x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 23 - UBAYD MALEEK

  • 66001 words
  • 69000 words
  • Out of 131724 words

Category: Romance Story +18

Views 199

30 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
cup din ta matso ta miqa Masa tareda tsayawa akansa Kamar zata fasa kuka sbd Jin yanayin take har cikin ranta.

Kurbi daya yayi ya dakata sbd abinda yakeji ta matsosa sosai cikin kulawa da damuwa tace"

Yace duka za'a shanye.

Ko kallonta Bata samu damar yayiba yasake daga cup din yasha Yana rufe ido tareda shanyewa ya miqa Mata cup din da sauri Yana saukowa gadon ya nufi toilet yafara kelaya wani irin aman azaba Wanda yasata kasa hkr tabisa ciki idanuwanta na cikowa da ruwa musamman ganin Aman hadda jini sosai aciki ta rude tana dafa bayansa da har lokacin yake bayyane ba Kaya ajikinsa Dan abin kamar daurin Rai da dai towel dinsa har lokacin be kunce ba koya kunce akwai qaramin gajeran wando ajikinsa.

Saidayayi mugun amai sosai kafin taji take zafin jikinsa ya sauka gabaki daya ta zuba Masa ruwa ya wanke fuskarsa da bakinsa ta fito tabarsa aciki ta sake gyara Masa gadon da duk suka cukuikuye sbd rudewa ta dauki cup din ta fice daga dakin tun kafin yafito sbd ta lura tun cikin toilet din yadawo MALEEK dinsa.

Gurinsu jekadi ta Isa da sauri itama cikin sa'a ta tararda ta amaye komai gabaki daya ta shigo suka kamata tareda goggge Mata jiki suka kwantar da ita take baccin wuya ya dauketa sai alokacin dukkaninsu suka saki ajiyar zuciya me qarfi abinda takeji tokare a zuciyarta ya fada Mata ta dafe goshinta tana sake sakin jerin ajiyar zuciya kafin ta dago dmta kalli mum Sarah tace"

Menene yafaru bayan shigewata da daddaren?

Ajiyar zuciya mum Sarah tasaki tareda sauke Kai qasa cikin rashin sanin takamaimai na komai tace"

Bansaniba
Kawai dai abinda nasani shine jekadi tashigo dakina acikin wannan halin
Abu daya tace shine na jininta na quna.

Wani sabon numfashin takuma saukewa me zafi kafin ta bude Baki tace"

Shikenan zuwa da safe idan duk sunji sauki zamuji abinda ya samesu
Ki lura da ita Mr Omar zai Kira Dr bayan asuba.
Juyawa tayi ta fice jikinta a matuqar mace sai yanxu takejin tsamin jikin guje gujen dataitayi daga sama zuwa qasa ta nufi dakinsu ta fada kan gado tareda lumshe idanu tana godewa Allah dayasa komai ya tsaya nan Amma Kuma zuciyarta na Bata wani irin yanayi Mara Dadi na afkuwar al'amarin sbd idan har ciwon maleek ne kaman yanda yasaba to ita jekadi fa?
Gabaki dayama wannan ciwon wani babban abune na daban sbd azabar dasuka Shiga sai me qarfin jini ne kawai zai iya dauka dan kuwa taga tsananin azabar dasuka shiga musamman MALEEK.

Bude ido tayi ahankali tasake lumshewa har lokacin tanajin dumin jikinsa daya Shiga jikinta sbd ba qaramin full body contact suka samu ba Dan ita yacire rigarta shikuma dama Babu anasa jikin.

Saurin rintse ido tayi da qarfi tana cire tunanin cikin ranta ta gyara kwanciya Dan tasamu bacci ya Dan dauketa kafin asuba.
##MAMUH#



_ZAFAFA BIYAR_๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

_Alkiblah--SAFIYYAH HUGUMA_
_Makauniyar qaddara--BILLYN ABDULL_
_Dalaal--MISS XOXO_
_Mabudin zuciya--HAFSAT RANO_
_Ubayd Maleek--MAMUH GEE_

_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._

ฦŠaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huษ—u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0903 234 5899*_Mamuhgee 28_*
Da asuba Saida afia ta tada ita sbd nannauyan baccin daya dauketa ta bude ido daqyar ta kalli afia kanta na wani irin sarawa sbd nauyi dayayi mata sbd rashin bacci da damuwar abinda yafaru cikin daren.
Tashi tayi daqyar ta nufi toilet tashiga tayo alwala tafito ta tsaya gefen afia ta tada tata sallar.

