nashi in details ba but she clearly understands abinda Waleed keso yafada mata, cikin wani irin muryan so da tsantsan tausayi tace "Waleed Arham ne yay hurting naka to this extend"?
[22/10, 21:33] Aishat Muhammad: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_💫
✍️ M SHAKUR
Gyadama Ammi kai yayi yana wani irin kuka, yace "Ammi wai nai raping mata guda takwas, Ammi nataba ma any mace fyade eh Ammi?" girgiza mai kai Ammi tayi tanajan majina trying tahana kanta kuka ta girgixa mai kai takai hannayenta kan fuskarshi tana sharemai hawayen sanan tai cupping face nashi tace "Waleed nina haifeka nakuma raineka I know who is my son, nasan what you can do and wat u cannot do, Waleed nasan cewa bazaka taba yima yara mata fyade ba, bazaka tababa, Arham ne yamaka shairin nan kuma yama kanshi, zakaran da Allah ya nufa da chara ko ana ha maza ha mata saitayi, kadena zubar mai da hawaye come here Waleed dina" Ammi takama kanshi ta daura akan kirjinta tana bubbuga bayanshi tana wani irin kuka mara sauti hawaye, tamafi Waleed jin ciwon abinda ya samai, but yanzu he should calm down first yay shiru tukunna kafin taji full labarin abinda yafaru, takai almost 20min lallashin shi take, jinshi shiru yana sauke ijiyan zuciya ahankali yasa tagane bacci yayi ahankali taja cinyarta ta tashi tsaye tana rikeda kanshi a kirjinta kaman dan jariri sanan ta kwantar da kanshi ahankali kan kujeran tana kallonshi idanunshi sun kumbura sosai sabida kuka fuskarshi yay ja, same da lips dinshi dayay jajir sabida tsabagen kuka, tashi tayi ahankali tadauko bargon saman gadonta tadawo ta lullube shi da bargon sanan tadau wayarta tabude kofar dakinta tafita daga dakin kirjinta na tafarfasa, sauka tayi kasa tazauna kan dogon kujeran ta shiga contact dinta number Mama Iyami ta nemo tai dialing number, ringing daya Mama Iyami ta dauka, Mama Iyami zata fara surutunta Ammi ta tsareta tace "please Mama Iyami, abinda nakeso kawai shine ki sanar dani maiya faru banson surutu kaina ciwo yake sosai, ina jinki" ahankali Mama Iyami ta shiga mata bayanin duka abubuwan dasuka faru har zuwa kan address din da Waleed yatura musu cewa yanzu hakama suna gidan, shiru Ammi tayi duk tana jinta sanan ta sauke ijiyan zuciya tace "ok nagode zansa akawo muku kayan abinci sabida kudinga girki" "to Hajiya mun gode Allah saka da Alkhairi, sanan Allah ya fitar da Waleed ya wanke shi daga wanan shairin" katse wayan Ammi tayi ranta na boiling takira Mom, tana daukan wayan tace "kizo gida yanzun nan" katse wayan tayi direct takira number vice president din Nigeria Osijoban.
