x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 1 - KUKAN ZUCIYA

  • 1 words
  • 3000 words
  • Out of 38354 words

Category: Tale Stories

Views 32

09 Aug 2025
Start ads
After Image Ads

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[6/4, 7:46 PM] maman sauban: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GMAOuujeP6dLtFTHo1Edxx


🌹 *KUKAN ZUCIYA* 🌹


Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰


☀️ *First Class Writer Assosciasion* ☀️


Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

MARUBUCIYAR
HALIN RAYUWA
SOYAYYA DA ZUMUNTA
SANYIN IDANIYYA
AIMANAH
AND NOW KUKAN ZUCIYA

1-2
Safa da marwa kawai take a ɗakin gaba ɗaya hankalinta yaki kwanciya tunda Prince AMEEN ya shiga wajan Abbi zuciyarta ta gaza nutsuwa so take taji mai zasu tattauna gaba ɗaya a Jiya zuwa yau xuciyarta ba daɗi tun da Prince yadawo daga CANADA tasan cewa tayi bankwana da kwanciyar hankali itakam ta matukar tsanar Prince AMEEN inama inama inama itama tana da ƴaƴan nan da tabbas saita shiga ta fita taga Prince bai sami sarautar nan ba tabbas a yanzu ma sai tayi duk abinda zatai wajan ganin ta ɓata masa suna ta yanda masarauta zasu hanasa sarautar "Ya zama dole naga bayanka Ameen ko zanyi yawo tsirara saina ga bayanka Ameen", jin karar tafiya ana sakkowa daga bene yasa tai saurin komawa kan kujera ta zauna ta fara tsinkayo muryar dogari na faɗin "Gaba salama baya salama a lafiyar takawa Prince Amin amanar mai martaba taka lafiya jikan sarki Abdulmunab" dai dai sannan Prince ya gama sakkowa nan falon inda Hajiya Jameelah ke zaune "Barkanmu da safiya Anty" Prince Ameen ya faɗa yana daga tsaye nan kafar benan, ɗan taɓe baki Anty Jameelah tayi kana ta ce "Barka dai sannu da fitowa" tana gama faɗar haka ko amsa mata baiyi ba yasa kai ya fice daga falon, da sauri dogari ya buɗe masa murfin mota ya shiga yana masa kirari, saida suka hau kan titi sosai sanan sarkin mota ya ce "Ranka yadaɗe ina muka dosa?"
"Masarauta" yafaɗa a dakile yana wani haɗe rai, har suka karasa gidan sarautar bai ko kara magana ba danna wayarsa kawai yake hankali kwance yana hakimce a bayan motar, suna parkin da sauri dogari ya fito daga tasu motar da take takewa tasu Yarima baya ya buɗe masa murfin motar ya fito "Kai tsaye sashin Fulani ya nufa yai sa'a kuwa tana nan part ɗin nata bata shiga wajan takawa ba, zama yayi kan lallausan kafet ɗin dake malale cikin ɗakin yana ɗan rusunawa ya ce "Barka da Hutawa Umma fatan na sameku lafiya"
Numfashi ta sauke zuciyarta fal farin ciki yau gata ga Aminunta kusa da ita tsawon shekaru goma kenan daya gudu CANADA yaki dawowa "Lafiya kalau ka same mu One Boy ya gajiyar hanya baka bari mun gaisa ba da safe ka fita ba sanarwa sai da na ce wa JAKADIYA ta kai maka break fast ta dawo ta sanarmin ka fita"
"Naje wajan Abbi ne ranki ya daɗe inya koma kafin mu haɗu za'a jima shi yasa nai sakko ayi min Afuwa FILANIN MAI MARTABA"
"Anyi maka ONE BOY yaka baro su? ya Hajiya Jamila fatan ka baro su lafiya"
"Lafiya kalau" yafaɗa yana bin Juhaina da kallo wacce ta fito yanzu daga bedroom ɗinta
"Yaya Ameen barka da Safiya" JUHAINA ta faɗa da wani iri sauti mai jan hankali
"Barka dai Juhaina ya school da fatan dai kina kokari sosai"
"Inayi sosai ma Yah"
"To da kyau Allah ya taimaka, Ranki ya daɗe in Allah ya kaimu gobe zan kaiwa Abokina FAHAD ziyara mun jima bamu haɗu ba fitar safiya zanyi sabida mu isa da wuri"
"Allah ya kaimu Ameen amma da kabi jirgi daga garin nan zuwa garinsu FAHAD akwai tafiya fa zaku iya shafe yini guda kuna tafe fa"
"Sarkin Mota yace na tafi da Yunusa dogari ya iya tuki sosai"
"Cewa zakayi zaku tashi sama, to Allah ya tsare gobe HIDAYA nada manyan baki koda yake nasan ka haɗu da FAHAD sai yanda hali yayi kilama ka kwashe kwana biyu a can batare daka lega wajan HIDAYA ba"
"Baza'ayi haka ba insha Allah" yafaɗa yana mikewa tsaye
"A huta lafiya UMMANA Zan shiga wajan Mai martaba daga nan zan shiga wajansu Momy Da Mama mu gaisa" yafaɗi haka yana ɗan risinawa alamar girmamawa
"Afito lafiya" Umma ta faɗa tana murmushi

