Qarfe goma aka Isa da lailah airport acikin wata sirrantacciyar mota
Lokacin afia tafi mintuna ashirin agurin tana jiran isowarsu Dan Haka tana ganinsu ta fiddo doguwar jallabiya da Dan qaramin mayafi da goggles datazowa da mum din Tata dashi ta nufi motarsu itama tata fuskar Bata bayyanataba yanda za'a gane itace ta bude motarsu ta shiga baya inda mum dinta ke zaune tana kakkama jikinta tayi wani duhu cikin kwana biyu ga wani irin tsamin dauda da wahala na tashi ajikinta
Cikin tsananin baqin cikin ganinta Haka da kaunar mahaifiyarta me qarfi afia ta rungumeta gabaki daya tana cewa"
Mum.
Zarewa Lailah tayi ta kurawa afia ido idanuwanta na cikowa da hawayen tsananin baqin ciki da dumuwa tarema da tsoron halinda rayuwarta tashiga kokuma ma Wanda tariga tashiga,
Ahankali ta bude Bakinta dake rawa wani tsamin Baki ya feso yacika motar Amma afia ita Sam batama jisa sbd Babu abinda uwarta zata zama ta gujeta da rawar murya tana hawaye tace"
Afia,afia my baby,afia my little princess I'm sorry baby ki yafewa mum dinki Amma ki yarda Dani bantaba aikata kisa ba Kuma bazan taba aikatawaba...ban aikata ba...bazan taba iya aikatawaba...ban aikataba...banyiba...
Riqota afia keyi tana cewa"
Mum mum na yarda Baki aikataba
Mum na yarda
Na yarda mum".ganin mum din takasa daina fadar Bata aikataba cikin firgici Kamar lokacin abin ke faruwa yasa afia rikicewa tana korarin kwantar Mata da hankali cikin kulawa hankalinta na neman tashi sbd ganin alamun kaman mum din har lokacin tana cikin shock saidai Kuma....
Imran ne cikin hali na damuwa daya shiga akan lailan tun lokacinda Mr Omar yayi Masa bayanin komai gameda Dan tabuwa da kan lailan yayi sbd Shiga hali na shock lafiya zata ringa komai Kamar yanda take sai dai idan ta tuno abindaya faru na kisan abin zai dawo Mata zata fara fizgewa tana fadar ba ita tayiba cikin tsananin tsoro da firgici,
Shi kansa bazaiso afia tasaniba sbd hankalinta zai tashi yakoma kan kula da neman lafiyar mum dinta bazata taba maida hankali kan karatuntaba Kuma Dan Haka shima ya shirya kula da al'amarin bazai Bari tasaniba yanzu sai tagama kammala karatunta tsaf yanama fatan zuwa lokacin lailan tasamu lafiya Dan Haka shima ya yanke shawaran komawa Vegas gabaki daya zai zauna da lailah Dan nema Mata lafiya ta dawo daidai ta gyara rayuwarta ta ingantata yanzu kan tunani da hanyar dazata bullar da ita sbd Lailah tamkar uwa ya dauketa Dan kuwa itace wadda tafi sonsa aduniya bayan iyayensa sbd itanema yake Paris baibi iyayensaba Koda tabar maleek dasu afia Basu rabu ba shida ita Kuma sbd itane yake tareda maleek Yana aiki a qarqashinsa farko sbd ya kula dasu farhat dasuka shaqu.
Ajiyar zuciya ya sauke ahankali tareda fitowa ya zagayo yashigo bayan ya zauna dayan gefen lailan suka sanyata tsakiyansu ya dago ya kalli afia data fara shiga firgici cikin kulawa da kwantar Mata da hankali yace"
Tana cikin damuwar abin daya faru sbd case na zargin kisa wani abune da bakowa ne zai iya daukaba
Dole zata shiga wannan halin musamman yanzu data fito Kuma taganta agabanki Dole zataji wannan damuwar da shauqin son sanar dake ba halinta bane.
