din tayi payment dakomai duk da komai nasa kafin ta aje wayar sbd Nanda mintuna goma zuwa Sha biyar kayan zasu iso ta miqe tareda zare doguwar rigar data Dora kan kayanta ta nufi toilet din dakin ta bude taga wani irin girmane dashi tashiga tana mamakin komai na dakin da toilet din harta tube tasakarwa kanta ruwan zafi ta gasa mararta datai nauyi Dan har lokacin be saukoba period din.
Saidata Gama ta janyo towel ta daura zata fito ta drwer jere da kalolin shavers da hair clippers a jere masu shegiyar tsada ta dauko ta kalli towel din jikinta sai alokacin tunanin dakinsa ne wannan din kenan yashigo Mata ta dafe kanta tana Jin wani iri kafin tafito.
Tana fitowa Yana zaune kan sofa yayi crossing legs Yana waya ahankali cikin nutsuwa da kamewa Amma tunda ta fito idanuwansa suke kanta duk wayar dayakeyi Kuma batareda yanayinsa ya sauya ba.
Jin idanuwansa akanta yasa takasa fita daga dakin ta nufi gaban madubinsa ta tsaya tana tunanin abinyi sai kawai taji mutum a bayanta tsaye Yana kallonta ta cikin mirror din da ido ya nuna Mata oil na Neutrogena ta Kai hannu ta dauka ta zauna gaban madubin tana shafawa ahankali
Ganin yanda takeyi yasashi juyawa ya fice Yana gyaran murya sbd muryarsa data Dan shake da wainda yake wayar Dan Haka ya fice yaci gaba da wayarsa.
Tana gamawa saigashi yashigo ya ajiye Mata jakar kayan shopping dinta daya iso yakuma ficewa
Ta bude kayan ta dauki pant da bra tasaka ta shafa turare saita tsaya tunanin kayan sawa sbd gabaki daya ta manta da cewa kafin kayansu su iso saisun buqaci kayan sawa.
Kayan baccin ta daga taduba tana fitarda numfashi me zafi sbd wainnan kayan sanyima kamata zaiyi idan tace ta yini dasu ajikinta Dan babu ta arziki ita saiyanzuma tunanin waya kaita siyansu yafado Mata.
Tattara kayan tayi tasaka wardrobe ta dauki riga daya ta saka ta daure kanta tareda Dora jallabiyarta akai ta tada sallar la'asar da akai hadda azahar da batayiba.
Tana cikin yi yashigo dakin ya Dan kalleta ganin tana sallah saidai baice komaiba ya nemi guri ya zauna Yana waya da Mr Omar dake basa bayanin komai na tafiya akan tsari.
Tana idarwa ta miqe tareda warware nadin kanta takasa cire rigar jikinta batareda ya aje wayar dayakeyi ba yace taje ankawo abinci.
Tanajin yunwa Dan Haka Bata tsayaba ta wuce Ashe Yana bayanta ya zauna dining din me kujera biyu rak ta waiwaya ahankali tace"
Farhat zandubo tazo taci abinci...
Aje wayarsa yayi tareda kashewa gabaki daya yana cewa"
Batanan tana gurin Sarah zata kula da ita.
Da marairaice fuska ta kallesa bama tareda tasan tayi hakan ba
Ya Dan bude idonsa akanta ganin yarintar datake Shirin zuba Masa Dan kamar zatayi kuka ta langwabe kai.
Saidata zuba Masa komai kafin ta hada ruwan zafi da kanta tazo ta zauna Tasha black tea me zafi tana lumshe ido sbd nutsuwar datakeji ruwan dumin nashiga cikinta.
Abincin kadan taci Tasha magani ta Dan daddaure ta gyara gurin Takoma daki ta kwanta take bacci ya dauketa sbd maganin yanasa bacci shikuma ya hau duba wasu tarin emails daya samu duk a yau din hadda na jiya dabai Samu damar dubawaba.
Bacci tayi sosai sai magriba ta tashi bawai Dan ya saketaba saima kashe Mata jiki da maganin yayi ta tashi da qyar tayo alwala tazo tayi sallah tana gamawa tadawo Palo tadan zauna tareda kunna tv Amma tsoron ganin ita kadaice yasa tana ganin lokacin ishai yayi ta koma daki tayi sallar ishai din tana gamawa ta tube tasake komawa toilet taduba har lokacin shiri period din Bai saukaba sai tayi wanka tafito ta shafa turare kawai tasaka kayan bacci kenan tana tunanin yanda zata koma dayan daki ta kwana ita kadai saigashi yashigo.
##MAMUH#
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899*_Mamuhgee 38_*
_*YERWA INCENSE & MORE*_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_
******************
Bayan fitarsa Haka ta tsaya a inda take tana bin inda ya fice da kallo zuciyarta na rarraba tunanin shin so ne takamu dashi me qarfi kokuwa Jin dadine kawai na kusantuwa dashi?.
