yaceda padima dake tsaye idanuwanta sunyi jajir zuciyarta na wani irin zafi da harbawa.
Kai tsaye sashensu datake dasu afia aka maidata sbd saqon maleek daya Isa gurin jekadi ta hanyar Anneti cewar basai ankar NURU gurinsaba yau din gobe zasu koma,
Tana Isa ta tarar da Afia zaune tagama hada musu kayansu tsaf sbd suma dad ya sanar cewa gobe zasu koma dama amatse take dasu bar Nan din sukoma Kota samu kanta tayi tunanin abinda yakamata.
Tsayawa tayi daga bakin kofa tana kallon afia da duk damuwa da sanyin jiki ya bayyana atareda ita taji tausayinsu su duka ya dawo Mata sbd tafi kowa sanin burin afia akan dawo da mahaifiyarta gidan MALEEK gashi yanxu su duka qaddara ta bullo musu ta inda basa zato.
Qamshin NURUn daya cika gurin yasata dagowa sukai ido biyu kowa yakasa motsawa suka tsurawa juna ido kafin Afia ta taso ahankali ta qaraso gaban NURUn ga mamakinta saitaji afia din ta rumgumeta tana cewa"
Thank God you're back NURU nayi kewarki.
Mamaki yasata daskarewa batareda tace komaiba ko motsawa.
Afia kuwa tarigada tasan zaman aure ko rayuwar aure tsakanin NURU da dad dinta bamai yiyuwa bane har abada Dan haka Bata sawa ranta damuwaba Dan duk duniya Babu Wadda dad dinta zaiso idan ba mum dintaba Dan haka tasan shima idan har aka koma Babu wani maganar aure dazaibi hakama NURU tana komawa Imran yadawo bazata yarda ba Imran zataso komawa Dan haka ta daure tacire damuwar komai aranta.
##MAMUH#
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐๐
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐๐
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN qNUMBER TAREDA SHEDARKU๐๐
0903 234 5899
*_Mamuhgee 22_*
Washe gari tunda safe sakon Anneti na gayyatarsu cin abincin safe tareda ita ya iso musu suka shirya dukkaninsu itadai jekadi dama tunda safe tazo da kayanda NURU zata saka tana Palo takasa ta tsare Dan kuwa komai daya danganci NURU yanxu saiya biyo ta gurinta kafin ya isa gun NURUn.
Da kanta tashirya farhat kafin itama ta shirya cikin doguwar royal gown dinsu me adon golden stones da sequence rigar ta tafine straight shiyasa ta fidda shape din tudun qirjinta zuwa shafaffen cikin har fadin hips dinta saidai adon sequence ne ya 'dan boye bayyanar shape din nata Sosai Sosai Amma duk da hakan yafito sai wuyan rigar dakeda Fadi sosai ta Sanya qaramar siririyar sarkar gold ta doro gyalen rigar akanta ta rufe gashinta dake daure Yana qamshin turaren hayaqin da akai Masa ta fito afia nabinta da kallon yaba kyawun datai Wanda duk be daga Mata hankaliba tunda dai duk abanxane suka fito jekadi na bayan NURU sai sauran masu Binsu suna bayansu kawunansu duk a soke kasa.
Afia ce ke kokarin janta da firar karatunsu da tun shekaran jiya yakamata su koma Amma Basu komaba itama NURUn abin sai lokacin yafado Mata musamman da tafara zuwa Court itama afian tana zuwa asibiti sama sama sbd karatun nasu.
Tun kan su qaraso aka sanarda zuwansu suna isowa suka tararda askarawan maleek kusan guda shida a sassan Anneti din afia na gani tasan dad dinsu na ciki ita Kam NURU batasaniba tunda Babu abinda tasani anan din Dan haka Babu tunanin komai dayazo Mata suna isowa aka wangale musu qofa Ana yiwa NURU gaisuwa ta musamman kafin aka juyo akaiwa AFIA da farhat suka shige.
Suna shiga palon farko duka sauran Yan rakiyarsu suka tsaya anan dagasu se jekadi suka wuce har cikin asalin palon hutawar Anneti suna shiga jekadi ta zube qasa cikin bada girma tace"
Allah yaqara MALEEK kyakkyawar zuciya data fuska,barka da fitowa.
Da hannu kawai ya amsa tareda juyowa Jin muryar AFIA na gaishesa cikin girmamawa itama.
