x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 22 - TWO DIFFERENT WORLD

  • 63001 words
  • 66000 words
  • Out of 139348 words

Category: Love Stories

Views 243

09 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
fadan ba saboda zata iya komawa kanta, ita kanta abin ya daure mata kai har lokacin yanda Arham yakama Waleed ya daka haka. Numfasawa Mama tayi ta goge hawayen daya zubo mata tace "Hajiya kima Arham kome kikaga dama, karki barshi kisa shima amishi fin haka, fin dukan dayama Waleed ma dan abinda yayi bai daceba nabaki goyon bayan nan dan inbama kisa amai hukunci ba ni wlh sainasa" wayan dake hannun Ammi tabude takira inspector general of police na tafada mishi komai sannan tace mishi atabbatar ankarya ma Arham hannu da kafa kafin dare da toture na police, tana katse wayan ta shiga turama inspector address din gidansu Arham.
[14/10, 20:18] Aishat Muhammad: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫





✍️ M SHAKUR





2️⃣9️⃣





Hayaniya da zata iya cewa tunda take a asibitin bata tabajin irinshi ba, hayaniyan ya mugun cika mata kunne yasa tabude idanunta ahankali tana kallon dakin, idanunta sunmata shegen nauyi sabida bacci bai isheta ba, sosai kirjinta taji yana wani irin faduwa, ward din datake gabaki daya ta kalla babu kowa cikin ward din sai ita kadai dake kwance akan gadon an lullubeta da bargo sanan anmata parking gashinta gabaki daya anyi mata parking na ponytail, ihu dawani irin masifa dataji yana sauka akan kunnenta yasa ta yaye bargon jikinta ta tashi zaune dagakan gadon tana kalle kallen dakin, ihu da hayaniya da masifan da akeyi jitake kaman a brain dinta akeyi, sakkowa tayi dagakan gadon tazira pink slippers dinta dake wajen sanan tadau Teddy dinta ta kankameshi akirjinta ta shiga tafiya ahankali kaman ana kiranta, hannu tasa tabude kofar dakin datake tafito tana tafiya dogon jelar gashinta na lilo tana kankame da Teddy ta kaganta kaman kasace ta kagudu, tai bala'in kyau doguwan yarinya da ita, batada wani kiba tana sanye da gown din asibiti daya wuce guiwanta da kadan, batada wani cikan kirji sosai, kirjinta moderate yan daidai irin na yaran larabawan nan, kanta an mata parking an daure da ribbon gashin na lilo, tundaga nesa take hango su Ammi, Mama da Mom na hayaniya dayasa ta tsorata tasake kankame Teddy gam gam idanunta na kawo kwalla dan tsoro taji sun bata hakan yasa ta shiga waige waige tana neman Waleed, fitowa tayi daga corridor ta shiga tafiyanta kaman bana mutum ba a reception din su Mom ko kadan basu lurada itaba, tunawa da ranan Waleed yayi kofa da ita yafita da ita yasa tai wajen kofan da sauri tana cikin tafiya kaman ance ta kalli glass din kofar emergency ta hango Waleed kwance kan gado fuskarshi a kumbure yasa tai dakin da sauri, hannu tasa tabude kofan ta shiga duksu Ammi basu lurada itaba, maida kofar tayi tarufe, ganin ciwo ajikinshi yasa tawani irin saki Teddy ta akasa tai kanshi da sauri, hannayenta tadaura kan cikinshi tabude bakinta tana kokarin ma magana takasa sai kawai tasaki kuka sosai tahau jijjigashi, amman bai motsa ba, kai hannunta tayi ta daura kan gefen idanunshi daya kumbura suntum ta taba tana kuka sosai tanaso tai magana tama kasa, bama tasan sunanshi ba amman sotake yabude ya kalleta, girgiza shi tayi tace "ahhhh, Umm mm" kafadarshi mai lafiya ta bubbuga tana kuka da kyar bakinta ya iya furta. "you, youuuuuuu, yo.....u" tasaki kuka sosai kaman zata mutu saikuma tadaura kanta kan kirjinshi tahau kuka tana jijjigashi tace "youuuu" sosai take kuka, takai kusan 5min ahaka tana kuka tana jijjigashi sanan tadago kanta ahankali ta kalli fuskarshi saikuma tajuya ta kalli TV dakin dake aiki da babu kara ko kadan dan anyi muting television din, tashar AIT ke aiki suna wani series na Korean film.





