x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 13 - KAMAL NE

  • 36001 words
  • 39000 words
  • Out of 58900 words

Category: Romance Story +18

Views 139

18 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
kece zakkar gidan ku an baki tarbiyya kece kika watsata a titi.? Ban de kula shiba, sbd gudun kar yamin duran yawu nayi shiru ban sake kallon inda yake ba har muka iso kofar gidan mu daidai lokacin kuma su umpah suka yi parking ɗin motar su a kofar gidan. Yana tsayawa na soma ƙoƙarin bude mota ina kiran umpah amman bazai ganni ba sbd glass ɗin me suhu ne. Hucin numfashin sa naji kusan kunnena, hannunsa yana gugar jikina, nai saurin ɗagowa idanunmu suka sarƙe guri guda, fuskokin mu suka haɗe, har lips ɗinmu na gugar juna, nayi saurin janyewa ina murguda masa baki, yana ƙoƙarin buɗe min motar, yana budewa na zuro ƙafafuna waje na ƙaƙalo yawun bakina na tofa masa a fuskar shi haɗe da kai masa duka tin karfi a kirjinsa na kece da kuka nace "na barka da Allah"na fice a guje na nufi motar umpah ina ihuuuuu.... Inde *Kamal ne...* Ba'ama fara ba!!! Hakuri da rashin Editing me kyau😌


*Labarin nan na kudi ne kan farashi me sauƙi, book 1&2 zaku same shi akan 200N kacal, ga mutanan mu na Niger zaku biya 400F, ba tsauwalawa hakan ta faru ne saboda masoyana na asali, karfa ku sake ayi baku wannna salon na daban ne, wannan karon bana cewa kome kune zaku faɗa insha Allahu, duk me bukatar siya zaku tuntuɓeni ta wannan*
*Lambobin👉🏻+22796515805/ +22792589446, karku manta nera 200 kacal zaku karanta book 1&2 ,Real ladingo na maraba da masoyanta har kullum💃🏻💃🏻💃🏻*

*💖😭KAMAL NE😭💖*

*Book 1*



NA

*Real ladingo*
*Sweet Baby💋*

Ƴar Mutan Niger🤙🏻



*Bismillahir Rahamanir Raheem*



*Free Page*


🅿️1️⃣5️⃣


Kamal tsumammun idanunsa ya zuba ma Mubina, ya sanya hannunsa ya dafe kansa ransa yayi mugun ɓaci, ya sanya hannunsa saman fuskarsa ya shafo yawun da ta tofa masa, kai ya girgiza ya gogo yawun ya ƙura masa ido, ciza lips ɗinsa, yama motar key, wayarsa ta ɗauki ringing ya kai kallonsa kan wayar yaga Sageer ne, ya ɗauka yay picking ya manna a kunnen sa cikin daddaɗar muryasa yace"ya ykk wai ina ka shige ne yau? kiran da na maka yafi a ƙirga." ya faɗa yana fizgar motar ya karasa get ɗin gidan su yana horn, megadi ya buɗe masa ya shige. Mubina kuwa banda kururuwa da ihuuuu babu abinda take yi, su umpah a guje suka fito suka yi kanta, umpah yace"Baby ina kika shiga? yau kin bamu wuya mun gaji da neman ki yanzu da police sitetion zamu bada cigiyar ki da gidan Tv da Redio ina kika shiga?" Mubina ta kara sa da gudu ta fada jikin umpah tana kuka. Abbu yace "Ah ya naga Kamal ya kawoki doter ina ya samo ki?" cikin kukan sangarta tace"Dady shine ya sace ni kawai muna cikin tafiya ana ruwa nida me napep se ya ɗinga bin mu muna gocewa , dama kuma tin da rana lokacin da zamu gidan su Basma ya biyo ni yake son sace ni Allah ne ya tsare ni , se ɗazu ya buge mu da mota ya zuba min wata hoda na suma nan take ya ɗauke ni ban tashi farkawa ba se hospital yanzu ma karfin Addu'a ce tasa ya maidoni..." ta karasa tana kuka.
Umpah ya waro idanu yace" Kamalu ɗin da kansa innalillahi wa'inna ilahir raji'un!! Me ya miki kenan...?" Abbu ya katse umpah cewar"Amma Kamalu ya bani mamaki ban taɓa zaton zaiyi haka ba wlh ɗiyar abokina ya lalata, doter ya miki wani abu ne?" Mubina tace"Eh duka na yayi tayi mari harbi wai baya son ganina se ya naka sani..." ta faɗa tana kara sakin kuka.
Abbu yace"Yi shurinki doter ai dole zai soki shiɗin banza , Abdulrahim pls ina son mu haɗa meeting yanzu da iyalan mu , ka tara naka iyalan nima bari na shiga ciki yanzu na fito da nawa da nace se dare to yanzu za ayi ta ta kare." ya faɗa yana kallon umpah.
Umpah ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, yace"Babu damuwa Abubakar se ka fito ɗin insha Allahu amman karka takura yarona baka san dalilinsa ba..." Abbu girgiza kai ya nufi get ɗin gidan sa.
Umpah ya kama Mubina suka nufi cikin gida, Haladu na riƙe da haɓa yana kallon ikon Allah.

