x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 7 - KAMAL NE

  • 18001 words
  • 21000 words
  • Out of 58900 words

Category: Romance Story +18

Views 134

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
tsaya cak ganin yayi wata irin juyi ya nufo waje yana faɗin " Ok bari kiga wasan karshe tsakanin mu yanzu zaki yi kuka da hawayenki, daman nayi haka ne naga ko kin horu." ya faɗa yana nufar gurina... Iya tsoro! na tsorata!! ganin yanayinsa na gigice na rasa ma fita, kawai sai nayi kansa da gudu na faɗa kirjinsa na maƙalƙaleshi na nitsa kaina kirjinsa, wani irin fitinanna kamshin san me sanyin dadi ya daki hancina, na saki kukan munafurci dan sam ba kuka bane nake, neman tsirane... Kamal ya fara ƙoƙarin cire ni daga jikinsa ya kamo fatar wuyana ya murɗa fatar iya karfinsa yana mintsinata, dan azaba se da naji fitsari, na fasa ihuu! Da sauri ya toshe min baki, ya finciko ni ya ɗaga kaina sama ya buɗe min bakina... Nan hankalina ya kuma tashi... Kafin nake wani yunƙuri naji ya tsirtamin yawunsa a cikin bakina kai tsaye ya gangara makoshina, ya rakani da gigitaccen mari fauuuu ya sake ƙaƙalo yawun duka bakinsa ya tofa mun cikin bakina haɗe da toshe min hanci tare matse min fatar wuyana, iya karfinsa...! Take naji jiri na dibana kaina ya shiga juyawa ga babu inda zan fitar da numfashi, dole na haɗiye yawun baki ɗaya idanuna na lumshe na na koma kirjinsa nayi lakwas, bana gane kome sakamakon wani irin tashin zuciya da nake ji haɗe da amai... Nan take hankalina ya fara gushewa ina yunƙurin amai a jikinsa, naji yana magana cikin kakausar murya yace"Wlh wlh wlh kika kuskura kika yi amai tabbas zaki ga abun da zan maki yau , gobe kiyi yunkuron zagin babba ko rashin kunya na fiki fitina , zan koya maki tarbiyyar da ba a baki a gida ba , yanzu na fara baki yawun bakina ba dai shine bakya so ba yanzu aka fara." yana faɗin haka naji ya tallabo kaina ya sake kusanto fuskana, daddɗan kamshinsa na kara ratsa min hanci, numfashin mu naji ya gwaraye guri ɗaya naji tsinin hancinsa na gugar hancina, still hannunsa manne a marata yana murza tare da ramin cibina, nayi wata irin zabura na ƙamƙameshi na saki wani marayan kuka tare da nadamar sanin sa, kukan da na saki ne ya bashi damar dora lips ɗinsa saman nawa, ya danne fatar bakinmu da ɗan karfi tare da done min hanci, zuciyata na buga da karfin gaske, na fara kokowar kwatar kaina da dan guntun karfin da bai fice cikin cokali ba, daidai lokacin ya tura ɓakinsa cikin nawa gashin kaina ya rufe mana fuskokin mu, ya shiga huramin iska cikin wani irin sigar yanayi ga wani fitinanan kamshi da yake fitowa daga cikin bakinsa, amman ni banda amai babu abinda nake buƙata... Wani yawun naji ya juye min haɗe kamo harshena ya gantsara min uban cizo yay saurin zare bakinsa yana murmishi ya toshe min hanci na kuma haɗiye yawunsa a karo na uku, wanda yay dede da fita haiyacina, bana iya kome dole na manne a jikinsa ina fitar numfashi daket.
Kamal yace"Gud haka nake so ni dake shege kan fasa yanzu duk abinda zaki min zan baki yawuna kisha shine hukuncin ki, ok?" yana faɗin haka ya sakeni daga tsaye na faɗi ƙasa wanwar, ko dan yatsana bana iya ɗagawa bare nayi yinƙurin tashi... Kamal toilet ya nufa kai tsaye yana zuwa ya kunna panpo yay brch ya cire kayan jikinsa saboda yanda zuciyarsa take masa zafi, ya kunna shower yayi tsaye tsakiyar sa ruwan me sanyi na sauka kansa yana sauke tagwayen ajiyar zuciya...
Mubina ganin Kamal ya shiga toilet ta fara yunƙurin miƙewa ta kasa ga wani irin amai da takeji, tana tsoron masa a cikin Office ya sake bata yawunsa.
Cikin dauriya irin tata ta miƙe zaune ta matsa jikin bango ta dafa bangon ta miƙe daket tana tangaɗi, ta nufi kofar fita bata wani ganin gabanta sosai saboda gashin kanta da ya since ya zubo har saman fuskarta...

