x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 19 - KAMAL NE

  • 54001 words
  • 57000 words
  • Out of 58900 words

Category: Romance Story +18

Views 140

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
gaske dan haka abar mgnr ki bari bayan auran sa se na faɗa maki abinda zaki yi ki rama cikin ruwan sanyi ai baza mu yafe ba tinda yaci zalinmu..." Mubina tace"my one ka tabbatar kuwa zamu rama?" Yes baby kibari se bayan auran yanzu ajiye ɗaukar fansar , kuma nima se na mare shi yayi fitsari wlh kangiwa ɗan iskane zai yi bayani ai." Mubina ta bushe da dariya ta kwanto jikin Sageer tana riƙeshi tace"Wayyo ciki ashe my one kaima mugune amman zan so naga fitsarin gurgu yasha mari wai niko kasan me? zan masa gobe a makaranta? Wlh karkashi zan zuba a roba na jiƙa shi naje saman bene nabi na zuba a matatakala ya fado nasan nan ma kara jirgewa zai yi."ta faɗa tana ruƙumƙume Sageer. Sageer ya janyeta jikinsa sbd yadda yake jin wani irin abu na tsirga masa, ga nonuwanta sai gugarsa suke. Ya bushe da dariya yace"wai baby A'A kibar kome a hannuna har ayi biki lfy zan baki shawara yanda zamu rama kuma bene a bashi ɗaya ba ke da office ko kin manta? Ai sai muyi barna dayawa kibar kome hannuna kinji" Mubina tace"Eh naji" Sageer yace"yauwa autar mata ƴar lelena yanzu dai ki hkr ok?" Mubina tace"Ai na yarda da kai bari nayi sallah." ta faɗa tana kama Sageer ta sauko daga saman gadon. Sageer yace"Au baki yi sallah ba?" kai Mubina ta ɗaga ta shiga toilet. Sageer ya miƙe yana jinjina kai irin rigimar baby darduma ya shimfiɗa mata, ya buɗe kofa ya fito.

Dudubawa yayi bai ga Kamal ba! Ya fito farfajiyar hospital ɗin, ya tsinkayo shi a mota ya nufi motar. Kamal kuwa tinda ya buɗe kofar room ɗin zai shiga yaji wane hali ake ciki, yaga Mubina idonta tar abuɗe tana hira, yaji iskanci ne Mubina take idonta ras wai dan ta ɗauki fansa ne, ya dawo mota yay kwancin sa yana amsa waya da abokan kasuwancin sa... Sageer ya buɗe motar ya shigo ya zauna yana tiƙar dariya harda tafa hannu. Kamal yace"Ok zamuyi mgn zuwa dare insha Allahu." ya faɗa yana tsinke kiran, ya kalli Sageer yace"kun gama gulmata?" Sageer yace"Wannan baby ina da aiki kar fa muyi aure duk abinda na mata tace se ta rama...?" Kamal ya taɓe baki yace "matsalar kuce yanzu dai Alhmdllh tinda lfy take jeka fito min da ita na kaita gida..."Sageer ya kai masa duka yace"Wlh bamu yafe ba kuma sai mun rama."Kamal yace"Ai nafi karfin ku wlh se dai ku rame... Ni jeka fito da ita mu tafi"Sageer yace"ka tafi zan kaita ai..."Kamal yace"ƙaniyarka kai ka kawota? bari idan na ajiyeta a gidan su kaje ka ɗaukota bai dame nuba , ai yarinyar ina tsoron sharrin ta." ya faɗa yana buɗe motar ya fito ya nufi cikin hospital ɗin.

Sageer ya biyo shi yana dariya. Kwance take kan dadduma ta gama sallah bacci ya fizgeta, ta ƙudundune cikin hijabi. Kamal ya buɗe kofar ya shigo kallanta yayi yaga kamar bacci take, sanin halinta na karya yasa yace"Ke!! Tashi mu tafi gida" yaji shiru bata motsa ba, Karasowa yayi ya sunkuya dab da ita yana leken fuskarta yaga tana fitar da numfashi a nutse, hannayensa ya sanya ya cicciɓeta yay sama da ita firgigit ta farka idanunta cike da bacci, amman ganin Kamal ne ta maida idanunta ta lumshe ta kara narkewa jiknsa ta zagaye hannunta bayansa take ta koma baccin daman sama-sama ne tashin. Kamal na buɗe kofa Sageer ya shigo ya kallesu yana dariya yace"baby ina sonki sbd bakya yafiya yanzu ma dakon kaita mota ne ko?" Kamal bai kulashi ba ya fice da Mubina tana rungume a kirjinsa har mota. Sageer ya rufe room ɗin ya biyo bayan su.
Kamal a gaban motar ya kwantar da ita, daman kujura na kwance take ya zaga ya shiga mazaunin direba, Sageer ya iso yana cewa"Se anjima mun haɗu ko?"Kamal yace"Yes insha Allah." ya faɗa yana ma motar key ya fuzgeta ya bar hospital ɗin. Sageer ma ya shiga mota yana dariyar Mubina, ya fuzgi motar ya nufi gida dan yayi wanka.