Daidai wata yarinya tashigo dakin wani namiji mara lafiya tana kuka tana zuwa kawai ta duka ta daura bakinta kan nashi sai saurayin ya farka, tana ganin haka da sauri tana kuka ta kallai, kafin ahankali tana kuka sosai takai fuskarta saitin nashi tana kallon fuskarshi yana mata wani irin kwarjini ta kafe pink lips dinshi da ido kafin ahankali ta saukar da bakinta kan nashi, tasaka all his lips inside her tiny mouth tai shiru tana kallon idanunshi ita adole tana jira yabude ido shima kaman na film hawaye na zuba daga idanunshi.

Kaman acikin mafarki yaji saukar wani tattausan lips kan nashi, bude bakinshi kadan yayi yay grabbing those soft tender lips yashiga kissing dinsu kaman zai cinye bakin, yatura tongue dinshi cikin bakinta yana lasowa kasa daurewa yayi yamika hannunshi trying to grab something yaji yakama mutum, ahankali yashiga bude idanunshi dasukamai nauyi kaman banashi ba, dishi dishi yake gani saikuma idanun suka washe tarr, ido da ido yayi da Widad da bakinta ke cikin nashi har lokacin bai dena kissing dinta ba idanunta sunyi jajir tsabagen kuka tana kallon idanunshi kuri kaman wata mayya, wani irin sakin lips dinta yayi da sauri yacire lafiyayyen hannunshi daga bayanta yaja jikinshi yakoma baya da sauri yana kokarin tashi zaune yana kallonta still, mikewa tayi itama tsaye takai hannunta kan idanunta tana share hawayen daya kasa dena zubowa sanan ta taho da sauri tazauna kan gadon tafada jikinshi ta rungume ta hanyar daura kanta kan kirjinshi tana kuka sosai, rasama mezai mata yayi hakan yasa yakai hannunshi mai lafiya yadaura akan bayanta yadan bubbuga alamun tai shiru sanan yatureta daga jikinshi ta tashi, hannunta ahankali takai ta daura kan wuyanshi dayaji ciwo tana turo baki kafin ahankali bama tasan tayaya maganan yafito daga bakinta ba tace "so....ry" gyadamata kai yayi cikeda dauriya, sanan ya tsareta da idanu, saikuma yace "who thought you how to do that"? Yanuna mata bakinshi, juyawa tayi kaman wata yar yarinya ta nunamai TV da yatsan ta hakan yasa ya kalli TV, Korean film yaga anayi yasan tunda ta nunamai wajen yasan anan tagani, shiru yayi yana kallonta, muryan Ammin shi dayaji yasa ya kalli kofa da sauri, faduwa gabanshi yayi, hakan yasa ya kalleta, dagata yayi tamike tsaye, anatse sabida tagane cikin harshen turenci yace "inaso kidauki Teddy ki ki koma dakinki kinji Saheeba, anjima kadan zanzo wajenki, now be a good girl and listen to me and go" makemai kafada tayi tafashe da kuka, girgiza mata kai yayi kaman zaiyi kuka yace "please Saheeba kitafi, yanzun nan zanzo kinji" sake makemai kafada tayi tana kuka, ahankali yasanya hannunshi ya jawota jikinshi rungumeta yayi tareda bubbuga bayanta a kunnenta yamata whispering yace "listen to me, please Pretty go, I don't want Ammi to see you here, please pretty go" yay maganan tareda dagota ahankali, fuskarshi ta kalla ya gyadamata kai hakan yasa ta sauka ahankali daga kan gadon, daukar Teddy dinta tayi sanan tajuyo ta kallai shima kallonta yake kaman yau yafara ganinta, ahankali tasa hannu tabude kofar dakin tafita tamaido kofar tarufe yana kallonta, ta glass din kofar yacigaba da kallonta ahankali take tafiya ta kankame Teddy ta, tai corridor dazai sadata da ward din da aka kwantar da ita. Ajiyan zuciya ya sauke tareda lumshe ido yadaura hannunshi kan fuskarshi kafin yasauke hannun kan bakinshi yay shiru yana tunanin what just happened.