Sageer ne tafe cikin nutsuwa yana kaɗa makullan motarsa, ya
fito daga Ajin su Iyamu, ya hango Basma da Nazeer a rana suna tiƙar shara, gunsu ya nufa.
Yana zuwa yace"Basma me kuka yi lafiya kuke tiƙar uwar shara haka?" Basma ta goge majina tana hawaye ta ɗago da kanta tace "Sir wlh bama mu mukayi laifin ba mu yan tsaron kofane Mubina ce tayi laifin amma Sir Kamal ya haɗamu duka , ita tana office ɗinsa bamu san irin wuyar da take shaba amma bata kai tamuba muda muke rana a tsaye..." da sauri Sageer yace" kina nufin Baby ma yana can yana bata wahala? Kubar shara maza ku wuce Aji bari na naje gurin Baby." ya faɗa yana juyawa harda dan gudun sa ya nufi saman bene office ɗin Sir Kamal. Basma ta saki tsintsiyar tana goge hawaye, Nazeer yace "kina nufin mu bari Sir Kamal bai ce mu bari ba mu tisa laifi?"Basma tace" se ka tsaya ɗin ni na tafi yo ba Malam Sageer ba yace mu bari." ta karasa maganar tana nufar toilet ta wanke jikinta se Allah ya isa take jama Mubina. Nazeer ma toilet ɗin ya nufa dan gyara jiknsa yaje yayi bitar abinda aka koya da baya nan..
Tana dab da isa kofar taji ana knocking, jikinta har rawa yake ta ɗan kara jan ƙafa, kofar aka buɗe aka shigo da sallama Sageer ya zaro idanu ganin Mubina a haka da ɗan gudun sa ya karaso gunta tana shirin faduwa ƙasa ya tarota ta faɗo jikinsa, hankalinsa a tashe yace" Subahanallahi me nake gani haka? Baby kashi ya baki me ya miki haka kika fita haiyacinki? kalli fuskarki tayi ja marinki yayi tayi ko me?". Mubina da ta galaɓaita ta shige jikin Sageer daket ta bude bakinta tace"Sir... Yawun...sa...ya...ba...ni... Na...amai ne ya kufce mata bata idasa maganar ba ta fara kelaya amai a jikin Sageer. Da sauri Sageer ɗin ya kara rungumota jikinsa, tana kwarara aman yana buga bayanta hankalinsa a tashe, yana faɗin" Baby sannu wani irin azaba ce ya miki haka me ya baki? Wannan mutum anyi mugu wlh kashe ƴar mutane zaiyi ko me?" ya karasa maganar yana cicciɓarta ya ɗauketa ya rungumeta ya juya zai fice, Kamal na fitowa daga toilet kansa na ɗigar ruwa, yaga guntun amai a saman carpet ɗin da yake shimfiɗe tsakiyar office ɗin.
Ya kalli Sageer yace"Dakata malam wlh baku isaba sai an goge min wannan ƙazantar uban waye zai goge maku? tab." ya faɗa yana sakin wani irin murmushi ya nufo kofar da sauri, amma kafin yazo Sageer ya fice da Mubina.
Kamal ya kaɗa kafaɗa yace"yanzu kuwa kawarta zata goge shi." ya faɗa yana isa bakin katon table ɗinsa me shaƙe da uwayan takardu, ya ajiye wayar da yana da tabbacin ta tashi a aiki har laptop ɗin ma, ya ajiye ya goge kansa da karamin towel, ya ɗauki hularsa ya murza a kansa se baza kamshi yake ya ɗauki wayoyin sa biyu ya zuba cikin aljihu ya ɗauki makullan motarsa yana sakin sansanyan murmmushi ya nufo kofar.
Sageer direct office ɗinsa ya nufa da Mubina yana zuwa ya kwantar da ita ta galaɓaita, daket take fitar da numfashi ya shiga toilet ya wanke inda ta masa aman da sabulu mai kamshi, ya ɗauko towel ya fito ya nufi table ya dauki sansanyan turaransa ya feshe jikins ya, yazo ya goge mata aman ya kamata suka nufi toilet ya wanke mata bakinta da fuskarta tace ya mata brch, cikin kulawa ya tatso makilin ɗin a hannunsa ya wanke mata bakinta ya kamata suka fito ya ɗauko faro me sanyi, ya zaunar da ita shima ya zauna dab da ita, ya janyota jikinsa ya ɗago da kanta ya kafa mata robar ruwan, babu musu ta fara sha se da ta kusa shan rabi ta janye bakinta ta kwantar da kanta kirjinsa tana maida numfashi.
Bayanta ya shiga bugawa yace"Baby me kika ma Sir ɗinku ya azabtar dake haka?" muryata bata fita sosai tace"Sir kaini gida gun umpah nah." ta faɗi hawaye na kwaranya saman fuskarta. Sageer ya sha mamaki dan bai taɓa kama Mubina na kuka ba sai yau. Cikin sigar lallashi yace "Ok kinyi alkawalin zaki faɗamin abinda Kamal ya miki da zaran kin dawo nutsuwarki?" Mubina ta nitsa kanta kirjin Sageer ta ɗaga masa kanta tana fitar da numfashi sama-sama. Agogon hannunsa ya kalla yaga 12: 30 cikin sauri ya kamata yace"Muje na ajiye ki masallaci zani." ya faɗa yana warware mata mayafinta da yake daure a ƙugunta ya tattara mata gashin kanta ya ɗaure mata ya yafa mata mayafin ya gyara mata jikinta tsaf ya kama hannunta suka fito.
Sageer ya hango Kamal yana waya sai murmushi yake suna saukowa da Basma tana riƙe da jakukunan su da towel a hannunta alamun ta gogema Kangiwa aman da Mubina tayi masa. Gun motarsa ya nufa cikin takunsa na isassun maza sam bazaka ce yana ɗingisawa ba idan ba ka luraba, duba da iya tafiyarsa ta isassun maza masu ji da kome..