Farhat kuwa kusadashi ta zauna tareda riqe hannunsa tana cewa"
Good morning Daddy.
Da sauri jekadi ta Raba gefen NURU data kusan sanqamewa a tsaye sbd shammatarta da abin yayi Sam ko kadan ko qamshinsa batajiba batama taba saka ran zata ganshi ananba.
Kallon afia yayi da idanuwansa masu haske cikin sautinsa na kamewa ya amsa Mata tareda cewa"
Kuna lafiya?
Gyada Kai tayi tana cewa"
Yes Inshallah.
Ahankali NURU ta tako ta qaraso ciki ta tsaya ta gefen NURU cikin sanyin murya batareda ta kallesa ba kanta na 'dan qasa tace"
Barka da fitowa.
Tsit gurin yayi kafin ya dago ahankali itama ya kalleta Wanda yayi daidai da fitowar Anneti tasaki murmushin ganinsu ta nufi hanyar dining room tana cewa"
Farhat zo ahau table cin abinci Afia zokiyi serving Dina.
Dan kallon NURU afia tayi ta sauke idanuwanta akan budaddiyar gaban rigarta daya bude sosai Dan idan har ba shedan ne yake Mata gixoba tana hango saman nonuwar NURUn kadan ta juya ta wuce tana Dan waiwayowa harta shige dama farhat ita tuni tashige.
Dauke idonsa yayi daga kanta tareda Miqewa baice komaiba ya wuce ciki.
Ajiyar zuciya ta sauke a boye sbd idan har akwai abinda yafi takura da firgici tashiga sbd taji idanuwa akanta saidai Babu tabbacin nasane Kona afia.
Kokarin zama takeyi taji Anneti takira sunanta tafasa ta nufi hanyar dining room din a sukwane tana Dan sauke Kai tana shiga Anneti ta nuna Mata kusada ita ta qaraso ta zauna kirjinta na bugawa sosai sbd duk wannan abin wani iri takejinsa Yana Mata nauyi sbd zuwan komai lokaci daya.
Afia ce tayi serving kowa Nan suka hau cin abincin Babu me mgn musamman itadai gabaki daya bataci abinda ya wuce Loma hudu ba sbd amatuqar takure take.
Maleek ne yafara tashi ya fice kafin Anneti saisu daga baya suna fitowa tuni aka fitarda komai na tafiyarsu suka dunguma zuwa ainihin fadar NEGES inda yayiwa NURU kallon tsaf kafin ya kalli MALEEK Dan kuwa yatabbatarda NURU bazatayima sa'ar afia ba Amma maleek ya aureta.
Yanaga Dole akwai dalilin dayasa MALEEK auren wannan yarinyar wadda akace asalinta ma 'yar bawan kaleeb ne,
Idan har da akwai dalili saiya bincika yaji Dan kuwa wannan karon bazai dagawa MALEEK qafaba Dan Bai shirya sauka mulkiba ya bawa MALEEK kujerarsa Dan haka zai binciki asalin ita yarinyar da zuriarta dole baza'a rasa abinda zaiyi amfani dashiba daga ciki ya rusa maleek gaba daya saiya mallaki kejeran da hujja.
Kyauta me girma yayiwa NURU tareda su afia kafin aka fito da NURU sai alokacin kowa yaganta 'yan jaridu kuwa sukaita dauka wasuma a sace suke daukar hotunan hadda maleek batareda sun saniba.
Kayan aure da aka bawa NURU Dole saidai aka barsu anan a hannun jekadi data riga yanxu tadawo gizah sbd sassan NURU daza'a fitar a tsara itace zata zauna Dan duk lokacinda NURU zataxo tananan Dan haka kayan acan sassan NURUn za'a ajesu.
Har airport jekadi ta rakasu tana sake jaddadawa NURUn wasu bayanan na cewa wannan aure ba saki ba warwarewa,aurene daya qullu har abada Dan haka ta nutsu ta rungumi abinda Allah yabata ta riqe da kyau tareda kiyayewa Banda Kuma yarda da kowa sbd za'a iya biyowa ta gurinki a cutatar da maleek.
Itadai saurare take kawai Dan batamasan wane turn rayuwarta zata daukaba daga yanzu Kuma.
Harsuka shiga jirgi suka miqa tana cikin tunanin yanda zatai rayuwa agidan amatsayin matar dadynsu afia gashi haryanxu bataga wani Alama daya nuna afia bataji dadin abinba ta bangare daya ga Imran datasan yanacan Yana jiran dawowarsu batasan me zatace masaba ya fahimta.
