sbd ba qura asthmanta be tashiba saidai ta kwaso zazzabi me qarfi Wanda tun a school tayi collapsing aka Kira MALEEK Koda suka Isa ta farfado Amma Kam tanajin jin zazzabi sosai siadai yanzu zazzabin ya sauka gabaki daya saitasamu bacci ya dauketa Dan hakane yasa Koda suka dawo gida da ita ganin su afia basanan yasa yatafi da ita samanshi yanzu ta balcony daya hango dawowarshi saiya daukota ya dawo da ita dakinta danta samu kulawa gurinsu afian sosai.
Fitowa tayi tana gyara zaman towel din farhat dayayi Mata kadan tana sauke ajiyar zuciyar nustuwar data samu tana qarasowa tsakiyar dakin taganshi tsaye bakin gadon da farhat ke bacci wata mummunar razana tayi ta damqi towel din da qarfi Jin zai sabule Mata ta sake dagowa da sauri ta kallesa cikin tsananin tsoro.
Tsabar rudewa rigarta dake gefen gadon ta nufo da sauri zata dauka kafin ta iso yabar gurin batareda yabari ta qaraso gurinba ya fice dakin gaba daya Dan towel din ko Gama rufeta baiyiba sbd qanqantarsa.
Zamewa tayi bakin gadon farhat tana kallon kanta tareda dafe goshinta tanajin wani irin yanayi na damuwa.
Zarar kayanta tayi ta fice da sauri ta fada dakinsu ta Sanya kaya tayi sallah ta zauna gefen afia batareda tace komaiba ta zurfafa tunanin wani Abu dayakasa fita cikin ranta afia na lure da ita Amma batace Mata kalaba.
##MAMUH#
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐๐
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐๐
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU๐๐
0903 234 5899
*_Mamuhgee 25_*
Tana aje wayar ta waiwaya ta kalli NURU har lokacin baccinta takeyi hankalinta kwance Kamar wata 'yar baby.
Kyakkyawar fuskarta ta kalla zuwa jikinta ta sauke ajiyar zuciya me qarfi sbd tausayin NURUn da Kamar rayuwarta ta raunane auren sa'ar mahaifinta bayan tanada Wanda takeso daidai ita sabon jini Amma yanzu gashi auren dattijo yahau kanta duk da MALEEK yawuce duk wani tsarin Imran nesa ba kusaba Dan kuwa Kota Ina Babu inda Imran yakamo maleek bayan qananun shekaru dazai nuna Masa Wanda shikansa maleek din kyau da hutu tareda wani irin iko da sarauta dake yawo a jininsa suna boye manyancinsa matuqa sosai dan kuwa jikinsa kawai masu qananun shekarunma bazasu kaisa kyawun jikiba musamman dayake Yana geamin sosai haryanzu shiyasa jikinsa koyaushe Kamar na yara.
Ajiyar zuciya tasake saukewa tareda cire wannan tunanin aranta Dan kuwa ita yanzu tariga ta cire kanta acikin maganar komaima Dan kuwa ko lokacinda take muradin raba auren nasu bataga ta inda zata faraba dama fatanta idan mum tadawo dad zai sawwaqewa NURUn sbd wadda zuciyarsa keso tadawo to Amma ita ta ina take gano yiyuwar saki arayuwar dad dinsu Wanda ko rabuwarsa da mum haryanxu duniya Bata gama saniba bare yayi wani sakin.
Aje laptop dinta tayi gefe tareda Miqewa ta Sanya slippers ta fita zuwa kitchen Dan yin wani aikin duk da Bata iyaba Dan debewa Kai kewa batason tunanin komai yadawo Mata musamman na mum dinsu datake fatar shafewa ta manta gabaki daya.
Sai gab da magriba NURU ta farka daga baccin miqe tashiga toilet tayi fitsari da brush ta fito ganin bakowa a dakin tasan wani Abu sukeyi ta zame gajeran wandonta ta dauko wani dogo da zo har qasan gwiwanta ta fito riqeda wayarta tana duba wani email da aka turo Mata daga karatun court din dataje jiya tana dariyar mark din data samu ta nufo kicin dan tunda tafito yanayin qamshin datakeji tasan afiace a kitchen din.
Ganin uban aikin da afia din keyi tareda farhat da mum Sarah sai Fana dake tayawa yasata sakin dariya cikeda mamaki ta miqawa farhat wayarta tana cewa"
OMG meyake faruwa anan ne?