Waiwayowa tayi ahankali ta kalli farhat dake gefenta tana kallonta kamar Bata santaba sbd ganin bayan sabon gida da aka sauya musu hadda aunt NURU da daddy dinta kaman suma sababbine aka kawo musu.
Murmushi me qayatarwa NURU tasaki tana juyawa takoma cikin palon ta zauna tareda kunna tv da remote tana Nemo tashar waqoqin yarensu ta Amstar farhat tazo ta zauna jikinta tana cewa"
Aunt NURU Zaki fassara Mana waqan da akeyi ko?
Da mamaki ta kalli farhat din tana murmushi tace"
Sweetie bazan iya fassa Miki dalla dalla ba kawai dai suna waqan soyayyarsu ne.
Da Haka ta rufe zancen farhat din sbd bazata iya bi tana fassara Mata suba kalaman sunyiwa kunnuwanta nauyi bama zata ganeba ko fassarawar tayi Mata sbd kalaman so din ko ita datake sabon Shiga sun Mata nauyi.
Saida lokacin sallah yayi ta miqe ta nufi ciki da farhat a dakinta sukai sallar bayan tayi wankan tsarki
Suna gamawa suka fito babban Palo gaba daya cin abinci daga ita sai farhat din akan dining Haka sukaci suka tashi tunanin afia yadawo Mata
Tanajin kewarta sbd akwai shaquwa da kauna a tsakaninsu ta haqiqa Dan haka takejin kewarta tun ranarda suka baro can saidai tana Mata uzuri sbd Babu Wanda zai zabi wani yabar uwarsa koman lalacewarta Dan hakan yasa Bata ganin Jin illar afia ko kadan kawai dai laifinta daya shine
Barin mahaifinta ta zabi mahaifiyarta daba itakeda gaskia ba ko acikin matsalar ta iyayen nata cire tunanin zancen tayi daga kanta sbd wannan ba huruminta bane dazata shiga tsakanin 'ya da iyayentane.
Ranar dasu mum Sarah suka baro gidan bayan kowa ya fidda kayansa anzo andaukesu akabarsu su kadai har lokacin a palon suke afia na kukan rasa cikin mum da dad din wazatabi
Lailah dakejin wata masifaffiyar hauka na bijiro Mata Jin take kamar ta Dora hannu akai tayita rusa ihu tana tsinewa maleek sbd tunda Allah ya halicceta ba'a taba muzanta taba da wulaqanta taba harma agaban bainar masu aikinta dake tsoronta da Bata girma Kamar zasu bauta Mata sai yau maleek yayi Mata wannan mummunan tabon,
Cikin tsananin ihu da masifa tareda tashin hankali ta miqe tana cewa"
Allah ya Isa tsakanina dakai MALEEK Kuma wlh bazan yardaba wannan wulaqancin dakamun kanka kayiwa Dan saina tabbatarda ka fuskanci tozarci fin wannan Kuma wlh zama matarka ko zan rasa Raina saina dawo matarka alokacin karuwarka zatasan matsayinta da nawa bazai taba zuwa dayaba Dan kuwa wlh ko zata samu damar zama cikakkiyar matarka to saidai idan Ni Lailah bana raye.......
Da sauri afia ta rufe bakinta cikin tsananin baqin cikinta da wannan karon yakai maqura baya boyuwa hawayenta na tsiyaya tace"
Mum mekike fadarwa kanki Haka?
For God's sake meye amfanin hakan?
Tun farko nayi gudun hakan mum ba kalar rokon daban mikiba karki tafi sbd duk duniya Babu abinda zakije kisamu dayafi Miki 'yayanki da mijinki Wanda mum ga dukkanin abinda nasani nake Kuma gani dad bazai taba dawo dakeba kema kinsani sbd kinsan wayeshi,
Kin Mata umarnin da kaleeb yabaki mum duk Kika shure Kika tafi?
Mum na rokeki ki hakura ki aje komai tunda yabar Miki Nan din kiyi zamanki tareda Gina sabuwar rayuwa ki maida hankali kan aikinki I promise to be with you aduk halinda Zaki shiga matuqar Zaki janye wainnan kalaman naki ki hkr da abinda zai ringa jawo Miki wulaqanci dacin fuska,
Mum menene amfanin wainnan maganganun na cewa saidai idan bakya raye
Mum ba'a yiwa Allah ganganci wainnan maganganun har daureki zasu iyayi Dan Allah mum Ina rokonki kadakiyi abinda zai cutatar da dad ko NURU sbd ita ba laifinta bane
Idan akwai me lefi nawane nice na hada auren...
