x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 10 - KAMAL NE

  • 27001 words
  • 30000 words
  • Out of 58900 words

Category: Romance Story +18

Views 132

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
bazai wuce tafiyar 3 munites ba , a kunna min daddɗan turaren wutar nan fura kada a sa min ƙanƙara wlh mura nake ji tin jiya , bye se na iso." ya faɗa yana tsinke kiran. Ya karya kwanar titin ya tsinkayo su Mubina, suna tahowa kallo ɗaya ya mata ya ganeta saboda face ɗin motar sa suke tahowa, yanda take takunta cike da jiji da kai se dai fuskarta ba walwala waya manne a kunneta tana mgn, ga takalmin ƙafarta da tsini, kirjinta se kaɗawa yake, hips ɗinta ya fito, se kallan baiwar kyanta jama'a suke, wani matashi na biye dasu a mota. Kamal ya zaro fitinanun idanunsa, yace"Ikon Allah wannan yarinyar ashe har yawon banza take haka wai ina iyayanta ne? Suka barta ta lalace gata jarababbiya , basa tsoron ta ɗauko masu abin kunya , kai Allah ka shiryemu amma nan babu tarbiyya bari kiga na hargitsa miki lisafi tinda baki san waye ba bare ki ɗauki fansa , masifafiya zakiyi zawo yanzu , muga karya tafiyar iskanci bari na fanshe ɓarnar da kika min." ya faɗa ya sakin murmushin mugunta ya saki hanya yay kanta a guje. Basma ta fasa ihu tace"Mubina kauce mota..." Mubina ganin mota tayi kansu ta fasa uban ihu! tace"Ablah hatsari..."ta saki wayar umpah ta faɗi ƙasa jikinta na rawa........