Sai dare sosai suka sauka motocin daukarsu suna airport jiransu Mr Omar sai wani rawar jiki yakeyiwa NURU Wanda yasa MALEEK yimasa kallo daya ya nutsu ya daina aka barta cikinsu afia kamardai yanda suka Saba tun ada.
Suna isowa gida su mum Sarah suka tarbesu suna zubewa yiwa MALEEK barka da dawowa Kai tsaye ya wuce samansa bayan ya amsa musu da hannuwa.
NURU suka jiyo sunawa barka da dawowa taredasu afia wadda tayi gaba sbd sai yanxu taji tasamu nutsuwa harwani ajiyar zuciyar nutsuwa take sakewa farhat mum Sarah takama hannunta suka nufi dakinta Dan wanka da hutawa.
Koda NURU tashigo daki afia harta shiga wanka Dan haka itama a qage ta cire kayan jikinta ta dauko towel ta daura tana warware gashinta afia ta fito tana gama warwarewa ta nufi toilet din tashige ta sakarwa kanta ruwan zafi tana rufe ido itamadai kusan dawowa gidan yabata nustuwa.
Tana fitowa ta Sanya kayan bacci ta saka jallabiya akai tayi sallolinta tana gamawa ko ruwa Bata nemaba ta cire jallabiyar ta haye gado ta shige bargo sai bacci Wanda afia tuni tayi nata baccin.
Washe gari sai guraren 11 dukkaninsu suka fito kowanne a shirye Banda farhat da har ankaita school sukuma sai zuwa gobe zasu fara zuwa.
Kai tsaye dining suka nufa suka zauna breakfast afia na fadawa nuru suna buqatan zuwa shopping sbd kusan turarukansu da mayukansu dasu shower creams dinsu duk sunyi qasa gashi ita tana buqatan wasu books na karatunta data siya tun last month sun iso ankirata tazo ta karba.
Ruwa NURU Tasha ta aje cup din tana cewa"
I also need some books zanbincika idan munje.
Miqewa tayi ta nufi daki tana shiga wayarta na ringing ta qarasa ta dauka cikeda mamaki da tsoro ganin Imran ne me Kiran ta ajiye wayar tareda kifewa hankalinta na neman tashi,
Me Imran keyine dazai kirani bayan nasan yariga yasan abinda yafaru.
A musulunce a al'adance duk laifine me girma Amma duk da hakan zatai magana dashi tafada Masa Dole hakuri zasu dauka haka Allah yaso Babu aure atsakainsu.
Tana daukan wayar tana tsinkewa sai kawai ta ajiye tareda kashe wayar gaba daya ta nufi closet dinsu ta janyo dogon pencil jeans da riga doguwa har qasa saidai daga qasan a tsage take har cinyoyi Wanda yasa ake Dan ganin jeans din idan tana tafiya ta janyo veil ta daura harta dauki wayarta sai ta fasa ta ajiye ta juya ta wuce.
Afia Dama a shirye take suka fito afia da kanta zataja motar yau suna sako qafafuwansu waje NURU ta tsaya cak wani tunani Yana fado Mata na sanin yanzu fa ita Matar aurece batada ikon fita kona kanta.
Waiwayowa afia tayi ta kalleta tana cewa" lafiya Kika tsaya?
Numfashi NURU ta sauke tana basarwa kada afia tagano dalilinta saita riqe gefen cikinta tana Dan yamutsa fuska kadan tace"
Marata tana ciwo inaga period Dina zaizo kije Bari nakoma na kimtsa najira zuwansa Dan kowane lokaci zaizo.
Da wani irin kallon mamaki afia tace"
Amma ai ba lokacin period dinki bane.
Sake yamutsa fuska tayi tace"
Eh ba lokacinsa bane Amma inaga abubuwan da akaita banine a gizah dama tun can sunata sani ciwon ciki.
Kallon mamaki da tsoro afia Tai Mata takasa cewa komai sai kawai ta juya tana cewa"
Shikenan ki koma Ni zanje nadawo.
Juyawa tayi Takoma ciki tana shiga Palo tana ta sauke ajiyar zuciya ta nufi daki ta cire rigar ta sauyo da qarama Mara kauri tabar wandon ta nufi kicin direct Dan aikin abincin Rana Kota samu abinyi dazai hanata zaman tunani.