Mamu na zaune a parlo ta rabka tagumi, dan yanzu Baffa ya gama mata faɗa sun gaji da yawo basu ga Mubina. Amrah tace" Mamu kinji su umpah shiru yamma tayi sosai basu dawo ba..." Umpah na yay sallama suka shigon yana riƙe da Mubina. Mamu ta miƙe ta kamota ta rungume tana sauke ajiyar zuciya, tace "Baby ina kika shige?" Mubina tace" malamin mu ne ya sace ni wlh..." Amrah ta iso tana rungumeta tace" Me kika masa sacewa kuma baby?" umpah yace"Karya tayi masa ne? tazo ma baza ku barta ta huta ba , baby jeki maza kiyi wanka ki huta." Mubina najin haka ta janye daga jikin Mamu da Amrah ta nufi sama da gudunta. Mamu tabita da kallo ta juyo ta kalli umpah, tace"Abban Mubina sbd Allah baza a tambaye ta aji ba'asi ba , se abarta ni sam abun baya min dadi pls ka aura da yarinyar nan..." katseta yayi da cewa"Wlh Nusaiba zamu sami matsala dake yazu dai ku shirya zamuyi baƙi a shirya parlon baƙi da kayan motsa bakina asa turaren wuta." ya faɗa yana haurawa sama. Mamu ta kalli Amrah tace"Hummm Allah ya kyauta Amrah jeki maza sa laure ta gyara parlon baƙi a kai kome na motsa baki keko kisa turaren wuta kiyi maza ki shirya bari na sami baby." ta faɗa tana haurawa saman bene. Amrah ta nufi kitchen gun laure dan ta fara girkin dare.
Mubina tana shiga ta cire kayan jikinta tai fatali dasu ƙasa ta nufi bathroom, tana shiga ta kunna shower sansanyan ruwa na sauka kanta ta lumshe idanunta tana ƙamƙame jikinta tana sauke ajiyar zuciya nipples ɗinta sun wani mimmiƙe sonyi tsini sosai bakinsu ya buɗe sai game ƙafafunta take, daket ta samu tayi wankan ta ɗauro alwalla ta saka rigar wanka ta daure kanta da towel ta fito.
Kai tsaye wardrobe ta nufa ta bude tana ciza lips ɗinta idanunta na lumshewa, ta zaro abaya tana ƙoƙarin cire rigar wankan, Mamu ta shigo da sallama, Mubina ta amsa tayi fatali da rigar tana ƙoƙarin saka abayar, Mamu ta iso ta mata duka a baya tace"Wai yaushe zakiyi hankali baby ke kome tsirara bakya jin kunya." Mubina ta rungume Mamu gam ta nitsa kanta kirjinta a shagwaɓe tace"Mamu ni samin rigar yo wa zai shigo daga waje ya ganin yo." Mamu ta girgiza kai ta amshi rigar ta saka mata. Mubina ta yane kanta da mayafin abayar ta hau saman dadduma ta tayar da sallah la'asar. Mamu tace" se ma yanzu kike la'asar?" ta faɗa tana kwashe kayan da Mubina ta zubar a ƙasa tana faɗa, tace" ke kullum da kin cire kaya se ki zubar a ƙasa Allah ya shiryeki." ta faɗa tana kwashewa ta kai toilet ta zuba a kwandon zuba datti. Tace"Maza idan kin gama ki shirya ki fito munada baƙi dan Allah baby ki nutsu bayan sun tafi zan maki tambaya ki faɗa min tsakaninki da Allah." ta faɗa tana ficewa. Bayan Mubina ta gama sallah harda su istigifari tayi na karyar da tayi, ta miƙe ta cire abayar ta murza mai ta ciro atamfa Super English blue me ratsin fari ɗinkin riga da siket ta ne, tana cikin sakawa Amrah ta shigo, tace"Wow auta kinyi kyau sosai." ta faɗa tana shigewa toilet. Mubina ta zumburo baki tana wata tafiya kamar tarwaɗa, jikinta se motsawa yake, ta isa bakin dreesing mirror taga yanda kayan suka mata cif a ɗan jikinta tayi kyau sosai. Murmushi ta saki dimple ɗinta ya loɓa ta shiga gyara gashinta ta fesar dashi ya bushe ta shafa mai ta ɗaure shi da ribbon, ta fesa turare ta ɗauki ɗakwalin atamfar ta murza ɗaurin zahra buhari ta nufi saman gado ta zauna ta ciro wayarta ta kunna. Nan take kiran Sageer ya shigo ganin bata san number ba taki ɗauka saida ya kira sau uku ta ɗaga tare da sallama tace"Wai dawa nake mgn?" Sageer yace" Baby Mubee sir Sageer ne ykk ina kika shiga na gaji da ne manki a waya?" Mubina tace" Sir ina yini barka da yamma , wlh wani ɗan tsautsayi ya same ni amma ka tambayi wannan mugun malamin gurgu ai yasan kome kar ya ha'ince ka." Sageer yay murmushi dan zatonsa tin abin safe ne yasa ta faɗi haka yace" Ok barni dashi babyna ykk yanzu fatan bakida damuwa?" Mubina ta zumburo baki tace" Uhm sir ykk y hutawa." ai fa Sageer ya sami abinda yake so sai zuba ya fara mata. Haka Amrah ta iskota ko me yake faɗa mata se kyalkyala dariya take yi. Ta girgiza kai ta shiga shiryawa...

