Ajiyar zuciya ta sauke me dumi kafin ta waiwayo ahankali ta kallesa da idanuwanta dake bayyanarda halinda zuciyarta ke ciki na tsananin tarin damuwa me nauyi sbd Jin guntun zancensa.
Batareda ya kalletaba Yana cigaba da karanta takardar yace"
You deserve it.
Wannan karon cikowa idanuwanta sukai da hawayenda batasan lokacinda suka balle mataba dama kukan take buqata kozataji saukin damuwarta.
Mr Omar guri yasamu gefen hanya Mara mutane sosai da hayaniya yayi parking tareda budewa ya fita ya rufo musu kofar yana matsawa daga gurin.
Shiru yayi tareda dungurar da takardar sbd gabaki daya baya gane me yake karantawa ya lumshe ido ya bude ya juyo ya kalleta
Kuka takeyi hawayenta na gudu akan fuskarta ya zuba Mata idanuwansa gaba daya akaro na farko dabaisan mezaiceba.
Zaro tissue yayi ahankali ya miqa Mata cikin muryarsa me kamewa da dadin sauti yace"
Kasa kallonsa tayi sai hawayenta dake qara gudu takasa bude bakinta.
Dauke kansa yayi Yana zaro wani Tissue din yakuma Bata ta karba tana goge hawayenta dasukaqi tsayawa
Ahankali yace"
Daga yau idan ba school ba karkije koina.
Da sauri wannan karon ta dago ta kallesa shima ita ya kalla cikin ido ya daga gira daya alamar yes abinda kikaji nace.
Wani irin mutuwar jikine kallonsa ya sakar Mata Wanda Kuma jikin nata ya nuna hakan sbd sakewa da hannunta me tissue yayi.
Dauke Kai yayi daga kallonta Dan kada sauyin dayaji daga nasa bangaren ya bayyana Kamar yanda nata ya bayyana.
Itama juyar da kanta tayi bayan ta Kuma kallonsa ya waiwayo ya kalleta saitaji Kuma kunyar kallon ta kamata ta sauke Kai tana share fuskarta.
Wayar Mr Omar yakira
Yana ganin Kiran yasan sungama ya dawo motar ya bude yashigo ya tada motar suka wuce.
Koda suka iso gida su afia sun Dade da dawowa
Koda Mr Omar ya budewa NURUn kofa ta fito maleek harya bude da kansa ya fito shiyasa kusan a jere suka shigo
Afia dake palon zaune ta dago tana kallonsu harsuka kawo maleek ya wuce Kai tsaye NURU kuwa Jin tayi nauyin afia ya kamata saidai itama Bata tsayaba sbd samun kanta tayi da rashin bawa afia wani bayanin komai tashige tana cewa"
Afia kundade da dawowa kenan.
Harta shige afia Bata iya waiwayawa ta kalletaba sbd kusan itama dai batasan tunanin mezatayiba
Itama yau dai komai ya kunce Mata daga mum dinta har dad din Kamar suna sauyawa.
Tubewa NURU tayi ta sauya Kaya zuwa free doguwar riga mara nauyi da tsayi tafada toilet tayo alwala tazo ta tayarda sallah.
Tana gamawa ta fito hankalinta kwance sbd tasamu nutsuwa ba laifi Wanda takega kila sbd tasamu tayi kukan ne.
Kitchen ta nufa ta dauko ledar crispy patato chips daya ta bude tun daga can tafara ci harta iso Palo tazauna gefen farhat da duk ta tsorata da rigimar dazu tsoron lailah yasak shigarta tana cewa"
Sweetie inzo mu kalla pj masks cartoon ko.
Kwantawa jikinta farhat tayi tana cewa"
Aunt next time idan mum LAILAH tazo daddy idan zai tafi dake kuje Dani tayita yiwa afia fada afia nata kuka inajin tsoro.
Kallonsu suka fara suna zaune mum Sarah tazo zata haye samansa tana tura wringer wheel mop bucket jekadi data fito kitchen takira NURU tana waiwayowa da ido ta nuna Mata mum Sarah ta juya ta kalla mum Sarah din taga abinda yake hannunta ta sauke ajiyar zuciya ahankali tareda Miqewa tsaye tana miqawa farhat ledar crispy 'dinda sukeci tace"
Ina zuwa sweetie.