*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*

*💖😭KAMAL NE😭💖*

_*Book 1*_



_NA_

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

_Ƴar Mutan Niger_🤙🏻



```IDAN KANA SON KAGA ASALIN MASOYAN KA DA ZALLAR KAUNAR DA AKE NUNA MAKA TA ZAHIRI DA TA BAƊINI, TO SAI KIN FARA SIYAR DA BOOK, NAN NE ZAKIGA HAKIƘANIN MASONYAN ASALI NA GASAKIYA, MASOYANA INA ALFAHARI DAKU, BANI DA BAKIN MAKU GODIYA SAI DAI NACE ALLAH YABAR ZUMUNCI, DAN ZO MUCI TUWO YAFI TUWON DADI, WALLAHI INA MATUƘAR GODIYA MUCH LOVE MASOYAN ASALI🤝🏻🤝🏻🤝🏻😍```..


_*Bismillahir Rahamanir Raheem*_



_*Free Page*_


_🅿️1️⃣2️⃣_


Mubina ta gigice tama rasa inda zata bi, dan motar gunta ta nufo gadan-gadan, tayi saurin kaucewa gefe da bai bita ba amman ya sake binta, duk inda tabi nan Kamal yake bi, kuma yaki bugeta se kewaya gun suke. Mubina gajiya ta fara yi, tsaye tayi cak cike da masifa da rashin kunya ta riƙe ƙugunta tana shasheƙa, tace" Ko uban waye wlh bazan gudu ba idan ka fasa kaɗeni kaki Allah da manzon sa." ta faɗa tana ƙarƙaɗa ƙugunta tayi tsaye kyam a gurin. Kamal ya bushe da dariya ya sake nufarta gadan-gadan, tako ki gusawa ta ware hannayenta tace"idan kai ɗan halak ne kabi ta kaina wake da zunubi...?" ta fada tana lumshe idanunta. Kamal ya zaro idanu yana dariya yace" ƴsr bala'i bazan kashe kiba zan dai baɗeki da kura nayi gaba naci bulus." ya faɗa yana tashin ƙura yay kanta gadan-gadan yana dariya. Basma ta rikice tayo kan motar a guje tana cewa" koji mugun mutum waye ne? me ta maka da zaka nemi kasheta." kafin take isowa tuni Kamal ya kai ga Mubina, saura kiris ya bugeta yaja burki da karfin gaske, yay baya yana dariya ya baɗeta ko da ƙura kasancewar gurin akwai rere. Mubina jin bai bugeta ba yasa ta bude idanunta ta kalli motar, amman sbd glass ɗinta me duhune ba'a ganin na ciki se na waje. Sukuyawa tayi tana cewa"wlh se ka sani idan ba tsoro ba ka fito ka baiyana kanka mana , kaga bala'i da masifa yau." ta faɗa tana cika hannayenta da ƙasa da wani katon dutsi tayi kan motar Kamal, amman kafin take isowa ya fizgi motar da karfin gaske ya waske ya barsu da ƙura. Basma ta riƙota tace"Mu barshi da Allah ko waye zubar da ƙasar mu tafi Allah zai saka miki." ta faɗa tana kakaɓe ma Mubina hannunta, da jikinta ta kama hannunta kenan wayar umpah da take hannun Basma wace Mubina ta yada ta a ƙasa ta soma ringing, Basma ta bata"Amshi Ablah ce." Mubina ta kalli tsirarin mutanan dake kallan su tace" uban me ake kallo jikinmu? ko munyi abun kunya ne? Kai wlh mutane basa rasa abin gulma , ki bari Basma ina cikin mugun ɓacin rai yanzu bazan iya magana ba , amman duk ranar da na hadu da wannan mutumin wlh zai san ya taɓo giɗan rina..." tace to ai akwai irin motocin babu yanda za'ayi kisan waye tinda bai bari munga number motar ba , inda kinga fuskarsa ne ko yaya amma motocin ai ko Sir kangiwa na da irinta fa ko yau da irinta yazo makaranta..." Mubina ta damƙe hannun Basma da karfi cikin ƙaraji tace"Wlh shine tabbas shine amman wannan karon zaiyi da nasani maras anfani..." Basma tace"A'A karki yanke hukunci kai tsaye mana taya zaki ce shine? Bayan kinsan baya shiga shirgin mutane se an taɓoshi , ai bamu tabbatar ba..." Mubina cikin ƙaraji tace"ubanki Basma kajimi da ƴar iska waye ɗan iska a garinan idan ba ɗan gurgu ba?. "Wlh shine"ta faɗa tana ciza lips ɗinta na ƙasa. Basma zatayi magana wayar hannunta ta sake ɗaukan ruri, tace" Ngd da zagi kawas pls ɗauki ki kwantar mata da hankali cewar ba ke bace kinga mashin ya faɗi ne shine kika cemata hatsari." Mubina ta amsa tai picking, ta manna a kunnata tace"Ablah karki tashi hankalin ki bani bace wasu masu mashin ne kinji my