kanta na bala'in ciwo, tadafe kan da duka hannayenta ba'awani dauki lokaci ba bacci yay awon gabada ita.
***
Wuraren karfe biyun dare cikinta yawani irin murda mata da sauri tabude idanunta rass ta tashi zaune tznabin dakin da kallo, fuskarta ta taba taji tahada wani uban zufa kaman wacce tai dambe dudda uban AC dake dakin, tashi tayi ahankali ta dauki wayarta ta lalubo number Waleed tana yatsine fuska sabida ciwon maran datakeji, dailing number shi tayi amman bai shigaba, hartai bacci taga bai dawo ba gashi number ta bayi shiga hakan yasa tamike tsaye ahankali da kyar tana daga kafarta tabude kofa tafito daga dakinta, dakin Waleed tabude taga baya ciki hakan yasa tai stairs tafara tafiya ahankali zata sauko, wani irin ciwo dataji ya tokare mata mara yasa ta kurma wani mahaukacin ihu. "Mai gadiiiiii" zama tayi awurin tana wani irin nishi kafin tasake kwalama mai gadi kira, akaro na uku ne yaji yafito daga dakinshi yana share idanunshi dake cikeda bacci, ganin daga flat ake kiranshi yasa yay flat din yabude kofa ya shige hango Ilham daga ita sai doguwan rigan bacci yasa yay wurinta da sauri yace "Hajiya sannu haihuwan ce bari nakira miki dakta awaya" zai ciro wayarshi tace "kabarshi bayi shiga, kiramin duk wanda zaka iya kira azo a kaini asibiti azaba nikeji mai gadi" takurma wani uban ihu da saida ya firgita yace "Hajiya salati zakiyi, salati ake" juyawa yayi ganin bamatasan inda kanta yakeba ihunta kawai take, saida ciwon yadan sarara sanan ta nemi number Arham amman harya gama ringing bai dagaba, sau biyar takirashi amman shiru, dialing number Ammi tayi shima bayi shiga, ganin haka yasa tai dailing number Mummy ta, ringing daya Mummy ta tadauka fashewa da kuka tayi tace "Mummy mutuwa zanyi, Waleed bai dawo gidaba number shi bayi shiga, ina kiran number Maman shi itama bata shiga, dagani sai mai gadi agidan, kuma bai iya tuki ba balle yakaini asibiti, Mummy mutuwa zanyi" tafashe da kuka sosa daya ruda mahaifiyarta, anatse tace "kinga ba'a kuka in ana nakusa, be strong kinji yar albarka, ga Babanku nan yanzu zai kawoni wurinki just stay where u are kinji am coming" ta katse wayan, daidai mai gadi na shigowa yace "Hajiya wlh duk basa bude gate kinsan anguwan manya ne nan" ko jinshi batayi tahau ihu tana kuka sosai mai gadi yama rasa maizai mata sai dialing number Waleed yake amman bata shiga.
Wani ruwane yafashe mata dayasa tahau ihu. "mai gadi zan mutu kataimaka min wayyo Allah na kataimaka min dan Allah, daidai lokacin akai knocking kofar gidansu, da gudu mai gadi yafita yana zuwa yabude gate iyayen Ilham dinne mamanta da Babanta da mota, Mmummy ce ta shigo tai ciki tafito da ita aka sata a motar Baba sanan takoma ciki taje ta nemo akwatin haihuwan ta adaki sanan tawuce takai motar ta shiga baban su yaja motar sai hospital.
Bakaramin wahala tasha ba sai wuraren karfe 8nasafe ta haihu, ta haifo danta namiji katoto mai bala'in kamada Arham kaman yay kaki ya tofar.
[16/10, 05:48] M Shakur: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫
✍️ M SHAKUR
3️⃣1️⃣
Shirya yaron akayi aka fito da fitoda shi aka kawoma Mummy shi, ahankali Mummy ta karbe shi tana murmushi tace "miji nasamu ko kishiya"? Dariya nurse din tayi tace "miji ne Hajiya" karbanshi Mummy tayi tana kallonshi yaron kato dashi Masha Allah.