Wani mahaukacin kallo lailah tajuyo tana yiwa afia da idanuwanta dasuka fiffito sukai jajir kamar me bori tace,
Kikace mene afia?????
Kallon mum din tayi tana dakewa tace"
Nice na hada auren batareda raayin ko dayansub......
Wani gigitaccen Marine akaro na biyu ya sauka a fuskarta Saida tayi baya ta zube kan kujera a dimauce ta dago lailah tace"
Wannan na tabbatar min da kikai bare tafi Miki uwarki
Dan kuwa kece silar duk komai daya faru ayau tsakanina da dad dinki.
Juyawa tayi a masife tayi ciki ko gabanta Bata gani sosai ta nufi dakinta tana shiga ta rufo wani irin kuka dataketa dannewa tsabar baqin ciki ya subuce Mata ta zube kasa tana sakinsa tareda rufe bakinta da hannuwanta kada afia ta jiyota abin ya Mata yawa.
Afian ma kasa bin mum din Tata tayi ta zauna agurin tana kuka ahankali ahankali.
Da daddare daqyar kowannensu ya iya kwantawa Babu ci bare Sha hakama kwanciyar kawai sukayi Babu Wanda ya samun bacci ya daukesa sbd fargaba da tashin hankalin rashin ko masu gadi Babu ko motsin komai aduk girman gidan sai rashin tsaro da motsin yasa sukaji basa cikin kwanciyar hankali musamman afia data rasa tunanin me mum dinta keyi tareda tunanin meye niyarta.
Washe gari Lailah tarigada ta yanke shawaran zuwa gizah Dan takasa hkr a Daren takira NEGES datasan shikadaine yanxu zai iya saka Baki a maganar sbd kaleeb ko Ana Mata dukan mutuwa bazata fara tunkararsaba bare Anneti datasan duk duniya bazatabi bayan kowaba indai akan 'dantane MALEEK,
Tariga ta yanke zuwa gizah sbd dawo fry da matartabarta na matsayin Matar maleek bazata taba yardaba 'yar bayi jikar bayi tasha gabanta harta karbi matsayinta.
Koda afia tashigo dakin da safe lailan na zaune tana duba agogon hannunta Dana wayarta akai akai sbd tayi booking din ticket na tafiya jira take lokaci yayi ta nufi airport
Drivern dadyn Imran takira aturo Mata shi take jira yakaita airport din
Shigowar afia yasata dagowa ta kalleta da idanuwanta dasukai jajir sbd rashin rintsawa da tashin hankali tareda masifar datake ciki ta dauke Kai daga afian tana Dan yamutsa fuska tace"
Afia idan kinzo Nan danki dameni da koke kokenkin Nan kokuma wani shirmen daban kadaki fara sbd inada ciwon kan danake fama dashi already bana buqatan wani sabo Dan bama zan dauka ba kece naki ran zaiyi mummunan baci so just get out of here"taqarasa fada tana nuna Mata kofa da ido.
Tray din da afia ta jero Mata tea da soyayyan kwai takawo Mata ta kalla tana tsiyayar hawaye takasa cewa komai ta juya ta fice hawayenta na sake gudu tana zuwa kitchen ta ajiye tray din ta juyo ta fito kenan mum din tafito janye da akwati da handbag dinta sai wayarta a hannu
Da mamaki afia ta qaraso tana share hawayenta dasuka kasa tsayuwa ta bude Baki muryanta na rawa tace"
Mum Ina....
Bata qarasaba lailan ta katseta da cewa"
Gizah zantafi idan Zaki iya zama anan ne to saina dawo idan bazaki iya ba ki nema gidan dad dinki ki koma can dama kece Kika hada auren saikije ki qarasa cike ladarki ta qara musu dankon zama.
Juyawa tayi ta fice tabar afia sandare a tsaye cikin 'dibbin mamaki da tsoron mum din Tata da sauyawarta.
Da gudu taqarasa ta riqe mum din tana cewa"
Mum Dan Allah na rokeki kada kije ki wulaqanta kanki acan
Tozarci da sake tonarda asirinki kawai Zakiyi Anneti bazata karbekiba Dan Allah kada kije mum,
Mum na rokeki Dan Allah...
Cikin quluwa lailah ta cire jikinta daga nata tana cewa"
Baki fahimci abin Dana fada Miki kenan ba nace ki nemi dad dinki ki tafi gurinsa bazan iya wannan hayaniyarba afia please just go kina batan lokaci Ina buqatan Isa airport kan lokaci.
Rabewa tayi ta wuce ta miqawa driver akwatinta ya karba yasaka mota tareda bude Mata tashiga ta rufe ya zagaya ya shiga ya tada motar suka fice.