Kamal driving yake a nutse har yazo kofar gidan su Mubina, wacce take baccinta tsakani da Allah. Parking yay ya kalli Mubina, ya ɗan rankwafo dab da fuskarta ya hura mata iskar bakinsa ya sanya hannunsa kan kyakyawar fuskarta yana shafawa ya ja dogon hancinta, ya kai bakinsa dab da wuyanta ya dora habarsa kan wuyanta, ya shaki wani daddaɗan kamshinta, ya lumshe tsumammun idanunsa yana sauke tagwayan ajiyar zuciya, yaji numfashin sa na ƙoƙarin sauyawa yay maza zai janye, Mubina kuwa ta sanya hannunta ta zagaye shi a shagwaɓe tace"Uhm Kamal nah ni wlh bazan iya ba fa wayyo ni bana so ka bari pls." ta faɗa a shagwaɓe tana sakin kukan sangarta ta ƙamƙame shi sosai, har lips ɗinsu na gugar na juna. Kamal ya zaro idanun waje ya fara ƙoƙarin janye ta zuciyarsa na wani irin mahaukacin bugo da sauri, a hankali muryasa mai cike da rauni ya furta" *Mubeena* me na miki me zan maki sorry yi shiri bari kuka kinji." ya faɗa yana ƙamƙameta kamar zai maidata cikinsa, fuskokin su na haɗe laɓɓansu ma na haɗe waje ɗaya har wani damshi-damshi yake badawa, yayin da bugun numshin su ma ya haɗe waje ɗaya suna shaƙar hucin junansu, kana jin bugun zuciyoyinsu yanda suke bugawa da karfi, se kukan Mubina marar sauti, har yawunta na ya fara shiga bakin Kamal , ta wani shige jikinsa sosai ta maƙaleshi. Kamal yayi saurin janye fuskarsa ya ɓanɓareta jikinsa, murya can ƙasa yace"Mubina kina mafarki ko?" ya faɗa yana kamota ya zaunar da ita, ya sanya hannunsa yana share mata hawayen fuskarta. Se lokacin ta buɗe idanunta ta kalli Kamal ta sauke ajiyar zuciya da karfi ta zumburo baki, ta buge hannunsa ta matsa baya ta kalleshi zata masa rashin kunya cikin tsiwa tace"Wlh se na faɗama umpah na ganka a mafarki na zaka min fyade mugu ta Allah ba ta..." wani irin kallo da ya watsa mata yasa sauran maganar ta maƙale a bakinta tayi ƙasa da kanta ta beƙa hannun ta dauki jakarta tana gunguni. Kamal yace "karya kike wacce za'ama fyade ce take wani ƙamƙame wanda zai mata ba ma ta shiga neman kwatar kanta ba , wuce min a mota kiban guri maras kunyar banza kawai."Mubina bata yi masa mgn ba ta buɗe motar tana riƙe da jakarta ta fito ta tsaya tace"kuma Allah ya isana mugu gurgu kawai sai na rama bayan auran ku da Aunty mugu mai katon kai." ta faɗa ta zuba da gudu tana ihu se kace ya biyota. Kamal dariya yake harda riƙe ciki, ya ɗauki wayar sa ya kira Amrah bugo ɗaya ta daga da sallama. Yana dariya yace"My cutie angel ga rigiman ma nan mun dawo harda hijab nasa mata , yanzu ta gama min fitsara tas duk marin da taci har ta manta." ya faɗa yana dariya. Amrah tace"Au haba kace ka cimin kaniyarta? Yarinyar bata ji wlh Hubbina" Kamal yace"angel zan leƙa kamfani se zuwa dare zan shigo ok bye." Amrah tace "ok bye my Hubbi." daga can ya tsinke kiran yama motar key yabar layin, ko get ɗin gidan su bai kalla ba, dan sauri yake yanada baƙi a company.