Gurin mum Sarah ta nufa Kai tsaye tace"
Mum Sarah kawo Bari natayaki kije kawai.
Kallonta mum Sarah tayi sbd wannan shine aikinta agidan tsawon shekaru Babu Wanda aka yarda dashi akan gyaran sama sai ita ko yanzu taso cewa NURUn tabarshi Amma ganin yanzu ita Matar maleek din ce saita miqa Mata tana cewa"
Dan wani kallo NURUn tayiwa afia na mamaki da fara shakku akan afia sbd zuciyarta na Bata kaman afia batason kusancinta da dad din sbd mum dinta idan ta tuna yanda Afia din taqi jinin a danganta dad dinta da auren wata mace ba mum dinsu ba ta sake dubanta tana cewa"
Wannan aikin bazaisa na gajiba Amma dai tunda Zaki Taya din muje.
Saman suka hau suka tsaya a palon farko NURU batareda ta kalli kofar dakin lailah ba tace"
Ta Ina Zaki fara?
Kallon kofar dakin mum dinta tayi tace"
Zanfara da dakin mum.
Waiwayowa NURU tayi ta kalli afia din da wani sabon mamakin tace"
Shiru NURU tayi tareda wucewa tana share tambayar afia din Dan ita Sam palon na Farko ma batason tsayawa ta tura kofa Kai tsaye ta shige palon ciki din.
Da Kamar afia zata tsaya tayi Nan din saita fasa tabita tana cewa"
Bari dai mugyaro daga can din gaba daya.
Ko data shigo NURU ta fara gyara palon ganin afia tashigo yasa wani qayataccen murmushi sauka kan fuskarta batareda ta waiwayaba taci gaba da aikinta tana gamawa tace"
Ki kiyi mopping Bari na gyaro kurya.
Bata jira maganar afia ba ta wuce Kai tsaye kofar bedroom dinsa sbd tunaninta bayanan tayi knocking ahankali harso biyu babu amsa ta murda kofar ta shige tabar afia tsume ta dauke wuta da mamakin daya Gama kasheta.
Tana shiga dakin ta sauke wata irin kasalalliyar ajiyar zuciya sbd komai datayi cikin karfin hali da mamakin afia dason tabbatarda tunaninta tayisa.
Kallon dakin tayi akaro na farko sbd last time ba acikin hankalinta tashigoba harma ta fita din.
Ganin baya ciki yasata nufar shimafidar gadonsa data Gama gaurayuwa da qamshin jikinsa takai hannu zata saka han zanin gadon Dan gyarawa taji anbude kofar toilet ta juyo da sauri.
Tsayawa yayi Yana kallonta da mamaki dakuma wani kallon dabam kafin ya saki kofar ya fito gabaki daya cikin dakin
Da sauri ta juya zata fice tabi hanya tana cewa"
Yi hkr bansaniba""kofa ta nufa da sauri ta bude harta fita Taki ya riqo hannunta tareda dawo da ita cikin dakin ya tura kofar wadda kararta tasa afia firgita har tana jefa kafarta cikin bucket din Bata saniba da sauri ya cire kafar ta nufi kofa ta fita tana cewa"
I need a break,I need some fresh air kaina Yana sarawa.
Benen ma bibbiyu take hadawa gurin saukowa daqyar ta sauko tayi waje tana shakar iska tana sauke ajiyar zuciya a jejjere.
##MAMUH#
Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki👇👇
0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB
saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)👇👇
*_08085405215_*
IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU👇👇
0903 234 5899
*_Mamuhgee 32_*
*_RANO NET_*
_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_
_INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_*RANO NET! RANO NET! RANO NET!*_
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN ‘DAI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON M1U: *_234 803 081 1300/ 234 808 540 5215_*
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
***************
Da sauri ta dago ta kallesa lokacinda ya jinginata da kofar dakin bayan ya rufe, ta kalli faffadan kirjinsa dake bayyane sbd fitowarsa wanka kenan daure da brown towel ta 'dan juyar da kanta ahankali ta iya bude Baki tace"
Afia na Palo tare muke...