Hawayene suka gangarowa afia ta rungumeta tana sakin siririn kukan tausayin mum dinta ta dago tana kallonta tace"
Mum Inshallah komai yariga ya wuce bazai sake dawowaba
Ki yarda da wannan wata jarabawace Allah yayi Miki danki gyara Kuma Inshallah nasan kin gyara mum kimin alqawarin bazaki sake zuwa gizah ba sbd bakida abinda yarage Miki anan sai tarihi.
Kallon afia kawai lailah keyi da idanuwanta dasukai jajir tanajin radadin abubuwa da dama data rasa arayuwarta sanadin son zuciya da son Rai,
Ta rasa MALEEK namijin da bazata taba samun kamarsa ba a fagen komai Dan kuwa ya nuna Mata so da kauna da gata da kulawa da komaima Amma duk ta watsar ta tsallake a tunaninta zai zauna dakon jiranta,
Ta rasa Farhat dinta yarinyar da Bata morewa komai na soyayya ko kulawar mahaifiyaba da shaquwa Dan kuwa tasan NURU tariga tashiga ran farhat ta yanda bazata iya rabuwa da itaba ko yiwa wani kallon uwa idan ba NURUn ba,
Ta rasa darajarta,sunanta,mulkinta, dukiya da career dintama gabaki daya
Afia ce kawai abindake gareta yanzu sai Imran datasan har abada shima bazai gujetaba adaidai yanzu datafi buqatan masoyanta atareda ita.
Kama hannun afia tayi ahankali hawayenta suka gangaro kan fuskarta ta kalli afian tareda gyada Mata Kai tace"
Nayi alqawarin Inshallah bazan qara zuwa gizah ba sbd Nima na tabbatarda banida sauran komai anan sai tarihi Wanda bana alkhairi ba Dan kowa zai ringa tunoni amatsayin wadda tayi kisa labarinta ya Bata.
Sake karyewa zuciyar afia tayi da tausayin mum dinta ta yanda lokaci daya ta rasa komai Kuma tana fatan zatai tawakalli ta karbi hakan.
Kayan data shigo Mata dasu ta Sanya Mata tareda rufe Mata fuska ta Sanya Mata goggles din ta bude motar suka fito dukkaninsu ta sake damke hannun mum din cikin kulawa da qauna ta tsakanin 'da da mahaifi tace"
Mum ki kula da kanki Zan ringa kawo Miki ziyara lokaci lokaci kinji¿
Allah yayiwa rayuwarki albarka afia
Allah yabaki 'yayan dazasu San darajarki irin Haka da Miki biyayya.
Amin tace ahankali tana dagowa ta kalli Imran tace"
Mum na hannunka.
Guntun murmushi ya saki Yana gyada Kai yace"
tana hannu mekyau.
Murmushin yaqe tayi tana cewa"
Thank you.
Kama hannun lailan dake waiwayen afia tana daga Mata hannu yayi suka wuce itama afian tana musu har suka bace Mata ta saki numfashi a hankali tanajin nutsuwa ta juya ta fada motar da kanta ta jawo ta tada taja tabar airport din.
Ko data koma sashenta ta nufa sai alokacin tasamu nutsuwar cin abincin data manta rabon dataci
Taci ta koshi ta miqe ta wuce bedroom dinta tayi sallar azahar ta kwanta Dan tasamu baccin dazai qarasa wargaza damuwarta Dan kuwa dukkanin damuwarta ta yaye takeji.
NURU zazzabi yakamata sosai Wanda ya Hana musu bacci da daddare daga ita har maleek din sbd sosai jikinta yayi zafi tana kwance cikin jikinsa Yana rage Mata zafin jikin da nasa Dan kuwa yanajin yanda dumin jikin nata ke shigarsa Yana saukan Masa da kasalar sake shigar da ita jikin nasa itakuma tana lafe tana sauke numfashi ahankali cikin sanyi.
