x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 34 - UBAYD MALEEK

  • 99001 words
  • 102000 words
  • Out of 131724 words

Category: Romance Story +18

Views 205

30 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
tsaye na nufi da akwai matsala babba sbd ko yayane dai tasan sirrinsu Kuma idan har ta tabbata 'bata tayi to maleek ya ankaro da akwai masu Masa zagon qasa kenan.

Kwana biyu yakoob na tsananta mugun nmbincikensa acikin gizah batareda sanin kowaba ko ankarewar kowa akan sha'anin bincikensa ya tabbatar Masa da cewan tabbas padima ta dawo gizah saidai Babu Wanda yaganta Kuma alamu da binciken da yayi a airport sun tabbatarda tareda jekadi ta iso gizah Kuma motar cikin masarauta ce ta dauko su take ya fada laluben drivern daya daukosu cikin direbobin masarauta suka cabkesa tareda boyesa wani mugun wuri cikin masarautar suka fara gana Masa muguwar azaba harsaida yafada musu cewar tabbas ya dauko jekadi da padima yafadi inda ya ajiyesu.

Gyara tsayuwa yakoob yayi tareda sauke Kai qasa Yana gurfanawa cikin tsananin girmamawa da sassauta harshe yace"

Allah ya taimaki neges tabbas tunaninka gaskia ne wannan yarinya tadawo cikin gizah tareda jekadin maleek saidai haryau Babu Wanda yaganta ko yasan inda take Wanda hakan ke nuni da MALEEK yasamu masaniyar akwai abinda yake faruwa Dan Haka yarinyar yanzu rayuwarta nada gargada akan sirrin Nan duk da batasan komai gameda aikin datayi ba saidai bama buqatar bawa kuskure kofa a dukkanin aikinka neges.

Wani numfashi neges AL'MANSOOR yasaki Yana gyara zaman mulkinsa kan wata doguwar kujerar hutawarsa dake cikin palon shaqatawarsa na kuryar sassanshi ya Dan waiwayo ya kalli amintaccen nasa yakoob yace"

Kartayi mutuwar banza ayi amfani da ita tunda ita tasaka kanta aciki,
Maleek Yana tsallake komai to Bari muga ta Yaya zai tsallake wannan,
Aci amfanin yarinyar na karshe
Tsohuwar matar maleek din takira da tata matsalar nabata damar zuwa dukkaninsu zasuyi Mana amfani Dan haka kasan abin daya kamata kayi.

Angama me delah da gizah.

Juyawa yayi ya fice daga Palon yabi ta wata hanyar dazata fiddashi sashen batareda kowa tagansaba ya fice.

Washe garin ranar lailah ta sauka a gizah Wanda yasa kowa cikin mamaki sbd sanin Bata taba zuwaba sai tareda maleek shima Saida babban dalili bare yanxu dasukejin kishi kishin rabuwarta da maleek sai zuwan nata yasaka kowa cikin mamaki musamman Anneti saidai Bata nuna Mata komaiba.
Matsalar farko data fara fuskanta shine sassanta shine akaiwa sabon gyara da tsari yazama na NURU saidai tun kafin zancen ya habbaka yazama wani al'amarin daban Anneti tasaka aka gyara Mata wani sassan daban Wanda beyi girman na NURUn ba ko kadan aka Aiko Mata da bayi biyu masu Mata hidima Wanda hakan yayi mummunan baqanta Mata wato har anan dinma saita fuskanci wulaqanci irin wannan?
Hmm zatayi lokacin kowa daga baya har Annetin sbd bazata dauka wulaqanci irin wannan ba.

Wanka tayi sai alokacin tasamu damar Dan cin wani abinci Takoma daki ta kwanta Dan hutu take tsananin buqatar yi ayanxun ko kyawun fuskarta ya dawo daidai na rashin hutu da bacci da nutsuwar dabata samuba tun shekaran jiyan sbd fitinar dake gabanta Dan haka zata huta sosai kafin tafara fitowa aganta asan haryanxu tana Nan a LAILAH MALEEK dinta kyakkyawar mace me lokaci.

Ta bangaren jekadi kuwa ganin yadda jikin padima yarikice yasata kebe kanta cikin dakinta ta nemi numbern Mr Omar tayi Masa bayanin dukkanin komai ta Dora cewa lailah na gizah ta iso.