Daidai mijinta yakaraso tace "Alhaji kaga mijina masha Allah dawa yay kama"? Dan dariya Alhaji yayi yace "ai kamanshi daban da uwar da baban, hala sai nan gaba zai dauki kamanni, sake gwada namban mijinta dana mahaifiyar shi kiji ko zasu samu yakamata" number Waleed tafara dialing amman bai shiga har lokacin hakan yasa tai dialing number Ammi, lucky wayar ta shiga, wayar na gab da katsewa Ammi ta dauka, kafin ma Ammi tai magana Mummy tace "kawata lpy kuwa? Tun jiya da daddare muke kiranki dagake har Waleed baya shiga wlh hankalina yatashi" dan murmushi Ammi tayi tace "Waleed ne yadan sami hatsari wlh yana asibiti agidan marayun shi har karyewa yayi akafada, ban fadima Ilham bane kinsan mai ciki ba'a daga musu hankali haka, nikuma ina dawowa gida magani nasha na kwanta sabida hawan jinina yatashi, Mom ce awurin shi amman yanzu nai wanka shiryawa ma nike nakaimusu breakfast" da sauri Mummy tace "innalillahi wa innailaihi raji'un, ashe abinda yafaru kenan Ilham takira takira mijinta bayi shiga daga karshe saidai takira mu mukazo gamunan a asibiti wlh tasami karuwa yanzun nan amman tun cikin dare mukazo, anmiki miji fa, baki ganshi ba dan lukuti dashi" Mummy tafada cikeda farin ciki sabida tasan yanda Aminiyarta keson jika, Ammi mutuwan zaune tayi tama kasa magana, hakan yasa Mummy ta kyalkyace da dariya ta kalli mijinta tace "Alhaji tayi mutuwar zaune fa" sukahau dariya sanan tace "ki shirya saiki biyo kiga jikanki kafin ki kaima su Waleed abinci, Allah yabashi lpy, anjima dazaran an sallameta zamuje mu gaidashi"
Ammi kasa yarda da abinda aka gayamata tayi hannunta har wani irin rawa yake tai dialing number Mom dake zaune dakin tana kallon Waleed da tun jiya daya lumshe ido yaki budesu bacci mai nauyi ya kwasheshi yanzu muka yatashi dan tasan yana jinta sarai wlh, kaman bazata dauki wayan Ammi ba saikuma ta dauka takai wayar kunnenta, wani irin zabura tayi tace "Ilham ta haihu?" rass Waleed yabude idanunshi jin ance Ilham ta haihu, katse wayan Mom tayi tana murmushi sanan ta kalli Waleed dake kallonta ta tabe baki tace "mara kunya aika bude ido dakaji matarka ta haihu, suna asibiti ta haihu ansami namiji" ahankali yadan saki wata yar kyakkyawan murmushi sanan ya yunkura zai tashi, kafadarshi kawai da akai dauri kehanashi motsi yanda yakeso, da taimakon Mom ya iya tashi, Mom tace "me kakeso?" ahankali yace "office dina zani, I want to shower na chanza kaya naje nagansu" taimaka mai Mom tayi yamike tsaye ahankali suka fito waje, nurses sai gaidashi suke gyadamusu kai kawai yake, haryakai kofa yatuna alkawarin dayama Widad, Mom ya kalla yace "am coming Mom" sanan yay hanyar dakin datake, hannunshi yasa yabude kofar ahankali yashiga yana kallonta ganin tana bacci, ahankali yakarasa gaban gadon ya tsaya akanta yana kallon fuskarta kaman yatasheta dan taganshi saikuma yafasa yajuya kawai yafito tareda kullo mata dakin sanan yafito yay office dinshi shida Mom suka shiga ciki, dakin shi ya shiga yay bayi, brush yayi sanan yay wanka da ruwan zafi, jikinshi ciwo yakemai bana wasaba bai taba fada a rayuwanshi ba ko saisa Arham yay galaba akanshi oho, fitowa yayi yadauko wani jean yasaka da kyar sanan yadauko wata riga sai saka yakasa sawa, kwalama Mom kira yayi hakan yasa ta shigo, wani scissors yanuna mata, saida suka yanke hannun rigan daman sabida hannunshi yay balance sanan tasamai rigan ta shinfidamai dadduma yay sallolin da ake binshi sanan suka fito, Mom kejan motar suka dauki hanyar asibitin da Ilham take, parking sukayi suka fito sanan suka fara tafiya har zuwa dakin datake akwance.