Kallonta yayi cikin Dan qaramin hasken dakin Ya shafa bayanta ahankali Yana sake ce mata"
_Azinalehu_ (Sorry) cikin kunnenta da wata sirrantacciyar muryarsa da tsakanin jiya zuwa yau tasanta.
Ahaka yayita lallabata suka samu bayan sallar asuba tasamu bacci ya dauketa me nauyi sai alokacin yasamu nutsuwar kansa ya gyara Mata kwanciya tareda fitowa Palo sanyeda milk jallabiya me taushi ya zauna Yana daukan wayoyinsa ya kunna sbd yau yakeson Kai qarshen matsalar komai tunda sungama hada dukkanin shedodinsu dasuka tabbatar musu da zarginsu Akan Wanda suke zargi
Yana buqatan komawa Paris kodan rashin lafiyan Nan daya sameta.
Mr Omar yakira Kai tsaye yace"
A bayyanarda duka shedu akan yakoob a cikin kotu yau.
Cikin girmamawa Mr Omar yace"
Maleek haryanxu Yana maganar son ganin 'dansa Kuma idan aka bayyanar a kotu cewan 'dansa ne ya mutu zai iya bayyana komai a gaban kotu Wanda zai taba gizah da Kuma Anneti sbd al'amarin zaizo Mata da tashin hankali tunda Bata taba tsammanin hakan ba daga Wanda take aure
Kana ganin yakamata mu fitar da zancen duka a kotu?
Yan media zasu yada abin fiyeda komai ta yanda zai Yi Muni.
Shiru maleek yayi na wasu mintuna kafin yace"
Yanada damar yasan mutuwar dansa saidai baida damar fadar komai bayan abubuwan daya aikata da wannan za'a yanke Masa hukunci basai anbari yafada komaiba bayan wannan.....
Shiru yayi Yana kokarin daure abin dayake ji a zuciyarsa dasuka bayyana a idanuwansa yaci gaba da cewa"
Neges Kuma sbd daraja ta auren Anneti zanji da matsalarsa ta cikin gida batareda duniya tasan abin daya aikataba sauran haqqin Rai dake kansa Kuma tsakaninsa da ubangijinsane.
Cikin yanayi na sanyi shima Mr Omar yace"
Allah ya kyauta ya sake tsare imaninmu
Allah Kuma yaqara maka tsarkin zuciya.
Ba Haka suka so ba duk su dukan Amma Kuma wani lokacin kanayin abinda shine zaman lafiyar kowa da Hana fitina.
Lokacinda aka tafi da yakoob har mortuary aka jawo gawa tareda yaye Masa yaga gawar 'dansa amed datai fari tas sbd ajiya da sanyi.
Sarewa qafafuwansa sukai sbd firgicin ba zata daya fizgesa lokaci daya da wannan mugun ganin dayayi
Cikin tashin hankali ya zube gaban gawar Yana ihun Kiran sunan"
Amed Amed Inidēti ibakíhìni¿
Yaushe wannan mummunan Abu yasameka batareda nasaniba?
Amed katafi kabarni Banda kowa sai kai.
Dagowa yayi cikin ficewa hayyaci da tashin hankali ya kalli Mr Omar Yana cewa"
Meyasa???meyasa??
Ta yaya?
Yaushe kuka kashesa?
Meya muku?
A Daren ranar daya tafi aikin neges yamun saqon cewa Yana lafiya tafiyan gaggawa yayi.....ko shekaran jiya yamun sakon Yana lafiya Dana kira..yaushe kuka kashesa.....
Kukan tashin hankalin masifa yakeyi sbd sanin tsaf wannan umarnin maleek ne ya sake gangaro da hawayen baqin ciki jikinsa na daukan rawar Shiga tashin hankalin rashin tsammani na wannan afkuwar dabai taba kawowa aransaba ya rasa dansa kwalli kwal Wanda duk suke wannan fafutukar rayuwar dansu tsira su Tara abin kansu su gudu wani gurin su Gina rayuwa.
