x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - KAMAL NE

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 58900 words

Category: Romance Story +18

Views 136

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
cikin nutsuwa take tafiyarta, tana waige-waige tsoro ya ɗan shigeta kaɗan, saboda yanda layin yake shiru ba jama'a sbd garin yakar ɗe da hadari, yayi duhu sosai baka ganin abu da kyau, ga iska ga ɗan yaiyafi anayi gashi zowa bakin titi da ɗan ja. Cikin ikon Allah ta shanyo kwana se ga me adaidaita sahu zai nufi bakin titi, cikin murna Mubina ta fara ɗaga masa hannunta sbd an fara ruwa. Cikin sa'a kuwa ya hangota tinda nan gabanta yake tinka rowa, kuma fitilar adaidaitar a kunne ya haske ta, yana ƙoƙarin ƙarasowa. Mubina ta ja mayafinta ta rufe fuskarta tana jan tsaki tai maga iya saman lips ɗinta, tace"Kaji iskanci aikin banza kawai wlh badan a tsorace nake ba ga gari yayi duhu da sai na koya maka hankali , haka kawai ka haske min fuska..." daidai me adaidaitar ya iso yana washe baki yace"Hajiya se ina amma zaki bada jaka biyu sbd kin san halin da ake ba kowa zai ɗauki mutum yanzu ba , nima na kawo matar da zan aura ce can ƙasa sai na hayo tudun manya.." Mubina cikin jin haushin sa ta buɗe mayafin fuskarta ta kalleshi, idanu Harun niga ya zaro!! yace"Kan uba kece wlh ko me zaki bani bazan ɗauke kiba muguwar yarinya baƙar kadara , anya ke mutum ce kuwa?" ya fada yana ƙokarin tashin a daidaitar shi ya fece.
Ai kuwa jin abinda harun niga ya faɗa ya kuma tsorata!! ga Mubina ma atsora ce! take, amma se taga ta sami dama ko ba kome zata amshe adeɗetar, ta tuƙa da kanta bayan nan zata masa sufar ita ba mutum bace ba ta cinma burinta na tuƙa adedeta, taje har kofar gidan Baffa a bati ba ko sisi. Da sauri ta sanya hannunta saman fatar idanunta, ta juye fatar idanun suka bultso waje, ma'ana fatar idanunta ta sama ta juyo ta ciki ta dawo waje irin dai na yarinta da ake, nasan wasun makaranta ɗayawa zasu gane nufi na... Ta cire mayafin kanta ta daure ƙugunta, ta nasa phone ɗinta cikin bra ɗinta, ta saki gashinta yayi buzu-buzu, Mubina ta zaro idanu ta gwalo harshe waje, ta koma sufa abin tsoro! ta damƙe kwalar niga tana wata irin dariya tace"Hhhhhhh Niga ne ko yaron da ya yaso yama jikanyar tattaɓa kunne na fyade ko? Hhhhhh yau irin ku muke nema zamu yanka ku muba ɗangwandarau jininku ana bikin cika shekarun sa dubu biyu." ta faɗa tana gwagwalo harshe tana zazaro masa idanu, ga idanunta sun tara kwalla dan zafi take ji yanda ta burkita su ɗin. Harun niga cikin matsane cin tashin hanali yace"ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba , wlh bani bane nama jikanyar tattaɓa kunnen ki fyade ki taimaka ya mai girma aljana na tuba..." ɗauke shi Mubina tayi da mari, cikin wata irin murya tace"ka yarda yanzu na kaika gidan da abin