x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 15 - KAMAL NE

  • 42001 words
  • 45000 words
  • Out of 58900 words

Category: Romance Story +18

Views 143

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
mu hadu." Amrah tace "Ayyah ka ɗan saukan ƙasa zan sauko yanzu mijin da zan aura ne yake kirana kaga kar ya ganmu yana ta layin nan pls Hubby kaji." Kamal yace" Ok nima ina tarw da wacce zan aura , amman daman tare kuka zo garin?" Amrah tace" Hummm dalilin da yasa kenan nake so mu hadu na baka hakuri akan yaudar da na maka KAK..." maganar ta ta maƙale ne sakamakon ido hudu da sukayi da Kamal shima ita yake kallo waya manne kunnensa. Yace "cutie ina jinki yi magana nima gani ga amaryata ko na baki ku gaisa?" Amrah ta zaro idanu tana kallonsa bakinta na rawa tace"Ba...na...ga...ne... Ko...me...fa." Kamal ya kura mata idanu yace" Ya ilahi wai dake ne nake wayar ko da wa?" Amrah cikin tsoro!! da murna ta kara matsowa kusan Kamal tace" Kaina daman KAK ne wayyo Allah naji kunya yau da na maka karya ashe abin sona ne iyayena suka haɗamu." Kamal ya tsinke kiran ya iso gabanta yana haɗe face yace " Ko zan iya sanin dalilinki na min karya?" Amrah ta isa kusan sa ta sunkuya gaban sa ta kai guiwowinta ƙasa tace"Na tuba Hubby zan maka bayanin kome wlh..." ya katseta ta hanyar rankwafawa ya kama kafadunta ya miƙar da ita yace" shittt bari har muje gida ki tabbatar kin riƙe kwakwaran hujarki bana son yaudara da kika ganni tabbas ina sonki angel amman zan maki hukunci idan hujarki bata gamsheni ba , Oya muje ki zaɓi abinda kike so." ya faɗa yana tafiya cikin takun sa na kasaita tafiya me cike da burgewa se ka kula zaka ga yana ɗan ɗnkisawa kaɗan. Ƙasa suka sauko tana ta zagaye ta kasa ɗaukar kome.

Mubina kuwa tana saukowa taje gun motarsu ta buɗe, haladu na zaune ta shiga ta zauna ,ta ɗauki wayarta ta kira Sageer bugo ɗaya ya ɗaga tare da cewa" Babyna ykk?" Mubina ta shagwaɓe tace"Sir pls kazo Kalla transa mall yanzu don Allah ka tayani zaɓar kaya zan sayama yayana suit ne kaji." Sageer cikin rawar jiki yace" Baby kinci sa'a kuwa gani a kusanta bari na karaso." cikin murna Mubina tace" tnx my one." ta faɗa tana tsinke kiran