##MAMUH#
KUYI MANAGE YAU INADA UZURI DAN ALLAH.
*_Mamuhgee 48_*
Kallon yakoob Mr Omar yayi Yana gyara tsayuwa yace"
Allah ya yafe Masa kurakurensa tareda Kai mahaifinsa daka dorasa akan irin wannan rayuwar da batada hanyar bullewa ko a duniya ko agurin ubanginka,
Son Rai da bin zuciya qarshensa baida Dadi yakoob Amma tunda kune kuka zabi hakan hakan shine daidanku,
Babban kuskuren daka aikata yakoob shine sako 'danka da baida kwarewa acikin wannan harkar dakai ka Jima da dadewa acikinta Dan kuwa gashi kuskurensa yakaisa ga Haka kaima yakaika ga hakan.
Allurar meriz ce ta kashesa kaman yanda kukai amfani da ita Dan kashe tsohon NEGES mahaifin maleek Kuma kukaso kashesa da ita,
Kun aikashi kashe padima saidai kun manta cewan a sashen maleek ne take
Kuma a sashen Babu wani lungu da Babu camera a maqale Wanda idonku da zuciyarku sun rufe da aikata hakan kuka saka Amed disconnecting dinsu Wanda ko karatun addini bayadashi bare na zamani Dan Haka ta Yaya kuke tunanin zainiya ciresu.
Ranarda muka samu labarin zuwan lailah gizah muka tabbatarda akwai dalilin zuwan nata Wanda anyi kirantane Dan ayi amfani da ita hakan yasa muka sauya tunani ta hanyar Dena shayarda padima meriz sbd ga hanyar sauki tazo Mana,
Tunda neges yayi magana da lailah tafara bibiyar jekadi Wanda jekadi tagane hakan ta sanar Mana daga lokacin mukasan meyake faruwa har lokacinda muka tabbatarda amed na bibiyar lailah itama bamui wani motsiba muka barku Dan ku aiwatar da naku Shirin dazai bamu tamu damar.
Kaf gizah Babu Wanda yasan da padima na cikin masarautar shiyasa muka kyaleku Dan munsan Dole bazaku barta ba duk da batasan ainihin waye yasakata aikin daya sakata ba ahaka rashin nasararku yakaiku aika amed kashe padima wadda taji sauki da kanta zata iya Kare komai kuma a Daren ranar jekadi ta miqa Mata allurar meriz a hannunta ta sanarda ita duk Wanda ya shigo kawo Mata farmaki ta tabbatarda ta kwaci kanta da allurar Wanda hakan zai fidda ita daga wannan rigimar gabaki daya har abada.
Padima na son ranta fiyeda masoyinta amed Wanda shima yakeson dukiya fiyeda rayuwarta Dan Haka a Daren ranar abindaya faru shine bayan yaja lailah da dubara zuwa gurin Dan kisan ya hau kanta mun gani Kuma mun sanarda jekadi komai kafin isowarsu gurin Dan Haka jekadi tasake nanatawa padima tana sane ya fito lailah ta doketa saidai bamuyi tsammanin amed yaqara doke jekadin ba yasamu ya qarasa dakin ya bige lailah ta hanyar kwada Mata katako akai Wanda ganinsa yasa padima shiga tashin hankali saidai Bata Bari tsoronta yabarta barin amed yasamu sa'ar kashetaba tayi amfani da matsayinta na mace ta nuna Masa kanta amatsayin su Raya darensu na qarshe kwadayin Zina yajasa ga rasa ransa batareda yasamu abinda yake kwadayinba.
Babu Wanda yasan padima na kasar tayaya Yan jaridar suka San waye aka kashe bayan Babu Wanda yaga gawar da idanuwansa wannan shine babban kuskurenku na biyu daya kawo karshenki batareda ansha wuyar hakan ba,
Padima ta kashe amed sbd Kare Kai itama Allah yabata nata sakamakon ta hanyar rasa cikakken hankalinta kamar lailah Da Haka kowa zai girbi nasa aikin.