Ringing daya, biyu ya dauka yace "Hello Hajiya" "don't call me Hajiya Osijoban" Ammi tafada da fushi sosai dan zuciyarta tafarfasa yake sosai tace "after all that I've done for you, banji kyashin baka all kudaden dakake bukata ba for you campaign, because my late husband kafin yarasu consider you his close one nima haka na dauka shine da ranka da lafiyan ka har alakama d'ana shairi sanan a kulle mai gidan marayu kayi shiru, no no no am disappointed and heart broken Osijoban" Ammi tafada kaman zatai kuka, cikin wani irin calm voice vice president yace "listen to me Hajiya, wlh ina shirin kiranki kenan kiranki ya shigo wayana, as am talking to you now yanzun nan case dinan ya shigo office dina, Ministry of Women suke incharge of orphanage sunada wanan ikon su kulle duk wani gidan marayu dake harka mara kyau, danaga gidan marayun d'ana ne Waleed raina saida yabaci, namasa acema Minister inason ganinta yau yau dinan bama gobe ba, and I will promise you one thing, kibani lokaci kalilan sabida dole ayi bincike bazan iya kawai nace baza'ayi binciken ba, amman kibani nan da 30days namiki alkawarin zan budemai gidan marayun shi, da ace nasan kan case din kafin su yanke hukuncin nan dana hana amman sai yanzu nake sani, I will do everything in my power nabude mai gidan marayun nan for now ki kulada shi kinji Hajiya, take care okay, sai gobe" ahankali Ammi tacire wayan daga kunnenta ta katse sanan ta ijiye tanaso takira Maman Arham amman saitaga enough sunma kansu but wlh tayi alkawarin zatai maganin Arham, tana cikin tunanin Mom tabude kofa 5a shigo tana rikeda hadaddiyan jaka tayi kyau sosai tana ganin idanun Ammi tagane da wani abu da sauri ta ijiye jakanta kan centre table takaraso kan kujeran da Ammi ke zaune da sauri ta zauna takai hannunta kan wuyan Ammi tace "Adda bakida lafiya ne eh? Maisa idanunki sukai ja haka kaman kinyi kuka"? Ajiyan zuciya Ammi ta sauke tace "idan da zanga Arham yanzu zan iya shakeshi sainaga yana gab da shurawa zan sakeshi, an rufema Waleed gidan marayunshi! Da sauri Mom tace "what" gyadamata kai Ammi tayi tana cijan lips tace "not just that yahada ma d'ana shairi kala kala, ciki harda yay raping yan mata guda 8, can you believe yaran sun fito sunyi confessing wai Waleed yay raping dinsu da gaske agaban kowa harda kuka" ahankali Mom tace "innalillahi wa innailaihi raji'un" ahankali Ammi tana wani irin kallon Mom tace "ance Waleed na saida yara, yana trafficking yaran gidan marayun and maltreatment, Waleed told me an kwashe yaran an maida su gidan marayun Arham shima wai yabude gidan marayunshi" kasa magana Mom tayi wanan lokacin sai
Kallon Ammi take jikinta yay morethan sanyi, cikin wani irin yanayi Ammi tace "ban taba son abotan shi da yaron nan ba daidai da sau daya, kullum sani kike nadinga ma Arham dariya tunda d'ana nason shi amman ban iyawa, kaman Allah ya nunamin nan gaba zai yaudari d'ana ne, Arham ya yaudari Waleed bakadan ba, he uses my child weakness against him, he cheated my son, ya yaudari yarona" tai maganan tana girgiza kai, ahankali Mom tamika hannunta takama hannun Ammi tace "Ammi listen to me, nasan halinki sosai, I know yanzu haka zuciyanki na kitsa miki abubuwa da dama, I want you to calm down Ammi, ba'a rama mugunta da mugunta, ba'a rama cuta da cuta, nasan yanzu haka duk inda Arham yake yana tunanin bama hakaba yana expecting zuwanmu for revenge ko rashin mutunci, Ammi kinajina please wanan karan ki sauraran, tunda dai Allah ya nuna