Cikin kanne dariya mum Sarah tace"
Princess na aikin abincin dinner ne.
Wani wargazajjen flat bread ta cire daga pan duk ya sauya kala sbd Kwan jikinsa duk ya kone afia tayi tana aje spoon din hannunta tace"
Alhmdlh na Gama waye zaiyi Mana testing?
Shiru kowa yayi NURU ta matsa tana sake kallon girke girken da mamaki da dariya akan fuskanta tace"
Nidai bana cikin 'yar dandanawa.
Farhat kuwa da sauri tayi bayan NURU tana cewa"
Nima bana ciki.
Kallon mum Sarah afia tayi da alamar ke fa??
Wani yawu mum Sarah ta hadiye tareda kallon Fana tace"
Saidai Fana kinsan Ni inada suga ba komai nakeciba musamman yau ya haye da yawa sugan.
Tana gama fadar hakan ta sulale ta fice daga kicin din.
Fana Kam ba damar wani zance ta matso ta diba komai daya bayan daya tana dandanawa harta Gama ta dago idonta na kallon qasa tace"
Komai yayi daidai ranki ya dade.
Da mamaki NURU ta kalli Fana daketa faman danne yunqurun amai dake taso Mata na abincin Amma ahaka sbd gudun batawa afia tace komai yayi.
Afia da kanta tajera komai a dining ta wuce tabarsu NURU ta kamawa Fana suka gyare kitchen din tsaf komai yakoma kaman ba'ayi aiki dashiba Fana ta wuce sashensu na ma'aikata NURU ta rufe koina na cikin ta fito ta nufi dakinsu tayi alwala tayi sallar magriba lokacin afia hartayi wanka ta shirya ta fito taje Tasha black tea kawai Takoma daki sbd karatu takeson yi.
Har akai ishai suna Palo suna kallon wani adventure film a Netflix daganan ta hadowa farhat _Rice Krispies_ har suka Gama suka koma daki sukai sallah sukai Shirin kwanciya Bata Bari dakin farhat ba Saida taga tayi bacci tukuna tabaro tadawo dakinsu har lokacin afia n karatu tazo ta zauna kusada ita itama tana duba wasu hardcover books na lauyoyi na _Michael Connelly THE BRASS VERDICT_
Karkata tunaninta yayi akan abincin da afia din ta dafa dake kan dining Wanda maleek zai iyaci yasa ta aje littafin hannunta tareda kallon afia da bacci bacci yafara fizgarta ta miqe ta fita Dan dauke abincin daga kan dining duk da tasan kilama ya shige zuwa yanzu.
Direct dining ta nufa ta kwashe kayan ta maida kitchen tana qoqarin barin kitchen din taji motsin bude kofar kicin din ta baya tayi saurin waiwayowa cikin sauri da Yar fargaba tace'
Waye??
Muryan mum Sarah taji daga bayanta ta kofar nata dakin tana cewa'
Fana ce zata shigo ta hadawa MALEEK tea yakira Yana buqatarsa yanzune kafin ya sauko.
Jin haka tasake ajiyar zuciya ta matsa jikin kofar tace"
Fana ki koma kawai zanyi masa.
Juyawa Fana tayi ta wuce itakuma ta juyo ta kalli mum Sarah tana cewa"
Tea kawai Koda wani Abu?
Tea kawai yace amma bansaniba ko Zaki hada Masa da wani abun.
Fara hada Masa tayi tareda dauko cake dinda tayi jiya ta jera masasu a plate ta dauko ganyen lemon daga fridge ta wanke tareda zuma ta hada tea din ta zube ta jero a tray ta fito mum Sarah na biyeda ita daukeda sauran kayan suna shiga dining room Yana shigowa itace agaba ta 'dan dago kadan cikin taushin murya tace"
Barka da fitowa.
Akaro na farko ya amsa gaisuwarta da "yawwa" Yana zaunawa kan dining ta ajiye tray din hannunta ta matso kusadashi Dan zuba Masa qamshin turarenta na _Black Opium_ ya bugo Masa cikin hanci ya dago ahankali ya kalleta
Jin idanuwansa akanta yasa ta dakatawa tana Dan juyowa suka hada ido ta sauke nata tana juyowa da sauri ta kalli mum Sarah dake gurin tun kan ta Gama juyowa mum Sarah tayi saurin aje tray din tabar gurin tana soke kai ganin abinda yake neman fun karfin mamakinta.