Shiru Mr Omar yayi tareda sauke Dan numfashi sbd baiso katse hutu da Jin dadin maleek ba Dan kuwa hutun gaske maleek din keyi a kwanakin Dan ko ayyukansu tuni suka taru suna Nan Yana Dan kokari Yana rage masu rayuwar sbd maleek din yasamu hutawa dakyau Amma Kuma wannan zancen Dole ya sanar Masa dashi.

Sake sauke numfashi yayi yace"

Zan sanar Masa duk abinda yace zakiji Amma dai kafin Nan inaga ki Dan Bata maganin meriz din kadan tasamu karfin Koda kyakkyawan numfashi ne sbd na tabbatarda maleek bazaiso ta rasa ranta ba dama amfanin riqeta din asan asalin su waye suke aikin Amma dai zan sanar Masa yanxu Inshallah.

Kashe wayar yayi tareda sake fitarda numfashi me zafi Yana tunanin Dole ya isarwada maleek wannan sakon batareda Bata lokaciba duk da ba Haka yasoba
Yaso ubangidansa yasake samun hutu wadatacce Dan kuwa tsawon shekaru Basu samu irin wannan hutawarba sbd kullum cikin aiki da bincike suke matuqar ba ciwoba maleek baya sati biyu a jere zaune baiyi tafiya sai kwanakin Nan dayaga alamar kila har fiyeda watama zasuyi suna hutawa yanxu ga wani aikin.

Ajiyar zuciya ya sauke akaro na biyu kafin ya daga wayarsa ya Nemo numbern MALEEK ya saka Kira Yana nutsuwa tareda daidaita murya
Saidata kusa yankewa kafin maleek din ya daga cikin kamewa yace"

Yes Mr Omar.

Barka da hutawa MALEEK,
Dama saqone daga gizah, jekadi takira jikin yarinyar Nan yakasa daukan meriz tana cikin mawuyacin halinda kowane lokaci zata iya rasa ranta shine jekadi ke neman qarin umarnin taci gaba da aikinta kokuwa ta dakata daga Bata din?

Shiru yayi na wasu seconds daidai fitowar NURU daga wanka fatar jikinta na daukan ido ya zubawa fuskarta fararen idanuwansa batareda ta ankareba yaji tunaninsa na sauyawa akan padiman ya sauke boyayyan numfashi ahankali tareda Miqewa tsaye ya fice daga dakin ya nufi Palo Kai tsaye yace"

Kada ta Bari wani Abu yasameta ta Bata magani sosai
Zamu sauya tsarin bincikenmu batareda yarinyar ba ta jinyaceta ta warke a maidata gida gurin iyayenta
Kada abari iyayen su San abin daya faru da ita sbd kada su 'dagawa 'dayar 'yarsu hankalin.

Angama maleek.
Sai maganar Mahaifiyarsu li'iliti tana gizah ta Isa Kuma ga dukkanin bayaninda jekadi tayi Kamar da umarnin neges ta Isa can sbd bada umarninkaba,badana Anneti ba badana kaleeb ba to tabbas idan badakuba shikadaine yakeda ikon Bata damar zuwa tunda ba sauran ummnnn wannan a tsakakaninku."ya qarasa fada Yana Dan rawar murya fada sbd girmama auren MALEEK din duk da ya rabu.

Shiru maleek yayi Jin abinda mr Omar yace
Ya Dan sake gyara tsayuwa Yana tunanin Dole akwai dalilin neges na bawa Lailah damar zuwa gizah ta zauna itakuma gata idanuwanta sun rufe gabaki daya batada tunanin komai yanxu saita yanda zata farfado da kanta ta jikinsa take ya yanke shawaran zuwa gizah ya bude Baki cikin nutsuwar murya yace"

Kayi Mana Shirin komai gizah din zamuje wannan karon Ina buqatan tunatarda wasu waye maleek Incase idan sun samu mantuwa.

Yes maleek"Mr Omar yafada Yana kashe wayar maleek din take yakira ya sanarda tafiyar maleek aka garzaya karban tickets da komai.
Yaso barinta anan gidan yaje yadawo tukuna Amma Kuma bazai iyaba sbd duk tsoron dazai Bata hankalinsa zaifi kwanciya idan tana cikin mutane shiyasa ya maidata can gida zibrian gaba daya kafin suka wuce.