Suna idarwa afia ta ringa satar kallonta a kaikaice sbd duk wani motsin NURUn qamshin turaren dad dinta takeji ajikinta yana tashi.
Shiru tayi sbd batamasan mezatace ba Amma mamakinta anan Ina NURU ta hadu da qamshin?
Ta Yaya?

Ganin idan tayi magana Kamar ta muzanta NURUn ne yasata yin shiru ta Adana kalamanta tukuna.
Gari nafarayin haske NURU ta fito ta nufi dakin mum Sarah ta dubo jekadi har lokacin bacci takeyi saita fito ta nufi dakin padima ta tura tajisa arufe taga key din ajiki ta waje saita bude dakin tareda shiga har lokacin bacci padiman keyi ta qarasa bakin gadonta ta taba bargonta ahankali zata tasheta
Padiman tasaki wani razanannan ihu tana zabura zaune gumi duk yagama jiqata idanuwanta duk a waje take kallon fuskar NURU jikinta na Dan rawa ta sharce gumi tana saukowa daga gadon.

Da mamaki da tsoro NURU ke kallonta tace"

Lafiya padima?
Mafarki kikayine kike wannan ihun kina hada gumi haka?

Kasa kallonta padima tayi sbd har lokacin gumi takeyi cikin tsananin firgicin mummunan mafarkin datayi batareda ta waiwayo ba ta nufa hanyar toilet tana cewa"

Mafarki nayi sbd banyi addua ba na kwanta.

Bayanta NURU tabi da kallo cikin mamaki sosai kafin ta juya ta fice daga dakin ta nufi kitchen tana Danna Kiran Mr Omar.

Saidata tabbatarda ita kadaice a kicin din tace"

Gud morning Mr Omar.

Barka da tashi ranki ya dade"yafada daga can bangaren cikin girmamawa.

Shiru tayi cikin nazarin abinda zata fada Masa...shikuma Jin hakan sai ya gyara murya cikin nutsuwa da Bata tabbaci yace"

Dr Damien yazo ya duba MALEEK tun six harya wuce ma inshallah komai ya wuce.

Sake yin shiru tayi tana wani nazari kafin ta sauke ajiyar zuciya me sauti tace"

Mr menene wannan ciwon?
Shin kodai wani abun sukaci kokuma ya taba skin dinsu?

Tsit Mr Omar yayi Jin tambayar tata saidai baija shirun da tsayiba Dan kada ya Bata hope na zai amsa tambayar ya Dan sake gyara murya cikin Bata girma yace"

Ranki ya dade Inshallah allergy ne kawai Amma bana saka ran da...
Qin qarasawa yayi tareda dauko zancen itama jekadi kowane lokaci duk zasu farka lafiya Inshallah.

Ajiyar zuciya ta sauke zuciyarta na wasi wasin abinda yace na cewan allergies ne,
Wane irin allergy ne wannan me tsananin azaba.

Daga sama tajisa Yana qara saita murya yace"

Ranki ya dade idan na hali Dan Allah basai 'yayan MALEEK sunsan meya faruba,kowama Dan Allah kada yasani sai maleek ya tashi anji daga garesa shida jekadin.

To" kawai tace tana kashe wayar cikin 'yan tunane tunanen dasuke shigarta.

Kasa yin komai na breakfast tayi tabarwa Fana aikin ta wuce daki tashiga wanka tafito lokacin har afia tagama shirinta itama tahau shiri suna gamawa ko breakfast NURU batayiba afia ce kawai tayi suka wuce makaranta.

