x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 30 - UBAYD MALEEK

  • 87001 words
  • 90000 words
  • Out of 131724 words

Category: Romance Story +18

Views 203

30 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_

_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _

_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215_

_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._

_RANO NET..!!!!_



*********************
Kallo daya yayi Mata ya dauke Kai ya ajiye wayoyinsa tana ganin Haka ta dauke Kai ta nufi kofa ta fita tana sauke ajiyar juya ta nufi kitchen ta bude fridge ta dauki ruwa Mara sanyi sosai Tasha ta juyo tana rarraba ido kan kofofin palon tana tunanin zuwa ta kwanta saidai bazata iya zuwa dayan dakinba ta kwana ita kadai sbd baqon gurine gareta da gidane zata iya Kuma da farhat na Nan tsaf zasuyi kwanciyarsu ba wani tsoro.

Numfashi ta sauke tareda daurewa Takoma dakinsa dan ta nuna batamasan da wani dakinbaa a gidan
Ta bude kofar dakin tashigo ta rufe cikin sa'a bayanan Yana toilet
Ta nufi gaban madubi tasake fesa turare ta haye gadon bayan tasake gyarawa ta kwanta tareda shigewa bargo ta rufe kanta ta lumshe idanuwa tana sauke ajiyar zuciya ahankali.

Yana fitowa Bai lura da ita ba harya Gama shirinsa ya Sanya kayan bacci Basu santsi milk kala ya rage hasken wutar dakin ya nufo gadon yayi Bismillah ya hau tareda shiga bargon Yana miqa hannunsa zai gyara yajita kwance bayansa har lokacin idonta biyu saidai idanuwanta dake arufe.

Tashi zaune yayi ya Kai hannu daga kan gadon yaqara hasken dakin kadan ya waiwayo ya yaye bargon kadan Yana kallonta
Jin Haka ta bude fararen idanuwanta tareda tashi zaune batareda ta dago ta kallesa ta zura qafafunta qasa tana qoqarin sauka gadon harta sauka ta miqe tsaye taji ya riqo hannunta ahankali tareda janyota ta fado gadon kan jikinsa kirjinta dake bayyane cikin wata figaggiyar rigar bacci saiti da fuskarsa ya dago ya kalli fuskarta da itama shi take kallo kafin ahankali ya maida kallonsa kan jirkin nata da har shafar fuskarsa yanayi tana ganin hakan ta rintse ido da sauri tana zamowa qasa ahankali ta mannu da kirjinsa atare suka lumshe ido Yana zura hannunsa daya bayanta ya manneta da jikinsa gabaki daya Yana Kai hannunsa daya ahankali kan fuskarta ya shafa zuwa wuyanta dake bayyane sbd rashin hannuwa da wuyan rigar jikinta.

Wata shafawa yayiwa wuyanta data sata qanqamesa tana Dora tarin hannuwanta tsakiyar bayansa
Ya bude idanuwansa dasuka Dan sauya ya zuba Mata ta kawar da kanta gefe tana kin kallonsa sbd kusancin nasu yayi yawa Dan tanajin hannuwansa kan fatar cinyayoyinta dake bayyane sbd rigarta data Gama kwashewa ahankali taji saukar hannunsa kan mararta zuwa kirjinta ta sake rintse ido tana dauke numfashin dayashi hade fuskarshi da tata tana shaqar nasa numfashin ta bude idanu a wahalce ta kalli fuskarsa dake manne da tata tana kallo ya hade bakinsu guri daya tareda tanajin qamshin spraymintt da dandanonsa na gauraya cikin bakinta ta lumshe ido wannan karon jikinta na mutuwa gabaki daya tanaji hannuwansa na yawo jikinta dakin yadau shiru
Tanaji mararta ta murda da qarfi taji period dinta ya zubo ta lumshe idanu har lokacin bakinsu na hade hannuwansa na cikin rigarta daya zame yacire gabaki daya ya tallafota suna sauke sauke numfashi ahankali
Ya bude ido ya kalleta idanuwanta a rufe har lokacin suna manne da juna tanajin yafara sauya komai ta rintse ido ahankali tareda matso fuskarsa ta zare bakinta ahankali takai kan kunnensa can qasan maqoshinta tace"

Yazo....saita kasa qarasawa sbd tsananin kunya da sanyin jiki.

Dakatawa yayi ahankali sbd gane abinda take nufi ya lumshe idanu tareda rungumeta kawai Yana sauke ajiyar zuciya ahankali.