Washe gari sassafe Prince Ameen ya ɗauki hanya gudun da sukai sosai yasa suka shiga garin bayan sallar la'asar gidansu FAHAD ba bakon gida bane a garesa amma dai a wannan karan ya kasa gano gidan a shekara goma dayai baya kasar harya manta gidan,
Prince Ya jingina a jikin motarsa kyakkyawane ajin farko wajan haɗuwa fari ne tas mai doguwar fuska wacce ke ɗauke da dogon hanci irin wanda ake kira da har baka ɗin nan, sumar kanshi wacce take baka kirin tasha gyara sai sheki take da walwali tayi luf luf kwance akan nasa kallo ɗaya zakayi masa kasan ya haɗa jinsi da larabawa, yana sanye da bakar shadda yar gaske mai sheki da walkiya hular kansa tangaran wacce tai matukar dacewa da shaddar jikinsa.
Ahankali yake danna tamfatsetsiyar wayar dake hannun sa, fuskar nan tashi murtuk da ɓacin rai yakusa minti goma a tsaye a wajan yana neman layin abokinsa amma bata shuga a karo na karshe yasake kira yayi sa'a wannan karon ta shuga amma harta gama ring ba ba'ayi picking ba, sake jingina yayi da jikin motar shi escape baka mai matukar kyau da tsada, kamar baya so ya buɗe back seat ya zauna yana kallon driver ɗinsa cikin raunananniyar murya ya ce

"Yanzu in muka ɗau hanyar komawa gida sai tsakar dare zamu sauka ko, har yanzu bai ɗaka wayar ba nakasa gane gidan" cikeda ladabi driver ɗin

Ya ce "Yallaɓai kadai sake gwada kiran kila yana wani uzurin ne shiyasa bai ɗaga kiran ba"

Yarima Ameen baiyi musu ba yasake kira saida kiran yakusa katsewa kana aka ɗaga cikeda ɗoki AMEEN ya ce "Hello freind yakake"

Daga ɗaya ɓangaran aka amsa da "Lafiya kalau amma ban gane mai magana ba"

"Da gaske ka manta ni Al'ameen Muhammad Bello Fu'ad"

Wani ihu ɗayan yasaki kamar zai fasa wayar ya ce "da gaske amma naga kamar da lambar nageria ka kirani yaushe ka shugo kasar tamu"

Fu'ad yana murmushi yace "Najima yanzu haka ina cikin unguwar ku dai dai asibitin nan amma nakasa gane gidan"

"Ok jurani bari na turo a tafi dakai ni ina airport naje ɗakko Daddy da Ummie sun dawo daga cairo bari naiwa Su'ad waya tazo ta karasa dakai gida"

"Ok ina jira" yafaɗa tareda kashe wayar yana gyara zaman sa a cikin motar.

Ina zaune gaban madubi ina tsara kwalliya ta murnar dawowar Daddy na daga Cairo, nagama saka kayana kenan ina ɗaura ɗan kwali najiyo muryar Mamina daga kicin tana kaɗamin kira, "Su'ad! Su'ad!! Su'ad!!! kina ina ne?"

Da sauri na futo zuwa kicin ɗin inda na tarar ta tsaye tana saka lemun data gama haɗawa a cikin frezeer, batare data kalleni ba tace "Ga wayan ki nan kin barta anan tun ɗazu kira ke shugowa"

Wayar na ɗauka tareda karawa a kunne na ina murmushi ganin Uncle Fahad ne ke kiran nawa cikeda karaɗi irin nawa nace "yeee su Daddy sun sauka ko"

"Kee sarkin karaɗi karki kashemin dodon kunne kije nan bakin layin su kawar ki Ameera akwai abokina dayazo yakasa gane gidan ki kawo sa gida muma gamu nan tahowa tun ɗazun jirgin nasu ya sauka"

"Ok" kurum nace masa sannan na kashe wayar na koma ɗakina, yau garin akwai sanyi sosai hakanne yasa nasa jibgegiyar rigar sanyi na mai tsayi da kauri, duk tsayina amma rigar sanyin saida ta kawomin har gwiwa ma saka baby hijab tareda saka plate shoe nafuto zuwa dinning inda na hangi Mami tana shirya warmars a saman danning ɗin.