Mum Sarah na wucewa ta juyo tana qarasa zuba Masa tareda jawo Masa cake din ta koma kitchen ta dauko ruwa ko zaisha ta ajiye tareda budewa ta zuba a cup.
Kasa wucewa tayi saida taga yagama tana daga kicin tana hangensa ya miqe ya wuce ta fito ta kwashe kayan ta maida ta nufi daki tana miqa sbd bacci takeji yanzu Kam.
Saidata shige ya kashe wutar palon farko yashigo ciki ya wuce sama.
Washe gari suna Shirin zuwa makaranta afia ta dauko zancen padima tafadawa NURUn tana qara cewa"
Inaga zaifi idan tazo Nan taga likita gaskia sbd Sam yanda nayi Mata tambayoyi da amsoshinta akwai rikitarwa bangane komaiba gskia sosai so inaga tazo taga likita zaifi.
Kallon bansan ta yayaba NURU tayiwa afia jikinta a sake tace"
Bansan ta inda zanfara bane,
Bansan ta gurinwa zan fara ba.
Kiyiwa jekadi bayanin komai da abinda kikeso ita zata isar Miki da saqonki koina dakomai saidai kawai kiga padima ankawota.
Shiru tayi hakanan tanajin wani iri kamar zata wuce guri idan tayi hakan Amma Kuma ceton 'yar uwartane zatayi tunda tanada damar yin hakan zatayi Inshallah.
Juyowa tayi ta kalli afia tace"
Thank you,zan yiwa jekadi magana idan na Isa makaranta inshallah.
Suna Isa makaranta takira jekadi saidata jira jekadi tagama gaisuwarta ta amsa cikin bawa jekadi nata girman itama kafin ta fadawa jekadi buqatarta tason akawo Mata 'yar uwarta padima tazo Mata ganin gida.
Ba musu jekadi tace"
Angama Inshallah MUSHRA,zanje yanzu na sanarwa Anneti ta sanarwa da MALEEK sai a aika gida ataho da ita Nan daganan sai akawo Miki ita har inda kikeso.
Koda jekadi ta isarda saqon NURU ga Anneti Bata musaba tace jekadi ta isarwa da MALEEK sakon aikuwa Kai tsaye shima ta isarda sakon a waya ta hanyar Mr Omar Wanda yace anbasu dama take washe gari aka aika aka taho da padima wadda Ta taho badan iyayensu sunso ba sai Dan saqon ta hanyar kaleeb ya iso musu.
Abal ya tabbatarwada padima duk yaji wani mugun labari yasamu NURU bashi ba ita har abada hakama ammi Kuma ahaka taji takuma amince saidai ta qudurta bazatayiwa NURU komaiba kodan kalaman iyayensu saidai bazata dawoba saitasamu nata rabon na ingantacciyar rayuwa ta taho tabar amed da mugun mamaki da baqin cikin daya kaisa Shan mugun qudurirrika akan ko zaiyi yawo tsirara bazata jimaba zaimata aikinda ko wata bazata rufaba acan saita dawo saidai Kuma wani tunanin daban yasashi Kiran mahaifinsa dake cikin amintaccin NEGES yafada Masa zuwan padima Wanda shima atake yafadawa NEGES.
Kallon jekadi Anneti tayi lokacinda take miqa Mata saqon NURU na wata sabuwar madarar raqumi da akaiwa Hadi da sinadarun Karin kyan fata Da wasu abubuwan ma tace"
Wannan sakon NURU ne da hannunki kullum Zaki ringa Bata tana shansa harya qare sbd na yanke shawaran kece Zaki Kai Mata 'yar uwarta ki zauna acan sai lokacinda tagama ziyararta kudawo tare sbd dalilai na Kare maleek da iyalansa duk da 'yar uwartane Amma bamusan Yaya halayenta sukeba musamman gashi ziyarar tazo a bazata.
Yanda kikace haka za'ayi Anneti.
Miqewa tayi ta fice Tana sake miqa gaisuwarta.
Tana fitowa duk da darene sosai saitaji tana buqatan zuwa ta duba lafiyar 'yar amanar NURU Dan kuwa tamkar amanartane NURU tabata Dan haka ta nufa sashen Kai tsaye.
Tun daga nesa taga kamar wutar sashen a kashe take sai abin yabata mamaki ta Dan dakata tareda dudduba sauran sassan duk hanyoyinsu wuta a kunne.