Shiru sukayi ahaka tsawon lokaci kafin bacci yayi gaba dashi ahankali cikin nutsuwa
Ta Dan dago fuska ta kallesa tanajin wani yanayi me qarfi azuciyarta game dashi ta gangaro da idanuwanta kan bakinsa tana tuno dandanonsa datakeji har yanzu acikin bakinta sbd mouth spray dinsa me qarfi da sanyi ne dayake dadewa abaki ta zame jikinta daga nasa ahankali ta sauka gadon tareda lalubo rigarta cikin bargon ta Sanya ta nufi toilet Dan duba kanta.
Period din yazo dai tadawo daki ta dauki pad da wani wandon ta gyara kanta ta fito ta haye gadon ta kwanta Bata jimaba bacci me Dadi yayi gaba da ita.
Da asuba Koda yatashi Bai tadataba tunda yasan batayi Yana gamawa yakoma ya kwanta Basu tashiba sai qarfe goma saura ita tafara tashi tayi wanka ta shirya ta Sanya riga da qaramin wando Suma na baccin ne ta nufi kitchen taga abubuwan da Mr Omar yakawo musu tunda safe na breakfast ta jera a dining tareda dauko sauran abubuwan buqatan cin abincin tana gamawa Takoma dakin daidai yafito wanka yagama shiryawa ta kallesa tanajin nauyi ta danne ta Kuma kallonsa tana qarasowa ciki tace"

Barka da tashi.

Kallonta yayi ya amsa Yana nufota itama taqi tafiya yaqaraso gabanta Yana kallon kayan jikinta Kamar zaiyi mgn saiya fasa ya nufi kofa Yana cewa"

Ki siya kayan sawa ta online su kawo miki.

Da wani kallo tabi bayansa kafin tabiyosa zuwa cin abincin
Takasa sakewa ta kallesa sai idanuwansa datake na yawo jikinta Haka suka Gama ta miqe ta tattara gurin tagyara ta dawo Palo ta tararda Yana waya saita zauna ta kunna tv takai murya qasa sosai sbd lurada bayason qara ko kadan.
Cartoon ta kunna sbd kewar farhat
Yana gani ya tsaya kallonta Yana aje wayar ya kalleta ya kalli TVn sai abin Bai bashi mamakiba saima murya daya qara Mata ta remote ta waiwayo ta kallesa tareda sakin wani kyakkyawan murmushi batareda tasaniba tana cewa"

Thank you.

Akaro na farko ya saki murmushi kawai Yana daukan wani file da Mr Omar ya aje Masa wainda zai sakawa hannu.

Zamansa gurin yasa takasa kallon yanda takeso yana lureda yawan kallonsa datake saiya dan dago ya kalleta ya nuna Mata kusa dashi ta taso ahankali tadawo Nan ta zauna ya miqa Mata wayarsa Yana cewa"

Ki siya kayan.

Karba tayi tana cewa" thank you ahankalin shima ya maida hankali kan aikinsa.

Da daddare yau da zazzabi takwana sbd sanyi daya 'dan shigeta yinin sbd rashin kayan arziki ajikinta shiyasa har asuba tana cikin jikinsa a lullube sai abin yazo Mata da sauki Dan duk Rabin zafin jikinta a nasa jikin ya shige duk da hakan sunsamu yin bacci sosai.
Guraren Sha daya Mr Omar yakawo Dr Damien yazo yadubata yabata yace wancan maganin daya Bata na farkoma zaiyi tashasa kawai zata ji sauki.
Da daddare da kanta tace adawo Mata da farhat baice Mata komaiba sbd baida tsarin komawarta yanxu so yake taji sauki gaba daya ta dawo normal kafin su tafi can sabon gidan.

Sabuwar rayuwar su biyu kadai aka bude a gidan Dan kuwa tuni ta warke ba wani sauran ciwon komai atareda ita sai period dinta da duka duka kwana hudu takeyi zuwa biyar ya dauke Dan Haka gobema takesa ran yin wankan tsarki.

Da daddare Mr Omar ya sanar dashi wata tafiyar gaggawa da ake buqatan maleek din Dan haka yau din batai wani bacci ba da safe karfe goma Mr Omar yazo daukansu ta shirya cikin riga da wandon pencil jeans da doguwar kimono suka fito Mr Omar yasaka kayansu mota suka shiga suka wuce har lokacin hankalinsa duka na kan waya sbd al'amarin babbane Dan ayanda takeji kaman daga gizah ne.