Ablah nah." daga can Ablah ta sauke ajiyar zuciya tace"Alhmdllh Mubeena bari zan ɗan kwanta anjima zan kiraki kiba Abdul wayarsa kinji." Mubina ta ɗaga kai tana sauke numfashi tace"Ok bye" ta faɗa tana katse kiran. Wannan saurayin da yake binsu a mota yay parking gabansu ya janye galss ya masu sallama. Mubina ko kallo saboda tana cikin ɓacin rai ta damƙe hannun Basma tace"wlh kika tsaya zan maki rashin mutunci wuce muje seda ya gama gulma sa zai mana mgn , inda shi jarumine fito na fito zaiyi a lokacin da Kankura gurgu yaso nakasani , dan ayi one one shi mugu da lkcn zai tare sa da mota suyi ɗauki ba dadi , amman ba ka laɓe ba sai da kaga ya tafi ka wani mana mgn kaji ɗan arrr..." Basma ko iskar da ta debosa bata kalla ba suka ida shan kwana Basma tace ƙawata ki daina cewa fa Kangiwa ne zato zunubi kida ya zamanto gaskiya." Mubina tace "mubar maganar kawai kar na miki zagin arnan da." Basma tace"na bari." Mubina ko cikin salon takunta babu abinda ya sauya haka suka karaso har get ɗin gidan su Basma guy ɗin nan na biye dasu har suka shige ciki, ya juya baya.

Masha Allah gidan ya hadu sosai babu karya ta ko ina. Hajiya lubah na zaune a parlo tana waya, Sakina na jikinta a kwance yarinya ce yar kimani 11 year, parlon suka shigo da sallama. Mubina tayi gun hajiyar tana zumburo baki tace" Ke Sakina se kina haye mana momy ko?" ta faɗa tana ture Sakinar ta shige jikin Lubah. Basma ma tazo ta rungumeta suka wani ƙamƙameta. Sakina ta bushe da dariya tace"Ƙatai basajin kunya se na gama ku da yaya Anwar." Momy tayi dariya ta rungume su tana shafa bayansu, tace"Sannunku a ƙafa kuka karaso ko?" Mubina ta ɗaga kanta tace"Momy ina yini." Lubah ta masa tace" maza ku tashi kuci abunci"Basma ta miƙe tana cewa "to bari na canza kaya ku fara ci." ta faɗa tana shiga bedroom ɗinsu. Mubina tayi wani luf jikin momy kamar mage, tana lumshe idanunta. Lubah tace"dota tashi maza kije dining ki cika cikinki nasan sarai baku tsaya kunci wani abun ba?" Mubina ta ɗaga kanta a cikin sanyi murya tace"momy bana sha'awar cin kome yanzu wlh , amman bari na ɗauko koda frech milk nasha bacci ma nake ji." ta faɗa tana janye jikinta daga na momy ta miƙe, ta nufi kitchen. Frech milk ta ɗauko tazo ta zauna kusan momy ta fara sha tana lumshe idanunta wanda suka ƙaɗe suka yi jajur. Kamal banda dariya babu abinda yake, yana driving se da yayi ta isheshi ya gintse yana driving ɗinsa a cikin nutsuwa, ransa fari fas ya ɓata ma mara kunya ranta. Wani hadadɗan gidane madede ci ya hadu ba karya, a unguwar citè nan naga Kamal ya tsaya a dede get ɗin yana zuba horn. Megadi ya buɗe masa ya shige ciki, nan farfajiyar gidan yay parking ya fito, yana riƙe da wayoyinsa bayan sun gaisa da megadi ya wuce ciki anutse yake takunsa me cike da jarumta da izza, kirjinsa me cike da yalwar gashi gwanin sha'awa se sama da ƙasa yake, Kamal ba karamin kato bane. Wani hadadɗan parlo ne me tsari, wata dattijuwa zaune ƙasa saman carpet, farin glass manne a fuskarta wata kwarya ce me zane me kyau, a gabanta tana dama fura wacce taji nonon kindirmo, wasu yara har uku sun baibayeta, maza biyu mace ɗaya, se surutu suke zuba mata. Ameer yace"Goggo Ruma zan sha fura ai baza a ba Sameera ba ko?" Lateef yace"se an bata kuji kai fura uncle Kamal ce fa ko goggo." Wata ƴar matashiyar mata ta fito zata kai 27 year tace"To maganatu in sake jin kace Kamal uncle ɗin dai yan maganatun uwa."goggo Ruma tayi dariya tace"Hafsat bake rabo da faɗa kina ji da ɗanki Kamal ko..."Sallamar Kamal ta katse ma goggo hira ta amsa, yaran suka yi kansa suna "Oyoyo uncle."