Bude kofan Mom tayi ta shiga, Ilham na kwance kan gado, fuskarta ya kumbura suntum tsabagen kuka, sai Mummy dake zaune kan kujera rikeda jaririn da aka shirya yay kyau, Mummy na ganinshi tace "subhallahi, innalillahi wa innailaihi raji'un, Waleed wanan wani irin hatsari ne kaga yanda jini yataru a idanunka kuwa, jibi wuyanka da fuskarka sannu Waleed" kanshi akasa duk take maganganun nan ahankali yace "ina kwana Mummy" "ina kwana Waleed, ya karfin jiki? Allah yabaka lpy kaji, Allah yasa kaffara ne sannu" gyada matakai yayi suka shiga gaisawa da Mom sunama juna barka, karasawa gaban gadon yayi yana kallon Ilham data tsareshi da ido itama tana kallonshi tana mamakin abinda yasame shi haka, dan murmushi yamata ya shafa goshinta da hannunshi saida ta lumshe ido tabude su ahankali ta kalleshi, murya chan kasa yace "thanks for giving me a baby khadija, Allah yamiki albarka" gyadamai kai tayi tareda mika hannunta takama lafiyayyen hannunshi tarike gam, cikin muryanta da baya fita sosai tace "what happen to you Babyna"? Baki yabude zaiyi magana Mom ta taho rikeda jaririn tace "wato agaban mu ake nuna mana sonkai ko kana nuna kafi damuwa da matarka kan yaronka dayazo duniya yauko" murmushi Mummy tayi ranta fess ganin Waleed naji da yarta. Mom tamikamai yaron tace "ga danka nan dauki abinka kaga yanda yay kama da abokin ka kuwa kaman yay kaki ya tofar" wani irin mummunan faduwa gaban Ilham yayi saikuma ta daure ta lumshe idanunta da sauri kaman wacce bacci ya sace, ahankali Waleed yasa hannunshi ya karbi yaron yana kallon fuskarshi sanan yazauna abakin gadon yana rikeda shi yana kallon fuskar jaririn dake bacci yana murmushi, ko Allah yasan cewan yanason Arham, so na domin Allah, Allah ya azurtashi da d'a amman sai yaron bai biyoshi ba bai biyo mahaifiyar shi ba saiya dauko kamannin amininshi hakan yasa yaji bazaima iya sakama yaron sunan mahaifinshi ba, dan da yace in namiji yahaifa zai sakamai sunan mahaifinshi but wanan da yaron ke kama da Arham dole Arham zai bama yaron kodan Arham yagane shibai rikeshi da komiba sanan har gobe har jibi shi dan uwanshi ne no matter what.
Bakinshi ya daura kan goshin yaron ya sumbaci yaron yana murmushi sanan yama yaron huduba ya karbi dabinon dasuka sayo da zasuzo yatauna yabama yaron yabashi ruwan zamzam, yadago kanshi ya kalli Mom yace "Mom sunan d'ana Arham Waleed Warbai" shiru Mom tayi tana kallon Waleed din for few seconds itama Ilham saida tabude ido gabanta nafaduwa ko Waleed yagane ne saisa yabama yaron sunan Arham sosai ta birkice saikuma cikeda siyasa tace "d'ana yawani kama yayi kama da abokin ka saikuma kawani bashi sunan shi" karban yaron Mom tayi tace "Allah ya rayaka Arham, daidai nan aka bude kofa Ammi ce ta shigo yar aikinta abayanta da direba rikeda basket din abinci, tace "ku yakuri ai danaji ya'ta ta haihu kitchen na koma da kaina namata abincin da maijego yakamata taci, sassanunku now ina Dr da nurses din dasuka karbi haihuwan jikana kuga" tawuce tafita waje tana kwalama nurses da Dr kira, duk wanda yazo bashi bandir din yan dari biyar