Zibrian suka Isa cikin qatoton sabon gidansa dake cikeda ma'aikatansu na tsohon gida kowa yakomawa aikinsa tun na tsohon gida hakama kayanta nacan duk ankwaso muta abinda duka,
suna shigowa har bakin kofar palon Shiga Mr Omar yayi parking mota suka fito Yana kallonta Yana karantar yanayinta
Suna shiga farhat ta qaraso da gudu ta fada jikin NURU tana cewa"

I miss you aunt.

Sakinta tayi tafada jikin dad dinta tana cewa"

I miss you both.

Janyota NURU tayi tana cewa"

Sweetie zo Naga kafanki
Ta warke ko?
Bata sakaki zazzabi ba ko?

Na warke aunt NURU kawai dai banajin Dadin bakya Nan Afia Bata nan daddy ma bayanan.

Murmushi NURU tayi tareda duba kafar tana cewa"

Shikenan ai gashi muntaho ko
So muje kifadamun me mum Sarah ke Baki Naga kin qara karfi.

Aunt kema me daddy yabaki kin qara kyau aunt, daddy Nima zanci abinda kasiyawa Aunt NURU.

Shiru NURU tayi cikin tsananin kunyar Mr Omar daya dauke Kai Yana sosawa da mum Sarah data Dan janyo farhat din tana cewa"

Muje mukaiwa aunt dinki kayanta dakinta.

Wucewa maleek yayi Yana Hana murmushinsa bayyanuwa ya nufi hanyar zuwa dakinsa
NURU ta miqe tabi bayan farhat data Kama hanyar dakin dasukace nata.

Kofar da maleek yashiga Nan suka Shiga wani palon ne dayafi na farko tsaruwa sai kofofin bedrooms guda biyu na maleek shine kurya nata farko Kuma da Alama nashin zaifi nata girma sosai sbd ta fahimci shi mutum ne me raayin makeken daki kokuma tace daga sarautane hakan.

Dakinta ta bude tashiga sanyin AC Dana qamshin turarukanta dake jere a gaban madubi Kamar za'a bude shago dasu suka doki hancinta ta qaraso tsakiyar dakin tana kallon koina cikin burgewa sbd komai na tsarin dakin Kamar ansan raayinta.

Wardrobe ta nufa ta bude tana waiwayowa ta kalli farhat saitaga ba ita zata tambaya ba ta maida kallonta kan kayan dake shaqe da wardrobe din ta waiwaya gefen kayan bacci batasan lokacinda tasaki murmushi ba tana Jin kunyar abinda tagani ta rufe tana duba bangaren takalma Suma dai kusan duk kowane designer brand akwai.

Gurin wayarta dake gaban madubi ta Isa bayan ta jera kayan data dawo dasu a dauka tareda kunnawa zata Kira gidansu saiga farhat data fita tadawo dakin tace"

Aunt kizo daddy na Kira.

Aje wayarta tayi suka fito tare ta nufi palonsa na cikin kofar bedroom dinsa suka Shiga tareda farhat Yana zaune kan kujera Yana duba wayarsa yaji shigowarsu Bai dagoba saidata kusa isowa dab dashi ya kalleta kafin ya kalli farhat data naniketa Kamar zata gudar Mata.

Kashe wayar yayi tareda Miqewa tsaye da wayar a hannunsa Yana kallonta yace"

Gizah zamuje da Mr Omar duk abinda zai faru ki sanar Dani a waya.
Akwai tight security anan Babu Wanda zai shigo bada izininki ba dan Haka ba kowa za'a bawa izinin shigowanba.

Wani card ya ajiye Mata akan table ya wuce harzai gota ta ya tsaya tareda kallonta yayo qasa ahankali setin kunnenta yafada Mata password na card din Yana fada Mata lips dinsa na gugar kunnanta ta lumshe ido ta bude ahankali tana kasa dagowa ta kallesa sbd kunya ga farhat a tsaye tana kallonsu cikin burgewa duk da batasan meyake faruwa ba farin cikin kawai takeyi.
Kallonta yayi yaso sakin murmushi ya fuske ya wuce ta biyosa baya daf da zai fice palon ta tsaya bayansa ahankali tace"

Allah ya yadawo dakai lafiya.