Can ko Kamal bayan ya shiga gida sun gama waya da Sageer cewar zasu hadu bayan sallah magarib, ya fito daga cikin motar ya nufi cikin gida. A parlo ya isako ummah tare dasu Hafsat da yaranta suna hira. Kamal yace "momy nan kuka yo bayan ruwan?" ya faɗa yana zama kusan ummah ya kwantar da kansa jikinta yace"Washhh na gaji." Samha tace"Brother ina ka shiga wai?" hafsat tace "ai kuwa tin kafin la'asar ya fito ina bacci daga gidan goggo fa." Kamal yay murmushi zaiyi magana Abbu ya shigo da sallama. Ameer suka tare shi da gudu. Hafsat tace"Oyoyo Abbu." Abbu yayi dariya yace"Hafsatu kece cikin lema haka? Sannu da zuwa" Kamal ya miƙe yay gun Abbu zai rungume shi yace"dakata kai Kamaluddin ni zaka wulaƙanta ko?" Kamal zaiyi mgn Abbu ya ɗaga masa hannu yace"Bana son jin kome maza shirya ka fito zamu unguwa , Fatima Samha ku shirya yanzu zamu je muzo harke Hafsat tinda kinzo." ya faɗa yana hawa sama. Hafsat tace"Kamal me kayi?" kai Kamal ya girgiza yace"Hummm bazai wuce sharrin wannan aljanar yarinyar ba , ba kome bari na canza kaya na fito."ya faɗa yana hayewa sama. Ummah tace"ikon Allah bari to mu shirya kar a haɗa damu." ta faɗa tana miƙewa ta tafi domin ta shirya. Kamal na shiga ɗakinsa yay wanka a gaggauce ya fito ya shirya cikin wata dakekiyar shadda maroon coulor ya murza hula se baza kamshi yake, kwashi wayoyinsa ya fito.
Nan ya isko suna jiransa yana fitowa Abbu yace"Muje magrib ta gabato." baki ɗaya suka fito kowa gabansa se faɗuwa yake, Kamal ko sanin babu wani abun aibu da yayi bai damu ba, damuwar sa ɗaya fushin Abbu gare shi...

Suna zuwa kofar gidan Abbu ya kira umpah sun iso nan ya fito da kansa ya tare su ya shigar dasu parlon baƙi wanda aka tana di kome, ya shiga can ciki ya kurawo nasa iyalin.