Tunda suka Isa NURU batada sukuni tunanin halinda yake ciki ya hadu da karatun exams dinta ya hargitsa Mata Kai har wani jiri jirin ciwon Kai takeji sauqinta dayane daga yau tagama exams dinta hutun gaske zatayi kafin sudawo hutu inshallah sbd tana tsananin buqatar hakan.


****
Qarfe goma Sha 'daya da mintuna shida maleek ya sauko ahankali yake tafiya cikin nutsuwa da kamewa Yana sanyeda jallabiya milk sai daukan ido takeyi sbd maiqo da laushin yadin jallabiyan.

Mr Omar dayake tsaye tuntuni Yana jiransa a palo yayi saurin sake sauke kansa cikin tsananin biyayya ya sake ja baya maleek ya wuce yabi bayansa cikin tsananin girmamawa yace"

Barka da fitowa MALEEK.
Allah yaqara lafiya da Nisan kwana tareda tabbataccen tsari da kariya.

Fitowa sukai suka nufi gym dinsa har lokacin Mr Omar na bayansa suna shiga a Dan qaramin palon dake ciki maleek ya zauna tareda Dan lumshe idanuwansa dasuke Dan nuna yayi rashin lafiya sbd sunyi haske sosai sun 'dan fada sai hakan yayi kaman yaqara Masa kyan fuska.

Cikin nutsuwa Mr Omar ya matso daga bayansa yace"

MALEEK garin meriz ne jekadi ta farka tun dazu nayi magana da ita a dakin littafai ta tabbarminda.......shiru yayi tareda sauke Kai.

Dagowa maleek yayi batareda ya kallesaba yace"

Uhum...

Sake gyara tsayuwa mr Omar yayi Yana Dan gyaran murya a raunane yace"

Jinin mushrah ce tayi wannan aikin.

Alokacin ya dago manyan idanuwansa dasuka koma fararensu tas ya dorawa Mr Omar dayayi saurin yin qasa da Kai Yana cewa"

Afuwa MALEEK Amma tabbacen zancen kenan na duba shayin da jekadin ta gabatarmin tareda tabbacin zancenta na cewa tun a gizah taga abin zargi atattare da jinin mushrah din.

Shiru dakin ya dauka tsit na tsawon lokaci maleek baice komaiba
Mr Omar Kuma jiran damar dazai cigaba da koro bayanin sauran zancen.

Ko motsi maleek yayi Mr Omar yasan manufarsa Dan haka shirun maleek din ya tabbar Masa da abinda zaiyi ya juya a nutse ya fita tsawon mintuna uku saigashi tareda jekadi da itakam ta zurma sosai ba laifi saidai jikinta lafiya kalau takejinsa Mr Omar ya rufe kofar ya qaraso yace"

MALEEK ayanda jekadi tayi bayani Babu sanin mushrah ko wani daga cikin ahalinsu gameda wannan aiki na 'yar uwarta,
Akwai banbancin halaye da ra'ayoyi me girma a tsakaninsu Wanda Kai tsaye zamuce hassada kokuma rashin wayo yasa wani daga cikin gizah yake amfani da ita batareda tasaniba.

Kallon jekadi maleek yayi cikin nutsuwa da kamewar murya yace"

Inawa jekadi ya jiki tareda barka da arzikin samun lafiya.

Cikin girmamawa me girma tace"

Godiya nake maleek hakama jekadi nayi maka sannu da jiki.
Maleek kaman yanda kasani Babu inda wannan aiki yafito sai a gizah Kuma kamar koyaushe dai zarginmu Yana yawone akan mutane da yawa musamman idan mukai la'akari da bincikenmu damuketa fama a dunkule na rasuwar mahaifinka,
Tsawon shekarun Nan Danayi a delah naqi barowa nayi bin duk wani diddiqin sirri Babu wani alamar acan ko wanenen me wannan garin na meriz yake Amma yau bayan shekaru masu tsayi garin yasake bayyana Wanda hakan na nufin garin meriz a cikin delah gizah yake.

A Daren ranar dazamu zo cikin dare Naga abin zargi a sassan baquwar mushrah Amma sbd na tabbatar nashiga najata da wani zancen Kuma tabbas hancina ya shaqi kusan qamshin meriz Amma sbd tabbatarwa naqi magana sbd tasamu damar zuwa dashi anan mu tabbatar da hujja saidai banyi zaton zatayi tsaurin aikata abinda aka aikota dinba ayimin afuwa MALEEK.