mana wayeshi, sanan Allah yabude mana ido harda da Waleed munsan waye Arham din mubarshi da Allah, kome yama Waleed yama kanshi, ni to me da Waleed ma yahakura da gidan marayun dudda passion dinshi ne yana ma mahaifinshi ne but kawai yakoma normal hospital yafara aikinshi still lada zaikai ga Abba, yabar Arham da halinshi, yana kanshi yaci amanar kanshi, ya manta dashi da abinda yamai and move on, ga yaron shi chan, jibi suna yakamata yaje yagansu kiyakuri Adda na" shiru Ammi tayi tana kallon Mom ko kadan batason ta hakura tanason ta gwadama Arham ba'a taba mata yaro a zauna lpy amman kuma tana tunanin maganganun Mom, wani irin ajiyan zuciya ta sauke ya jingina da kujera ta lumshe ido takasa daina tunanin abinda Arham yama Waleed, takasa daina tunanin yanzu Waleed baida gidan marayu yanzu Arham ne mai gidan marayu da yaran gidan marayunshi. Ajiyan zuciyan takara saukewa hakan yasa ahankali Mon ta rungumeta tace "ya isa Adda I know what you are going through is okay, kiyakuri Allah natare da masu hakuri duk wanda ya cuceka kanshi ya cuta Adda so kibarshi da halinshi" haka Mkm ta dinga bama Ammi baki harta saukko sosai, suna zaune nan akasa sukaji anbude kofar dakinta daga sama da sauri Ammi da Mom suka daga kansu, Waleed ne yafito idanunshi sun kumbura suntum da sauri Ammi tai hanyar stairs din tace "Son katashi" tai maganan tana mika hannunta tarikeshi ahankali tace "katashi Waleed" gyadamata kai Waleed yayi yana kallon Mom dayagani biyeda Ammi tana kallonshi murmushi ya sakin mata yace "Mom kinzo" gyadamata kai tayi ahankali tace "nazo Dan Yaro na" ahankali yake saukowa daga stairs din tareda Ammi, murya chan kasa yace "Mom yunwa nakeji" Ammi jitayi kuka yazo mata tuntuni fushi take dashi tasan baya wani cin abinci yan kwanakin nan tunda yafadi da bakinshi cewa yunwa yakeji dat means yaji yunwa sosai dan Waleed bayacin abinci sosai, muryan Ammi na rawa sosai tace "sh.....shiga kitchen ki dafamai abin.....abin....d....yakes....." kasa karasa maganan tayi saikuma tafashe dawani irin kuka Ammi tayi da sauri tasaki hannun Waleed zata koma sama dan batason yaga tana kuka rike mata hannu yayi gam ahankali yace "Ammi" fadawa jikinshi tayi tasaki kuka tace "Waleed I am sorry, nima I abandon you jibi yanda kakejin yunwa eh, you have been going through alot Waleed wlh ban kula dakai yanda yakamata ba inda nayi da non of this would have happen to you" girgizama Ammi kai yayi yadagota share mata fuska yayi yace "shiiii Ammi don't cry, idan kina kuka I will break down Ammi, you are my strength, please kidena kuka if anything happen to you bazan yafema kaina ba, stop crying kinji Ammi na" gyadamai kai tayi tana kara share fuskarta, ahankali tace "Arham hurt you Waleed" hannun Ammi yarike yace "Ammi kidena maganan Arham, abinda yamin hurt me deep but such is life nayi imani da kaddara mai kyau da mara kyau, please ku manta da komi kima dena kiramin sunan shi, I want to forget everything and move on Ammi, kinji" gyadama Waleed kai tayi, Waleed yakama hannunta sukai dinning, Mom kuma ta share gajeren hawayen daya zubo mata tai kitchen, spaghetti kawai ta dafa musu hadadden gaske, sosai Waleed yaci yanuna ma Ammi babu abinda ke damunshi duddan karsu damu itada Mom, saida yaci ya koshi sanan yatashi yace "bari naje nai wanka" murmushi Ammi tayi tace "ka shirya gabaki daya kawai sai muje muga Ilham da Baby mukai musu kayan suna ko" gyadamata kai yayi kawai yawuce yafita, duk suka bishi da kallo.
