ya chuka alkhairi zai gani wanda kuma ya shuka akasinta shima zai gani, ga Arham yanzu gabaki daya abubuwan dayamai sunyi backfiring sun dawo kanshi, ko amafarki baitaba tunanin shairin daya kullama Waleed za'a gano gaskiya ba gashinan yanzu shairin cost him all his property za'a biya yaran dayama ciki bayan sun haihu kuma za'a cigaba da kuladasu da kudin in yaran suka girma araba musu kudin, yanajin yana gani aka kaishi prison direct batare da hiring ba, kukuma a bashi chance din kiran lawyer shiba wanda hakan kuma duk aikin vice president ne abokin Ammi tunda aka sanar dashi angano gaskiyan shairi yama Waleed yabada izinin they should deal with him, ta karkashi za'a kulleshi karma aji news din, haka zaiyi rot in prison yamutu daga baya amman bazaibar prison ba yar abada, kaico! Allah karabamu da Hassada dakuma bakin zuciya, Allah kacire mana kwadayi dason abun wani, gashinan Arham da hannunshi yaje yakai kanshi ga halaka, abin tausayi baida kowa, tunda yasa kai yabar gidan marayun baikara dawowa daidai daso daya yagaida kanwar Mamanshi ba Maman Sadiya, har suka tattara suka bar gidan Ammi tasai musu wani gida daban tabude masu business sosai kuma Alhamdulillah ta chanza, tunda taga Arham baida lokacin su kuma bai shirya tubaba suka tattare shi suka linke dan basusan ina yakeba, su basusan kan Abuja ba balle suce zasu tashi suje su nemoshi hakan yasa sukabar zancen.
Karfe biyun rana jirginsu ya sauka a Qatar, mota suka shiga tana kusada Ammi har zuwa gidansu, bayan sunkai gidan har flat dinsu Ammi ta kaita ta shigar da ita uwar daka ta zaunar da ita sanan itama ta zauna, ahankali tai cupping face din Widad din, murya chan kasa Ammi tace "alkawari daya zan miki bazaki taba nadaman auren Waleed ba, my son is a goodman, verysoft and very loving zakiji dadin Waleed, please kiso d'ana kaman yanda yake sonki he has been through alot wlh, tausayinshi nake dan ciwon zuciya na gab da kamashi" Ammi taidan shiru sanan tace "I am a mother am so worried for my son Widad, please kiso d'ana koma yayane" saiga hawaye da sauri Widad tasa hannunta ta sharema Ammi hawayen dasuka zubo mata sanan ta rungume Ammi ahankali, rungumeta back Ammi tayi sun dade ahaka sanan Ammi ta saketa tace "tashi kije kiyi wanka" gyadama Ammi kai tayi ta tashi tana kokarin cire kayan jikinta itakuma Ammi tawuce tafita daga dakin tarufo mata kofa.
Tana fitowa daga bayin daure towel shikuma yana shigowa dakin dan tun dazu yana tareda Uncle a dakinshi, hada ido sukayi yabita da wani mayen kallo dauke kai tayi tai wajen wardrobe tabude batare datace mai komiba ta bude tashiga neman kaya, ganin baice mata komiba yasa tawani irin kama cikinta taredayin ihu. "wayyooo cikina" da sauri yazo wajen yadagota saikuma yadauketa yay kan gado da ita yace "menene Pretty ina ke miki ciwo"? Fadawa jikinshi tayi ta rungumeshi tsamtsam tana sauke ijiyan zuciya, jin yanda ta rungume shi yasa ya rungumeta back tareda manna mata kiss acikin gashinta yace "am happy my wife is back, Widad ina sonki kuma zan cigaba da sonki har karshen rayuwata, zamuyi rayuwan dazamu dinga shayar da junanmu soyayya mai tsafta" yay shiru yana shafa bayanta, shafa kirjinshi tayi ahankali tace "Ya Waleed Zaujy" wani irin sassanyar ijiyan zuciya ya sauke, ahankali tace "I've been wanting to thank you for all you've done to me, little by little inata tuna abinda yafaru dani bayan nahadu dakai dudda ban tuna komaiba but the little dana tuna give me more reason to love you and more reason to be your wife till eternity, kaine sanadin fadowata Nigeria, u are my destiny Ya Waleed, and am morethan ready to accept you as my husband, let's be the first people to show the world cewa DUNIYA BIYU MABANBANTA suhadu atarayya ta aure, sanan this same TWO DIFFERENT WORLD sun gina soyayyan da wayanda suke duniya dayama basu ginaba, I love you Dr Waleed Warbai" chak ya tsaya yana kallonta saikuma kawai yadagata sama ta kyalkyace da dariya yashiga mata chakulkuli kafin su fada gado suhau faranta ma junansu rai.