A gizah kuwa sosai yakoob yagano akwai abinda jekadi ke boyewa musamman Dama sunsan Dole itakadaice tasan inda padima take sbd itace wadda tashigo gizah din da ita Dan Haka ya kasa ya tsare cikin taku sosai harya gano inda take zuwa acan bayan sassan maleek duk da Bai Isa cikin sassanba ya isa kofar yasan akwai babban abinda maleek yasakata take boye gurin dangane da padima Dan Haka yakoma yafadawa neges komai
Cikin wani irin yanayi neges ya murmusa Yana jinjina Kai yace"

Ayi aike gurin tsohuwar matar maleek lailah cewa nabata damar zuwa muyi mgn.

Allah yaqara ma girma da lafiya."yakoob din yafada Yana yin baya baya ya juya ya fice.

Ta bangaren lailah kuwa yau ta samu damar Isa gurin hutawar neges Dan maganar aurenta da maleek data kawota har cikin palon akai Mata iso ta qaraso gabansa ta gaidashi cikin girmamawa kafin ta zauna cikin tata isar ta zamtowarta Matar asalin me mulkin
Take aka fara shigo da kayan marmari dasu Zuma da kayayyakin tabawa aka cike gurin tsab ta dago ta kalli kayan tareda dauke Kai sbd hakan tamkar cin fuskane ga maleek ace macen dake matsayin matarsa tana zaune gaban wani Wanda ba maleek ba har akawo Mata abinsha Dana ci Ana nufin taci gabansa wannan rashin darajar yayi yawa tana matsayin Matar maleek guda.

Numfashi ta sauke tareda waiwayowa ta kallesa Kai tsaye cikin tausasa harshe tace"

Allah ya taimaki neges me gizah ta yanxu ina maka barka da hutawa tareda barka da ganin wannan lokacin.

Kallonta yayi daka zaman hakimcen dayake ya Dan saki fuska wani murmushin dattijantaka na sauka kan fuskarsa yace"

Neges ya amsa Kuma Yana biki barka da fitowa medakin maleek na gizah.

Lailah tunda tashigo cikin zuriarsu take tsaye a wuyansa sbd mace ce me tsananin son mulki da Isa tareda kwadayin komai yazama Yana qarqashinta da ikonta Dan kuwa Jin take kamarma itace maleek din sbd sosai ikonta da gadararta ke bayyanarda mijintane me kujerar sosai take shigar Masa hanci Yana dannewa sbd taku da zamanta sirikarsa amma zai Bata darasi daidai da ajinta sbd ita takawo kanta gurinsa yanzu neman mafitar matsalarta da maleek.

Cikin nutsuwa da kulawa ya Dan juyo da Kai a kame yace"

Abu dayane akan matsalar aurenku da maleek shine karkata da hankalinsa yayi ta wani bangaren
Ma'ana wani Abu daya rinjayi tunaninsa akan iyalinsa.

Dagowa tayi cikin mamaki tace"

Akwai abinda ya rinjayesa kuwa bayan wannan auren da yayine...

Wani murmushin yakuma saki Yana cewa"

Mace bazata juyarda maleek ba ko wacece kuwa nafi sakaran wani Abu daban Wanda Banda sani akai Amma Dole saikin Saka ido kin bincika kin gano kafin asan inda gyaran zai faro.

Shiru tayi tana nazarin zancensa sbd Bai wani shigetaba zancen Dan kuwa duk me lafiya ya kalli al'amarin dakyau zai fahimci cewan Babu wani dalilin sauyawar maleek zallar halinsane rashin daukan reni ko kadan sai aure daya qara take hasaso wani abun daban Amma tunda yafadi hakan zata bincika tagani Dan a shirye take da maganin dukkanin abinda zai shata Mata layi da zamowa Matar maleek.

Batareda ya kalleta ba yasake Dora Mata tunanin bibiyar daddaqin abinda maleek ke tunani ta hanyar bibiyar jekadi sbd itace mafi amintar maleek a duk gizah da rayuwarsu bayan kaleeb da Mr Omar ko mahaifiyarsa Anneti batasan sirrinsaba sai wainnan mutanen uku.

Da wannan tunanin sosai lailah tasakawa jekadi ayar tambaya Dama tajima da sanin jekadi maqiyiyarta ce ba kauna atsakaninsu munafukartace kodan yanda tasamu cikakken bayanin jekadi itace tsaye akan komai na NURU a rayuwar maleek Dan Haka ta kanta zata fara saita rusa yardar dake tsakaninsu da maleek bayan tasan menene matsalar tukuna.