Daga can ciki kuwa gyara tsayuwa yakoob yayi Yana kallon padima dakewa tarin darhamai da danyen zinarai daya zube agabanta kallon haramun Kamar zata cinyesu abakinta yace"
Yaya Zaki iya kokuwa??
Hadiye wani yawu tayi tareda danne kwadayinta ta kallesa tsoronta na bayyanuwa tace"
Bazan iya kisaba wlh sbd ban iyaba bantabayiba.
Wani kallon Kai tsaye yayi Mata Yana sake zuba Mata wasu akan wainnan yace"
Ba kisa zakiyiba zuba Masa kawai Zakiyi a abunsha sauran aikin anan zamu qarashi,
Idan Kika cika wannan aikin akwai alqawari me girma na cikar buri da akai Miki alqawari daga shugabana haka zalika Kuma fitar maganar daidai take da bakin rayuwarki.
Wani kallon tsoro biyu tayi Masa kayan cikinta na juyawa sbd duk balainta batakai na kashe wani ba
Waninma maleek datake 'dan yiwa kanta kwadayinsa dukda tasan da wuya ita ko bashiba burinta dai gidan mulki
Yanxu ta Yaya zata iya kisa?.
Kuma aikinma batasan na ainihin wayeba tunda yadaice shugabansa bai fada ko wayeba.
Ciro wani qyalle yayi ya miqa Mata tareda cewa wannan ki warware gashinki ki dauresa aciki idan kinje can so daya kawai akeso ki juye Masa duka a abunsha kawai Banda abinci,
Idan kinzuba kiyi flushing din kyallen.
Miqa Mata yayi ya juya ya fice Yana cewa"
Sauran bayanin idan andawo Nan zakijisha.
Fitowa yayi fuskarsa rufe da kayan bayi Mata ya wuce batareda waiwayeba ya fice gabaki daya daga gurin.
Da mamaki jekadi tabi bayan baiwar data fito daga sassan Dan Haka ta qaraso da sauri tana sake duddubawa kafin ta nufa kofar Kai tsaye tashiga
padima dataji motsi tayi saurin boye darhaman tareda janyo abincinta da bataciba gabanta tareda zaunawa ta kishingida tareda rufe idanu har jekadin tashigo.
Da rashin yarda da mamaki jekadi ke kallon koina kafin ta kalli padima Kai tsaye tace"
Kallon tsaf jekadi Tai Mata kafin tayiwa abincin da aka kawo din ta tako ahankali tana kallon abincin takai hannu ta bude tayi Masa kallon tsaf tareda Dan Kai hannunta a kaikaice taji dumin abincin Wanda baida dumi ko kadan ta dago ta kalli padiman kallon tsaf tasaki wani murmushin bazata dayasa padiman Dan washe Baki itama tace"
Saida safe ki huta lafiya"" ta juya ta fice batareda yiwa padima sauyiba ko alamar komai.
Tana fita padima ta sauke ajiyar zuciya tareda warware gashinta tasake gyarawa kullin zama cikin yalwataccen gashinta.
Ta zaro uwar dukiyar data boye tana tunanin inda zata kaita kafin tadawo.
Zagaye tafara cikin tsananin tsoro da firgici Dan ganinta da wannan darhaman masu tarin yawa zasu iya kaita lahira, gabaki daya tsoro da tashin hankali takeji wace masifar ce wannan daga zuwanta ko Paris din Bata qetaraba ta hadu da wannan balain yanxu idan taqi Yi ance abakin ranta,
Idan tafadawa wanima abakin ranta,hakama idantace zata tona tafada gskia batasan waye ya aikoba Dan aikenma fuskarsa rabi arufe babbar masifar datafisu shine idan ta aikata tayi kisan Kai ga Wanda tasan ko gunduwa gunduwan gawarta Kare suka samuci tayi arziki to ita Kam wane tashin hankali ne wannan.
Tana hada wani mugun zufa ta dauresu waje daya tareda cusawa cikin kayanta na sawa takoma gefe ta zauna har lokacin gumi take hadawa ta Nemo numbern amed sbd sanin shikadaine abokin cin mushenta na rayuwa.
Yana ganin kiranta yasaki ajiyar zuciya sbd abinda yake jira kenan Dan mahaifinsa ya fada Masa komai Dan shine yaje gurin padiman.
Dauka yayi cikin matsewa sbd har lokacin takaice yake da ita yace"
Lafiya dai ko Kira da wannan tsohon daren.