Da daddare yana tareda Uncle yana aiki da system dinshi yaga shigowan email duba email din yayi yaga daga ministry aka turomai, suna bashi hakuri kan duk abubuwan da akamai akan yanzu sunsan gaskiya, sanan inya shirya yazo ya karbi komi dayake bukata yacigaba da running gidan marayun shi, yau kwana uku kenan suna neman wayanshi basa samu if he get this email yamusu reply, yanda fuskan shi yay wani irine yasa Uncle yace "menene son" ahankali ya sanar da Uncle abinda yagani, tabe baki Uncle yayi yace "kagama aiki agidan marayu daman cimaka time yake, ka gina masallatai, islamiyu, kagina ma alumma rijiyoyi da bohole, ka taimakama ma bukata ko wanan kadai ya isa, asibiti zaka koma da aikin ka ba gidan marayu ba, start planing on building your family ankusan fara haifo maka yara", murmushi yayi baice ma uncle komiba yana ganin fuskan Widad a system din.
_Bayan nine month_
Ilham dasu Hassana kusan duk lokaci daya suka haihu banbancin kawai shine dan da Ilham ta haifa tun aciki aka sanar dasu yamutu aikima aka mata aka ciro kaman bazata rayuba tai ciwo kaman ta mutu, tun iyayenta da yan uwanta suna nuna mata tsana akan halin datayi har suka rungume abunsu suka shiga neman mata magani, ga Arham little sai girma yake yaron kamanshi daya sak da mahaifinshi, sosai ta wahala sanan aka samu ta samu lafiya, wani irin hankali natsuwa da nadama tashigayi tana istigifari kullum, tama dena fitada gyale kullum hijabi har kasa da Safa tazo ta natsu kaman ba itaba, yanda tadena ganin Arham dakuma denajin labarin shi ya bala'in mata dadi da kwantar matada hankali. Arham nada shekara hudu wani mai mata biyu malamin islamiyan su na matan aure datake zuwa yafito kan zai aureta, Baba ko musu baiyiba yahada aurensu haka aka kaita gidan mijinta bayan anmata fada sosai su Mummy suka karbe Arham karami yakoma hannunsu itakuma tacigaba da rayuwan gidan miji da mata biyu, yau dadi gobe wahala amman haka tadaure dan tariga ta tuba kuma tai nadama.
Arham ko ba'a karajin duniyan shiba yanachan yana cin ubanshi a undisclosed gidan yaro da akekai wayanda gwamnati kejin haushinsu.
Widad Twins ta haifo dukansu mata masu bala'in kama da Waleed, gashinta kawai suka dauko, Waleed yadinga kuka, a ranan data haiho ranan Aby yadiro Nigeria, dan baitaba zuwa Nigeria ba, kowa saida yasan Widad yar gatan Babanta ne sabida kyauta da Aby yayi, ranan suna yara sukaci suna Anan da Anah.
Haka rayuwa tacigaba da tafiya, Widad batasan miye matsala ko fada da mijiba, hakama Waleed, baisan me fada da mataba, dan Widad sonshi take kaman ta cinyeshi bata kunyan nunama kowa hakama shima, bayan yan Biyun bata kara haihuwa ba dan takoma school saida tagama her dream course Mass com sanan tai wani cikin ta haifi da'a namiji.
End!!
Alhamdulillah anan nakawo karshen kagaggen labarin nan nawa mai suna DUNIYA BIYU MABANBANTA, kuskuren danayi ciki Allah ya yafemin, wani zubin don't just read book for fun take note of lessons din dake ciki, Allah ya shiryar damu gabaki daya, masu hali irin na Arham ku gyara, be your sister keeper, adena bakin ciki da hassada, kisani komi lokaci ne, kobaki kudi ko baki samu wata Nasara anan duniya ba ki kaddara naki Nasaran na lahira Allah ya ijiyemiki itane, Allah yasa mudace.
_*duk wacce takaranta min littafin nan batare data biyaba, wlh ban yafemata ba, bazan kuma taba yafewa ba, subscribing fee na book dinan is 500, ya Allah kabimin hakkina akan duk wacce takaranta bata biyaba dan ban yafemiki ba*_
_I want to give a special thanks to Hajiya Asma'u wacce akafi sani da Moxi, bazan karyaba this woman help me alot akan al'adun morroco dama komi nasu, thank you so much and thank you for the support and love 😍_
_ina mika godiyata ga, Platinum, VIP, ICTM, GGM, you guys are great, you make me this M Shakur thank you so much I love you all_
To anan nace cemuku sai anjiman ku sai kunjini a littafi na nagaba.