guda take zukuga yanda aka cika Mummy sai murmushi take, saida ta rabar da kudin tass sanan ta shigo dakin ta kalli Mummy Ilham tace "bakin ciki kikemin ne aminiyata bazaki tashi akan kujera na zauna na dauki jikana ba"? Kwashewa da dariya akayi, Mummy ta tashi daga kujeran tace "maida wukan dadin abin nidai kafin nayi wanan jikan naki nayi wasu balle amin yanga" zama Ammi tayi tace "yanga yanzu kika fara gani" all this maganganun ko Waleed dake zaune bata kalla ba, saisa ma bataje gadon ta duba Ilham ba sabida yana wurin, ahankali Mom ta taho rikeda Arham junior sanan tamikama Ammi shi ahankali tace "ga Arham Waleed Warbai, Arham karami" Mom tai maganan tana kallon fuskarta kaman yanda itama Ammi tadago tana kallon fuskar Mom kafin ahankali tadaura fuskarta kan yaron, shiru tayi ganin yaron kaman Arham yay kaki, dudda yaron jariri ne but kamannin was so obvious da kana gani zaka gane da Arham yake kama, gabaki daya Ammi jitayi duk wanan farin cikin da murnan nan da rawan jikin datake yi na zatazo taga jikanta yakoma ciki, abinda ma yafi bata abin shine sunan dataji Waleed yasamai, kuma tai alkawari bazata sake shiga rayuwan shiba kaman yanda yafadi, so yasaka sunan abokinshi ma danshi danyaci mata mutunci itakuma bazata cemai komiba ya kyauta, murmushi kawai tayi tace "Allah rayaka Ar.....an jikalle" tafadi ahankali danta kasa kiran sunan Arham din, bude kofa akayi Baban Ilham ya shigo ciki yana ganin Waleed yace "assha, sannu son wanan daurin asibiti ai saikafi shekara baka warkewa tashi muje nakaika wajen wani mai dauri yana maka zaka warke cikin sati tashi muje" yay maganan yana kallon Waleed tashi yayi ahankali yabita gaban Ammi da kanta kekan jaririn, suka wuce suka fita, a mota baban Ilham ya daukeshi sai janshi yake da hira amman baya wani iya amsawa da kyau dan nauyin mutumin yakeji, agaban wani gida yaga sunyi parkin, fitowa sukayi baban Ilham yace "muje" shiga sukayi har wani dankareren falo inda wani mutumi ke zaune, Baban Ilham yace "Barka da rana malam, ga dana nan ya karye akafada munzo agyaramai" tashi baban yayi yazo yadaura hannunshi kan wajen saida Waleed ya yatsine fuska sabida zafi, Baban yace "ba karaya bace kashi ce ta goce ina gyarawa yanzu shikenan" da sauri Baban Ilham yace "kagani ko babu abinda asibiti suka iya indai kan dauri ne, yace Baba ayi mun gode" kwalama wasu maza kira Baba yayi, Waleed yaga wasu karfafan maza su kusan shidda sun shigo, hannu Baba yasa ya warware daurin sanan aka rike Waleed din, addu'a Baba yayi yatofa kan kafadar sanan yakai hannunshi kan wajen yafar kokarin saita kashin sosai Waleed yaso yadaure dayaga azaban ba nan bane yafara kokarin kwace kanshi amman ko motsi baya iyayi, da azaba yay azaba kuka yafara kaman zai mutu Baban Ilham sai sannu yakemai kusan awa daya aka dauka a hannun sanan baban ya gyara tsaf aka sakeshi da sauri yasa hannu yana share hawayen Baban Ilham sai sannu yakemai, magani Baba ya shafamai akafadar yace "ka warke baka bukatan wani dauri kuma angama" kudi Baban Ilham yaciro mai yawa yabiya mai sanan suka tafi.
