za'a jita ba ruwanki bane ki Kama bakinki kadaki fadawa su abal abinda zaisasu damuwa sbd padima ba ruwanki da abinda zai kawo musu bacin Rai ko damuwa.
Kiji da matsalar gabanki ta zaman aikin gida da renon mijin wata Ni kibarni zanji dasu abal din naki idanma labarin yakaimusu wata Rana Dan yanxu banjin zanyi lokacin isar musu da wannan labarin inada nawa sabgogin kawai dai kishirya min komai nafada Miki gida zankoma.
Wucewa tayi ta fice daga dakin tabar NURU nabinta da kallon takaici takaici sbd halin padima dai haka yake tun suna yara saidai kwana biyun Nan datazo musu tayi tunanin tafara sauyawane shiyasa taketa kiyayewa sbd kada suyi halinsu agabansu afia subarwa kansu abin takaici.
Zaunawa tayi kan kujera tana furzar da numfashi tace"
Zanyiwa jekadi magana ta maidaki tun kafin mufara halin acikin gidan Nan tunda kinji kingani kinfasa neman lafiyar ai shikenan kije ko Dan lafiyar iyayenmu.
Da daddare har daki tasamu jekadi zata zauna jekadi tayi saurin miqewa tana cewa"
Ba girmanki bane mushrah idan kinason ganinane duk inda kike zan sameki naji bayaninki ko umarninki.
Murmushin yaqe kawai tayi sbd duk ranta a jagule yake yau din daga wannan sai wannan.
Daga tsayen ta kalli jekadi da taushin murya da zallar gajiya da damuwar komai tace"
Jekadi padima zata koma gida jibi nafadawa Mr Omar yayi muku komai na tafiyar,
Idan kunje kibata wadataccen kaso acikin wainnan dukiyar dake can na dukiyar auren......kasa karasawa tayi sbd Jin nauyin fadar kalmar aurenta
Itakuma jekadi Jin tayi shiru tace"
Yanda kikace haka za'ayi Inshallah"sbd ta fahimci abinda take fada.
Godiya jekadi keyi Allah yaqaro girma da kusanci tsakainki da MALEEK tareda tabbaciyar qauna.
Shiru tayi batareda tace komaiba saima sanyi da jikinta yayi ta juya zata fice jekadi tadago takalleta cikin tausayi da kaunarta saitaji bazata iyaba ta gyara tsayuwa tareda aje matsayinta na jekadi takira sunan NURUn cikin tsananin kulawa kaman yanda ta Saba a da.
Tsayawa NURUn tayi tareda waiwayowa ta juyo gaba daya damuwarta na raguwa sbd tasan jekadinta ta Da ce kafin tazama Matar maleek.
Takowa jekadi tayi tazo har gabanta takamo hannunta tajata zuwan kan kujera ta zaunar da ita kafin itama ta zauna ta fuskanceta cikin kulawa a natse tafara cewa"
NURU aure da kike gani Kona soyayyane saika dage da kulawa da naci akan wasu abubuwan sbd kusan a rayuwar aure ke mace kece zakija ragamar Kama hanyar zuwa wani mataki,
NURU kinshigo wata irin baudaddiyar rayuwar aure wadda kike buqatar juriyada kokartawa kafin kisamu matsayinki na Matar gida idan ba hakaba rayuwarki da quruciyarki zasu qare su tsufa cikin tausayi me tsanani,
Aure gidan sarauta musamman irin naki auren dayake da qalubalai da tazarori masu yawa,
Shawara daya anan itace ki maida hankali ki dage karki dage a Gina karatu kawai ki zauna kiyi nazari aurenkima kina buqatan dage Masa Dan bawa kanki suna da matsayi a gidanki sbd karki tsufa agidanki bakisan suna ko matsayinki a gurin Wanda kike aureba Dan kuwa wannan wata rayuwace da Kika shigo ba Babu fita sai mutuwa hakama akwai qalubalai agabanki Dan haka ki nutsu kiyi abinda yakamata kiyiwa kanki yaqi kema Dan tabbatarda zamanki acikin aurenki sbd auren MALEEK babban rabone agareki ki,
Kibude idanuwanki ki daina yadda da kowa da komai sai abinda zuciyarki ta nutsu dashi NURU.