Kuma kaman yanda Mr Omar yafada hassadace me qarfi a tsananin padime da mushrah wadda ta samo asali daga cigaban aure da mushrah tasamu na MALEEK Kuma haryanzu mushrah batasan da wannan halayen na 'yar uwartaba Dan kuwa ko wannan zuwan nata inada tabbacin Babu alkhairi acikinsa sbd iyayensu takanas kaleeb yayi magana dasu bayan nayi Masa bayanin komai na ranar danaga mutum yafita daga sassanta Dan haka Ina me roqo da neman afuwan maleek akan kada yayi fushi da mushrah akan laifi mafi Muni da jininta ta aikata.

Tsit suka kumayi gabaki dayansu na tsawon lokaci maleek na nazartar abubuwa da dama acikin kansa wainda ba komai bane sai mutuwar mahaifinsa dayayi wato mutuwar azaba yanaji Yana gani duk da Yana yaro qarami lokacin Amma Yana iya tuno azabar dayaga mahaifinsa aciki,

Tun daga lokacin Basu sake ji ko ganin wani Abu daya danganci garin meriz ba sai yau sama da shekaru arbain kenan.
Tabbas zarginsu ya tabbata cewar a gizah kowanene yake Dan haka yanxu Kam aikinsu na gaske zai fara.

Dagowa yayi ya kalli Mr Omar dake jiran umarni ya maida idonuwansa kan jekadi Kai tsaye cikin kamewa yace"

Baza'a bari kowa yasan da zancenba ciki kuwa harda ita datayi aikin ki maidaita gizah idan tanacan ne za'a San waye shugaban aikin nata sbd na tabbatarda ita kanta nasan wa takewa aikiba sbd al'amarin me girmane bazasuyi saurin bayyanarda kansuba,

Amfanin wannan aikin na meriz da aka sata shine komawata gizah neman magani sbd sunyi tunanin acan ne kawai za'a samu maganin warkar Dani dagacan ne zasu qarasa niyarsu wadda baasantaba.

Gyada Kai jekadi tayi tace"

Kabar komai ahannuna kafin ka iso gizah Inshallah aikin yayi nisa
Inshallah sai Allah yacika nufin kaleeb Dan kuwa alqawarine sai anciyar da dabbobin gizah Naman duk Wanda ko da ido yataba ganin garin meriz bare ya taba.

Mr Omar ne ya matso yace"

Jekadi sai magana ta gaba itace umarnin maleek ne kada mushrah tasan abinda yafaru sai lokaci yayi hakama iyayenta
Duk abinda tayi idan lokaci yayi zatafada musu dakanta aranar qarshe da Babu gyara.

Gyada Kai jekadi tayi tana sake yiwa MALEEK fatar samun lafiya ta miqe ta fice.

Mr Omar kuwa gyara tsayuwa yayi yana sauke Kai yace"

Maleek meye ainihin wannan hukuncin na jinin mushrah da aka sanarwa jekadi.

Jininta ta aikata kuskure babba na cutatar da 'yar uwarta hassadarta tasa tasaka kanta cikin masifarda tun kafin mahaifinta yazama saurayi bare yayi auren haihuwarta.

Wayar kaleeb ya karba da Mr Omar ya miqo Masa bayan yagama yimasa bayanin komai dasuke ciki suka fara magana kowanne cikin kalar nasa ikon da kamewa ta sarautar dake jininsu kafin ya ajiye wayar.
Miqewa yayi tareda nufar kofa sai ya dakata ahankali batareda ya juyoba Kai tsaye yace"

Ka bawa jekadi muriz din damuke ajiya sbd bincike abisaga umarnin kaleeb kullum abata drop daya acikin abinsha ahaka har agama gano ainihin shugabanta duk tsanani kada abari asan muriz ake Bata sbd kaucewa basu alamar ansan dasu.

Cikin jinjina Kai Mr Omar yace"

Yanda kaleeb yace shine daidai.