Haladu yace " Auta nima a ɗan siyomin ko da ƴar choukulata ne mana na tsotsa." Mubina ta bushe da dariya tace" Haladu baka da matsala zan siyoma kuwa." ta faɗa tana fitowa daga motar. Bata cike 2 munites ba Sageer ya iso yay parking anan kusan motarsu Mubina ya fito ya haɗe tsaf cikin kananun kaya, ya nufo gunta.
Murmushi ta sakar masa, da sallama ya iso ta amsa tace" My one ngd fa muje to." Sageer yay murmushi suka jera suka shiga. Suna shiga suka ci karo da Kamal dasu Amrah da Samha se kaya suke jidama Amrah. Sageer ya rungume Kamal yana dariya, Kamal yay sansanyan murmushi ya bugi Sageer yace"Kai akwai labari ka smaeni bayan sallar isha." Sageer yace" Ok insha Allahu..." Amrah ta gaishe sa tare da Samha da Zakiyya. Sageer zaiyi magana Mubina ta kama hannumsa tana cewa" Pls my one muje mana." Sageer ya bita yana murmushin farin ciki, suka haura saman bene. Kamal ya basar ya kama hannun Zakiyya yace " ya dai ko tazo ne?" Zakiyya tace" uncle da saura mu tafi naga ji wlh." Janta yayi ya kara jido mata ice cream ita da Amrah su chocoulet alewa turare kaya niki.niƙi sukayi. Amrah kuwa kunya take ji sosai ɗaurewa kawai take wani gefen ga farin ciki ashe zaɓin ranta zata aura. Bayan sun Kamal ya gama biyan kuɗin ma'aikatan gurin suka kai masu kayan har mota suna biye dasu. Zakiyya ya zaunar gaba Samha na baya, Amrah ta masu sallama, Kamal ya rakata har gun motar su ya buɗe mata set ɗin baya ta zauna ya mata sallama yace" Cutie nah zan kiraki zuwa dare naji hujjarki tama masoyin ki wanda baki taɓa ganiba , kuma kina sonsa karaya bye." ya faɗa yana ɗaga mata kira ya nufi motar su. Yana zuwa ya shiga ya mata key ya gizgeta da karfin gaske, yabar wajan a guje yana hawa saman titi ya fara driving ɗinsa cikin kwarewa da nutsuwa, suna hira da kanninsa sama sama...
Mubina irin wanda ta zaɓa a farko sune Sageer ya zaɓa mata, taji dadi sosai kuwa se godiya take masa. Sageer ya hana tabiya kuɗin duk tsadar kayan shi ya biya kuɗin, ya ce kuma ta zaɓi duk abinda take so taki babu yanda bai ba taki karshema fushi tayi masa, dole ya dawo ya shiga lallashinta ga gurin da suke gun jama'a ne, se kallonsu ake soyayyar tasu abin sha'awa yanda yake riritata tana botsewa.
Daket ya samu ta amshi ice cream da chocoulet da ya saya mata tayi godiya cikin shagwaɓa, wacce ta sake dulmiyasa kogin sonta da kaunarta.
Har mota ya kaita yana riƙe da kayanta, ta zauna gaban mota Haladu se washe baki yake yace" Ah su auta sannu Yallaɓai ina yini." ya gaishe da Sageer. Sageer ya amsa yana cewa" Amryarmu allah huta gajiya a sauka lafiya." Amrah tayi dariya tace"Ameen" Mubina tace" My one bye" Sageer ya rufo masu motar yana ɗaga masu hannun ya nufi motarsa shima. yana zaune se da motarsu ta cira yay ma motar sa key yabar wajan cike da farin ciki maras musaltuwa, ji yake ba wanda ya kaishi sa'a a duniya...

Mubina ta jingina kanta da kujera ta lumshe idanunta, tace" Wai na gaji wlh wani irin bacci nake ji gashi magarib ta kusa ma." ta faɗa tana jan tsaki tana rungume jakarta gam a kirjinta, tana lumshe lumsassun idanunta. Amrah tayi dariya tace" Kanwata yau akwai labari amman sai zuwa dare idan mun dawo daga tarbar yaya Kabeer zan faɗa maki." Mubina ta turo ɗan karamin bakinta gaba ta shagwaɓe
tace" Allah ni Aunty se kin bani lbrn yanzu nan ko na maki karya wajan umpah nace tinda muka zo Super market tare kike da maza , baki sayi kome ba sune suka saya maki bayan kinsan an maki miji..." Amrah ta zaro idanu waje tana kallon Mubina. Haladu yace "Ikon Allah Auta waye ya kula maza tsakanin ke da ita? ita wanda zata aura ne ke fa? Ince har kiran kato kika yi a waya yazo ku ka hige ciki kika fito da kaya niki-niki a leda." ya faɗa kansa tsaye yana dariya yana driving ɗinsa... Mubina ta zaro idanu ta juyo cike da tsiwa tace" Kai kai kai Haladu nice zakama ƙage me kake nufi...?
Hkr dan zaku ga error typing😌