Allah ya tsare Mana imaninmu yabamu kariya daga mutane kamarku Wanda suka Tara arziki ta hanyar kisa da miyagun ayyuka gashinan dukiyar Zaki tafi ku barta abawa mutane suna Kuma tsine muku.
Juyawa yayi ya fice yabar yakoob din tsaye cikin rashin sanin makamar tunanin Yi sbd dukkanin gangar jikinsa da jininsa sun tsaya cak Babu abinda yake motsi ajikinsa bayan zuciyarsa dake bugawa ahaka aka jasa Yana tangadi aka fice dashi
Take 'yan jarida aka sakar musu labarin suka fara yadawa cewan
Yakoob amintaccen bawan neges ne ya kashe tsohon NEGES na gizah
Take aka bayyanarda shedu dasuka hada da garin meriz dake ciki sarkar da padima ta taba boyewa da aka samu a sashensa gurin bincike.
Hankalin jama'ar gizah ya tashi tareda girgiza matuqa sbd kishin kishin fara zargin NEGES da akai Wanda yasa akai gaggawar yankewa yakoob hukuncin kisa ta hanyar cire kansa sbd kada ragewa fitinar tsayi
Amma duk da hakan ba a daina bayyanarda zargin NEGES ba Wanda yasashi kasa fitowa sbd tsananin kunyar kansa da baqin ciki me nauyi daya lullubesa sbd Kai tsaye ko an boye laifinsa saidai yasa jama'a yin shiru Amma wannan zargin da laifinma gabaki daya bazai rufu ba musamman da kaleeb da maleek sukai shiru sunki saka Baki a maganar sai hakan yasake bawa jama'a kwarin gwiwa aka fara kishin kishin sauke neges jama'a da jinin sarautar gizah da 'yan delah gabaki daya kowa yafito ya nuna sha'awarsa ta sauyin neges sbd kobabu saka hannunsa zamtowar bawansane ya aikata hakan to tabbas hakan ya shafesa Dan Haka gabaki daya kusan ya rasa girmansa da mutuncinsa a idon jama'a
Musamman Anneti da yakejin Kamar bazai iya hada idanuwa da itaba sbd girman kunyar abindaya aikata Wanda yasan itama yagama fahimtar komai saidai kawai tayi shiru sbd wani abin basai kafadaba Allah ya kyauta kawai yafi maka saukin fada
Da wannan ya kebe kansa da kansa a sashe dabam bayan ya fitar da wasiqar sauka mulki da kansa ya aika har delah gurin kaleeb Wanda har lokacin yaqi cewa komai bare maleek daya fara Shirin barin qasar bayan ya bayarda sunan Mohan YONAS (autan kaleeb) amatsayin Wanda za'a nada sabon NEGES na riqon kwarya kafin lokacinda zai karba Dan haryanzu Yana buqatan wani Dan lokaci kadan kafin yadawo gabaki daya ya karba gizah din.
******
Zazzabinta yayi sauki sosai ba laifi Dan kuwa Daren tasamu tayi bacci sosai sbd wani magani da jekadi ta kawo Mata Dan Haka gari na wayewa tun karfe shida da mintuna ta fito cikin doguwar jallabiya data rufeta koina ta nufi sashenta tana Isa ta wuce bedroom dinta tashige tana sauke numfashi ahankali kafin ta dago ta kalli farhat dake kwance kan gadonta tana bacci cikin nutsuwa
Ta qarasa gadon ta zauna tana kallonta tasaki murmushi ahankali tace"
Sweetie nayi missing naki da surutunki sosai.
Miqewa tayi ta zare rigar jikinta ta jefa cikin wardrobe ta nufi toilet ta shige.
Kodata fito komawa gadon tayi ta haye ta kwanta gefen farhat ta gyara musu rufa Takoma bacci sbd baigama isartaba.