Duk suna zaune adakin Dr ta shigo ta duba Ilham sanan tabasu sallama tawuce tafita, ahankali Mummy tace "aminiya natafi da ita gida tai jego ne?" ada Ammi tai alkawari bazata je jegon gidaba amman sai kawai taji gwara sun tafi, gyama Mummy kai tayi tace "eh kuwuce kuma a kulamin da matan d'a da jika da kyau, suna arba'in zanzo na kwashi abuna wlh" duk akai dariya Mummy tace "nina nafi kowa sanin bala'in ki ai bazanyi wasa ba yallabiya" tai maganan tana kallon kofa ganin anbude Baba ne da Waleed da idanunshi sukai jajir da sauri Mom tai wajen Waleed din tace "sannu Dan Yaro an gyara" gyadamata kai yayi, Baba yace "bama karaya bace ashe gocewar kashi ne yanzu an gyara an shafamai magani, Allah yabashi lpy" ahankali Mom tace "angode Alhaji" Mummy tace "Allah baka lpy" itadai Ammi tai kaman bataji su ba, Mummy ne tace "Alhaji an sallamemu mutafi dasu gida, agida zatai jego" da sauri Baba yace "to bari nakai kayan mota" daukan kaya yashiga yi Waleed yaje zai tayashi da sauri Baba yace "kaga jeka zauna kaida hannu ba lafiya ne zakadau abu jeka huta" yay maganan yana fita, ganin haka yasa Mom ta shiga tayashi suka kwashe komi sukakai mota, sanan Waleed yadau hijab yabama Ilham tasaka ahankali yace "test me all that you need zan aiko miki dashi" murmushi tayi ya gyadamai kai ganin yana wani ji da ita kodan ta haifamai d'a ne, kofa yabude mata tafita suka jera atare tana tafiya ahankali har motar Baba ta shiga ta zauna sanan ya matsa ganin Ammi tazo baby ta shiga ta bama Mummy sanan suka rufe musu motar suka tafi Ammi tajuya tai motar ta ta shige direba yajata banda Waleed daya tsaya chak awajen, ahankali Mom tace "mutafi" daga kafa yayi yawuce ya shiga motar ta suka tafi, gida sukaje yana fitowa flat dinshi yaje kwanciya kawai yayi, yaciro wayarshi number Arham yakira amman harta gama ringing bai dauka ba, 3 miss calls yamai ganin bai dauka ba yasa yamai message.
_"Hey blood, I called no answer I guess you are still angry with me, I called nafada maka Khadija ta haihu, an sami baby boy, yaron yay kama dakai sosai blood, and do you know what's even great? Yaci sunanka, sunanshi Arham Waleed Warbai, blood you mean alot to me, u make my life colourful, I am sorry idan maganan dana maka jiya kajita somehow I was just trying to know what you've been up to lately, and I am also sorry akan abinda Ammi na tamaka please forgive us, take care, anjima zan shigo_"
Yaturamai sakon tareda lumshe ido bacci na saceshi kafin baccin yay nasaran daukeshi.
[17/10, 18:47] Aishat Muhammad: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫
✍️ M SHAKUR
3️⃣2️⃣ & 3️⃣3️⃣
Wuraren karfe biyun rana ya farka, sosai yaji karfin jikinshi kawai gajiya yakeji bawani abuba, tashi yayi dagakan gadon yaje gaban madubi ya tsaya ya kalli kwayar idanunshi na dama ganin har yanzu akwai jini aciki yasa yabar gaban madubin yana tunanin inya fita anjima zai tsaya a pharmacy yasai maganin dazai saka jinin idanun ya washe, bathroom ya shiga, wanka yayi yasake yin brush sanan yafito, wardrobe dinshi yaje yadauko wasu native, farin yadi ne mai taushi da akamai jumper yasaka sanan yadau turare yafeshe kanshi dashi, dadduma yahau yay sallan azahar sanan ya zira takalmi bayan yadauki wallet dinshi yafito, side din Ammi yayi gabanshi nafaduwa, ahankali yabude kofar ya shiga hada ido yayi da Ammi dake zaune kan dogon kujera hannunta rikeda remote ko taji zai shigo ajikinta ne oho dayasa take kallon kofar oho, suna hada ido ta ijiye remote din ta tashi daga kan kujeran da sauri ya shigo dakin yamaida kofan yarufe yace "Ammi, Ammi please wait" sama Ammi tayi da sauri yabita kafin yakai harta shige dakinta tarufe da key dan bamata son ya shigo, tsayawa jikin kofar yayi yay shiru, yakai kusan 5min ahaka sanan yace "Ammi please listen to me, kiyakuri kinji please Ammi na" yay maganan ahankali yana knocking kofarta yakai kusan 10min ahaka awurn ganin bamata da niyyan bude kofan yasa yawuce ya sauka kasa, dinning yaje yazauna sabida shegen yunwa yakeji, warmer yabubbude, tuwon shinkafa yagani da vegetable soup, zubawa yayi baima wani iyaci da yawaba yasha ruwa yamike tsaye key motar Ammi dake kan centre table yadauka yawuce yafita, motar ta ya shiga ya zauna sanan yaciro wayarshi ganin har lokacin