Bayan tabaro can sassan Anneti ta nufa akaiwa Anneti shelar isowarta tashigo cikin shigar alfarmarta kamar koyaushe ta zauna ta gaida Annetin Kamar dai yanda suka Saba cikin yanayi na Ni Matar neges nikuma Matar MALEEK Babu wata qarin Hira akai sbd Lailah har cikin ranta duk tsanarsu da qiyayyarsu takeji sbd sune munafukanta dasuka tsayawa NURU akan auren MALEEK Dan Haka Bata wani tsayaba ta wuce tabar Anneti da bin bayanta da kallon mamakinda baigama sakintaba saidai bazatani takan zancen lailah ba zata jira maleek yazo tana buqatan bayanin dawowan lailan.
##MAMUH#*_Mamuhgee 39_*


_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_

_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_

_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_

_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_

_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._

_MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_

_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_

_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_

_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_

_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _

_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234 803 081 1300/+234 808 540 5215_

_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._

_RANO NET..!!!!_



****************
Direct dakin afia din NURU ta nufa data fito farhat ma ta tashi tana biyeda ita suna shiga dakin ta waiwayo tana kallonsu farhat ta qarasa gurinta da gudu cikin tsananin farin ciki me yawa tana cewa"

Yeeee afia.

Rungumeta afia tayi cikin farin cikin ganinta da kewarta datayi kwanakin tace"

My baby I love you I love you.

I love you too afia Kuma nayi kewanki sosai musamman kafin Aunt NURU da daddy sudawo nikadai dasu mum Sarah munata Jin dadinmu.

Rungumeta tasakeyi tana kallon NURU dake kallonsu cikin murmushi ta qaraso tana kallon afia din tace"

Sannu da zuwa.

Murmushin afia tayi tareda sakin farhat taqaraso gaban NURUn suka Dan rungume juna NURU ta bude Baki ahankali tace"

Am sorry afia ban....

It's ok yawuce Dan nice yakamata na Baki hakuri akan abinda mum Dina ta...

No afia yawuce kaman yanda kikece abar maganar.
Zamewa sukayi NURU na gyara tsayuwa tace"

Bari natayaki jejjera kayanki a dakin kafin agama breakfast muci.

Tayata bubbude kayan tayi suka jere suna fira anan NURU ke sanarwa afia din gobe zata fara zuwa Court Inshallah ita dayake tafara zuwa asibitin kafin wannan rigimar ta dakata sai itama tace gobe zataci gaba da zuwa kada tun wuri rashin bada himma yashiga cikin aikin.

Suna gamawa NURU ta fito ta nufi dakinta tayo brush ta sauyo Kaya ta cire na baccin dake jikinta wainda takejin nauyinsu tun dazun agaban afia.
Afia dasuka zauna cin abinci Bata wani samu damar sakewa taci sosaiba sbd tunanukan dasukai yawa akanta musamman na mum dinta da batasan meyake faruwaba a gizah din ga dad dinta har lokacin wayarsa Bata Shiga gashi takasa tambayar NURUn dad saidai ta tambayi farhat tafada Mata yayi tafiya baya Nan.

Sosai NURU ke kokarin janta da fira sbd su samu duk su dukan su sake dan sukoma kaman yanda suke wannan sabon yanayin nasu bayayiwa kowaccensu Dadi
Da Haka dai gurin firar suka fara sakewa suna danne komai tareda qoqarin mantawa kawai ahaka dai har dare yayi suka kwanta washe gari kowannensu ya tashi kan lokaci sbd Shirin fara fita zuwa gurin ayyukansu
Sukai breakfast suka fito NURUn na sanye da white long sleeves da White pencil trauser sai black kimono har qasa sai brawn and white scarf dake kanta da takalmi wedges na _Le labo_ sai handbag da Jakarta rigarta
Afia kuwa cikin jeans da shirt take sai white coat dake jikinta ta likitocin asibiti suka fada mota Edward ya fita dasu aka fara aje afia kafin aka wuce aka Kai NURU.



*************
Ranarda jekadi suka iso gizah tundaga shigowarsu padima ta 'dan kalli jekadi tana gyara zama cikin motar da aka daukosu daga airport tace

Saqona na NURU datace za'a bani ko za'a banishi tun ayau inason hada kayana guri dayane idan ba damuwa.

Waiwayowa jekadi tayi ta kalleta tareda sakin murmushin manya tace"

Babu matsala saqonki a Daren yau Zaki fara karban abinki basai kin damu kanki da tambayawarbama za'a Baki komai dukkanin abinda Kika cancanta.

Murmushi padima tayi tana dauke Kai tareda cewa"

Yawwa dai Ngd Sosai.