Sageer ya zabga masa harara yace"Zan kama ka ne bari a taso daga juma'ah dai." Mubina kallo ɗaya ta masa ta ɗauke kanta tana ciza bakinta se lumahe shanyayyun idanunta take tana kara damƙe hannun Sageer. Basma ta yasar da towel ɗin ƙasa ta nufi gun su Mubina da gudu.
Tana isowa ta rungume Mubina Mubina ma ta rungumeta, suna sauke ajiyar zuciya a tare. Sageer yace" Muje na ajiye ku a gida tinda an tashi kafin azo ɗaukarku..." Haladu ne ya sanyo kan motar cikin makarantar Kamal shi kuma na fita daga cikin makarantar, cikin wata araniyar Jeep baƙa sudik. Mubina janye hannunta daga na Sageer tayi cikin sanyin murya tace"Sir nagode da kulawarka gareni yau badan kaiba da na rasa raina hakiƙa bazan manta da kaiba , tnx so much sir mun tafi ga direban gidan mu yazo." ta faɗa tana juyawa cikin sanyin jiki tana cirawa jiri ya kwasheta zata faɗi ƙasa Sageer ya tarota jikinsa yana cewa"oh my god wlh Kamal anyi dan iska wai meye ya miki haka? Sannu baby muje na sakaki mota ya faɗa yana raɓata jikinsa Basma na biye dasu na mata sannu. Mubina batiyi magana ba har suka zo gun motar ya buɗe ya sakata baya Basma ma ta shiga ta zauna.
Sageer yace"gaya min unguwarku zanzo da yamma na duba ki?" Mubina ta lumshe idanunta tana murmushin karfin hali tace"Sir zan dai baka number na dai sbd karamawarka gareni." Sageer ya ciro wayarsa ya lalubi tattausan hannunta ya saka mata. Se lokacin ta bude idanunta ta saka masa number ta bashi yayi godiya ya rufe masu motar Haladu yaja motar ya nufi get. Sageer kuwa cikin farin ciki ya nufi parking spece yana jin dadin ta wani fannin wani fannin haushin Kamal ya saka babynsa damuwa...
Haladu na fitowa da mota direban gidan su Basma na zauwa ɗaukarta, Basma ta kurasa cewar ya tafi gata a motar su Mubina suna hanyar gida daga can zata gangaro a ƙafa. Suna dab da isowa gida Basma tace "Don Allah Mubinata ki fita harakar Sir *Kangiwa* kar ya ilataki ashe har amai ya sakaki? ni ya kirawo na goge , pls ki fita batunsa." Mubina dai batayi magana ba se shigewa jikin Basma da tayi tana ƙamƙame jikinta ta kece da kuka tace" Allah ka saka min kuma nima zan sakama kaina , bazan barshi ba." Haladu yace" Autar gida waye yau ya saki kuka a garin Maradi? Tab asje yau a kawai yaƙi..."Mubina cikin shashekar kuka ta ɗago tace" Ban son tambaya da tsigididi da gulma da munafurci fa , ina ruwanka?" Haladu yace babu kam Autar gida." Basma danne dariyar ta tayi, gudan kar abun ya dawo kanta. Dai-dai lokacin Haladu yay horn aka wamgame masa katon get ɗin ya sayo kansa cikin gidan ...