Tanayi su Fana da mum Sarah na tayata harta gama tafito ta jera a dining tana baro dining din saiga farhat andaukota daga school tun daga Palo tana shigowa tace"
Aunt NURU yau akwai drwing dazamuyi babba na _Eiffel tower_ competition ne inason nazama 1st.
Yes yes sweetie Inshallah zamuyi shi babba me kyau Wanda zaisa ki cinye afterall who's gonna help you drw????
Da qarfi tana tsalle tace"
Our beautiful Aunt NURU.
Hmmn that sounds like a bribe sbd bantaba Jin kince our NURU ba saidai kice your NURU to yau kenan kinyadda keda afia.
Suna qarasawa kofar shiga palon kurya farhat na cewa"
No not afia,Ina nufin me and my dad since you are his wife now.
Tsit NURU tayi sakamakon hada ido datayi da maleek dayake saukowa tayi saurin dauke kanta tana riqo hannun farhat wadda ta kwace tayi gurinsa tana cewa"
Daddy barka da fitowa.
Kama hannunta yayi Yana nufar hanyar dining Yana cewa"
Hw is daddy's little princess?
alhmdlh dad but today I have.......kallonta yayi cikin nustuwa yace"
Go and freshen up first kafin kizo naji menene.
Da gudu tayi ciki tabarsu tsaye sai alokacin NURU tadan gyara tsayuwa tana rage murya qasa qasa tace"
Barka da fitowa.
Kai kawai ya gyada Mata ya nufi dining Wanda yasata Dole binsa Dan serving tunda dai Babu kowa agurin.
Zama yayi taqaraso cikin Jin nauyin kayan dake jikinta musamman dayake kujeransa tana seti da inda take tahowa tamafi Jin kunyar rigar dake jikinta din sbd Ana ganin yanayin kalar bra dinta fara ta ciki sbd transparent ce Amma ba sosaiba Dan Bata tana tunanin har lokacin Yana gidaba.
Tana qarasowa tafara serving dinsa cikin nutsuwar Dolen data tattarowa kanta.
Tana gama zuzzuba Masa ta nufi kicin ta hado drink dinda tasan yanasha tareda ruwa masu sanyi Amma ba sosaiba takawo ta aje tareda zuba Masa drink din a cup ta Dan dago kadan ta kallesa zatai magana ta rude ta kasa sbd kallon dayayi Mata yasata neman rudewa hartana neman fada Masa Bata saniba Saida ya tareta da hannunsa daya Wanda ya ba tsammani ya sauka daidai kan shafaffen cikinta daga ita harshi da saida suka kalli juna ya dauke Kai Yana kamewa tareda janye hannunsa tayi saurin juyawa tabar gurin jikinta na neman sakewa sbd duk duniya Babu Wanda yataba taba mararta sai yau gashi abin kamar na tsautsayi batasan yaushe rigarta tadan dagaba Dan kuwa direct taji saukan dumin hannunsa akan skin dinta da gudu taqarasa daki ta nufi toilet da gudu sbd har wani fitsari fitsari takeji na shiga rudu.
##MAMUH#
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐๐
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐๐
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU๐๐
0903 234 5899
*_Mamuhgee 24_*
Saida safe dukkaninsu sukasan farhat batada lafiya Koda suka Isa dakinta tana zaune jikin dad dinsu Yana zaune bakin gadonta sanye da black jallabiya ta maza me tsananin taushi sai kyallin maiqo takeyi alamar ta masu abun duniya ce.
Itace agaba ashigowa kafin Afia Amma tana ganinsa tayi slow afia ta wuceta tana qarasa dayan gefen ta farhat din ta zauna tana cewa"
Gud morning dad,
Farhat bakida lafiya bamusaniba mum Sarah ke fada Mana yanzu da safen Nan.
Dago fuskarsa yayi dake fayau dinta sai wani daukan ido take ya kalleta da idanuwansa Wanda itama daidai shi ta sata kallo suka hada ido tayi saurin sauke idonta muryarta da wani irin salon sanyi dabata saniba tace"
Barka da safiya.
Har lokacin kallonta yakeyi
Tasake dagowa ta saci kallonsa suka sake hada ido sai kawai tunanin ganin dayayi Mata jiya da daddare kusan Babu komai a jikinta take wata matsananciyar kunya ta mamayeta batasan lokacinda ta rufe idoba ta fita da gudu Kamar karamar yarinya.
