAYUWA
AND NOW KUKAN ZUCIYA
25&26
Kuka yake sosai yajima yana kukan wanda kukan nasa ya kuma karyarwa da Mami zuciya ta wuce ɗakinta itama tana kuka,ya jima yana kuka har sanda Yaya Jabeer yadawo yai masa rakiya makabartar da'aka binne Ankul, sosai yai masa addu'a kafin zuciyarsa ta karye yashuga basa hakuri kan rashin zuwansa, kamar wani mahaukaci haka yake zaro zance naban hakuri kamar wanda yake magana da yarayyan mutum, har saida Yaya Jabeer ya rukosa suka futo zuwa wajan mota har sannan kuka yake, bayan sun dawo gida Abinci Ummi ta kawowa Fu'ad ba yanda zaiyi haka yafara tsakurar abincin dan yafaɗawa Ummi shifa a koshe yake amma ta kafe saiya ci, zuba idanu yake yaga gilmawar Su'ad amma shuru ba alamarta, kunya tasa yakasa tambayar ina take, gabansa yabuga da karfi har saida yasa hannu ya dafe kirjinsa ya lumshe idanu yana addu'ar Allah yasa ba wani auran tayi ba, tabbas idan akace Su'ad ta auri wani bayan Uncle to kuwa ya cika mara sa'a a rayuwa, lumshe ido yayi tareda kwantar da kansa saman seater yanajin zuciyarsa naci gaba da bugawa kamar zata fasa kirjinsa ta fito saboda fargaba.
Tun daga bakin gate na gidanmu nasan yau munada babban bako ganin manya manya motoci acikin gidan, can gefe na faka motata Ameera ta kalleni da alamar tambaya ta ce
"Anty yau wa muka samu a gidan nan yacika da fadawa haka?"
Ban bata amsa ba sakamakon gabana da yai wata irin faɗuwa, na futo daga motar na ruko laidar hannuna dana siyo mana yoghurt Ameera tuni ta shuge ciki ni kuma saida na tsaya na kulle motar sannan na shuga zuwa ciki, lumshe idanuna nayi saboda wani daddaɗan kamshin turare dana shaka tabbas nasan kamshi nan amma na rasa a inda nasansa, cigaba nayi da tafiya har zuwa falo na uku inda komai nawa ya tsaya cak na wucin gadi sakamakon idonsa daya shuga cikin nawa ledar hannuna na saki sannan na wuce ɗakina da gudu ina sakin wani marayan kuka😥ganinsa danayi yatuna min da masoyina Fahad, sosai nake kuka har zuwa sanda Ummi ta shugo ɗakina
"Wai wannan kukan na menene najin daɗin ganin Fu'ad ne kona me?"
"Ummi Uncle! dana gansa sai naga kamar zan gansa tareda Uncle ɗina,ban saba ganinsa shi kaɗai ba ko yaushe zan gansa yana tare da Uncle ɗina, Ummi da gaske Uncle yatafi kenan bazai kuma dawowa ba?"bazai sake rayuwa tare damu ba?"shi kenan mun rabu, bazan sake ganin saba bare naji ko muryarsa!"
"Su'ad zaki fara ko, to kije sitting room Fu'ad ɗin yana can zai maki gaisuwa"
"Gaisuwa kuma Ummi shekara nawa da mutuwar Uncle maiya hana sa zuwa sai yau yaga damar zuwa"
"Idan kikaje sai kiji dalilinsa na kin zuwan" tana gama faɗar haka ta fuce daga cikin ɗakin, ban futa ba har saida Amira tazo tace "Ummi tace lalle ki futo wajan Uncle Fu'ad karta shugo ta sameki"
Da sauri na ɗago na kalli Ameera sai kuma na duro daga gadon na yafa mayafina na fuce daga ɗakin.
Zaune na same sa ya saka kansa cikin kafafuwansa sallamar danai tasa ya ɗago yana kallona da jajayan idanunsa dasuka sha kuka, kujeran dake kallon wacce yake kai na zauna batare da na gaidashi ba dan Allah yagani batun yau ba nakejin haushin Fu'ad saboda nasan yanda suke da Fahad bai kamata ace har zuwa shekarun nan baizo gaisuwa ba.