Yace Amin batareda ya waiwayoba ya fice tabi bayansa da kallo.
##MAMUH#
*_Mamuhgee 36_*


_*YERWA INCENSE & MORE*_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_

_(MASARAUTAR KAMSHI)_

_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._

_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_

_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_

_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_

_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_

_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215/09044191709! _

_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_



****************
Suna fitowa Kai tsaye wani qaramin underground gidansa dake cikin anguwar suka nufa Wanda keda 2 bedrooms rak da manyan Palo guda biyu sai kitchen me hade da dining acikinsa komai na gidan is milk Mr Omar ne kawai yasanda gidan Babu Wanda yasan gidan nasane Haka gidan komai a kip kip yake anan yake wasu private wayoyinsa da ayyukansa hakama wata maganar me buqatan tsananin sirri anan suke zuwa suyita da Mr Omar.

Parking Mr Omar yayi yafito ya budewa MALEEK yafito kafin yabudewa NURU ita saiya zagaya ya budewa farhat tareda kamo hannunta suka biyo bayan maleek dake gaba tareda NURU dake tafiya ahankali sbd ciwon Mara.
Suna shiga palon NURU ta dago ta kalli koina cikin palon cikeda mamakin tsaruwar gidan da cikin yafi wajenma kyau sosai saidai sbd yanayinta bazata iya qarewa koina kalloba a matse take data samu guri ta kwanta Tasha ruwan zafi masu zafi Sosai ko zata Dan fada Mata tasamu period din ya sauko wahalar ta rage Mata.

A palon farko ya dakata tareda kallonta Yana nuna Mata kofar palon qurya inda bedrooms suke cikin nutsuwa yace"

Ki Shiga ciki zanyi mgn da Mr Omar.

Dan dagowa tayi ta kallesa har lokacin ita yake kallo ta gyada Kai ahankali ta juya farhat na riqeda hannunta suka wuce cikin.

Palon cikin baiyi girman na farkon ba Amma yafisa tsaruwa ta juya gurin bedrooms din ta nufi Wanda yake damarta ta murda tareda budewa ahankali batasan lokacinda ta sauke ajiyar zuciyaba sbd ganin girma da tsaruwar dakin ga makeken gadon daya kusa cika dakin komai fes fes sai qamshi koina gidan keyi da Alama kullum Ana gyara koina agidan ayi mopping Dan ko yau kila anyi Dan qamshin dayake koina dagaji sabon gyarane.

Tana Isa bakin gadon ta sulale ta haye tareda kwantawa tana dungulewa guri daya tana dafe mararta rufe idanuwanta tana Jin Dan dama dama data kwanta din.
Sai daga baya ta bude idanuwanta ahankali ta kalli farhat da duk tayi wani iri sbd halinda aka shiga sai taji yarinyar tasake shiga ranta sbd tausayinta ta cire hannu daya takamota kusada ita ta bude Baki daqyar tace"

Sweetie kadakiji tsoro ko damuwan komai kinji daddy Yana Nan Nima Ina Nan Afia ma zatazo komai lafiya Inshallah,yanzu Kinga Banda lafiya I can't treat and drss your wound kije kifadawa daddy Akira mum Sarah tazo ko Dr aduba kafanki kafin anjima nasamu naji Dan sauki kinji.

Gyada Kai tayi tareda juyawa ta fice zuwa gurin daddynta din.
Tana fita NURU tasake nadewa guri daya kaman jira Marar keyi ta kwanta tasamu nutsuwa sai ciwon yasake taso Mata wani irin zafi da zufa suka fara karyo Mata ta tashi zaune daqyar ta kunna AC Takoma ta kwanta tana shigewa cikin bargon dake kan gadon me tsananin laushi fari tas.

Kallon Mr Omar maleek yayi yace"

Kasan abinda zakayi next idan an daukosu din.

Gyada Kai Mr Omar yayi Yana cewa"

Za'a kaisu wancan gidan ne na 7579 zibrian kowa yasan aikinsa yakama suyi gyaran koina Kafin zuwa gobe ko jibi ku Isa can din.

Gyada Masa Kai maleek yayi Kai tsaye zai juya saiga farhat ta qaraso gurinsa ta shige jikinsa tana cewa"

Daddy aunt NURU batada lafiya bazata iya duba ciwona ba tace Akira min mum Sarah ko Dr" taqarasa fada tana nuna kafarta.

Kallon kafar sukayi dukkaninsu inda ruwan zafin suka zubar Mata a kafa sai alokacin sukasani ga 'yar farar kafar tata har tayi ja
Maleek ya dago ya kalli farhat din yace"

Aunt dinki bazata iya duba Miki qafanba ta gyara?