Wani kallo yayi Mata da idanuwansa dake kan fuskarta ya sake matseta jikin kofar har jikinta na mannuwa da nashi ta ja wani guntun numfashi tana Dora tafin hannunta kan qirjinsa batareda tasaniba
Hakan yasa maganar dazaiyi ta bace masa yayi shiru Yana kallonta
Ta sake dagowa ahankali sai suka hada idanuwa taji wani sanyi da kwanciyar hankali na shigarta sai fuskarta tafara yunqurin bayyanarda murmushi tayi saurin sauke Kai Tana motsawa ahankali sbd qamshinsa daya Gama cika hancinta Yana neman sage qafafunta.
Motsawar datake yasa qirjinta ringa gogarsa ya rintse idanuwansa Yana budesu akanta tareda yin baya Yana sakinta sbd Jin zata iya jawo damuwa.
Closet ya nufa batareda ya waiwayo ba bare ta iya gane halinda fuskarsa take ciki.
Bayansa tabi da kallo zuciyarta da dukkanin gangar jikinta na karbuwar da kowane irin sako ne yasoma isar mata.
Waiwayowa yayi ahankali ya kalleta idanuwansu suka shiga cikin na juna ta dauke kanta tana sakin wani boyayyan murmushi Wanda yasashi juyowa gabaki daya Yana Mata kallonda yasata bude dakin ta fito da gudu tanajin gabaki daya jikinta na daukar vibration Kai tsaye dakin farhat ta nufa ta zauna bakin gado tana sauke numfashi tana warware daurin gashinta Dan tasamu iska Tako Ina ya shigeta.
Dagowa NURU tayi ta kalli farhat din tana zuba Mata idanuwanta tana kallo kamanninta da mahaifinta ta janyota jikinta tayi kissing Kumatunta ahankali Yana rungumeta ahankali tace"
I love you sweetie.
Da farin ciki farhat ta maqale NURUn tana cewa"
I love you more my Aunt.
Zamansu sukayi a dakin saida kowa yashige sallar magriba tukuna ta fito ta haye saman batareda kowa yaganta ba taje sharp sharp tayo aikinta ta fito batareda shima yaganta ba sbd yafita sallah baya saman.
Kodata sauko takaiwa mum Sarah kayan gyaran dakin farhat Takoma acan tayi sallah tukuna ta fito Takoma kicin tasaka hannu a aikin hada abincin maleek din na dare ta jera a tray takai saman tadawo ta nufi dakinsu tashiga tanajin nauyi da kunyar afia nason shigarta Amma ta daure ta danne tashigo dakin tana kallon afian dake zaune da littafi a hannunta tace"
Karatu Kuma ayanxu afia?.
Kasa kallonta afia tayi tace"
Eh wani Abu na dauko Ina dubawa.
Ok kitashi anyi sallah tun dazu.
Toilet ta wuce tayo wanka tana fitowa afia tabita da satar kallo tana cewa"
Kingama aikin?
Dakatawa NURU tayi daga shafa spray ajikinta ta 'dan waiwayo ta kalli afian tace"
Eh na gama na yau dai.
Cigaba tayi da abinda takeyi tagama tasaka kayan bacci ta fita dakin ta nufa dakin farhat acan sukasha oat suka sallar ishai sukai kwanciyarsu.
Washe gari tunda safe dakin padima ta nufa dan tayata shiri saidai padimar Bata buqata Kamar yanda tafada Mata Dan haka bata takura kantaba ta juya ta ficewarta ta nufa kitchen aikin breakfast tana gamawa ta nufi daki ta tada farhat tayi Mata wanka tareda Shirin school suka fito tabata breakfast da kanta ta rakata bakin mota driver ya wuce kaita tadawo ciki ta hadawa padima kayan breakfast a tray ta nufi dakin datake takai Mata sbd dama bakowa ke cin abincin a dining din gidan ba daga maleek sai iyalansa.