*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*

*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*



NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻


```WANNAN PAGEN RANKATA KAF ƊINSA, SADAKARWA CE GA REKU MASOYAN WANNAN BOOK NA KAMAL NE... HAKIKA INAGA ZALLAR KAUNAR KU GA WANNAN BOOK, HAƊE DA RUWAN COMMENTS TARE DA SHARHI, DA KUMA ADDU'O'INKU GARENI, WALLAHI ABUN NA FARANTA RAINA MATUƘA BANI DA BAKIN YI MUKU GODIYA, HAKIƘA KUN CANCANCI NA BAKU KYAUTAR PAGE DUK WACCE TAKE KARANTA WANNAN BOOK TO TA SAKA ARANTA TANA CIKIN WANNAN KYAUTAR, NAGODE MAKU MASOYA ALLAH YA BIYA MANA BUƘATUN MU NA ALKHAIRI NI DAKU DA SAURAN AL'UMMAH MUSULMAI BAKI ƊAYA AMEEN DAN ALFARMAR RABIHIL RAHAMATIHI```


*Bismillahir Rahamanir Raheem*



*Free Page*


🅿️1️⃣7️⃣

"Kana nufin ni ƴar iskace ko me? Haladu?" ta faɗa tana riƙe baki, ta kafe shi da fararan manyan idanunta wanda suka fara rinewa suka bada launin ja, tana girgiza jiki. Amrah dariya abin ya bata amman ta gintse, tana kallon Haladu taji me zai ce mata.
Haladu yace"Niɗin banza na isa na faɗi wannan maganar ga yarinyar albarka , kawai dai naga kece kika kira rabin ranki yazo ya miki sayayya ba Amrah ba , amman tuba nake hajjaju." ya faɗa yana murmushi. Mubina ta kauda kanta ta gyara zamanta, tace" nazata kazafi zaka min ina bin maza wlh da umpah zan faɗama , ince kace wai mairo bata iya kome ƙazama ce kauye zaka maidata wai ya aura maka ni , Allah nasan yau umpah da ya kore ka." ta faɗa tana dariya. Amrah tace" mai karya dai dan wutane." Haladu yace" sosai ma Amrah ,Haba Auta ina zan iya dake ai wlh na yafe ko sadaka ma." ya faɗa yana dariya. Mubina hararasa tayi ta kauda kanta tace" abinda ba asamu ba ne daman." Amrah dai dariya take kawai...
Mamu ce tsakiyar parlo se kai komo take tsaka nin kitchen da kan dining table ana jera kayan abunci, itada da Laure. Da sallama suka shigo niki-niki da kaya, Haladu na biye dasu. Mamu tace " Sannu ku yaran kirki kun jima me aka sayo ma Kabeer ɗin?" Mubina ta cire takalmanta tayi jifa dashi da jakarta da ledojin hannunta tayi kan Mamu da gudu ta fada jikinta ta rungumeta tana dariya. Mamu tace"Baby ya dai an gaji ko?" kai ta ɗaga ta shige jikin Mamu sosai tana turo baki. Haladu ya ajiye kayan ya gaishe da Mamu ya juya zai tafi. Mubina ta janye jikinta daga Mamu tace" Haladu ga chocoulet ɗin fa." ta faɗa tana sunkuyawa ta kwance ledar ta kwaso chocoulet ɗin ta bashi, yayi godiya ya fice. Mamu tace" Me kuka kwaso haka ne?" Amrah ta karasa jikin Mamu ta rungumeta tace" Mamu kinga Hubbi Kamal ne fa yamin siyayya." Mamu tace "madallah Allah yayi albarka." Mubina ta zumburo baki gaba ta kwaso kayan da Sageer ya siya mata tace"Mamu kalli kayan da Sir Sageer ya siya mani malamin mu ne abokin gurgu mijin Amrah ta faɗa tana kwance ledar kayan Kabeer, ta ciro tana gwadama Mamu. Mamu tace" Auta karki sake cema sa gurgu ta ina yazama gurgun? Ko ba kome mijin yayarki ne fa." ta faɗa tana amsar suit ɗin blue coulor masu kyau, tana dubawa. Mubina kuwa fushi tayi ta turo ɗan karamin bakinta gaba tana bubbuga ƙafa ta faɗa kan kujera ta kwanta, ta juya masu baya.
Amrah tace " Kiyi fushin baza a faɗi gaskiya ba , wow Mamu kinsan kayan nan zasu ma Brother kyau." ta faɗa tana duƙawa ta ɗauki robar ice cream ta zauna tana sha. Mamu tace" Autata Kaya sunyi kyau sosai..." Ablah ce ta fito tana jan casbi tace" Auta Mubinat sannu ya gajiya?" Mubina ta miƙe zaune tana narai-narai da idanu tana langwaɓe kanta. Mamu na ganin haka ta sulale tabar gurin.