Sai alokacin ta dago ta kalli jekadin jikinta duk yakuma yin sanyi ta bude baki ahankali tace"
Nagode jekadi.
Gyada Mata Kai jekadi tayi tana miqewa tace"
Ranki ya dade Zaki iya tafiya.
Miqewa tayi ta nufi kofa tana Jin gabaki daya gajiya takeji sbd sanyin da jikinta ketayi ayau din daga wannan sai wannan.
Dakin farhat ta wuce kawai sbd acan zata samu nutsuwa yanzu kawai
Tana shiga ta nufi toilet tayo alwala ta fito daidai shigowan farhat Nan suka shirya sukai sallah tare daganan tacewa farhat baccin awa biyu zasuyi kafin la'asar
Nan suka kwanta.
##MAMUH##
KUYI MANAGE.
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
*_Mamuhgee 30_*
_*YERWA INCENSE & MORE*_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: _08095215215/ 09044191709_
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_
***************
Washe gari tunda safe Kamar kusan dai yanda ta Saba kitchen ta nufa aikin breakfast tayi su Fana da mum Sarah na tayata suka hada abincin safen saina maleek data hada Masa daban ta jera a tray sbd har lokacin Bai fara saukowa qasa cin abincin tareda 'yayansa Kamar yanda ya Saba ba
Ga afia har lokacin batasan yayi rashin lafiyaba ko da safen taje har sama ta gaidashi Amma bataga komaiba lafiya kalau ta gansa.
Tana gamawa tabarwa Fana aikin jera abincin a dining ita ta dauki nasa ta fito saidataga alamamun afia na daki kafin ta haye sama cikin sa'a kuwa baya palon saita ajiye ta juya ta fitowarta.
Tana saukowa dakin Farhat ta nufa Dan har lokacin bacci take itama kusan gidan yau kowa na gida tunda hutu suke.
Zaunarda farhat din tayi tana cewa"
Sweetie kitashi Haka fa ko kinmanta yau zamuje yawo.
Cikin bacci ta bude Yan idanuwanta tace"
Aunt ai ba yanzu zamuba Saida Rana kibari muyi bacci Mana.
Murmushi tayi kawai tareda kyaleta ta wuce toilet dinta anan tayi brush ta fito ta nufi dining Bata jira kowaba ta zauna taci ta koshi ta tashi ta nufi dakin padima dake zaune tana latsa wayarta ta dago suka kalli juna tasaki murmushi tace"
Ranki ya dade ta tashi kenan.
Batajin biyewa padiman Dan haka ta datse zancen da cewa"
Padima idan kinci abinci ki shirya anjima zamu fita ko.
Kashe wayar tayi tareda dagowa ta kalli NURU data tsaya tana kallonta cikin son Jin wayene baida lafiya taga duk afian tashiga damuwa.
Numfashi me zafi ta fitar kafin ta zauna bakin gado cikin sanyi tana cewa"
Jikin Imran ne yayi tsanani tana cewa sai anyi Masa aiki,
NURU inaga duk wannan nice sanadi.
Kallonta NURU tayi jikinta amace sosai itama da tausayin Imran din sbd tabbas tasan Imran na Mata so me qarfi Amma ya suka iya Haka qaddara ta taho saidai hakuri.
Muryarta a Sanyaye tace"
Kidaina fadan haka wannan duk yin ubangiji ne haka ya tsaro dama
Shima Inshallah zaiji sauki ahankali zai Saba ya rungumi kaddara da zaran yasamu wadda zata kula dashi.
Kallonta afia tayi da tunanin idan kulawa zatashi mantawa da komai ya dangana ya warke itace tafi kowa kamata tabashi sbd itace sanadin rabasu harya shiga wannan halin Dan haka Inshallah zatai iya kokarinta gurin sauke wannan alhakin dake kanta ko Dan haqqinsu ya sauka daga kanta.