ya faru harda kawarta ɗiyar dogarin sarkin aljanun Ethoipia , har jikanta yaje ya ceceta , bari muje kaga gidan daga can se mu kaika gurin sarkin yanka ya maka sallatu a maka askin mutuwa , dan bama kashewa se an ma mutum kaciya da askin mutuwa , maza koma baya bani gaban na tuka muje gidan da kaso kama jikanyar tattaɓa kunnena fyaɗe , maza shiga baya zauna wlh idan kayi ƙoƙarin guduwa zamu lauye ka mu maido ma mafitsaraka goshinka ." ta faɗa tana sakin sa tana gwagwalo masa idanu da harshe.
Niga wanda ya gama rikita cikin rawar jiki ya miƙe ya dira bayan adedeta jikinsa na kyarrrrrma.
Mubina ta gyara idanunta tana kumshe dariyarta, ta kunna adedeta sahun ta fizgeta da karfin gaske ta tafi a guje, ta nufi bakin titi. kuma a lokacin aka saki ruwan sama me karfin gaske irin me iskar nan sosai. Harun banda rawar jiki da zufa da take keto masa babu abinda yake har ya fara ɗigar fitsari, saboda yadda Mubina take tukin bada wasaba tana magana ita ɗaya tana cewa"Sarkin wanzanman aljanun arewa maso kudu ka gyara askarka mun kamo kwarton jikanyar tattaba kunne na , za'a masa sallatu da aski kafin mun kashe shi." ta faɗa tana ƙoƙarin shan kwana ta hau saman titi, dan bata ganin gabanta sosai saboda ruwan da ake zabgawa ga duhu tamkar dare... A daidai lokacin kuma Kamal ya danno hancin motar sa kwanar, idanu ya zaro ganin mace na tuƙa adedeta, ƙoƙarin kaucewa yake daket ya samu ya ɗan kauce ya basu guri su wuce. ganin harda namiji... Ai kuwa Mubina itama sai ƙoƙarin jan burki take adedeta taki tsayawa, ta fasa ihuuuu tana ƙoƙarin direwa ƙasa. Niga yace"don Allah karki kasheni tinda ke ko kinyi hatsarin ba mutuwa zakiyi ba." ya faɗa yana wutsulowa waje. Mubina kuwa tayi muguwar tsorata! ta gigice ta rasa abin yi, saboda faɗuwar gaban da tayi ganin adedetar taki tsawa kuma niga ya dire ya fadi ƙasa, se kiran umpah da Mamu da Amrah da yaya Kabeer da Baffa inusa take, tana ƙoƙarin tsayar da adedetar tama rasa ta ya zata dire irin yanda niga yay... Kamal yayi saurin yin baya da motar yana zaro idanu ganin Mubina ce, ya furta"Ya Salam Allah me iko mai halitta kala-kala anya kuwa yarinyar n..." bai idasa maganar ba ta bugi motar sa da adedeta sahun, ta fasa ihuuuu! tayi baya ta faɗi bata ko motsi... Niga ya dora hannuwa akai yace"Allah ka fitar dani wlh zaiyi wuya nakai gobe , ganin hatsarin mutanan ɓoye ba abu bane me kyau." ya faɗa jikinsa na kyarma. Kamal ya ɗauki bazara ya budeta ya fito ya shiga duba gaban motarsa inda ta buga har ta ɗan lankwasa kaɗan, yaja tsaki ya nufo gunsu. Niga ya ƙarema Kamal kallo yace" wa'innahu sulemanu wa'innahu bissmillahir rahamanir rahim, don Allah ku rabu dani , jikanta karka cutar dani wlh ban ma kakarka kome ba." ya faɗa yana zube ƙasa sumamme fitsari na tsiyaya, amma bazaka ganeba saboda ruwan sama da ake ya jiƙashi jagab.