*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*

*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*



NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻



*Bismillahir Rahamanir Raheem*



*Free Page*


🅿️9️⃣

.... Shin jama'ah wai su waye iyayan Mubina? ina ne asalin su?, *ABDULRAHIM KABEER ALGÈRIE* cika ken balarabe ne na asali. *KABEER NABEEL* balaraban Algèrie ne, Allah ya masu tarin dukiya me yawa, Kabeer Nabeel mutune shi wayayye ɗan son aji dadi, kuma shi ɗaya Allah yaba iyayansa, dan haka ya sami tarbiyya me kyau yayi karatu sosai, bayan ya kammala karatunsa ne ya kama aiki Allah ya haɗa shi da Jawahir, sukayi aure cikin so da kaunar juna, bayan auransu da sati biyu suka shiga yawo ƙasa daban-daban, wanda daga karshe suka yada zango a Niger a babban birnin Naimey, suka sauka a grand hotel, tsawon sati ɗaya suna cin duniyar su yawo babu inda basa zuwa Kabeer yaji duk duniya babu ƙasar da yake sha'awar zama kamar niger a yanzu... Nan akwai wani bazabarme me suna maiga da suka saba ma'aikacin hotel ɗin ne, yake faɗa masa buƙatarsa ta yana so ya dawo niger da zama se dai yana tsoron iyayansa bazu yarda ba... Maiga ya kwatanta masa ya koma ya bisu a sannu har su amince harakar mahaifa ba'a wasa da ita.
To daga nan yabar maganar bai sake neman shawara ba har suka koma ƙasarsu. inda kafin su tafi ya amshi number maiga.
Tinda Kabeer suka dawo yake ma mahaifinsa wayo da kwatanta masa su koma ƙasar niger mana da zama, rayuwar akwai dadi. Irin tsawar da fushin da Nabeel ya nuna ƙarara akan Kabeer da ƙyamar abinda ya faɗa, yasa Kabeer koda wasa be sake maganar ba ya barta ya rungumi aikinsa da matarsa suna soyewarsu... Cikin ikon har ta sami ciki, murna ba'a cewa kome wajan Kabeer da iyayansa da itama nata dangin. Har cikin ya girma ranar haihuwa tazo Allah ya sauki Jawahir lafiya ta haifo yaranta kyawawa mace da namiji, murna a dangi da iyayan yaran ɓata lokacin faɗi ne... Ranar suna ta zagayo yaran sukaci sunah Namijin Abdulrahim macan kakarta ta uba Sabeela.
Haka yaran suka taso cikin gata da kulawa dangi kowa na sonsu, suna shekara biyu Allah yama Nabeel rasuwa mutuwar ta girgiza Kabeer ba kadan ba, yayi kuka har ya gaji ya barwa Allah yaci gaba da kula da matarsa da yaransa da mahaifiyarsa... Bayan cikon shekarar Nabeel ne Sabeela mahaifiyar Kabeer take faɗa masa ita garin ya fice mata aranta! kamar ta koma tunis da zama... Kabeer najin haka ya bijiro mata da manufarsa ba yauba yana sha'awar komawa niger, nan tayi na'am da maganar. Ba a ɗauki lkc ba Kabeer ya kira maiga yana faɗa masa kome nan ya masa gaisuwa da tambayar sa garin da yake so a niger? Kabeer yace nan Naimey yake so zai zo ya sayi fili a maka masa gini irin nasu na larabawa... Ba ako