Tana shiga ajiye Mata kawai tayi ta fice
Qarfe goma driver ya kawo mota bakin kofar shigowa Palo Yana jiran fitowarsu jekadi wadda dukkanin saqon Anneti na miqawa NURU sauran Wanda ya rage ta shanye da safiyar suka fito NURU na gefen padima data matsu su Isa gizah rayuwarta itama ta canza gaba daya.
Shiga mota tayi ta zauna tareda kallon NURU tace"
Allah yabawa kowa rayuwar daya cancanta Dan haka gamo na alkhairi uwar renon farhat.
Wani qayataccen murmushi NURU tayi zancen padiman Bai tabataba ta dago tace"
Idan kinje Ina gaidasu abal da meryam, Jekadi zata Baki saqo a gizah da nawa Dana MALEEK duka kafin ki wuce delah,
Allah ya tsare hanya.
Maida kallonta kan jekadi tayi cikin kulawa tace"
Jekadi a sauka lafiya.
Da girmamawa jekadi tace"
Allah yasa mushrah Kuma godiya muke Allah ya qaro girma.
Shiga mota jekadi tayi aka shigar da kayansu motar driver yaja suka fice NURU na juyawa Takoma ciki direct ta nufi daki ta tube tafada wanka.
Tana fitowa ta zauna gaban madubi tana kallon fuskarta datakeson shafawa janbaki Dan Bata taba sawaba Sam ita Bata kwalliya iyakacinta shafa bronzer itama sama sama sai lip balm shima Mara Kara Amma yanzu son yin kwalliyar taji Kamar ya shigeta tana ra'ayi Dan haka tana gama shafa oils da creams dinta saita shafa face primer ta shafa powders kawai da liner cikin idonta ta dauki Nude lipstick tashafa akan lips dinta me sirkin pink pink.
Kallon fuskarta tayi aga kwalliyar tayi Mata sbd batai yawaba Kuma sbd Bata taba yiba sai tayi Mata kyau sosai.
Tashi tayi ta dauko doguwar English grown tasaka peach kala ta Sanya Sanya Dan kunne qarami ta fice daga dakin tabar afia da idanuwanta suka fara yaji yaji sbd kallon ikon Allah.
Tashi afian tayi itama ta nufi toilet tayo wanka tafito ta shirya cikin doguwar riga kusan irinta NURUn Dan dama kusan duk kayansu iri dayane.
Makeup tayi me kyau itama ta fito Palo daukeda laptop tazo ta zauna tareda bude laptop din tafara wani aikin tanashan tea data saka Fana hado Mata.
Murmushi kawai NURU dake zaune tayi tareda janyo musu firar wani program sunayi sbd kada shedan yasamu Shiga ranta.
Suna cikin firar Kiran lailah yashigo wayar afia
Suka kalli wayar atare kafin NURU ta dauke Kai tana miqewa tace"
Bari naje nataya Fana aikin abincin lunch.
Tana barin gurin afia ta maida kallonta kan wayarta tana tunanin daukan Kiran sbd tasani Babu wani abin kwanciyar hankali a wayar mum saina buqatarta wadda ita koyaushe abinda takeso shi zaayi Dole akuma lokacinda takeso din.
Kasa daukan wayar tayi ta saka wayar silent tareda Miqewa tabar palon ta nufi daki sbd kada NURU ta fahimci Bata dauki numbern mum dintaba.
Koda tashiga daki kashe wayar take kokarin Yi wani Kiran yasake shigowa ta sauke numfashi tareda dauka cikin sanyi tace"
Mum.
Dagacan bangaren lailah ta amsa da cewa"
Afia since when did you become this foolish dazan Kira kina ganin kirana bazaki daukaba?.
Ajiyar zuciya afian ta sauke tana Jin gajiya da halayen mum din tace"
Mum bana kusa Kuma Dan Allah mum kidaina wannan fadan kina bani tsoro ne sai inringa tunanin kina cikin wani halin ne sbd gabaki daya kinayi kaman bakya cikin kwanciyar hankali.