Shiru sukayi dukkaninsu kowa da tunanin daya Dan fada musamman NURU datake ganin gwara Imran din yasan rashinta shine takamaimai matsalarsa idan yaso yaqar matsalar Yana tilastawa kansa mantawa da ita shikenan yayi maganin tasa matsalar
Amma ita haryanzu batasan matsayin kantabama bare tasan meye tata matsalar hartakai ga maganinta
Ita kawai rayuwar take aduk yanda tazo Mata.
Qarfe biyu Sukayi wanka suka shirya
afia ta fita zuwa Taya farhat shiryawa tabar NURU na sauya wasu kayan sbd riga da wando tafara sakawa taga basuyiba ta sauya zuwa riga da skirt Suma taga basuyiba qarshe ta Sanya wasu maroon _Yves Saint Laurent_ riga da wandon Palazzo dasuka fiddo zallar yarintarta na matashiyar wayayyiya musamman kalar ta yiwa fatarta kyau ta Sanya wedges takalmin _CH/HC carolina Herrera_ black tazo gaban mirror zata fesa turarukansu dake jere saita fasa ta dauki _Lady l_ na _Acqua di parma_ ta fesa Wanda ya hadu da kamshin body mist dinta da spray na _ royalle Nina Ricci_ suna bada qamshinda sai ka kusantota sosai zakajishi
Tana daura scarf a kanta afia tashigo ta Isa gaban mirror tasake gyara fuskarta ta juyo tace"
Everyone is waiting for you fa kowa yafito.
Wayarta kawai ta dauka Banda handbag suka fito tareda afia din wadda itakuma heels ne takalmanta kusan Koda yaushe.
Suna fitowa Palo farhat tayi gurin NURU da duk ta cika musu ido musamman padima datake Mata kallon qyashi kafin ta dauke Kai tana sakin boyayyan tsokin da NURUn taji Amma ta qyale kaman bataji komaiba suka fito dukkaninsu afia ke driving sai ita NURUn a gaba sai padima da farhat sai jekadi a bayan.
Mr Omar yaso NURU tabi motar driver sbd ganin kaman sunyi yawa a motar Amma tace tafi buqatan cikinsu din suka fice Yana musu adawo lafiya.
Gurin wasan farhat suka fara zuwa sukayi kusan 2 hours agurin kafin suka fito suka tafi wani qaton mall
acan suka Bata lokaci sosai Dan sai yamma sbd irin kayan da padima tayita dauka Babu Wanda yace tabari
Dan kanta dataga kayan sunmata nauyi tabari suka fito aka aika duka siyayyan kayan dasukai direct zuwa gida da motar mall din.
Har zasu fito afia ta nufa bakery dinsu akai Mata packaging cupcakes guda shida masu icing na chocolate kadan ta biya ta karbo ta nufosu NURU ta kalleta tana cewa"
Mezakiyi da cupcakes?
Zamu biya dubiyan Imran a hospital so nayi tunanin abinda zamu Kai bansaniba kila wannan zaiyi.
Mum manta duka amma da a gida za'ayo Masa wannan din Amma ko hakan ma inaga yayi.
Mota suka shiga suka nufi hanyar asibitin farhat se murna takeyi zataga Uncle Imran sbd akwai shaquwa da sabo tsakaninta dashi Dan Kam acikin dangin mahaifiyarsu shikadai tasani duk da shima bawai tasan asalin asalin alaqarta dashiba kawai abinda tasani uncle Imran kaman family dinsu ne.
Suna Isa harabar asibitin sukai parking dukkaninsu suka fito NURU da afia ne agaba sauran na biye dasu NURU na riqeda hannun farhat wadda sai tsalle tsalle take tana cewa"
Aunt NURU mu bamu siyawa uncle imran komaiba kaman afia.
Murmushi tayi tana cewa"
Munkawo Masa addua ai muma.
Receptionist suka tambaya room number din Imran jalal tafada musu a third floor room 10.
Suna zuwa kuwa dakin na farko farko afia ce tafara knocking tareda bude kofar ta tura tashiga ahankali da sallama abakinta saidai ganin wadda ke dakinta yasa dukkanin bakinta qafewa saidai gudun wani tashe tashen bacin Rai da bazasu qari kowa da dadiba yasa ta danne ta qarasa shigowa dakin NURU da afia suka shigo hannun farhat har lokacin yana riqe acikin hannun NURU.