"Mami zanje bakin titi Uncle ya ce yanada bako a can na karaso dashi gida"

"Ok saikin dawo karki manta da addu'ar fita, in kuma baki gansa ba ki dawo karki daɗe"

"TO Mami" nafaɗa ina fucewa daga third falon zuwa seceound falo, ko'ina kamshi ne kawai ke tashi murmushi nayi ina karasa futa daga first falo, zuwa compound, saida na gaida sojojin dake tsaye baki get kana na futo, seteven na tsokana ta ina zani bayan Daddy yana hanya, dariya kawai nai masa harya buɗemin kofa na futa, ahankali nake tafiya cikin nutsuwa irin tawa kamar yanda nasaba tafiya, mutane dayawa idan sukaga yanda nake takuna sai su zata yanga nake ni kuma sam ba haka yake awajena ba tun tuni haka nake tafiya tun ina yarinya kamar yanda naji Mamina na faɗa idan su Uncle da yaya Jabeer sun tusoni a gaba suna tsokana.

Harna karasa inda Uncle Fahad yagayamin banga kowa ba, hasali ko mota ɗaya babu, hannuna nasa cikin aljihun rigar sanyi na na ɗakko wayata na kira Uncle Fahad ina gaya masa gani a wajan amma banga kowa ba, kashe wayan yayi kusan mintina uku wata bakar mota ta faka a gabana

Sosai motar tabani tsoro ganinta baka wuluk sai walwali take, glass ɗin motar tinting ne shiyasa baka ganin wanda ke ciki.

Kafar sa yafara sakowa waje kafin ya futo gaba ɗayan sa, subhanallah nace a fili ganin yau gani ga balaraben kasar saudiyya sam banyi zaton yanajin hausa ba shiya sa bance masa kala ba, yajima yana kallona kafin naji muryar sa mai daɗin sauraro kamar bayason magana

Yace "Are you Su'ad?" ya tambayeni yana taɓe fuska kamar yaga kashi

Ina girgiza kaina nace "Yess i Su'ad" taɓe baki yayi kana

Ya ce "Amma kika tsaya ɓatamin lokaci dan Allah wuce ki kaini gida"

Nidai sakin baki nayi ina kallonsa yanda naji yayi hausa raɗau,kin shuga motar nayi har sanda nafara jiyo jiniyar motar yan sanda motace Hilox baka cikeda yan sanda da bindigogi sai wata farar mota a tsakiya sannan wata Hilux ɗin shake da yan sanda har sun gifta mu naga sunyo baya sun tsaya dai dai inda nake da sauri ɗaya daga cikin yan sandan yadiro daga saman mota yabuɗe murfin karamar motar da suka sako a tsakiya,Yah Mukhutar ya fito daga motar yafara takowa inda nake tsaye, kamewa nayi ina binsa da kallo harya karaso inda nake na sara masa tareda faɗin
"Ouwr wellcome sir"
"Wellcome Su'ad mai kike tsaye anan wajan"
Uncle FAHAD ne ya ce nazo na tafi da bakonsa gida" hannu yaya Mukhtar yabawa bakon balaraben suka gaisa kana ya umarce sa daya shuga motarsa, ni kuma ya tusa keyata zuwa tasa motar inda na tarar da babbar yayarmu Fateema zaune aciki, itama tambayata tayi mai nake tsaye a bakin titi, nabata amsa kamar yanda na bawa mijinta, ba jimawa muka koma gida na shuga ciki hannuna ɗauke da Sajad ɗan Anty Fatima, "Ke kuma ina kika samo wannan yaron" Mami ta tambayeni tana amsar Sajad dake hannuna, kafin nabata masa Daddy ya shugo wani tsalle nayi na ɗane Daddy ina masa sannu da zuwa tareda tambayar sa yaya jikinsa.

Ummie dake biyeda bayan Daddy ta daka min tsawa tana faɗin na sakesa banga bashida lafiya ba, niko ko sauraron ta banyi ba naci gaba da makalkale Daddy na da shima yake murnar ganina yana faɗin "Auta me Mamie take baki ne naga kin yi kiba kamar ba keba" dariya nayi ina bin kofa da kallo ganin shugowar Uncle Fahad da bakon balaraben sa, da gani zakasan ba karamin farin ciki sukayi ba da ganin juna ba, nifa har ga Allah mamaki bakon nan ke bani yanda naji hausa raɗau a bakinsa kamar jakin kano😂 yana gaida su Daddy yanda suke amsawa cikin sakin fuska ya tabbatar minda sun san sa, bayan sun gama gaisawa kai tsaye Uncle Fahad yaja hannun balaraben bakon sa suka wuce sashin samarin gidan mu.