Kamal yace"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un!! Wannan yaron bashi bane ya kusa mata fyade? Kuma na gansu yanzu? A gaskiya wannan yarinya bata da hankali ko kuma nace tarbiyya." ya faɗa yana nufar niga ya sunkuya ya kara kunnen sa yaji baya numfashi, tura masa yatsarsa cikin kofar hancin sa da karfin gaske, se gashi ya sauke ajiyar zuciya saboda ruwan saman da yake dukan sa. Niga yace"Don Allah jikan aljana kar kumin kaciya da aski inada duka..." Kamal yace daka masa tsawa"Kai!! Dallah bana son hauka uban waye aljanin?" Nan cikin rawar jiki harun niga ya zaiyanewa Kamal kome. Kamal ya jinjina kai yace"Tab to Allah ya kyauta ni ban haɗa iri da itaba ni mutum ne itama mutum ce se dai ita daban take da mutane , bata da hankali tashi maza ka wullota waje ka dauki adedetar ka ka tafi wlh idan ka daka ta wannan sheɗaniyar yarinyar to tabbas zata hallaka ka karka sake tsayawa idan ta tsayar da kai , ko kadai kuna iskanci ne kai da ita?" Niga yace "wlh ko ɗaya ranar ma tsutsayi ne." Kamal yace"Wlh ka kiyayi zini da ƴaƴan mutane , kaji tsoron Allah." ya faɗa yana juyawa ya nufi motar sa ko kallon gurin Mubina bai ba. Niga ya miƙe cikin rawar jiki ruwa ya gama jibgar sa, ya nufi adedeta ɗin yana zuwa ya ganta rabinta a ƙasa a waje rabi a cikin a dedeta ya leƙa da kyau yaga bata motsi amma tsoron sharri irin nata, yasa ya juya da gudu ya nufi Kamal wanda yake ƙoƙarin shiga mota. Yace "Don Allah yallaɓai temaka min wlh bata motsi inajin da ta bugu da motar ka taji ciwo." Kamal yace "No ba ruwana shiga sabgar wannan yarinyar wlh haɗarine ibilisuwa ce..." ya faɗa yana shiga mota. harun niga hankalin sa a tashe ya sunkuya ya riƙe ƙafafun Kamal, ya kece da kuka yana roƙonsa ya raba shi da ita ya temaka ko hospital ya kaita se ayi cigiyar iyayanta. Kamal ya jinjina kai yace"Ok sakeni ni ba asibitin da zan kaita muje na temaketa don Allah ba dan itaba." ya faɗa yana fitowa daga motar. Harun dadi kamar ya kashe shi zai rabu da jaraba.
Kamal isa gurin ya sunkuya ya janye bazara sa, ya kare mata kallo yaga bata numfashi, gashinta ya rufe mata fuska ya soma jiƙewa, ya saka hannun ya janye gashin yaga goshinta ya ɗan kumburo, baki ya taɓe haɗe da fesar da wani irin numfashi me zafi, ya sanya tattausan hannunsa ya ciccibeta ya miƙe da ita, ya rungumota kirjinsa, rigarta da ta jiƙe ta lafe a jikinta nipples ɗinta sunyi wani irin tsini sun manne a rigarta wada tai nasara jiƙewa. Kamal ya dora tattausan hannunsa a saman goshinta ya murza da karfi yana lailawa, kumburin ya ƙura mata fitinannun idanunsa, cike da haushinta, sosai yake murza goshin nata har ƙullutun ya fara bajewa, ya ƙara manneta jikinsa, A hankali ya fara mgn kamar me ciwon baki yace"Mace kamar ƴar tsanar wasan yara se fitinar tsiya , Allah yasa kina da rabon shiriya." ya faɗa yana yamutsa fuska ya nufi motarsa da ita. Niga ai Kamal na cirawa ya faɗa cikin adedeta nan yaga tafkekiyar wayar yako ɗauka ya saka aljihu yace"wlh naci blusu akan wuyar da kika bani ƴar banzar yarinya zaki ga sakaiyya wlh zaki gani bade bakida mutumci ba."ya faɗa yana fizgar a dedetar.
Kamal yana isa mota ya bude set ɗin baya ya kwantar da ita ya rufe, ya zagaya ya shiga ya fizgi motar yabar gurin. Kuma a lokacin ruwan saman ya ɗauke sakammakon kiran sallah da ake ta la'asar. Kamal ganin ruwan ya tsaya cak lkc ɗaya ya fara gudu sosai ya dafe kansa da hannunsa ɗaya, yana muriƙar mamakin wasu irin iyaye ne wannan da basa kula da ƴarsu, wacce Allah ya basu amana amman sun barta ta tambaɗe haka tana tuƙin adedeta a saman titi. A hankali ya furta"Tabbas yarinyar nan bata da iyaye inko tanada to basu bata tarbiyya ba , mace da aka santa da kamun kai da mutunci , a yanzu na gano takura ko horo baza su saka yarinyar nan ta nutsuba kamar ma haukatata suke shirin yi , abu mafi sauki a sami me sata a jiki yana nusar da ita ko Allah yasa ta shiryu , amma tabbas rayuwarta tana cikin garari waye zai temake ta waye ne...? Sageer ne tabbas Sageer ne...." Ya faɗa yana zura hannunsa cikin aljihu ya zaro waya ya kunna, nan take ya shiga neman layin Sageer amma duka layinsa har uku a kashe.