Eh daddy tun jiya da daddare aunt NURU tace cikinta na ciwo haryanxu be Dena ba gurin karbo Mata tea ne ruwan zafin ya zuba a kafana mum taketa fada.

Shiru maleek yayi kafin ya dago ya kalli Mr Omar dayayi saurin rage kansa Yana cewa"

Za'a kaita gurin Sarah acan zibrian ta kula da qafar kafin ku iso zankira Dr Damien ma yazo ya duba kafan Inshallah.

Kama hannun farhat Mr Omar din yayi Yayi gaba suka fice ya nufi mota ya bude ya sakata ya zagaya yashiga Yana waya da Edward akan idan sun Isa zibrian din da kowa yace Masa eh ankai kowa Babu Wanda aka baro a tsohon gidan sai tsohuwan madam da princess afia.
Kashe wayarsa yayi ya fita harabar gidan yahau hanyar zuwa zibrian din Yana yiwa farhat 'yar Wasa tadawo yanda take sbd yarinyar ta Dan razana da komai daya faru.

Bayan tafiyar Mr Omar ya juyo Kai tsaye ya nufi hanyar dayan bedroom Wanda ba nasaba ya Murda Kai tsaye ya tura yana kallon koina baiganta acikiba ya fito tareda rufo qofar ya nufi bedroom dinda yake gefe dabam Wanda yake matsayin nasa Yana zuwa ya bude kofar ahankali ya shiga tareda rufowa yana kallon yanda ta kwanta a dungule ya ajiye wayoyinsa kan qaramin glass table dake gefen sofar dakin ya qarasa gadon tareda tsayawa akanta Yana kallonta har saidataji mutum tsaye akanta ta bude idanuwanta ahankali ta dago dasu ta kallesa ta Mayar ta rufe tana yunqurin tashi zaune ya dakatar da ita ta hanyar Kai hannunsa daya ya maidata kwance Yana kallon wuyanta daya taba yaji zafi.

Wayarsace tayi blinkin na wuta batareda ya daukaba ya waiwaya ya kalli wayar yaga massage din Mr Omar ne daya rubuto" _Dr Damien na ya iso Yana kofa_

Zaunawa yayi bakin gadon tareda yaye bargonta ahankali tareda tayarda ita zaune da kansa Yana kallonta ahankali yace"

Dr Damien zai dubaki.

Zuba Masa idanuwanta dasukai laushi tayi tanason ce Masa Bata buqatar likita Amma sai batace komaiba ta gyada Masa Kai tana matsowa bakin gadon ta zura qafafunta qasa ya miqa Mata hannunsa ahankali ta dago ta kallesa kafin ta Dora nata akai ta Kama nasa ya miqar da ita hannunta cikin nasa suka fito Palo suka sake wucewa zuwa na farko acan suka tararda Dr Damien tareda Mr Omar dake tsaye Yana ganin fitowarsu ya sauke Kai tareda juyawa ya fice Dan Basu guri.

Daga yanda Dr Damien yafara tambayarta tabashi amsa Kai tsaye Dr Damien ya fahimci ciwonta yace"

Bawani matsala bane menstrual pains ne kawai
Ya Bata pain reliever da wasu maganin ya miqe ya fice.

Kallonta maleek yayi Kai tsaye yace"

Kina buqatan wani Abu?

Gyada Kai tayi tana miqewa suka nufi ciki tana cewa"

Zanyiwa Mr Omar texting dinsu.

Kallonta yayi bayan sunshiga dakin ya matsota jikinsa sosai ya ranqwafo da kansa daidai fuskarta yace"

Kiyi online shopping akawo daga can Mr Omar baya buqatan sanin abubuwan dazaki buqata.

Kasa dagowa tayi ta kallesa sbd sai lokacin ma takejin kunyar ciwon nata da maganar Dan kuwa itama bazaso Mr Omar tayi Masa texting su pad da panties da kayan bacci da komaima.

Rintse idanu tayi tareda zamewa ta juya ta nufi bakin gadon ta zauna tana tunanin dame zatayi shopping din ba tunda batada wayarta atareda ita.

Miqa Mata wayarsa yayi bayan ya bude Mata password ya fice daga dakin.

Panties da bra dasu pad sai turaruka da kayan bacci data siya guda uku sbd tasan zuwa anjima ko gobe za'a kawo musu kayansu na sawa itada farhat sai brushes data siya musu itada farhat da kayan baccin farhat
End Ads