*******





Within 30min IGP yayi deploying police zuwa address da Ammi ta tura mai. Knocking Gate din gidansu Arham one of the police men yayi, fitowa daga daki maigadi yayi yaleko, ganin police ne yasa yace "bayin Allah wakuke nema"? Wani daga cikinsu ne yace "Goodday please we are looking for Mr Arham" mai gadi da tuni jikinshi yahau bari ganin yan sanda yasa yace " yes gidan nan ne gidan Mr Arham" daya daga cikinsu policeman dinne yace "is he in"? Ware ido mai gadin yayi dan baigane turencin ba hakan yasa daya daga cikinsu yace "yana nan? Da sauri yace "yes.....eh,yana nan, yanzun nanma ya shigo gidan" "kaimu wurin shi" da sauri yajuya yay gaba suna biyedashi abaya har flat dinsu yabude kofa yashiga suma haka, a palour suka sameshi ya daura kafa daya kan daya yayi resting head dinshi a kam one seater kujeran dayake zaune akai hannunshi rikeda chilled maltina, jin mutane akanshi yasa yadago yana kallonshi, babban su ne yace "good-day Mr Arham we are here to invite you to our office for some questioning" yana gama maganan yafito mishi da ID card dinshi ya nunamai, bin ID card din yayi da kallo sanan yatabe baki yamaida kanshi kan kujeran yana girgiza kafa, kara maimaita mishi maganar sukayi but no response still saima maltina shi daya cigaba dasha, mai gadi ne saya gama tsurewa yace "Alhaji dakai fa suke" dago kanshi yayi ya musu wani irin kallon banza yace "what questioning"? Cije lips policeman din yayi yace "when you reach our office you will find out" "and where is your office located at"?

Shiru police din yanasa baicemai komiba dakin ya tsit, maigadi dake shirin sakin fitsari yace "Alhaji kabisu kar su maka wani mara kyau, kagan sunata binka ahankali tun dazun, kawa Allah kamike kabisu" y
policeman dinne ya juya ya kalli wasu manyan officers guda biyu da sauri sukai heading directing to kujerar da Arham yake zaune. "Sir you are under arrest" fisgoshi daya daga cikinsu yayi ya tayar dashi tsaye Arham bayyi wata wata ba ya dauke policeman din da mari mai kyau, bai ijiye hannun kasa ba yaji saukan mari to ko'ina akan fuskarshi dayaji yaji kwakwalar warshi tajuya abaibai.



[16/10, 05:47] M Shakur: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫





✍️ M SHAKUR





3️⃣0️⃣






Kamar jira suke suka haushi da duka kaman an aikosu suna bugamishi gindin bindiga all over his body, jin duka tako'ina yasa Sadiya tafito daga ciki dagudu tana ganin Arham ya sanda ke duka tahau ihu, mai gadi shima jikinshi narawa yashiga rokonsu su yakuri subarshi amman ko jinshi basayi saida suka tabbatar da sunmai lilis, he is totally weak baima iya motsi jini nafita daga hancin shi da bakinshi sanan suka barshi suka sakamai ankwa handcuff sanan suka jashi kamar ragon layya suka fita dashi daga dakin zuwa cikin motarsu.



Binsu har waje Mai gadi yayi shida Sadiya suna rokonsu akan susakeshi amma basubi takanshi ba, suna jefashi ciikin motarsu suka shiga direba yatada motar sukai gaba dashi.


Koda suka Isa police station fuskar Arham yay subu subu tsabagen mari kan dayasha, janshi suka karayi zuwa cikin station din suka bada report that lead them har suka mishi dukkan nan sanan aka jefashi cikin cell, babban su ya shigo cikin cell din rikeda wata zungurariyan takarda ya fara karanto mai offense dinshi na trying to murder Dr Waleed warbai. Janshi akayi zuwa toture room aka Fara tambayarshi why he strangulated Mr Waleed Warbai. Dago jajayen idonshi Amma baice musu komai ba. Fara dukkanshi sukayi tako Ina Yana ihu Yana " Don Allah kuyi hakuri, it was a mistake" kuka yafara yi Amma still basu barshi ba. Sai dasuka tabbatar da sun mushi lis har kasa daga lafanshi guda dayayi sannan Suka kawo mishi ruwan zafi suka bashi yasha.