Tsaki Kamal yay ya jiye wayar saman kujera, bai ɗauke hannunda ba ya dafe kansa yana fesar da iskar bakinsa waje, a hankali ya furta "oh my god yanzu meye abun yi? Bari dai nayi sallah na kai ki hospital , na temaka miki karki min mushe a mota , gantalaliya kawai..."Ko gama janye hannunsa bai ba daga ajiye wayar ta ɗauki ringing, ya kalli screen ɗin wayar yaga sunan *my cutie angel* na yawo saman screen ɗin wayar, hannu yasa ya ɗauka yay picking ɗin call ɗin ya manna wayar kunnesa tare da cewa"My angel nah ykk ya garin ku mu munsha ruwa sosai fa." ya faɗa cikin cool voice ɗinsa me ratsa jini da tsoka.
Amrah daga can da take kwance hadadɗan bed ɗinsu ta naɗe cikin lallusan bargo ta lumshe idanunta tana jin muryashi na ratsa jininta da bargonta da tsokarta.
Cikin sanyi murya haɗe da ƴar shagwaɓa tace"My hubby ina yini i miss you rabon muyi mgn tin safe , nayi ta kiranka bana samun ka lfy?" ta karasa maganar a shagwaɓe. Kamal da yake dab da isowa get ɗin gidan su ya saki sansanyan murmushi yace"uhm uhm my cutie soryy mana banda kukan da zai zautani irin wannan shagwaɓa , so yanzu ki kashe an jima zamu yi mgn yanzu zanyi sallah ne bayan haka ina tare da alƙaƙai har na rabu dashi kar a mun mushe a mota , zan kira ki an jima." ya faɗa yana murmushi. Amrah tace"Ok amman Hubby wane irin alƙaƙai? To gaskiya kayi ƙoƙarin rabuwa dashi bye i love u ina jiranka fa." ta faɗa tana dariya ta tinƙe kiran... Mamu ce ta shigo tana cewa"Ke Amrah maza kira Baby naji inda take kinsan halinta sarai taga damar ta fito cikin hadarin nan , kirata muji tana gidan su Basma ko ta tafi gidan Baffa nah , tin kafin umpah ya farga." Amrah tace"To Mamu bari muji wlh nima se yanzu hankali na ya bado." ta faɗa tana kiran number Mubina a kashe, tace "Mamu wlh a kashe wayar bari na kira Basma naji." ta faɗa tana shiga gun ma'adanan lumbobi, ta fito da number Basma, tai dailing. Lkc Basma ta farka taga ji da neman Mubina bata nan ta iske momy ɗaki nan ma tace bata nan maybe ta tafi gida ba tasan halinta ba...!! ta kirata da layin umpah ba'a, ɗauka, shine ta shiga tayi wanka idan ruwan ya ɗage ta tafi gidan Baffa dan tasan tana can. Tana bedroom ɗinta tana cikin toilet bayan ta gama wanka tana alwalla, taji ringing ɗin wayarta. Ta fitowa ganin Amrah ce yasa ta ɗauka tai picking ta kara a kunnenta tace"Aunty ina yini Mubina gida ta dawo ko ta tafi gidan Baffa??" Amrah tace"A'A bata zoba to bari na kirashi muji." ta faɗa tana katse kiran... tai dailing ɗin number Baffa. Wanda lokacin ya fito yana sauri zai shiga masallaci, tsohine ɗan kimanin shekaru 65 me tsukeken jiki. Se sauri yake ya shiga masallaci, yaji rurin waya yayi saurin cirota daga aljihun yay picking, ya kara a kunnensa tare da sallama. Amrah tace"ɗan tsoho Amrah ce Mubina tazo nan gidan ka?" Baffa inusa yace"Ah matar ya gida ya ruwa? A'A amaryata bata zo ba fitowa tayi ne? bata iso ba ina ga amma bari na fito masallaci zan shiga sallah har antayar." ya faɗa yana katse kiran. Amrah tace" Mamu mun shige su Mubina bata gidan su Basma bata gidan Baffa..." Mamu ta buɗe baki zatayi magana taga Umpah a tsaye a kansu ya kafe su da idanunsa ransa a mugun ɓace. Amrah tace "Umpah Baby ta kira ka ne?" bai yi masu magana ba ya juya ya fice dan masallaci zai shiga. Mamu tace taso Amrah yi maza kiyi sallah ki fito nima bari nayi sallah." ta faɗa tana ficewa daga ɗakin. Amrah ta miƙe ta sauko daga saman gadan ta shiga bathroom.......