jima ba Kabeer ya kwashi dukiya yaje niger inda suka fara fafutika neman guri me kyau nan ko a yantala ya samu filin da ya masa aka kafta masa maƙareran gida. Cikin wata uku aka gama kome ya damƙama maiga amanar kome koma ya riƙe amana har aka gama aka zuba kayan duniya tare da saukar AQura'ani mai girma. Suka tattara suka dawo ƙasar niger tare da dukiyar su wata kumana can ƴan uwa suna juyawa masu, suko suna rayuwarsu me dadi tare da yaransu biyu.
Haka suka kasance a niger Kabeer ya gina babbar asibiti domin temakon al'ummah duk da tana asibitin kudi amma akwai sauki sosai, haka jama ke tururuwar zuwa.
Akwana a tashi har su Abdulrahim suka girma sun sami tarbiyya me kyau da karatun book da na mahammadiya, tin daga haihuwarsu Allah bai sake ba Kabeer haihuwa ba, cuɗanya da suke da hausa da zabarmawa yasa suka iya hausa sosai hakama duk ma'aikatan gidansu daga bahaushe se zarma. Sabeela tana gama secondary school ɗinta aka mata aure ta auri wani buzu babban ɗan jarida me suna Saleem sabo a gidanta ta shiga jami'a, yayin da Abdulrahim ya maida hankalin sa kan karatunsa medicine, saboda yay aiki ana hospital ɗinsa me suna *Clinique Annur hospital*. Akwana a tashi babu wuya har ya gama ya fara aikin sa tare da mahaifinsa, watarana an kawo wani maras lafiya abin tausayi gasu talakawa likis, cikin ikon Allah Abdulrahim ne akan aiki shi ya masu kome kyauta sun bashi tausayi barin budurwar yanda take kuka tamkar mahaifinta ya rasu. Nan take yarinyar ta burge Abdulrahim duk da bayada ra'ayin auran bahausa. Dattijon kwanan sa uku ya warke ras zuwa lokacin Nusaiba ta shaƙu da Abdulrahim, duk tasan ba lallai ta sami balarabe ba. Nan yake tambayarta wane unguwa suke? ta faɗa masa su ba ƴan gari bane ƴan maradi ne, labarin irin temakon da ake a likitan yasa suka seda kadarasu suka zo ita da babanta da mamarta da yayanta... Kamar wasa kafin ake sallamar su suka kulla soyayya saboda Nusaiba kyakyawace son kowa kin wanda ya rasa fara doguwa me diri kawai de tallauci ne da ya masu cikas babu wadatar abunci me kyau da sutura shi ke boye kyanta.
Seda suka kwashe shekara guda suna soyayya ya wanke ƴan gidansu tass, yasa aka masu ginin zamani duk karshan wata se yaje maradi daga Naimey har yaji sha'awar zama maradi fiye da Naimey ɗin. Koda Abdulrahim ya gwadama iyayansa pic ɗin Nusaiba sunyi na'am da ita basu nuna kyama ba cewar se balaraba ƴar uwasa saboda tana da kome na mace da ake buƙata a tare da ita, dan haka basu yi ƙasa a guiwa ba wajan nemarwa ɗansu auran Nusaiba sukayi tattaki har garin maradi. Babu ɓata lokaci aka saka ranar aure, lokaci yazo akayi biki na kece reni, wanda har yanzu babu na biyun sa da aka taɓa yi a garin maradin... A ka ɗauko amarya aka kawota gidanta dake
End Ads