Wani wahalallen numfashi tasaki cikin qasa da murya tace"
Amed inason ganinka a Giza komai tsanani gobe Dan Allah.
Kallon mahaifinsa yayi sbd tun Rana ya iso Giza din yau shima sbd wannan tarkon nasu ya Dan sake Bata murya yace"
Sbd me zanzo kiranki?
Kinga karki rainamun da hankali Mana.
Cikin rawar murya tace"
Dan Allah amed kazo kokuma idan bazaka samu zuwa ba ka hadani da mahaifinka wlh Ina cikin wani mummunan tashin hankali ne na..... shiru tayi tana tuno maganar da Dan Aiken yafada Mata dazu hawayen cikin idonta suka gangaro Mata ta sauya zancen da cewa"
Akwai dukiyar NURU ce a hannuna inason baka ka Adana min harna dawo sbd bazan bataba batamasan da itaba.
Washe Baki yayi Kai tsaye Yana cewa"
Ganinan tafe yanzu kuwa.
Da mamaki tace" yanxu Kuma?
Kana gizah ne dama?
Da sauri yahau gyaran zancen da cewa"
Aa inanufin zan fadawa mahaifina zaishigo ya karba ta sirrance.
Bata yadda dashiba Dan taji gargada a zancensa Amma yanxu tunda tanason kubuta daga wannan saita ciro maganin da aka Bata ta Raba biyu ta bude gaban wata sarqar daham dake cikinsu tasaka dayake qaramine saiya shige ta maida Dan locket din ta rufe tana cewa"
Idan ta 'batarmin acan tareda zamuje qasa Dan ga shaida nan nasaka acikin kayan Kuma bazaka taba ganowaba.
##MAMUH#
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐๐
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐๐
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU๐๐
0903 234 5899
*_Mamuhgee 26_*
Washe gari sakayau taji ta Dan rage tashin hankalinta sbd ta rabu da dukiyar Dan hakanan taji Kamar jakadi Bata yarda da itaba ita yanxu data tabbatarda mutuwa ba abin Wasa bace data ji tafara Jin kamshinta zuwanta gizah sbd jiya harzuwama yanxu cikin matsanancin tashin hankali takejin kanta gabaki daya kusan Rabin zumudin tafiyar yabarta tsoro da shakkun abinda zai iya faruwa gaba shine yafi komai cikata yanxu gefe daya gasu abal tana Isa sukaji wani abun yafaru ayanda tasan abal dinsu dakansa zai iya bada shedar kome yafaru itace...
Gyaran muryan jekadi ya dawo da ita zurfin tunanin data shiga ta dago ta kalleta jiki duk amace ta Dan rusuna ta gaidata
Jekadi ta amsa cikin sakewa tace"
Bismillah zamu wuce Inshallah.
Janyo Jakarta tayi suka fito daganan har sassan Anneti aka fara kaita ta gaidata cikin tsananin girmamawa da tsarguwa kafin suka fito bayan sun Isa gate na biyu Dana uku Saida aka bincike kayanta tsaf kafin suka fito main gate inda dakarun tsaro suke sunfi guda ashirin suka fice daga delah gizah zuwa airport manyan motocin tsaro biyu na bayansu har airport.
********
Yau tunda safe suka fice duk su dukansu sbd exams dasuka fara ayau din ga uwa uba ita NURU tana gama da ciwon Mara sama sama dam idan zatayi period kusan kowane wata saitayi ciwon Mara ga uwa uba Imran da kwanakin Nan tunaninsa yakasa barinta Jin cewar bayada lafiya sosai
Tausayinsa takeji har cikin zuciyarta saidai tasan matuqar ba afiace zataje ganinsaba tabita itadashi iyakaci addua.
Suna fitowa yau sbd sammako dasukayi cikin itace agaba tana gyara daurin kanta na scarf fari shikuma Yana fitowa daga geamin dinsa wasu qananun zufa dasuka fiffito Masa suna gangara daga fatarsa da tsantsinta ya hanasu zama ta dago ta kallesa wata irin mummunan kunya ta kamata tayi sauri dauke Kai kasa batasan lokacinda tace"
Gud morning ba.
Kallo daya tayi Mata daga sama zuwa qasa ta dauke kansa ya wuce Kamar bai lura dasuba afia dayake tasan halin dad dinta saitayi gaba sbd sanin jinin mulkin ya motsa akansu su 'yayansa.
NURU ma hakanan tabi bayan afia tana kashe wayarta suka fada mota suka wuce.