*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*

*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*



NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻



*Bismillahir Rahamanir Raheem*



*Free Page*


🅿️1️⃣4️⃣

Kamal Amrah na tsinke kiran ya saki lallausan murmushi, ya shiga danna horn tin karfi, se ga megadi ya bude masa tamƙameman get ɗin gidan, ya shige ciki.
Nan farfajiyar gidan yay parking ya juya ya kalli Mubina wacce take sheme a sume, kayan jikinta a jiƙe jagab sun dameta, tsaki yaja ya ɗauke idanunsa daga kallonta ya fito ya kulle motar ya nufi cikin gidan.
Parlon ya shigo shiru ba kowa se Tv, saman bene ya haura cikin saurinsa, yana hawa ya zaro key daga aljihun sa ya saka jikin kofar ya murza ya buɗe kofar yasa kai ciki, wani daddaɗan kamshi ne yake tashi cikin ɗakin kome fes a gyara, kome na ɗakin adon Maroon coulor ne, wani lumtsumeman carpet ne malale a tsakiyar katon filin ɗakin se wani makeken gado da tafkekiyar wardrobe da ta kusa cin rabin bangon ɗakin, da wasu manyan kujeru. Cikin sauri ya rage kayan jikinsa, daga shi se boxer ya shiga bathroom. Shower ya kunna kome agagguce yake, yayi wanka ya ɗaura alwalla faffaɗan kirjinsa mai yalwar ni'imar gashi se ɗigar da ruwa yake, ya daura towel ya fito. Wajan shirin ma a gaggau ce ya shirya ya murza maiyukan sa masu sanyin daɗin kamshi, ya gyara kwantacciyar sumar kansa baƙa lut, se sheki take tana walkiya sansanyan kamshi ke tashi daga cikin jikinsa. Wardrobe ɗinsa ya nufa ya buɗe wace take shaƙe da launin kaya iri iri, wata Jallabiya ruwan toka ya ciro sabuwa dalla a leda ya saka.
Ya dawo gaban dreesing mirror ya fesa sansanyan turansa, ya fice da gaggawa dan an fara sallah. Nan parlo yaga hijab saman kujera a ajiye, ya ɗauka ya fice, nan motar ya bude ya nasa hijab ɗin ya fice Masallacin. Bayan ya fito daga masallaci ya tsinkayo umpah da Abbu sabida gaggawar da yake bai masu magana ba, kuma suma basu ganshi ba, yay wuff ya shige ciki. Yana shiga ya shiga ciki bai jima ba ya fito, ya shige mota yay mata key yana ma megadi horn, ya wangame masa get ya sulala motar waje. Har yanzu su Abbun suna tsaye amman yanzu ƙoƙarin shiga mota suke wacce Haladu ya fito da ita, Kamal ya girgiza kai ya ba motar sa wuta ya fice a guje, yaga suna nunushi, murmushi yayi yana driving ɗinsa cikin nutsuwa, ya nufi hospita nan Katsina hospital kasancewar itace cikin unguwar ba nisa sosai.
Yana zuwa bayan ya shiga ciki yay parking ya ɗauki wayar sa ya kira Dr Munnir, cikin sa'a bugo ɗaya ya ɗaga, Kamal yace"Dr ykk? pls ina son room guda nazo da wata yarinya zan dubata da kaina , ta ɗan sami accident ne."Dr Munnir yace"Ok yallaɓai ba damuwa se ka shigo bari na fito na tare ka." Kamal yace"ok tnx" ya faɗa yana tsinke kiran, ya saka wayar cikin aljihunsa ya buɗe motar ya fito, ya zagaya set ɗin baya ya buɗe ya shiga ya zauna ya sanya tattausan hannayensa ya ɗagota ya tallabota jikinsa ya sanya mata hijab ɗin, ya kwantar da ita ya fito ya rankwafo ya cicciɓeta ya
End Ads