Da mamaki afia ta dago ta kalli kofar kafin ta juyo ta saci kallon dad dinta da bataga alamar ma yasan da NURU tashigo bare tace kofar yake kallo ta maida kallonta kan farhat tana cewa"
Sorry baby aunt NURU taje Sanyo kayane sbd batasan dad na Nanba ta taho da sleeping dress ajikinta shine Takoma ta sauyo nasan kin matsu tazo gurinki ko baby?
Gyada Kai farhat din tayi tana kwantawa jikin afia din tace"
Afia I saw mum yesterday a school dinmu she was there before I fainted......
Da sauri AFIA ta dago ta kalli farhat din tareda kallon dad dinsu da sauri shima saidai ko Gama juyowa batayiba ya miqe ya fice kamarma baiji me farhat taceba afia tabi bayansa da kallo kafin tadawo da kallonta kan farhat cikin mamaki tace"
Baby dagaske Kinga mum?
Gyada Kai tayi tana kallon afia din tace"
Eh naganta tazo kafin ta iso gurina I fainted daganan shikenan saidai Naga dad kawai.
Wani yawu afia ta hadiye kafin ta ta danne mamakinta da farin cikinta tana miqewa tace"
Ok baby Bari naje naturo Miki NURU tazo tayi Miki wanka da brush saita Baki abinci akwai abinda zanyi yanzu na gaggawa ok baby.
Wucewa tayi ta fice da sauri ta nufi dakinsu ta janyo doguwar riga tasanya akan kayan baccin jikinta ta dauki wayarta da sauri ta fice ta nufa library dinsu Dan Yin waya.
Doguwar kimono NURU ta doro akan kayan jikinta na bacci kafin ta wuce ta nufa kicin ta hadawa farhat Dan guntun breakfast sharp sharp ta dauko a qaramin faranti ta nufa dakin tana adduar Allah yasa ya fice.
Ganin baya dakin yasata qarasowa da wuri ta ajiye tray din tana cewa"
Sweetie kiyi hkr bamu San bakida lfy ba,jiya ma anan nayi wanka Amma banluraba sbd hankalina yatafi wani gurin dabam na......kasa qarasawa tayi tana sake tunano abinda yafarun sai kawai ta sauya zancen da sakin qaramin murmushi tana cewa"
Ok sweetie muje ayi brush kizo ga breakfast sai asha magani.
Tayar da ita tayi suka nufi toilet din suka shige.
Harsuka gama komai har wanka da Shirin farhat din kafin suka fito zuwa nasu dakin itama NURU tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga suka fito Palo ta kunna Mata cartoon takoma ciki tayi Shirin makaranta tazo ta fice har lokacin afia Bata shigowaba tanacan.
Tsaye take cikin libry din idanuwanta sunyi jajir sbd tsananin baqin cikin dake mamaye da zuciyarta ayanxun datake waya da mum dinta cikin tsananin sanyin murya da sarewa tace"
Haryanxu Babu 'yayanki acikin ranki kenan?sbd wani burinki na duniya mum kike fadar haka? Tayaya kike tunanin dad zai iya rayuwa ahaka for how long kikeso yayita jiranki?mum please ki......
Cikin iko da muryarta me taushi ta katse afia da cewa"
Zandawo wa MALEEK Amma ba yanxuba haryanxu akwai abubuwan dake gabana,afia kinada naci akan zance daya koyaushe bayan nace Miki zandawo Amma ba yanzu ba idan akwai abinda yafi cancanta yanzu dakiyi shine ki raba maleek da yarinyar daya aura Kuma tabar gidan gabaki daya sbd matuqar tananan koya saketa bazan iya dawowaba infact inason sauyin gida tunda harta zauna a wannan gidan koba komai idan haryanzu kunason aikinta zaku iya zama da ita acan Amma dai Ni Kam a sauyamin gida musamman farhat da lalurorinta sunyi yawa yau ciwo gobe lafiya....
Cikin mamaki,takaici da baqin ciki daya Gama kashe afia tabude Baki tace"
Mum shin akan abindake gabanki kika watsar da 'yayanki musamman Yar qanqanuwa Kamar farhat harkina cewa lalurarta yayi yawa?
Ciwone fa atareda ita Wanda Allah ne ya Dora Mata ba ita tadorawa kantaba, badan NURU ba da yanzu dukkanin mu munshiga wani hali and now kina cewa akoreta?a koreta kokuma mubita can mu zauna kenan kin