ɗaya bayan ɗaya ya ɗagasu yana masu kiss ya ajiye su yana cewa"ƴan kanina yaran kirki bari na gaisa da momyna autar goggo." ya faɗa ya nufi gun Hafsat, yana murmushi kusanta ya zauna ya jingina da kafadata, yace"momy ina yini ashe kuna nan naku zuwa gidan naki fa." Hafsat ta shafi kansa tana murmushi tace"Eh gani nan munzo yini , ina yayana da aunty Mamu da Samha? Wai auta ina kabar Sumaiyya da ibrahim ɗin zan zama auta ƴan biyun goggo kake maidamu baya, se na faɗama Sumaiyya." Kamal ya miƙe yace"ni fa ba daga gida nake ba kuma na kashe wayoyina so nake nai bacci har zuwa la'asar , sorry momy Hafast kawo ibrahim namijine shine babbanku a yanzu ko goggo Rumana."ya faɗa yana zama kusa da goggo ya rungumota yana dariya, ta bugeshi tana cewa"sakeni ban saniba , idan fura ta zube fa." sakinta yay yana murmushi, yaran suka haye saman sa, seda Hafsat ta masu tsawa!! Kamal sosai yasha fura yana santin yace idan yayi aure goggo zata koyama matarsa. Bayan ya gama shan fura, ya miƙe Hafsat na tsokanar sa ya shige cikin ɗakin da yake kwanci, ɗakin yasha gyara an shimfiɗa sabon zanin gado se baza kamshi ɗakin yake, ya tube yay wanka ya saka rigar bacci dan yanada kaya a nan, ya kunna Ac ya faɗa saman gado ko 5 munite bai ba se bacci.

Ɓangaran su umpah kuwa suna zuwa company suka taras Kamal baya nan, Abbu yace kawai su wuce police sitetion ɗin. Shine fa suka je, sukama Acp bayanin kome, nan ya haɗasu da ƴan sanda suka zo gida nan suka isko Mubina bata nan se Amrah da Mamu, umpah yake ma Mamu bayanin suna tare da ƴan sanda, nan Mamu ta bashi labarin yadda Basma ta faɗa mata. Mamu tace"Wlh kuma cewar tasha ruwan toilet karya ne irin nata , amma idan baka yarda ba kuje gidan su Basma tana can ta faɗa maka malamin , naji dai Basma tace kangiwa ne..."Nan umpah ya zaro idanu cike da mamaki!! yace" anya kuwa?" bari na kirata naji" nan ya kira number ta a kashe, ya kira wayarsa ta wajanta yaji tana amsa waya. Umpah yace"Tabbas kangiwa ɗayane maradi, Kamalu ne kenan? Tare fa muke yanzu da mahaifinsa Abubakar wannan makocin namu me kirki , amma yau da na tafka abin kunya Nusy abar maganar Baby kenan ashe lfy lau gashi ta fita yawo , bari na sallami yan sandar." ya faɗa yana juyawa. Amrah ta kyalkyale da dariya harda riƙe ciki tace "Wlh idan umpah na biya Baby se ta saka shi jin kunya."Mamu tace"hummm barshi ai tin farin maganar nasan karya take shi marinta dai da yayi har san hannunsa suka fito shine ilar amman ita taja..." Amrah ta miƙe tana dariya tace "bari na leƙa naga ya zaiyi da ƴan sandar." ta faɗa tana ficewa daga parlon.
Umpah kuwa sallamar ƴan sandar yayi yama Abbu bayanin wai Kamalu nasu ne... Habawa ai kuwa Abbu yace se an kai sa police sitetion sunji dalilin da yasa yaci zalinta. Daket umpah ya ba Abbu hakuri ya hakura nan sukayi sallama da juna Abbu yace masa zuwa dare zasuyi magana me mahimmanci... Da haka de suka rabu umpah ya koma gida, Abbu ya shiga gida shima.

Samha ce zaune a parlo tana waya da Safiyya ƙanwar Abbu cewar hutu gatanan zuwa kebbi... Abbu ya shigo da sallama. Samha ta miƙe tana cewa"mamah ga Abbu ya shigo." ta ƙarasa tana faɗawa jikinsa ta kara masa wayar a kunnesa, ya fara magana"Ah Safiyya ya kebbi?" daga can tace"Yayana lafiya lau yasu goggon mu? Ga zakiyya na fa tafe tace nan zata haihu wlh ba yanda mijin baiba ta haihu nan sbd haihuwar farko ce amma tace niger zata zo gidan kawunta , Mamu ta bata kulawa." ta kai ƙarshen maganar tana dariya. Abbu yace"Gud Safiyya naji dadi sosai to mijin ya kawota da kansa saboda cikin yayi girma sosai ina Muhuseen da iyali? Dazu mun gaisa." Safiyya tace"rabona dashi shekaran jiya naje me sunan goggo ta fadi ta goce." Abbu yace "wh ai da sauƙi Allah bata lfy bari na shiga na ɗan huta." nan suka yi sallama ta kashe kiran. Ya kalli Samha yace"Ina ummah ki ne?" Samha ta saki Abbu tana dariya tace" Tana bacci fa tinda tayi sallah bari nima naje na huta , Abbu ina Yaya "Kamal ne? Ko ya tafi gidan goggo?" Abbu ya shafi kanta yace"Oho masa laifi yayi bari naje na sami mamarki muzanta , na masa mata yau zan nemi izini gun mahaifinta." ya faɗa yana haurawa saman bene. Samha tayi ihu da tsalle tana murna tace"mun kusa raƙashewa a she." ta faɗa tana nufar saman dan ta kwanta ta huta...