Kallo daya NURU tayiwa Matar dake zaune ta dauke wuta zuciyarta na harbawa da qarfi ta dauke Kai ahankali tana kallon afia da yanayinta ya sauya gabaki daya ta maida kallonta kan dad din Imran din dake tsaye da Alama fita zaiyi duk saitaji tana neman shiga wani mummunan hali ta samo nutsuwa daqyar cikin kannewa ta saki fuska ahankali tacewa dad din Imran din"
Ina wuni,ya me jikin?
Alhmdlh Mrs MALEEK
Ya gida?ya maleek?and fmly?
Alhmdlh sir"tafada tana waiwayowa gefen LAILAH dake zaune dukkanin qamshinta na turaren _Calvin klein boss lady_ yacika dakin tana sanye cikin wasu set na byredo ash kala komai nata kana gani kasan manyan kudadene suka siyesa musamman makeup din dake fuskarta Wanda akoda yaushe LAILAH Bata rabuwa da ita.
Wani abune ya wucewa NURU da kayar tasamu numfashinta ya saki ta bude Baki daqyar tace"
Barka da yini miss.
Wani irin murmushin tausayinsu su duka yaran tasaki sbd sai yau Allah yayi zataga matarda maleek yake aure yanzu,
Afia ta kalla zatayi magana
Afia tarigata da cewa"
Ina wuni mum.
Kin amsawa tayi tana cewa"
Wannan shine sabon manner dinki da farhat?
Da mamaki afia ta kalleta tace"
Sabon manner kuma mum?
Maida kallonta tayi kan farhat dake jikin NURU tana kallon lailah da dukkanin hankalinta sbd tanason zuwa gurinta tana shakkar irin tsawar da lailan ke Mata wani lokacin duk Bata mantaba sbd lailah batason Ana fado Mata ajiki kokuma yaro yace koyaushe Yana cikin jikinta.
Farhat kixo ki gaida mum.
Wani kallo lailah tayiwa NURU wadda gabaki daya Bata sake kallon inda lailan takeba sbd Jin take gabaki daya dakin ya gundureta ga Mr jalal ya fita ta zare hannunta daga na farhat da har lokacin take tsaye bataje gurin mum dinba ta nufi gurin Imran daya bude idanuwansa alokacin ya zuba Mata ta qarasa gurinsa ta zauna kan sofa ta qaqalo murmushi daqyar tace"
Ka tashi kenan Yaya jikin?
Bai dauke kallonsa daga kantaba ya gyada kai Yana miqawa farhat hannu cewa tazo.
Lailah zuwa lokacin ranta yafara baci sbd kowa sai acting dumb yakeyi ta gyara zama ranta nafara baci akan afia tace"
Afia nice na haifeki komai girman dakike ganin kinyi Dan haka you better stop acting dumb with me kafin ranki ya baci kokuma kinason nunamin zama da bayi kin manta girman uwarki,...
Da mamaki afian take kallon mum din cikin rashin sanin abinyi tace"
Mum please idan wani yabata Miki Rai acikinmu daga zuwanmu kiyi hkr Amma wlh Ni bansan me mukayiba anan,
Farhat kije gurin mum ki gaidata nace....
Just shut up afia
before I lose my cool ki fita daga gabana Dan Naga gabaki daya kin rasa tarbiyanki Kamar Ni Ina Miki magana kina cewa Farhat ta gaidani sbd nace Miki gaisuwan ne agabana kawai.
Hawayene suka ciko idanuwan afia sbd gabaki daya batasan metayiba da mum din keta faman wannan janye janyen ta bude Baki cikin rawar murya tace"
Kiyi hkr mum Amma dai kaman kina saukemin fadan da banawa bane.
Sai alokacin NURU da duk takejinsu ta Dan waiwayo afia din takai hannu zata dafata sbd ganin yanda hawaye suka tsinke Mata
Lailah ta aika Mata wani qanqantaccen kallo tana cewa"
Excuse me miss wannan tsakanin uwa da 'ya ne stay within ur limits ok
Bana saka trashes cikin al'amurana
For God's sake ma meyasa haryanxu kikeda auren MALEEK akanki bayan duniyama tasan bazaki tana zama Matar da maleek zai iya zama da itaba
Ke yarinya ce bazaki gane hakan ba Amma nasan Zaki gane kalmar pack and leave sbd ma nafasa komawa San Francisco zandawo gidan sbd afia na wannan little ant din sun dauki wani hali da bazan dauka ba..