Ablah tazo ta zauna ta rungumo Mubina tace" Amrah ce ko?" Amrah ta bushe da dariya tace" ni me daɗin suna Ablah kalli kayan da mijina ya saya min." ta faɗa tana kai mata ledojin kayan gabanta, ta ajiye ta juya tana dariya. Ablah tace"ki rabu dasu maza amshi ice ceeam kisha kije kiyi wanka lokacin sallah magarib ya kusa. Ta faɗa tana ɗauko robar ice cream ta buɗe tana bata abaki. Ba ko kunya Mubina ta lafe jikin Ablah tana amsar ice ceam ɗin tana sha.

Kamal daga nan gidan goggo Rumana suka yadda zango, ta ko haɗa masu dambun shinkafa ya sha zogale da man kuli, ta zuba masu cikin kula tare da lemon zobo mai daɗin gaske, suka nufo gida. Danja tana tsayar dasu Kamal waiga war da zaiyi suka haɗa ido da harun niga, ai harun niga bai jira an basu hannu ba ya fizgi keke napep ɗinsa yay gaba a guje kamar zai tashi sama. Kamal ta tintsire da dariya yace"Ikon Allah wato nima ya shiga guduna kenan ko , tab Allah ka shirya fitsarara yarinyar nan." ya faɗa yana sakin murmushi. Zakiyya tace"uncle me akayi ne?" Kamal ya kalli gefenta ya zungure ta a kai yace, "gulma akayi." Samha tayi dariya. Dede lkcn danjar ta basu damar wucewa ya fizgi motar a guge ya wuce.

😀Harun niga kuwa sosai yake gudu kamar zai tashi sama, matar da take bayan napep ɗin tace"Haba yaru karka kashe ni mana kabi a sanun." niga yace"Humm mama karki damu nasan hannuna na iya tuki ki zauna kawi da kyau shine." ya faɗa yan kara gudu dan sam bai yarda da cewar Kamal bai biyo bayan sa ba. Matar nan na bambami, amman niga bai ɗaga mata ƙafa ba gudu yake sosai. Abinda ya faru kuwa ranar da Mubina ta saka niga fitsari, shine bayan Kamal ya ɗauketa niga yabar wajan a guje, kai tsaye gida ya nufa yana zuwa ya kare ma wayar kallo yaga babbar waya ce, ya fara murna yace wlh ruwa da iska bazai bayar da wayar ba yaci blus, nan aka fara damun sa da kira ya kasheta baki ɗaya ya cire layikan ya taune su a lokacin yasaka layikan sa, gashi dama ba security a wayar nan ya goge duka pics ɗin wayar da numbers kowa ya shiga ɗaukan hoto iri iri, ranar niga bai koma neman kudi ba, sabon wanka yayi yaci kwaliya ya fasa yawo a ƙafa. Umpah da suka gaji da kiran layin suka ji baya shiga dole yaje aka masa welcome back ɗin layinsa, ya sayi wata wayar ya haɗa da waccen, niga kuwa har yanzu yana cin duniyar sa da wayar. Kamal suna shuga gida ana kiran sallah magarib, a gaggauce yayi wanka ya zura jallabiya ya tafi masallaci.
Bayan sallah isha su Mubina suka shirya harda Basma tazo suka rankaya Airport tarba Kabeer. Bayan sallah isha Kamal da su Zakiyya suka baje cin dambun da gwaggo ta basu, se santi suke bugawa, bayan sun gama yasha lemon zoɓo suna santi Ummah sai dariya take masu. Yana gamawa yay wanka ya shirya cikin kananun kaya ya tafi can gidansu Ummah ya gaishe da tsoho Sidi.


Zaune suke a cikin Airport gurin da aka tana da domin zaman masu tarba baƙi. Mubina tana laɓe jikin umpah tayi kyau har ta gaji. Amrah ma tayi mutikar kyau sosai, Basma ma tayi kyau ba karya lass ne blue me ratsin fari ɗinki riga da siket ya mata kyau se hijab ɗan karami da ta saka. Haka Umpah da Mamu masha Allah dasu. Karfe 9:23 pm na dare jirgin su Kabeer ya sauka maradi. Mubina najin saukar jirgi ta ruƙumƙume umpah tana murna tace" umpah wlh su yaya Kabeer ne suka iso yanzu." ta faɗa tana murna. Amrah tace " Wayyo yau zanga brother nah..." Basma tace"Aunty brother ɗinmu dai ko Mubina?" Umpah yay dariya.