Fitowa sukayi suka nufo ciki Koda suka shigo direct sama maleek ya wuce kasancewar NURU batanan hakama afia yasa jekadi da kanta ta tsare kitchen harsaida Fana tayiwa maleek din breakfast aka jere Masa Mr Omar Kuma na daga bakin kofar Palo shima ya kafa ya tsare.

Padima datake jiran Jin mugun labari na kuka ya faru agidan taji Babu komai batajin motsin kowa alamun lafiya Amma duk da hakan qin fitowa tayi tanajin hankalinta Sam be kwantaba gabaki daya gizah takeson komawa ta karbi dukiyarta da tukuicinta na aikin da aka sakata da dasa tata cin sabuwar duniyar.

Sai yamma sosai su NURU suka dawo cikin farin ciki da walwala suke duk su dukan sbd Gama exams dasukai.

Wanka nuru tafarayi ta Sanya blue pencil jeans da farar _Gaultier_ top me hannun shimi ta fito a kicinma taci abinci tanason mgn da jekadi Amma Sam jekadin taqi Bata dama qarshema ce Mata tayi allergy ne Kamar yanda Mr Omar yafada Mata.

Padima Saida NURU tadawo tafito suna fira sama sama Dan takasa sakewa Kai tsaye tacewa NURU gida zata koma.

Da mamaki NURU ta kalleta zatayi mgn jekadi ta qaraso cikin girmamawa ta kalli NURUn tace"

An kammala maganin maleek.

Da wani irin farin ciki me tsanani data danne padima ta juyo ta kalli jekadin tanajin dukkanin damuwarta ta yaye kenan yasha tea din boyewa suke baida lafiya kenan.

Miqewa NURU tayi tabar gurin tana cewa"

Padima Ina zuwa.

Murmushi me Fadi jekadi tasakarwa padime tana cewa"

Ki huta lafiya jinin mushrah.

Cikin farin ciki padime tace"

Yawwa.

Dama tanason sanin halinda yake ciki duk da tasan yanzu ko kallo bazata samu daga maleek dinba Amma tanason tabbatarwada yasamu lafiyar Dan haka ta dauki tray din ta fito kenan ta hadu da farhat tana cewa"

Aunt NURU abincin daddy ne wanna?

Gyada Mata Kai kawai NURU tayi tana cewa'

Bari na aje anan ki jirani na sanyo jallabiya saimu Kai Masa.

Jekadi dake fitowa daga kicin ta matso gaban NURUn a natse tace"

Abincin maleek ba'a barinsa ako Ina shiyasa ko jiya yasamu allergy.

Kallon kanta tayi taga shigar Sam Bata daceba da zuwa gurinsa zatai magana jekadi ta sauke Kai tana cewa"

Afito lafiya.

Numfashi me sanyi ta sauke tareda daukan tray din tana satar kallon hanyar dakunansu tafara hawa saman sbd kada afia ta fito.

Tana shiga palon farko ta tsaya kofar palonsa na kurya tana sauke ajiyar zuciya sbd gabanta dake faduwa ta kalli farhat data bude kofar Kai tsaye ta shige tayi gurinsa da gudu Yana zaune kan royal kushin yayi crossing fararen qafafuwansa da Babu takalmi sai daukan ido suke kaman baya taka kasa dasu.

Shigowa tayi qafafunta na Dan rawa ta qaraso ta ajiye tray din kan table tana dagowa maleek dinma na waiwayowa yayi Mata kallo daya ya juya sbd kayan dake jikinta.
##MAMUH#



_ZAFAFA BIYAR_๐Ÿ’–๐Ÿ’–๐Ÿ’–

_SAFIYYAH HUGUMA_
_BILLYN ABDULL_
_MISS XOXO_
_HAFSAT RANO_
_MAMUH GEE_


_DUKA KUDIN WANNAN DADADAN BOOKS DIN SUNA KAN FARASHIN NERA 700. WATO KUDIN PAGES KENAN. DOCUMENTS IDAN AN KAMMALA SUMA KUDIN SU DABAN.._