Flat dinshi ya shiga ya maida kofan yarufe bedroom dinshi ya shiga ya zauna akan gado yanzu ne komi yake kara dawomai fresh, kaman zai fashe da kuka yakeji, wani irin ciwo yakeji da bazai iya misiltawa ba, baison yana tunanin Arham ne yay mishi all this abubuwan saiya kawar da tunanin kawai dai yasan yarabu dashi, tashi yayi da kyar ya shiga bayi wanka yayi yafito ya shirya cikin wata Ash color shadda gizna datamai bala'in kyau kaman bashine ke cikin matsala ba, turare ya feshe kanshi dashi sanan yadau dark shade yasaka dan idanunshi sunyi ja, yadau wallet dinshi yafito, bude kofa yayi yafito ahankali yake tafiya haryay wajen da motarshi take a pake ya kwalama Ammi kira da Mom. "Ammi, Mom kufito am outside" yay maganan yana juyawa ya kalli gate jin anyi horn gateman yafito da gudu yana bude gate din, wata brand new ferrari ne yaga ta shigo compound din da baima iya hango na cikin motar glass din motar is tinted, dawani irin gudu mahaukacin motar ta taho harsaida gateman yace "kai" saura kiris motar ta buge Waleed a inda yake tsaye amman ko matsawa baiyiba sabida hakanan ranshi ya fadimai Arham ne, daga kofar akayi Waleed na kallon kofar daga inda yake, kashe motar akayi aka sawo kafa akasa, kafanshi na sanye da wani tomford mai bala'in tsada sanan yafito daga cikin motar, Arham ne yana sanye dawasu hadaddun suit ajikinshi baki idanunshi sanye da bakin glasses yana kallon Waleed yana wani irin murmushi sanan yafara taku daidai yana tahowa gaban Waleed din daya tsareshi da ido yazo har gabanshi ya tsaya yace "call me Mr Arham Abdallah CEO of Arham jikan Malamai orphanage home and home of the disables, Mr Waleed I heard what happen to your orphanage saisa nazo nan, I come to offer you a job agidan marayuna".
[23/10, 07:45] M Shakur: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_💫
✍️ M SHAKUR
3️⃣8️⃣
Dan murmushi yasake yi yakai hannunshi ya zare bakin glass din kan idanunshi ya kalli Waleed din yace "am willing to offer you a Nani job a boys section dina, idan irin kananun yaran nan dabasu iya magana ba sunyi kashi ko fitsari ajiki saika wanke musu, am ready to pay you 100k monthly for just that Waleed" daidai lokacin Mom da Ammi dasukaci gayu sosai sun fito yar aikin Mom biyedasu takwaso wasu hadaddun kaya dazasu kaima Ilham, hango Arham yasa da sauri Ammi tace "Arham!" juyowa Arham yayi yazuba mata idanu da sauri Ammi tayi wurin Mom biyeda ita tana zuwa ta tsaya kusada Waleed sanan ta kalli Arham din cikin fushi tace "how dare you step into my house with those your filty legs, ubanme kazoyimin agidana" wani irin kallon Ammi yayi sanan ya kalli Mom kafin yatabe baki ya nuna mata Waleed da hannu yace "nazo nabama danki aikin Nani ne idan yanaso agidan marayu na" wani irin sake handbag Ammi tayi akasa ta chakumo rigan Arham tace "how dare you Arham? Kasa an rufemai gidan marayu har kanada gut din shigowa gidan nan eh? How dare you waye kai? Kai dinan waye? Uban waye ubanka waye ya tsaya maka, kasan waye Waleed kuwa? Dan kasa anrufe gidan marayun shi sai me? Bari kaji yanzu haka Waleed nada kudin dazai iya gina gidan marayu dari inyaso, d'ana baida lokacin ka, baka gabanshi yanzu, yabarka har, so I expect you to do dsame stay out of my sons way inba hakaba Arham zan koyamaka hankali wlh" tai maganan tana sakinshi ta tureshi dan murmushi Arham yayi yasa hannu ya kakkabe kwalan shi yace "my expensive suit, anyway is fine" ya kalli Waleed yace "katuna abinda nataba fada maka kwanakin baya Waleed?" wani irin murmushi yayi batare daya kalli Ammi ba yace "nasan ka manta, lemme remind you, Waleed nafadi maka cewa duk abinda kaci sainaci, duk abinda kasaka saina saka" yanuna mai suit din jikinshi dan irin wanda Waleed yake sakawane masu tsada, yace "duk abinda kahau sainahau Waleed" yanuna mai motar sanan yace "duk matakin daka tsaya wlh saina tsaya, meet Arham the newest CEO of orphanage home how does that sound a kunnuwan ku" gate Mom tanuna mihsi tace "munji Arham kayi gidan marayu and muna maka fatan alkhairi the gate is over there kawuce kabar mana gida" girgixa mata kai yayi yace "a'a Hajiya bangama da danku ba tukunna" ya kalli Waleed yace "not all those orphanage student are in my orphanage, kasan kuma wanake cewa nabaka awa uku kasa wanan specific one din dakasan akanta nake magana kasa amaidata gidan marayu na dan ina bukatan ta if not things will get dirty yaro".