Da sallama suka shigo parlon baƙin, Mubina tana riƙe da hannun umpah. Kamal ya ɗago karaf suka haɗa ido da Mubina tayi saurin komawa bayan umpah tana cewa"Umpah nah ai ga ɓarawon da ya sace ni wlh shine me yazo yi gidanmu?" ta faɗa ta na murguda masa baki ta ƙamƙame umpah ta baya. Kamal kuwa abin dariya ma ya bashi wai barawo, idanu ya ƙura mata tayi masa mugun kyau atamfar ta amsheta ɗas a jikinta duk da bata da ƙiba akwai diri. Idanunsa ya janye daga kallonta yana taɓe baki. Umpah yace"Eh Auta shine ajiye hankalin ki bazai kuma sace kiba." ya faɗa yana ɓanɓare ta daga jikinsa. Mamu kai ta girgiza ta isa kusan ummah suka gaisa cikin raha ta gaishe da Abbu ya amsa cikin sakin fuska. Mubina ta isa kusan Abbu ta zauna tace"Dady ina yini." Abbu ya dafa kanta yana murmushi yace"lfy lau doter ƴar albarka." murmushi tayi ta gaishe da Ummah da hafsat suka amsa cikin sakin fuska, se dai Hafsat tana mamakin katuwar budurwa se sangarta. Samha ta gaishe da umpah da Mamu suka amsa cikin sakin fuska. Amrah ce ta shigo da sallama ta kara so ta zauna kusan Mubina ta gaishe da Abbu da Kamal da su Ummah cikin girmamawa, suka amsa suna yabon hankalinta. Mamu ce ta miƙe ta tsiyaya ma kowa ruwa da lemo tabi kowa ta bashi suna godiya, se lokacin Kamal ya rankwafa ya gaishe da umpah da Mamu, suka amsa cikin mutunci. Mubina ko da wasa bata sake kallan sharan Kamal ba... Bayan son sha ruwa da lemo an kara gaisawa, Abbu yayi gyaran murya ko da Abbu yayi gyaran murya Mamu ta kira Mubina ta taso ta dawo gunta ta zauna kusanta. Abbu yace ba kome ya tara mu anan ba se ina son Abdulrahim in roƙi alfarama wajanka kaba Kamal auran ɗaya daga cikin ƴaƴanka masu albarka , da farko Wannan na zaɓa masa" ya nuna Amrah yace "so sai na lura kamar wannan yake so" ya nuna Mubina Kamal ya zaro idanu waje! zaiyi maga Abbu ya watsa masa mugun kallo. Kansa ya maida ƙasa. Abbu yace dan haka ina nema ma Kamal auran Mubina a bamu..." Mubina tayi wata irin zabura zata bude baki tayi magana tana kallon umpah Mamu ta danne mata cinya ta rufe mata baki... Abbu ya zayyanewa Ummah da hafsat da Samha kome tinda safe irin diramar da ke kaftawa... Umpah ya kalli Mubina yaga yanda hankalinta ya tashi... Take ya gano ƴarsa bata son Kamal. Gyaran murya yayi yace" Masha Allah naji dadin wannan lamarin insha Allahu bazan hana ɗana Kamalu gudan jinina ba se dai Mubina karatu take , tana da burin karatu kaga misali da anyi auran Allah ya kawo rabo da wuri idan cikin mai laulayi ne zai ɗatse mata karatunta , ko kuma ma daga baya mijinta ya hanata dan shike da ikonta , so sai nake ganin a bashi Amrah tinda ita ta gama ko gobe ma ashirye nake haɗa zuri'a dakai! Abubakar na ba Kamal auran Amrah idan yaso zata ci gaba da karatu ko aiki a gidanta." ya faɗa yana murmushi. Mubina ajiyar zuciya ta sauke ta kalli sharan Kamal ta cinno baki baki gaba ta lumshe idanunta ta tura kanta cinyar Mamu taji dadin jin ba ita bace ba!! Mamu kuwa haushin umpah ya cikata se hararasa take a ɓoye ga yarinya me buƙatar aure ya kasa ganewa ya bada watanta... Abbu cikin farin ciki ya isa gun umpah ya rungume shi yana godiya sosai da fatan Allah ya sanya alkhairi. Ummah ma da Hafsat da Samha sunji dadin samun Amrah a matsayin matar Kamal, dan sun fahimci tana da nutsuwa gashi abin kai tsaye taji amman taki nuna ɓacin rai sai kanta da ta sadda ƙasa. Kamal dauriya yake kurum sai yau yayi nadamar kin faɗa cewar ya sami wacce yake so, gashi za'a masa auran dole. Abbu ya zaro daurin ƴan dubu-dubu na dubu hamsin ya beƙama umpah yace"ga kuɗin tambaya mun gani muna so insha Allahu zamu zauna cikin satin nan a saka rana da kome wlh abun yamin dadi ban taɓa zaton kai tsaye zan samu karbuwa haka ba , Allah yabar zumunci."Umpah yace "Amin ni ke da godiya ni da ake son haɗa iri dani..." Haka suka kasance cikin farin ciki sosai kiran sallah ne ya tashi taron su Abbu suka tafi gida suma suka koma ciki...