Qarfe tara ta farka lokacin har farhat ta Jima da farkawa ta bude idanuwanta ahankali tana kallon farhat dake Kiran sunanta cikin murna da farin ciki tace"
Aunt NURU yaushe kika dawo?
Tashi zaune tayi tana gyara gashinta da murmushi akan fuskarta tace"
Sweetie na barci nadawo
Ya kike?
Fadawa jikinta tayi ta rungumeta tana cewa"
Next time idan zakije tare Dani Zaki Zan biki kinji Aunt NURU.
Wani irin Murmushi ne ya saukowa NURUn ta kalli hancin farhat din zuwa bakinta dasuke Zak Zak Dana dadynta saita sake sakin murmushi tana saukowa gadon tace"
Kinyi brush?
Biyota tayi tana cewa"
Eh nayi nace next time zakije Dani??
Tsayawa tayi tareda juyowa ta kalli farhat din ta kamo fuskarta taja hancinta ahankali tana murmushi tace"
Wannan hancin Ina sonsa sosai kaman yanda nake son sweetie dan haka kidainama tambayan idan zanje wani guri ba dakeba ok¿.
Cikin murna tace"
I love you too lewa.
Knocking kofa akai ahankali tareda bude kofar aka shigo
NURU ta dago tana waiwayowa kofar sukai ido biyu da afia dake kallonta da dukkanin hankalinta tana nazarin NURUn da akace batada lafiya saidai bataga alamar ciwo atareda NURUn ba jikinta ba inda ya nuna alamar akwai ciwo tareda ita ta karaso ahankali cikin 'yar kulawa da alamar tambayarta tace"
Jekadi tace bakida lafiya da fatan dai ba wani serious ciwo bane ko??
Murmushi NURU tasake tana matsowa gaban afia din tace"
Naji sauki kawai gajiya ce da rashin isashen bacci Amma yanzu lafiyana kalau.
Mezaisa ki kasa samun isashen bacci bayan kina samin hutu sosai bakida aikin komai a gabanki....
Aiki dad dinku yabani Wanda duk ya kawo hakan yanzu dai inason Baki hakuri akan rashin samun damar zuwana gurin mum dinki I am really really sorry for that Kuma Ina fatan komai yatafi yanda ake fata?
Ajiyar zuciya afia ta sauke tana qarasawa bakin gadon dakin ta zauna tana cewa"
Komai yatafi yanda akeso mum Dina tana Las Vegas tareda Imran Wanda yakoma can yanzu da zama da aiki sbd su manta rayuwarsu ta baya su fara sabuwar rayuwa Mara damuwa da Danasani.
Numfashi NURU ta sauke cikin ahankali tareda ajiyar zuciya tana kallon Afia da taushin murya tace"
Ina musu fatan kyakkyawar rayuwa me Dadi da amfani.
Thank you afia tace tana kallon fuskar NURUn data sauya Mata gabaki daya.
Wanka NURU tashiga ta fito cikin nutsuwa ta shirya cikin doguwar riga golden me sequence ajiki suka zauna dukkaninsu su ukun anan sashenta sukai breakfast tare suna gamawa suka dawo Palo suka zauna NURU na Shirin zuwa gurin Anneti afia ta kalleta tareda dawowa gefenta ta zauna cikin nutsuwa ta kalleta tana tattaro abinda zata fada Mata tace"
Shin kinsan case din kisan da mum take ciki padima ce wadda ake cewa ta kashe......
Wani irin kallo NURUn juyo tanayiwa afia din da dukkanin fararen idanuwanta.
Padima ce wadda dukkanin labarai da duniya ta shedarda an kashe....
Hawayen dasuka ciko fararen idanuwanta dasuka koma ja Nan take suka gangaro kan fuskarta ta sake kallon afian da kyau tana kasa gasgata zancen sbd bazai yiyuba babban zance irin wannan a boye Mata
'yar uwarta jininta aka kashe ace Bata saniba sai yanzu bayan wadda