Mubina tana shigowa cikin gidan, Haladu ya fara cewa"Ah Hajjaju hijab kuwa yayi kyau."Baba megadi yace"Haladu baka rabo da tsokana ko?" idi me bama plowers ruwa yace"Ai ya santa sarai ba raga masa zatayi ba..."Mubina bata juyo ba tace"Baba megadi baba idi ku barshi wlh yaci bashi zan kamashi."ta faɗa tana shigewa can ciki. Dariya suka yi, Haladu yace"uhumm kyaji dashi an fita da wando an dawo da hijabi yanzu haka Kamalu ne zai korota ya temaka ya suturtata yarinya se kace haihuwar jinnu..." dariya dai suka yi basu tanka masa ba ya kari mitarsa.
Parlour ta fado kamar an nasota tayi wurgi da jakar tana kiran"Mamu kina ina Mamuuuuuuu nah..." ta faɗa tana diddira ƙafa. Mamu ta kaɗo da gudu daga kitchen tana hadama Ablah shayi. Mamu tace "Mubina lfy ya nagan ki da hijabi?" Mubina ta afka jikin Mamu tana zumburo baki tace"yo wannan gurgun bane yayi ta marina ya samin hijab ya koroni gida Allah sai na faɗama umpah, Ablah kina ina zo kiji abinda akamin Mamu kalli fuskata..."Mamu ta rufe mata maki tace"don Allah yarinyar kirki karki faɗa yi shiru abinki muje na dafa maki indomie da kwai kici kayan ki , ga shayi nan me dadi ina dafawa." ta faɗa tana shafa fuskar Mubina tayi jajur alamar taci mari. Mubina ta shige jikin Mamu tana diddira ƙafa tace"to Mamu goyani ni wlh se kin giyani ko na faɗa masu" Mamu tace "Ok hau muje ai ba yauni gareki ba."ta faɗa tana sunkuyawa, Mubina tako ɗare bayan Mamu tana ɓangala dariya Mamu ta miƙe da ita babu wani nauyi atare da Mubina amman duk da haka Mamu se da tace"Woshhh baby."Amrah ce ta sauko tana riƙe baki, Ablah tana fitowa ta tsinkayo Mamu ta goya Mubina tana kyalkyata dariya, taji daɗi sosai tace"Yauwa Nusy ko ke fa yarinya karama agida ba'a kula da ita a gida." Kabeer yana sanyo kansa parlon yay tozali da Mamu ta goya Mubina, yace"Kai Mamu salon ta kashe mana ke katuwar budurwa zaki goya haka?" Amrah ta karasa ta kama hannun Kabeer ta masa mgn ƙasa-ƙasa, ya bushe da dariya yace"Au haka abin yake?" Ablah tace"Amrah munahirci ne zai kasheki ƴar banzar yarinya , yanzu wannan baƙin ciki kike yi ko?" Amrah ta murguda mata baki taja hannun kabeer suna bin su Mamu. Mamu a kitchen ta ajiye Mubina, laure na masu dariya, Mubina na manne jikin Mamu, Kabeer dariya yayi sosai ya wuce part ɗinsa dama ɗaukar wata laptop yazo. A haka Mubina na manne da Mamu har ta haɗa shayin ta bata ta kaima Ablah, ita ko ta haɗa mata indomie da kwai ta soya mata.
Jikin Ablah take a zaune tana cin indomien tana haɗawa da shayi tana zuba santi tace"Mamu ki koyamin irin wannan suyar idan nayi aure na ma oga ko ba haka Ablah nah?" ta faɗa tana ɗagama Amrah gira. Mamu tace"ke dai ci abinki ba wani surutu ba..." Basma ce ta shigo da sallama. Mubina ta miƙe ta taro ta tana dariya. Basma ta zaro idanu tace"Ni inacan ina larura ashe ke ko a jikinki?" Ablah tace"Me ya faru ne.? Mamu ta ƙif tama Basma idanu. Basma ta kara so ta gaishe su tace"Ablah daman na zata bata iso ba daga makaranta dan direban mu ya riga nata zuwa." Ablah tace "Ai Haladu ya cika shiririta sakare ne." Amrah tayi dariya ta miƙe. Mubina tace"zo kici indomie tayi dadi" ta faɗi tana zubama Basma shayi ta beƙa mata. Nan suka baje suna ci suna hira Basma na mamakin taurin rai irin na Mubina... Umpah ne ya shigo da sallama. Mubina ta miƙe ta tarbo shi da gudu ta ruƙumƙumeshi tana dariya. Umpah ya rikota yace"Baby ya naga fuskarki tayi ja lafiya?" zatayi magana Mamu tayi saurin cewa"yo ba dole ba goyo fa tasa na mata tana gurza fuskarta bayana." umpah yace"Ah lallai yau baby tasha bayan uwarta." ya faɗa yana janyo hannunta suka zauna yana gaishe da Ablah, tana murmushi ta amsa tana masa sannu da zuwa. Basma tace"umpah ina yini." umpsh yace"Basma ya gida dasu isma'il mun hadu dazu gun meeting." Mubina ta miƙe tana cewa"umpah bari na zuba maka shayi yayi dadi umpah kaji kuwa indomie da kwai da Mamu ta soya min wai dadi , wlh yau ko dan naji yunwa ne se naji tafi ta kullum." Amrah tace "umpah ni inata sannu anyi banza dani" hannu umpah ya bata ta ko kama ta zauna kusansa. Yace"to shikenan ko?" murmushi tayi. Mubina taba umpah shayin tace"Basma tashi muje sama muyi hira." Basma ta miƙe suka haye sama. Ai fa Mubina se da ta faɗama Basma kome... Basma tace"Tab yanzu da sai ki zauna a matsayin makauniya ki kawoma karatunki cikas?" Mubina tayi fari da ido tace"Ai Sageer yace bayan auran Aunty zai tayani na rama. Basma ta bushe da dariya dan tasan wayo Sageer yay mata. Mubina tace"uban waye kike ma dariyar ne?" Basma tace"irin yadda zamu rama ne nake hasasowa yana fitsarin wuya..." Mubina ta bushe da dariya tana riƙe ciki... Haka suka kasan ce se bayan magarib Mubina ta raka Basma gida Haladu ya kaisu a mota.