Ajiyar zuciya afia ta sauke ahankali tanabin inda suka wuce da ido tana rasa tunanin Yi akan mahaifiyarta sbd yau da mahaifiyarta tasake tsallakewa ta barta akaro na biyu ya rusa duk wani sauran hope datake dashi akan uwarta sbd duk uwar data tsallake babbar budurwa kamarta a qaton gida irin wannan Babu kowa ta tafi ta barta batareda tunani ko fargaban wani abun yafaruba tabbas babu 'yayanta cikin ranta,
Dad dinta tasani ta tabbatarda Koda Wasa bazai iya kwatanta wannan gangancin akantaba shida yake uba Amma uwarta mace takasa yadda ta runguma takuma yadda data zama uwa me nauyin 'yayanta akanta.
Sake sauke numfashi tayi tareda juyawa ahankali ta koma ciki tana daga qafafuwanta dasukai Mata nauyi daqyar.
Dakinta direct ta nufa ta zauna bakin gadon tareda dagowa ta kalli dakin tafashe da kuka ahankali tana sunkuyar da kanta sbd yau ta wayi gari batada kowa atareda ita bawai Dan tarasa kowa din ba.
Ta share awanni a hakan tana kuka cikin hali na ciwon dakecin zuciyarta kafin ta share hawayen ahankali ta miqe tsaye ta janyo akwatinanta tafara kwashe kayanta tana zubawa ciki harsaidata Gama kwashewa tadawo ta zauna tana tunanin Kiran mahaifinta datasan ransa abace yake da ita.
Kasa kiransa tayi Takoma ta kwanta kan gado tana tunanin meya hargitsa rayuwarta cikin kwana daya da awanni akai.
Kasa kiransa tayi Takoma ta kwanta har batareda tasan matsayar inda ta dosa ba sbd wata zuciyarta na Bata shawaran in mum dinta gizah sbd dakatar da ita ga wani abin dabai kamataba Wanda zai iya janyo zubewar mutuncin dad dinsu da ita kanta mum din saidai Kuma Tana Jin gwara ta qyale mum din tayi nisa zuciyarta batajin kira.
Wayarta ta dauka ta duba Babu available tickets na zuwa gizah Dan Haka ta yanke shawaran jira kwana biyu tagani.
Bayan kwana biyu haka tasake dubawa ba tickets sai jikinta yayi sanyi ta sawa ranta ba alkhairi cikin zuwan nata Dan Haka tasake daurewa ta zauna har gari yasake wayewa ta yanke shawara takira dad dinta saidai Bata samesaba sai kawai ta Nemo wayar NURU takirata Kai tsaye.
Da safe ne suna cikin bacci itada farhat a dakinta washe garin ranarda MALEEK ya wuce kenan,
Basu tashiba sbd guraren karfe takwas ne taji ringing din wayarta ta lalubo ta dauka batareda ta tantance sunan me kiranba saidataji muryar afia ta wartsake tana bude ido tareda dubawa taga sunan afia din ne cikin kulawa tace"
Afia kina lafiya kuwa?
Ajiyar zuciya afia ta sauke dagacan bangaren tareda bude Baki tace"
Kituromin Edward yazo yadaukeni anan tsohon gidan Ina jira.
Ahankali NURU tace"
Ok Bari nakirasa nafada Masa zaizo yanzu Inshallah.
Da haka suka kashe wayoyin kowacce cikin Jin nauyin 'yar uwarta.
Batareda ta sauko gadonba daganan kwance ta Nemo numbern Edward ta saka kiransa Yana dagawa ta sanar dashi yaje ya dauko afia yace ok.
Komawa baccinta tayi sbd Bai ishetaba kafin afian ta iso.
Cikin bacci tasakejin ringing na wayarta ta lalubo ta daga cikin bacci tace"
Mum Sarah lafiya kuwa?
Sorry na tasheki dama afia ce tazo nace zan sanar dake za'a Kai Mata kayanta asalin dakinta da aka ware Mata.
Guntuwar hamma tasake tana tashi zaune tace"
Mum Sarah shine sai angayamin Kuma?
Eh nafada Miki ne sbd umarnin maleek ne.
Lumshe idanuwa tayi sbd sunansa da aka ambata yashigeta tace"
Ok shikenan akaita dakinta ganinan ma fitowa.
Duk abinda ake fada afia din na tsaye tana saurare tareda kallon ikon Allah daya sake kasheta da mamakin saidai batace komaiba ta nufi dakinta tashige tana kallon koina na gidan daya fi wancan gidan nesa ba kusaba.
##MAMUH#*_Mamuhgee 39_*
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_
_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
****************
Direct dakin afia din NURU ta nufa data fito farhat ma ta tashi tana biyeda ita suna shiga dakin ta waiwayo tana kallonsu farhat ta qarasa gurinta da gudu cikin tsananin farin ciki me yawa tana cewa"