"get out butulu kawai, leave my house kafin ka kirga uku matsiyaci dan gidan talakawa," kallon Ammi yayi saikuma ya kyalkyace da dariya yadaga hannu sama cikeda isgilanci yace "I come in peace, you seems angry menene wai? Bari nabar miki gidanki kinsan they can't arrest newest CEO" wajen motarshi yayi ya shiga sanan yasake leko da kanshi ta window mota ya kalli Waleed yace "don't forget my offer and maganan dana maka Waleed I need that girl in my orphanage nabaka 3hrs" yatada motarshi yay reverse yawuce yabar gidan, juyowa Ammi tayi zata rufe Waleed da fada dataga baicema Arham uppan ba Mom ta girgixa mata kai alamun kartayi sanan tace "mutafi Waleed" juyawa kawai yayi yabude gaban motar ya shiga sukuma suka shiga baya suka zauna Waleed yatada motar, Ammi ta shiga masifa tace "wanan irin yaron ne Waleed zai kama danshi ya radamai sunanshi tirrr wlh, tier, I hate Arham with passion my heart is burning with rage, I want to deal with this boy dabazai kara tunanin crossing anylane with my son ba amman kin hanani kina cemin nabarshi da halinshi sabida yaga d'ana karami baida shekaru kamanshi sanan baida fada he is calm shine zai dinga gayamai maganan just look at the gut har gidana zai tako yama d'ana rashin mutunci wlh Arham yaci ganye, yaci ganye sosai, and zai gamu dani" tai kwafa Mom ta shiga bata hakuri, Waleed duk yana jinsu yay kaman baya jinsu at this point ya shafe zancen Arham a ranshi gabaki dayan hankalinshi ya karkata zuwa kan Saheeba, yasan tanachan gidan nan tana musu kuka dan batasan dukansu ba, and maganan da Arham yamai yasan kan itane yamai maganan, and koda zai bada komi daya mallaka ne bazai taba bari Arham ya karbi yarinyar nan ba, sabida yarinyar nan nabukatan kulawa da medication shikuma baidashi dazai bata koma bawanan ba bazai taba bama Arham itaba.
Horn yayi agaban gidansu Ilham mai gadinsu yafito yabude musu suka shiga ciki, yarane atsakar gidan sunata wasa saiga Mummy tafito tana murmushi tana musu sannu tazuwa tace "oyoyo oyoyo" parking Waleed yayi su Ammi suka sauko daga motar sukai wajen ta, sanan Waleed ma yafito yabi bayansu, cikeda girmamawa dakuma kunya yace "ina yini Mummy" "ina yini Waleed, sannunku da zuwa ku shigo dan Allah kunga yara duk sun cika gidan wlh yaran yan biyu ne, sunyi tafiya suna dubai fa bama suga baby ba har yanzu, amman yau mukesa ran zasu dawo in sha Allahu" Mom ce tace "Allah yadawo dasu lpy" hadadden falon su suka shiga Waleed yasami kujera ya zauna su Ammi zasu zauna Mummy tace "kawa bazamu bar yara su zanta ba, muje sama, Waleed bari aturo ta" tai maganan tana kwalama Ilham kira. "Ilham, Ilham kifito ga mijinki" wani daki Mummy tabude musu suka shiga, basu dade da zama ba saiga Ilham ta shigo tana sanye cikin wata atampa riga da zani, tai wani irin kiba nonon ta sun ciko sunyi suntum sabida shayarwa, tai duhu sosai kaman ba itaba sabida zafin ruwan zafin jego, har kasa ta tsugunna agaban Ammi da Mom tace "sannunku da zuwa Ammi ina yini" kanta Ammi ta