Mami ce ta umarceni dana kaiwa su Uncle Fahad abinci, nakuwa ɗauka zuwa ɗakin sa suna baje saman bed sai hira suke, nayi sallama na shuga ina ajje warmars ɗin hannuna bakon balarabe ya kalleni kallon dana kasa fassara sa wanda ban cika ganin irinsa awajan kowa inba Uncle ɗina Fahad ba "Wai da gaske wannan Su'ad ce ta girma haka?" bakon ya tambayya yana kallon Uncle Fahad, zama nayi a kan kujera ina kallon Fahad dan naji amsar da zai basa ai kuwa naji yana faɗin

"Itace mana kaga tazama yammata ko?" ɓata rai nayi ina kallon Uncle Fahad batare da nace komai ba, nasaba sosai da Uncle Fahad kusan komai tare mukeyi dashi kama daga cin abinci buga kollon kafa ya kaini makaranta ya ɗakkoni, dan duk cikin samarin gudanmu banida Amini kamar Fahad, ganin zaman danai na jiran yazo muci abinci ne yasa yace "Yau inada bako bazanci abinci dake ba kije kuci tareda Daddy ko Ummi" na ɓata rai tareda mikewa ina faɗin "Ai dai bakon naka zai tafi! zaka dawo ka same ni, ni kuma a sannan zan canza Amini na komawa yaya Yazeed" ina gama faɗar haka na fuce a fusace ina bugo masu kofa, murmushi Fahad yayi yana bin Fu'ad da kallo ganin yanda yabi Su'ad da kallo harta futa bai kawo komai a ransa ba yace

"Kaganta nan yar rigimar gidan nan kenan haka take hukuma ce ita saida lallashi" murmushin gefan baki Fu'ad yayi batareda ya kalli inda Fahad yake ba yana sauke ɓoyayyar ajjiyar zuciya.

Kwanan Fu'ad biyu a gidanmu bana shuga sabgar sa haka shima bai shuga tawa, ko gaisuwa bata taɓa haɗamu ba, haka kurum dai inason ganin sa shiyasa sau tari nake zuwa wajan Uncle Fahad innasan suna tare, wasa wasa nafara gane son bako ya shuga zuciyata.

Mami tana zaune a bedroom ɗinta na shuga da sallama zama nayi kusada ita ina wasada zoben hannuna da Uncle Fahad ya kawo min kwanakin baya dayaje Saudiyya umara

"Mami wannan bakon balaraben wai a ina Uncle ya samo sa yazo ya zaunawa mutane a gida duk ya hanamu sakewa nida Uncle ɗina" mami kallona tayi tana murmushi "Abokin Fahad ne tun zamanin scoundry harma da jami'a, shekarunsa goma kenan yana CANADA acan yake aiki tun bayan kammala karatun su na jami'a Ƙanin mahaifinsa yasamar masa aiki a can" mikewa nayi na koma ɗakina ina shirin tafiya makaranta yau lacture ɗin yamma nake da'ita, tsab nagama shirina cikin doguwar rigar Atamfa kamar yanda na saba nayi kusan rabin kayana duk dogayan riguna ne acewar Uncle Fahad wai doguwar riga tafimin kyau shiyasa in muka kai ɗinki kannace komai yagayawa telor ɗin amin doguwar riga, tun ina mita harna saba koni ɗaya nakai ɗinki ita ɗin nake cewa amin saboda ina son duk abinda Uncle ɗina keso, kamar yanda shima yake son abinda nakeso, rolling mayafi karami nayi na futo ina baza kamshi, Uncle na tarar a falo shida bakonsa wanda yakafe ni da lumsassun idanuwansa kamar na maijin barci, harna karaso na zauna hannun kujerar da Uncle ke zaune akai

"Kinyi kyau besty irin wannan tashin kamshi haka sai ina?" "Uncle inada lacture yau na shirya ka tashi ka kaini"

"Besty futa nakeson nayi a hospital inada feshan amma bari na ajje ki inyaso in kika tashi zansa Seteven ya ɗakko ki" mikewa mukai atare muka jera zuwa wajan adana motoci na gidanmu.

Ahankali Uncle ke tukin motar kamar bayaso yanayi yana kallona wani bin yayi murmushi wani bin ya kashe min ido ɗaya nidai bance masa komai ba harya ajjeni cikin school ɗinmu yana ɗagamin hannu har yabar harabar makarantar tamu, jinai an ruko hannuna na juya da sauri ina kallon kawata Ameera dake min dariya

Tace "Nakasa gane maku keda Uncle Fahad kamar wasu masoya ko yaushe kuna tare jibi yanda yake wani ɗaga maki hannu yana kashe maki idanu kamar yana gaban budurwar sa" dariya nayi tareda soma tafiya ina faɗin "Ina kikaga Amini ya koma masoyi akwai abota mai karfi a tsakaninmu shiyasa kowa yake mana kallon masoya amma ni
End Ads