Wani baqin cikin afia ne ya tasowa lailah taji kaman ta zageta ko zata rage Jin abinda takeji na abinda yake gabanta na contact data rasa bayan dukkanin dukiyar data kwashe ta zuba Dan kawai ta samu contact din wanda zai sauya rayuwarta gabaki daya tazama abin gogayyar maleek saigashi ta rasa babban abin damuwar shine a qarqashin maleek contact din yatafi shiyasa yanzu a haukace take da buqatar komawa maleek kafin abinda take dashi yafara yin qasa Amma wannan wawuyar Yar tata tanayi kaman batasan abinda takeson tayi Mata ba.
Afia banason doguwar hayaniya sbd kaina Yana Dan ciwo Dan haka sai anjima idan na huta zankiraki Amma kafin Nan ki sanarwa dad dinki na shirya dawowa rayuwarku.
Shiru afia tayi da zallar mamakin mum din tace"
Mum inaga wannan ba hurumina bane ki nemesa kuyi mgn kokuma uncle jalal ya nemesa.
Da mamaki Lailah tace"
Nasan numbernsa Amma nace ki fada Masa ai.
Mum Dan Allah kidaina haka kufa iyayenane tayaya zanshiga cikin zancen maganar aurenku.
Baqin ciki yasa lailah cewa"
Idan bazakiyi abinda naceba afia karki sake kirana mum sbd bansan alaqata dakeba.
Kashe wayarta tayi tabar afia da idanuwa na cikowa da hawayen baqin cikin irin wannan uwa da Allah yabasu wadda duk duniya kanta kawai ta sani,buqatar kanta kawaice agabanta su 'yayanta amfaninsu kawai agurinta shine irin hakan idan ta taso Mata.
Kasa shigowa tayi ta juya Takoma Palo ta zauna tana Shiga wani yanayi,
Lailah zata dawowa maleek to idan tadawo ita zata tabbata a 'yar renon farhat da gaske dinne kokuwa ma kila gaba tayi¿.
Numfashi ta sauke tareda dagowa ta kalli kofa da aka bude farhat ce tadawo daga school tayo gurinta da gudu tana Kiran sunanta.
Rungumeta daga zaunen NURU tayi tareda zare Mata school bag tana cewa"
Muje a cire Kaya ayi wanka.
Dakinta suka nufa ta tayata cire Kaya akai wanka ta dauko Mata riga da mini skirts ta Bata ta Sanya itakuma Takoma dakinsu tayi sallah tafito ta nufi kitchen tasa fana ta fito da komai suka shirya dining.
Tana Shirin komawa kitchen hada Masa nasa a tray tajiyo qamshin turarensa na shigowa ta dakata tareda juyowa daidai Yana shigowa dining room din ya zuba Mata idanuwansa dake Dan yawo akanta sbd qarara kwalliyarta da kyawun datayi suke a bayyane.
Kallonsa tayi tana bin bayan Fana data sulale ta fita da sauri ta bude Baki cikin sauti me taushi tace"
Barka da fitowa.
Bai amsaba ya qaraso gabanta kenan saiga farhat tashigo da gudu
Saiya zauna kan kujera Yana dauke idonsa akanta.
Murmushi tasakarwa farhat tana kallonsa tajata takaita kan kujera kafin ta koma kitchen ta dauko sauran ruwa da drinks takawo.
Sai data zuba Masa komai kafin tazo gurin farhat tazuba Mata kenan saiga afia ta shigo taqaraso ta zauna kan dining din tareda kallon dad dinta tace"
Barka da fitowa dad.
Kallonta yayi yana amsawa cikin kulawa.
Harsuka gama cin abincin idon hankalin afia baya jikinta gabaki daya ita Bata cikin nutsuwarta da walwalarta.
Yana lureda ita Kuma kallo daya yayi Mata yasan matsalarta bazata wuce lailah ba, Saida yagama ya goge bakinsa da Tissue ya dago ya kalleta cikin kamewa yace"
Afia akwai matsalane?hankalinki baya kan abinda kikeyi.
Aje spoon din hannunta tayi tareda sauke ajiyar zuciya me zafi da shakkarsa cikeda