Misalin karfe goma na dare iyamu da Leeza suna zaune leeza tace"amman ina ga kamar wannan ba mafita bace ko ya kika gani?' iyamu tace"wlh itace zamu bi na rama dan wannan hanyar itace mafita zai fi jin kunya har ma ya tsani kansa da kansa bayan haka na ruguza farin cikin sa kuma anyi biyu babu🙅🏻‍♀️ ni ban samu ba ita bata samu ba ,🙅🏻‍♀️kuma sunan sa ya ɓaci duk bazan ɗsu video ba bana son gani..." dariya suka saka suna tafa hannu, leeza tace bari kiji yanda abin zai faru kafin su ankare" ta kama kunnen iyamu ta mata raɗa. Ihun dadi ta saki tace "na fa yarda ai in dai zaka ɗauki fansa cire kishi a ranka kawata." dariya sukayi suka yi suka tafa hannun nan suka shiga yadda zasu yi abin ta ruwan sanyi ba tare da an ankare ba...

Yau saboda tsabar bacci da Kamal yake ji ko zama parlo baiba tinda ya ci abuncin dare, wanka yayi ya kwanta sbd wani irin baƙon yanayi da yake ji a jikinsa wayoyin sa ya kashe ya kwanta. Ko da ummah ta shigo domin taji lfy yake kuwa? Ta isko ya naɗe cikin lallausan bargo yana sharara bacci. gyara masa kansa tayi saman pillow ta rage gudun Ac ta kashe wutar ɗakin ta fice. Mubina ma da wuri tayi bacci suna tsaka da hira da Sageer wayar ta suɓuce mata ta fadi saman bed, jin saukar numfashinta yasa Sageer kashe wayar. Amrah ce ta jima tana jiran kiran Kamal dan bayan isha ya kirata yana tafe kuma taji shiru, kiransa tayi taji a kashe, itama a haka har bacci ya ɗauketa...