Jekadi da padima dake bakin kofa suna Jin komai dadin duniya yagama kashe padima duk da Jin takeyi Kamar tashiga tayiwa lailan mugun duka Amma dai Kuma yanda take nuna isarta akan 'yayanta da NURU ta mallake yasata Jin Dadi taji inama tanada ikon shiga dakin taga yanayin NURU sbd har lokacin NURU Bata juyo ta sake kallon ko gefenda lailah maleek takeba sai lokacinda tace zata dawo rayuwar MALEEK NURU ta waiwayo ta kalleta daidai suka hada ido lailan ta gyara zama zatayi magana aka turo kofar data Sanya NURU kallon kofar da idanuwanta dasukai jajir sukai ido biyu da MALEEK Wanda Mr Omar ya budewa kofa
Shima ita ya kalla dakyau sbd baisan da zasuzo asibitin ba Amma ganin su jekadi a waje yasa yasan suna ciki.
Dauke kanta tayi tareda maidawa kan Imran sbd rashin sanin abinyi Dan gabaki daya dakin jintake numfashinta a toshe yake.
Lailah dake zaune har lokacin ta zubawa maleek fararen idanuwanta tana jiran abinda zai fara fitowa daga bakinsa idan ya idanuwansu suka Shiga cikin na juna.
Da fararen idanuwansa ya kalli Imran dake kokarin tashi Amma Babu me kamasa sbd NURU ce kawai a kusa dashi afia har lokacin tana gaban mum dinsu hawaye take na baqin cikin wannan halin da mum ta nuna.
Cikin kamewar murya Kai tsaye MALEEK yace"
Kana samun sauqi kenan,
Allah yaqara lafiya.
Maida kallonsa yayi kan NURU dataqi waiwayowa ta sake kallon kowa ahankali yace"
Muje.
Dagowa tayi ta kallesa direct cikin ido kafin ta dauke tana miqewa tsaye da wayarta a hannu ta wuce batareda ko sai anjima tayiwa Imran ba sbd a rayuwarta Bata taba yin mummunan danasaniba Kamar zuwanta asibitin Nan yau.
Tana fitowa Jekadi ta taso zata bita Mr Omar yayi saurin Yi Mata hannu Yana nuna Mata MALEEK da ido Takoma ta zauna tana cewa"
Allah ya tsare hanya MALEEK.
Harya fita ko afia alamu Basu nuna yasan dasu a dakinba bare lailah harya fice,
Ita kanta afia tashiga shock
ta dago ta kalli mum dinsu da Bata nuna damuwaba sbd tasan halin MALEEK dama Dole saita fuskanci fushinsa kafin yasan yanda zata sauko dashi dakanta sbd soyayyarta me qarfi dake ransa,
Ganin NURU yanzu datayi yasa taji bazata iya komawaba tana buqatar kasancewa da maleek yanzu Dan kuwa batai tunanin NURUn takai hakanba duk da yarinyace Amma tanada wani irin kwarjini me fizga.
##MAMUH#*_Mamuhgee 31_*
_*YERWA INCENSE & MORE**_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_
_(MASARAUTAR KAMSHI)_
_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen had’i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._
_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_
_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: ___08095215215 / 09044191709_
_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-‘dai_
*************
Mr Omar ita yafara budewa kofar mota tashige kafin ya zagaya ya budewa MALEEK yashige shima ya zagaya yashige ya tada suka bar asibitin sbd fita irin wannan Mr Omar shine yakejan MALEEK hardai idan zasuyi sirrantacciyar magana sai basa fita da drivern maleek din.
Tafiya suke Babu me magana acikin motar sai numfashinta dake fita ahankali ahankali sbd nauyin da kirjinta yayi.
Dan dagowa yayi ya kalleta ahankali tareda ajiye wayar hannunsa ya maida kallonsa kan wani envelope daya bude da muryar me kamewa yace"