Basma ta jima kafin ta fito lokacin Mubina ta shanye frech milk tana gyangyaɗi har baccin ya kwasheta, momy ta gyara mata kwanciyarta ta rufa mata mayafinta tana dariya.
Basma ganin Mubina tayi bacci yasa ta kyaleta taje kan dining ta cika cikinta dam, ta ɗan fita kofar parlo tana leƙe taga garin ya fara duhu sosai akwai hadari, cikin farin ciki itama ta kwanta nan parlon sbd tana son ruwan sama sosai tace ma momy ta tasheta idan an fara ruwa... momy itama janye Sakina tayi suka shiga bedroom domin suma su ɗan taɓa barcin...

Kamal baccinsa yake cikin nutsuwa da kwanciyar hankali yana fitar da numfashi me cike da lafiya. Ameer ne ya murɗa kofar ɗakin, ya shigo da gudu yana ihu yana kiran Kamal"Uncle taso kaga garin an fara duhu kamar dare." ya faɗa yana hayewa saman gadon ya fadawa saman kan Kamal. Firgigit Kamal ya farka salati dauke a bakinsa, yace"Oh yaranan baku barin mutum ya kwanta bari ma na tafi gidan mu kawai." ya faɗa yana janye Ameer daga jikinsa ya sauko daga saman gadon, ya sanya takalminsa ya kwashi wayoyinsa ya zuba aljihu ba tare da ya kunna ba, yana yamutsa fuska sai lumlumshe tsumammun idanunsa yake, ya kama hannun Ameer suka fito. Goggo tace "amman Ameer anyi maras ji , ka tado yayan ka ai kuwa se na faɗama Hafsat." Kamal yace" tsofuwa na gudu se kin jini gobe ina mom Hafsat"? Goggo tace tana ciki wai bacci take , amman a wannan yanayin zaka fita ka bari har a lafa mana." Kamal ya galla mata harara yace "anki ɗin Abbu yanzu haka na nema na duk yasan ban wuce nan ko Company , na tafi se na dawo." ya faɗa yana sakin hannun Ameer ya rankwafa yama goggo kiss ya miƙe yana murmushi ya fice. Ameer ze bishi goggo tace"Maza dawo kasan halin gambo nemi gu zauna idan ta tashi zata kai ka..." Ameer ya dawo ya zauna. Kamal yana fita ya shiga motarsa yaja ya fice daga gidan, a guje saboda yanayin garin...

Mubina baccin ta take me mahaukacin dadi se wani mimmiƙewa take tana ɓaƙaro kirjinta, ai kuwa se gata ta fado daga saman kujera dimm. A firgice ta buɗe manyan idanunta ta zumburo baki gaba tana riƙe ƙugunta tace"Woshhhh bayana Ashhhh naji zafi ya ma akayi na fado? tirrr." ta faɗa tana kallon Basma tana sharara bacci. Tsaki taja ta miƙe tana riƙe da kugunta ta ɗauki wayarta tayi kan Basma ta ɗaga hannunta zata shirga mata ƙulli ko me ta tuna ta fasa, ta saka takalminta ta yane kanta da ɗan gyalan Abayarta ta fice tana yamutsa fuska. Tana fitowa ta zaro idanu ganin garin yayi duhu sosai kamar dare, ga iska kaɗan-kaɗan, har an fara yaiyafi. Da ɗan saurinta ta fara tafiya tana sakin murmushi tace"Wow dama na taso Basma mun tafi gidan Baffa inusa ruwa ya bamu kashi a hanya ina son ruwa sosai , se dai duhun yayi yawa bari nayi sauri na samu adaidaita sahu." ta faɗa tana isowa bakin get ta bude kofar ƙarama ta fice..........



_*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*_
_*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*_

*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*



NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻



*Bismillahir Rahamanir Raheem*



*Free Page*


🅿️1️⃣3️⃣

Mubina
End Ads