ฦŠaya___300
Biyu____400
Uku_____450
Huษ—u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB


saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

0903 234 5899
*_Mamuhgee 29_*



_*YERWA INCENSE & MORE*_
_(The scents with diff essence for YOU& your HOME)_

_(MASARAUTAR KAMSHI)_

_Ina masu neman kayayyakin kamshi yan nahiyar ketaran chadi da Senegal? Kai harma da ingataccen hadโ€™i yan bornu? To ku matso domin nesa tazo kusa..._

_YERWA INCENSE & MORE: Sun zo muku da kayayyakin turaruka kamar haka:_

_Khumra kowacce Iri._
_Turarukan Wuta_
_Mopping khumrah_
_Washing khumrah_
_Bathing khumrah_
_body mist_
_kullaccam_
_scented hair cream/spray_
_wardrobe balls_

_carpet spray_
_air-fresheners_
_scented pebbles_
_body sprays_
_oil perfumes_
_Perfumes_

_kabbasa_
_burners_
_coal igniter_
_tong_
_kasko_
_english coal_
_dilke&halwa set_
_scented body mist_

_kai dama sauran kayayyakin da bamu ambata, YERWA INCENSE AND MORE, Na tura kayayyakin su koina a fadin Nigeria da ketare. Domin tuntubar su. Suna instagram: _@yerwaincense_and_more. Ko Facebook site:YERWA _COLLECTIONs. Ko a duba su ta number su: _*08095215215/09044191709*! _

_suna bada kayan su kan sari ko sayi dai-โ€˜dai_




**********
Harta Gama zuba Masa ta ajiye Bai Bai Kuma waiwayowa ba amfani yake da wayarsa sai farhat dayake tankawa ahankali,
Juyawa tayi zata fice batareda ya kalla inda take ba yace"

Kijira ki tafi da kayan.

Dakatawa tayi tareda sauke ajiyar zuciya boyayya sbd atlas dai yanuna yasan da shigowar mutum ba farhat kadaiba.
Juyowa tayi ahankali tadawo daga gefe ta tsaya tana Dora kallonta kan tv dake aiki Sam bama murya kusan gabaki daya Wanda ta fahimci qaidar iya muryar tv dayake buqatane ahakan.

Ganin tsayuwar Kamar zata damesa saita sulale ahankali Takoma palonsa na farko ta zauna tana kallon tsari da haduwar palon Wanda kusan komai na palon milk ne.

Juya idanuwanta tayi kan wani qaramin hoton LAILAH dake cikin qaramin milk frame tana tareda maleek din dukkaninsu cikin qananun Kaya black shi Yana zaune gabaki daya hankalinsa nakan wayar dake hannunsa itakuma ta rungumosa tana dariya fararen haqoranta tas a bayyane sunyi kyau.

Dokawa taji qirjinta yayi ta dauke kanta daga kallon hoton tareda Dan hadiye yawu tana qoqarin Wasa da yatsun hannunta.

Kasawa tayi tasake juyowa gabaki daya ta qurawa hoton ido tana qarewa LAILAH kallo.
Kyakkyawace da kyanta yake a bayyane,gata da kyawun jiki Kamar ba ita ta haifi afia ba Kamar dai yayarta,
Wayewarta ko acikin hoton a bayyane take sbd yanayin shigarta da yanda take nanuke ajikin MALEEK Wanda son datake Masa yake bayyane afili shima alamunsa da yanda hankalinsa ke kwance qarara a hoton ya bayyanarda soyayyarsa ga matarsa.

Sake dauke kallonta tayi daga hoton jikinta nayin sanyi bugun zuciyarta na qaruwa ta waiwaya gefenda kofar dakin lailah din saitaji jikinta na Gaza Mata ta miqe tabar gurin ta koma cikin palonsa wannan karon sallamarta daqyar ta fito qasan maqoshi sbd shaqewar dataji maqoshinta yayi.

Qarasowa tayi kanta a qasa ta dauki tray din ta fice batareda tabi takan farhat ba dasukazo tareba.
Tana saukowa kitchen takai kayan ta wanke da kanta ta maidasu gurinsu ta fito ta nufi daki
End Ads