*************** ******* ***************

Bayan kwana biyar
Tinda abin nan ya faru, Mubina ta ɗauke kanta daga duk wani abu da ya shafi Kamal, ko makaranta bata yarda ta kalleshi idan ba ya kama dole ba yana masu lecture ba to ba yanda ta iya idan ya kama dole se magana ta haɗa su, ko tambaryata a kan wani abun dole take bashi amsa dan karatun ya kawota... ko wayar Amrah da take sata ta kira shi zaman Amrah ta daina, sabgar gabanta kawai take. Shiko Kamal sosai yanzu yake son mgn da ita ba kamar baya ba ko yay ta kallonta yana sakin murmushi shi kadai, dan rigimarta ta fasa bashi haushi, yau tsawon kwana uku baya fashin zuwa zance, kawai dan ya rinƙa ganinta da dare yadda take ninniƙewa jikin Mamu, dan da yaje se ya shiga ya gaishe da yan gidan. Sageer kuwa sosai yake ba Mubina kulawa ganin tana ji dashi sosai kuma babu namijin da yake gabanta se shi. Yau ake kawo kayan Amrah tin safe gidan su Kamal yake cike da ƴan uwa da abokan arziki anata shiga ganin kaya, anata sanya albarka dan Kamal ya kashe maƙudan kudi ba kadan ba, babu irin kayan da bai sakawa Amrah na yayi ba, karfe 4:30 pm za'a kai kayan, gidansu Amrah, Kamal baki har kunne yaji dadin yadda ake yabon kayan. Su Samha kuwa anata famar ɗinka kayan anko na kece raini. Gidansu Amrah tin safe cike yake da ƴan uwa Mamu da Sabeela abokiyar haihuwar Umpah da yaranta sunzo daga London gida ya hargitse da murna, Mubina kuwa ana makaranta daga can tace gun tella zata wuce bazata dawo ba har yanzu ko anko ɗaya bai ɗinka mata ba! Anko kuwa har kalla hudu ne less material shadda atamfa, ga wani uban narkeƙen less biyu da umpah ya kawo mata, duka sunagun Mezamani telan mata...

Zaune yake cikin Office ɗinsa yana juyi saman lumtsumemiyar kujera wani fitinannan kamshi ke tashi ajikinsa dama Office baki ɗaya, ya haɗe cikin wata arniyar shadda gizna ruwan zuma ɗinkin zamani ya murza hula zanna bukar, yayi masifar kyau na fitar hankali kamala da cikar zatinsa sun baiyana tare da kwarjinin sa. Se lumlumshe idanunsa yake yana buɗewa yana jin wani irin yanayi a jikinsa tsikar jikinsa na mimmiƙewa har da hamma yake se yace "A'uzubillahi minal shaiɗanir rajim" dan hammar tayi yawa, baya rufe 2 munites bai ba. Tsaki yaja ya buɗe tsumammun idanunsa ya beƙa hannunsa ya ɗauki cup ɗin gabansa ya kurɓi haddaɗan coffee ɗin ya ajiye. Ya kalli tsadaɗiyar agogon hannunsa yaga karfe ɗaya cif-cif na rana, kansa ya dafe yace"A gaskiya ina da uzuri sosai ya sun ce karfe sha biyu da rabi zamu yi taron gashi har karfe ɗaya lokacin sallah." ya faɗa yana jan tsaki ya miƙe tsaye ya nufi toilet. Wayarsa ta ɗauki ringing, kin juyowa yayi ya shige toilet ya ɗauro alwalla ya fito yana dafe kansa yace" Wlh banajin jikina ga gabana na faduwa ko dai na fasa zuwa taron ne?" ya faɗa yana isa gun wayar da take ta ruri kira kan kira, ɗauka yay yayi picking ɗin call ya kara a kunne yace"Nifa bana son jira ko an fasa taron kunce kun shigo gari domin ni amman inata jira..." ko me aka ce masa yace"Ok kuna *JAN GWARZO HOTEL* ganinan." ya faɗa yana tsinke kiran, yana ciza lips ɗinsa har wani duhu yake gani, ya dauki makullan motarsa ya zura wayarsa aljihu ya dauki ɗayar wayar a hannunsa ya nufi ƙofar fita. Anutsu yake takun sa me cike da izza yau ƙafarsa tana ɗan ɗingisawa sbd yadda jikinsa yake a sake ba kwari, lkcn ɗalibai duk suma na fitowa daga class, ba wanda ya ishe sa kallo masallaci ya shiga ana shirin tada sallah yako bi sahu. Ana gamawa motarsa ya shige yabar makarantar Kai tsaye *JAN GWARZO HOTEL* ya nufa...

Se karfi 2:30 pm Mubina ta fito daga class Basma yunwa ta korata gida, Mubina dan ta rantse se ta gama rubutun da Kamal ya basu da safe,
End Ads