Suna Isa har kofar dazata sadasu da sassan Matar maleek ma'ana sassan NURU anan akai parking suka fito Kai tsaye suka shige hanyar suka wuce sassan NURU sukabi wata hanya sukai tafiya me tsayi datasaka padima fara waiwaye tana son yin mgna Amma tana dannewa sbd tasamu tafara riqe abinda za'a Bata din tukuna.

Sassan maleek suka nufa suka kusa can baya sosai inda wani boyayyan gurin sirrinsa yake jekadi ta waiwayo tareda kallon padima tana bude kofar tace"

Bismillah shigo daga ciki.

Ba wani tsoro padima ta qaraso tana leqawa ta shige sbd ganin kamar dakin ajiyar dukiyane ta qarasa ciki tana dube dube tanajin matsuwar abata abinda za'a Bata ta bar gurin sbd kaman tsoro da fargaban gurin na neman shigarta.

Mintuna biyar ba'ayi ba da shigarta saiga jekadi dauke da ruwa da drinks masu sanyi a tray ta qaraso tana ajiyewa kan table dake dakin tana cewa"

Bismillah.

Dagowa padima tayi ta kalli tray din kafin ta kalli jekadi tace"

Anan ne saqon yake?

Wannan karon jekadi Bata kalletaba tace"

Eh saqon ne za'a Baki idan kinyi hkr Yana isowane.

Shiru padima tayi cikin qaguwa da gagfawarta ta saqon yashigo hannunta tasaki guntun tsaki cikin ranta tareda Kai hannu ta dauki lemun takai bakinta tafara kurba ahankali tana kallon kofa tana Jin matsuwarta na qaruwa harta shanye lemun ta dauki ruwama Tasha kadan ta ajiye tareda Miqewa dagakan kujera daya tal dake dakin sai table da kayan adon daki masu kamar zaiba ta juyo tana kokarin komawa ta zauna taji wani irin gumi da zafi zafi me tsanani Yana tasowa daga cikin jikinta ta hadiye wani wahalallen yawu sbd bakinta dake gauraya da wani irin mummunan daci ta juyo da sauri tana share gumin fuskarta tana kallon jekadi da alamar tashin hankali da azaba tace"

Me Kika bani???
Me kikeson yimin???
Innalillahi wayyo Allah
Mutuwa zanyi azaba nakeji me tsanani....
Wurgi tayi da dankwalin kanta tana fige rigar jikinta cikin wata mummunar azabar dabata taba Jin makamanciyartaba arayuwarta ta zube qasa tana yagar jikinta tako Ina tana cewa"

Dan Allah ki taimakeni
Jikina cikinsa wuta ake hurawa
Dan Allah kibani ruwa
Zan mutu......

Shure Shure tafara jikinta na rikidewa jajir duk inda ta Sosa Kota fizga saiyayi wani irin kumburi kaman wuta ta koneta a gurin take ta haukace tana Shure shuren azaba tana ihun mummunan yanayi Jin takeyi kamar ruwan dalma na sirkuwa cikin jininta da bargonta..

Ihunta yasa jekadi juyawa ta fice daga dakin tareda rufewa ta waje ta cire qaton mukullin ta bar gurin Takoma can kofa daganan ta dauki hanyar zuwa gurin Anneti da akaiwa isarwada sakon zuwan jekadi.

Da murmushi Anneti ta kalli jekadi tace"

Barkan jekadi da dawowa lafiya,
Muna fatan anbaro Mana su maleek da mushransa tareda 'yayansa lafiya?

Da murmushi akan fuskan jekadi cikeda biyayya tace"

Alhmdlh muka barosu Inshallah.

Masha Allah to Yaya bakuwar mushrah?
Da ita kuka dawo dai Ina fata?

Sauke Kai jekadi tayi tace"

Da ita muka dawo saidai tariga ta wuce delah inshallah Bata biyo ta Nanba.

Masha Allah shikenan kije kihuta kin debo gajiyar Kai baquwa da dawowa da ita Dan Haka kije ki huta na tsawon kwanaki shida bakya buqatan fitowa kawo gaisuwa nabaki daman hutawa tukuicin Kai baquwar NURU da dawo da ita.

Cikin tsananin farin ciki jekadi tace"

Allah yaqarawa Anneti tsawon Rai da lafiya tareda girma, jekadi godia take sosai da matuka.

Murmushi kawai Anneti tayi tareda gyada kai tana cewa"

Amin.

Tashi jekadi
End Ads