Wani hadadɗan gaye fari kyakywa ya haɗe cikin suit baƙaƙe masu matiƙar tsada da kyau, baƙin glass manne kan kyakyawar fuskar shi, kallo ɗaya zaka masa kasan balarabe ne. A nutse yake saukowa daga matatakalar jirgin yana riƙe da wata ƴar jaka mai masifar kyau.
Bayan sun gama saukowa an gama duk binci kar kayan su da posport ɗin, su Kabeer yana janye da katuwar akwatinsa ya nufi inda yasan ƴan gidan su na jiransa. Daga nesa ya hango su umpah da su Mubina tare da wata haɗaɗiyar yarinya kusan Mubina, kallo ɗaya mata ya gane Basma ce ƙawar Mubina dan tana yawan tura masa pic ɗin su tare da ita. Mubina tana hango Kabeer ta fasa ihu ta saki umpah ta ruga a guje tai kansa tana dariya. Amrah ma da Basma suka bi bayanta a guje. Kabeer yana hango Mubuna ta taho da gudu ya a jiye jakarsa ya ware mata hannayensa, tana isowa ta fada saman kirjinsa tana dariya, ya zagaye hannunsa bayanta yana juyi da ita yace" Wow my baby kanwas kin kara kyau da girma masha Allah iye babyn umpah." ya faɗa yana ɗagata sama kamar ƴar tsana, itako sai dariya take tana cewa"Wayyo my brother nah ka tsaya na maka sannu da zuwa mana." dariya yay ya ajiyeta. Dede lokacin su Amrah da Basma suka iso kusan su Amrah ta rungume shi ta baya tana dariya tace" Oyoyo my brother nah sannu da zuwa ka wani biye ma baby ko ta ni dasu umpah baka yi ko?" Kabeer ya saki Mubina ya rungume Amrah yace "Ayyah my kanwas sorry nayi missing ɗinku sosai fa." ya faɗa yana ɗagata yace" Aushhh kanwas kin fiye lukutanci ba kamar Baby ba sakwat ba nauyi..." Mubina ta bushe da dariya tace" Ai shine yaya wlh ni bana son ƙiba ko kaɗan ko na girma na isa aure an mini aure , ba zanyi ƙiba ba..." Basma ta bushe da dariya ta rungume Mubina tace" Aunty Amrah karki raga mata yasin dake take." Kabeer ya kalli Basma jin zazzaƙar muryata ya ƙura mata idanu yana kallon yadda take magana abun burgewa. Ɗagowar da Basma zata yi suka haɗa idanu da Kabeer, da sauri ta sadda kanta ƙasa cikin jin kunya tace"My brother sannu da zuwa ina yini." Kabeer ya janye Amrah jikinsa yace" lfy lau Basma yan mata ko?" murmushi tayi ta nufi gun akwatinsa ta sunkuya ta janyota. Su umpah ne suka iso yana cewa" Bari mu ma mu iso tinda kannin ka sun janye maka hankali..." Kabeer ya karasa yana murmushi ya rungume Umpah yace" i miss u my daddy na same ku lafiya?" ya faɗa yana sakinsa ya nufi gun Mamu ya rungumeta yana murmushi. Mamu ta shafi bayan sa tana murmushi. Umpah yace" Yanzu dai mu kara sa gida mu gaisa da kyau." ya faɗa yana kama hannun Mubuna da ta manne Kabeer. Basma na jaye da akwaitin Kabeer suka nufi kofar tafiya kowa ransa fari tass, suka dunguma gida. Ko a mota Mubina tana kusan Kabeer se sangarta take zuba masa.

Suna zuwa gida Mubina ta haɗa ma Kabeer ruwan wanka, daman itace ta gyara masa part ɗinsa, kome tsaf se gamshi ke tashi. yay wanka ya shirya cikin kananun kaya ya fito. Kamshi ya cika masa hanci dan Mubina tayi turare yafi kala biyar na wuta, kamshi har farfajiyar gidansu.
Zaune suke a parlo Mubuna tana jikin Ablah. Kabeer ya zo ya janyeta ya rungume Ablah yana mata kiss yace" i miss u Ablah
End Ads