"Ashe Fahad mutuwa yayi?"mai yasa ba'a gayamin ba?"ina can ina rayuwa ashe nayi rashin aboki amini ɗan uwa"
"Ashe dama ka damu dashi ainazaci daka damu dashi daka nemesa a tsawon wannan lokacin"
"Bana kasar nan Princess ina london shekaru uku kenan, yanzu hakama saboda shi nabaro tarin ayyukan dake gabana nazo kawai danna gansa saboda ina kiran lambobinsa basa shugowa, gaya min ina yan fashin da suka kashemin aboki an yanke masu hukunci"
"E! an yanke masu, amma Zainaba har yanzu tana raye a gidan yari"
"Maiya kawo Zainaba cikin wannan zancan" komai daya faru na kwashe na gaya masa, idanunsa yai ja sosai alamar ɓacin rai ya ce "Matsalar kasan nan kenan shi kenan ita baza'a kasheta ba yanzu ba time damunje gidan yarin amma zan dawo nan da friday yazama dole akashe ta kamar yanda takashe min aboki" mikewa yayi yana kallona ya ce
"Zan koma sai...shuru yayi bai karasa ba sakamakon shugowar Ameera ta miko min wayata tace "Anty gashi Yaya Nurein ke kiranki" amsar wayar nayi ita kuma ta futa, kara wayan nayi a kunnena ina murmushi
"Ina kika shuga kika bar wayarki inata kira?"
"Nayi bako ne ina sitting room nabar wayan a ɗakina"
"Bako Su'ad maiyazo yi wajanki" murmushi nayi ina kallon Fu'ad ta gefan ido ganin yanda ya kafeni da idanunsa yana aunamin wani kallo dana kasa gane na mene, hakan yasa na kara narkar da murya cikeda shakawaɓa na ce
"Kai Hubby maine na damuwa abokin Uncle ne fa yazomin gaisuwa kaima kasan babu wani a zuciyata inba kai...ban karasa ba naga Fu'ad a kaina yana huci ya fisge wayar yasa ta a aljihunsa yafuce daga ɗakin a fusace, murmushi nayi inabin bayansa
"Kabani wayata nidai" bai juyo ba yaci gaba da tafiyarsa ina biye dashi har mukaje falon karshe, saida yakama handling na kofa ba tare daya juyo ba ya ce
"Karki sake naga kafarki a compound wallahi sai ranki ya ɓaci harni zaki rainawa hankali a gabana kina kiran wani da Hubby"
Dariya yabani sosai amma na maze nace "To naga mijina ne sainaki kiransa da Hubby dan kana wajan nidai ka bani wayata in kuma baka da wayane tona bar maka" juyowa yayi ya kalleni yai kwafa tareda girgiza kai yafuce da sauri, dariya nayi nima na juya zuwa ciki ina murmushi...
Tunda yashuga mota ransa ke ɓace ko kallon Chiroma dake masa hira baiyi ba yana kallo kiran Baraka yana shugowa harya katse bai ɗagaba sai dare sosai suka shuga garin nasu dan suna tsaya yin sallar mangariba da insha data riskesu a hanya,yana shiga gida wanka yayi yai shirin barci sai sannan yakira Baraka bugun farko kuwa ta ɗaga kamar daman jiran kiran nasa take, gaishesa tayi kana ta ce
"Dan Allah Abban Su'ad zan biyi su Usman zasu taho nageria duk zaman nan bayamin daɗi gashi kai har yanzu baka dawo ba kusan satinka biyu kenan"
"Bance ki tawo ba ki zauna nima na kusa dawowa" rokonsa tashugayi hardai ya sakko ya barta ta biyo Usman ɗin su tawo tare, yana ajje wayar ya ɗauki wayar Su'ad duk yanda yaso ya gano pin ɗin scirity dake jiki kasawa yayi sai ajje wayar yayi da niyyar gobe zai bawa Chiroma asan yanda za'ayi a cire masa scurity ɗin jiki.
Nikam tunda na koma ɗaki nake cikin nishaɗi wanda na rasa na menene fushin da Fu'ad yayi yatabbatarmin da har yanzu yana sona saidai niɗin ina sonsa har yanzu tambayar danaiwa zuciyata kenan inma ina sonsa ina zankai soyayyar Nurein anya inna juya masa baya banci amanarsa ba, amma to Fu'ad har yanzu bayada aure ko yanada shi kilama bayan mata harda yara, shuru nayi tareda jan uban tagumi anan har Ameera ta shugo ta sameni,wayar Mami ce a hanunta ta ce
"Anty Game fa nake amma Nurein sai kira yake Mami tace nakawo maki ina kika saka wayarki?" amsar wayar nayi na kirasa tambayar daya faramin
"Ina wayarki?"maine tsakaninki da Turaki Fu'ad an tabbatarmin shine yazo gunki yau"
Murmushi nayi inabin wayar da kallo nace "Wayata ta faɗa ruwa, Fu'ad kuma banida wata alaka da shi a yanzu kawai yazo gaisuwar abokinsa ne"
"Abaya akwai wata alakar kenan?" ya tambayeni ransa ɓace bai jira amsata ba yaci gaba da magana "Su'ad gaskiyya bazan laminci ganinki da wani ba kibani dama kawai na turo manya na indai da gaske kike sona kuma zaki aure ni"
"Amma kasan tsakanina dakai ba yaudara ko?"
"Ki tabbatarmin da hakan ta hanyar bani izinin turowa gidanku a saka mana rana"
"Naji to na amince ka turo ɗin" kashe wayar yayi tareda mikewa zuwa ciki