Bayan sallah isha suka hallara gurin cin abunci, Amrah idanunta sunyi jajur taci kuka ta koshi a ɓoye. Yanzu ma sai juya spoon take ta kasa ci, Mamu tace"kici abuncin ki ni banga aibun yaron ba wlh ga hankali kiyi hkr..." Mubina ta ajiye robar ice cream ɗin ta bushe da dariya ta rungume Mamu tace"Kai Mamu nah gurgu ne fa yana ɗan ɗingisawa amman ai dole zata ma umpah biyayya.." Mamu ta buge mata baki, ta saki ƙara ta saketa ta koma wajan Umpah. Umpah ya kalli Mamu yace"Nusaiba wlh na fahimci kina nuna banbanci tsanin yaranan duka dai ke kika haifa kuma Amana Allah ya baki , ke Amrah kuka kikayi saboda na zaɓa miki miji na gari?" kinada tsayayye ne da zaki fitar? kuma inama zaki sami kyakyawan yaro mai nutsuwa irin Kamalu ga nera gashi yakai a so shi ki riƙe abinki da kyau." Amrah tace"A'A umpah bana kuka insha Allahu zanyi maka biyayya ina sonshi mana." ta faɗa tana danne kuka nata ta miƙe ta nufi sama. Umpah yace" yauwa Allah ya miki albarka."Mamu tace "Amin itako ta gaban ka se ka mata Addu'a Allah ya shiryata." umpah murmushi yayi ya shiga ba Mubina abunci a baki yace"Adawa bata yi ba wlh." Mubina tayi dariya. Ta miƙe ta haura sama.

Can gidansu Kamal haka suka kasance cikin farin ciki da walwala, amman banda Kamal. Misalin 12:pm na dare kwance yake a makeken gadansa yana sanye da kayan bacci riga da wando farare idanunsa lumshe ya dafe kansa shi kaɗai yasan meke damunsa ya rasa me yake ji, yana jin zafin yadda ɗazu ya roki Abbu cewar ya masa alfarama yanada wacce yake so ya haɗa su su biyu ya aura, amman Abbu yaki yarda yace ko kusa da duk zamn sa bai ce yana da wada zai aura ba se da ya samo masa matar aure... Juyi yayi ya ɓeka hannuns na gefan gado ya janyo wayarsa ya sake kiran Amrah amman a kashe sakonta ya sake karantawa na cewar su hakura da juna an mata miji zatayi biyayya wa mahaifinta anman tana sonsa har karshen rayuwarta... Cillar da wayar yayi ya dafe kansa yace" Kina mace ma kin hakura bare ni namiji zan amshi kaddarata insha Allahu." ya faɗa yana buɗe idanunsa ya miƙe zaune ya sauke ya shiga toilet ya dauro alwalla ya fito ya dora jalabiyya kan kayan baccin sa ya hau saman darduma ya tayar da sallah nafina ta neman zaɓin Allah...

Amrah na kwance Mubina na manne jikinta se kwasar barci take a nuntse tana sanye da yar guntuwar riga ta bacci. Amrah ta rushe da kuka tace" Wlh ni KAK nake so amman dole zan amshi kaddarata zan mantaka insha Allahi." ta faɗa tana shasheƙar kuka ta rungume Mubina gam. Mubina kukan ya tayar da ita bude ido ta zabura ta riƙe Amrah tace "Anty lfy kuwa?" Amrah tace "Baby bari kiji abinda ke faruwa inada wani saura yi bayan Lameer daman kinsa shi ba sonsa nake ba
End Ads