Bayan sallan magrib Ammi da Mom da Mama suka shigo dakin dan sunje masallaci sunyi salla, ganin Waleed azaune yasa da sauri Ammi ta saki jakanta kasa tazo gadon tazauna gefen kafafunshi takai hannayenta kan fuskar Waleed, kaman zata fashe da kuka tace "My baby katashi, tell me meke maka ciwo eh? A ina kakejin ciwo ajikinka, tell me Waleed dina meka maka ciwo"? Tai maganan hawaye nata ruwa a idanunta tana shashafashi kaman zata cinyeshi, dan murmushi yamata ganin yanda tadamu yace "am fine Ammi karki damu, meya kawoku orphanage haka? Mama" yakira sunan Maman Arham ahankali yana murmushi, karasowa Mama tayi wajen zuciyarta tamata mugun nauyi, wani irin kunyan Waleed dinma taji tanaji jibi yanda danta yamai, yaron dake sonshi dake nufinshi da alkhairi ne yama wanan jina jinan, tsayawa tayi ahankali agabanshi, dan murmushi tayi mai kama da murmushin dole sanan ahankali tahada hannayenta biyu tace "Waleed dan girman Allah kayakuri abinda Arham yamaka, wlh naji kunyan halin......" da sauri Waleed yamika hannunshi mai lafiya yakama hannun Mama yace "Mama me haka kike cewa dan Allah? Please kidena bani hakuri, ninace miki Blood yamin wani abune"? Wani wawan harara Ammi ta watsa mishi, Mama tace "Arham yamaka abinda ba daidai ba, Arham bai kyauta ba, kalli halin dayasaka ciki, wlh naji kunyan abinda yamaka, kunyan kallonku dukama nike, Arham bai kyauta ba wlh, saisa nabama Ammi goyon baya takiramai yan sada amai lilis akaryashi kaman yanda shima yamak......" kafinma takarasa maganan Waleed yatareta yace "waya kirama Arham police"? Cikin fushi Ammi tana ballamai harara tace "nice nasa aje akamashi akaishi police amishi shima dukan dayamaka, ko angayamai banison kane dazai kama yamaka wanan dukan eh? Karfinku dayane yasan da shekara nawa ya girmeka dazai kamaka ya bubbuga haka saisa nasa inspector yasa aka kamashi akaishi Station amai wanan shegen dukan dayamaka" sosai idanun Waleed sukai wani irin ja ranshi yawani irin baci, cikin fushi yace "Ammi wai mesa in everything saikin shiga rayuwana ne eh? Friends fight don't they? Sabida munsami miss understanding da blood saiki shiga fadanmu har kisa akulleshi, ninace miki ki kullemin dan uwane eh"? Wani irin kallonshi Ammi take kaman ta rufeshi da duka amman bazata iyaba, wani irin kunci da haushin abinda Ammi tasa akama Arham yaji hakan yasa yace "Ammi call that inspector right away kicemai yasaki Arham" cikin fushi Ammi itama tace "bazanyi ba dan ubanka" Waleed zaiyi magana da sauri Mama datake ganin duk laifin ta ne komi tace "kaga Waleed abinda mahaifiyar ka tayi tayi gaskiya, daidai tayi wlh ko ansakoshi nida kaina saina sassaba mishi, dan haka kamabar maganan nan" gyada musu kai Waleed yayi cikin kunan rai yace "ok" wani irin yunkurawa yayi daga gadon yana cije baki sabida yanda bayanshi da kafadarshi da aka daure ke mugun ciwo, da sauri Ammi ta tareshi tace "kai ina zaka Waleed" ture hannunta yayi cikin karfin hali irin na maza ya shiga kokarin sauka daga kan gadon, rikeshi daga Mama har Ammi da Mom sukayi, fashewa da kuka Ammi tayi tace "Waleed wai mesa bakajin magana ne kacika taurin kai eh? Ina zaka, sokake daurin da aka maka ya turgude, Waleed kasheni kakeso kayi kahuta eh Waleed, mena maka? Mena maka nace da zaka tashi zakabar gadon da kake kwance kana ganin bamaka da karfin tashi" tureta yayi a haukace ya kabar da hannunta daga jikinshi yace "leave me alone Ammi, kurabu dani, I can't fight with my friend again, friends can't fight again? Eh dole saikun shiga, dole sai kin shiga komi nawa? Ko kasheni Arham yayi he's my friend, Ammi you have no right to interfere in my affairs, sabida Arham ya dakan saiki aikamai police su kamashi a kulle shi adaka haba Ammi, haba Mom" yay maganan yana kallon Mom itama yace "bakuji kunyan Mama datake nan tsaye dakuba kuna saka a chaza danta eh?" da sauri Mama zatai magana Waleed yadaga mata lafiyayyen hannunshi yace "Mama please kiyi shiru" sanan ya kalli Ammi yace "Ammi baki kyautamin ba, and inhar you feel wanan abun dakikeyi akaina shine son dakike min then guess what am not proud of the love you have for me am not, cus kinsa inajin kunyan abokina, my childhood friend, my only friend my blood Ammi, Ammi you hurt me today" yay maganan yana kwanciya a gadon ahankali tareda lumshe ido, shiru Ammi tayi tana kallonshi kalaman shi sun mugun sosamata rai, zatai magana Mom ta girgiza mata kai, dauke kai tayi tace "Waleed nikake ma magana haka akan nace a hukunta Arham ko" tai shiru tana kallonshi ko bude idanunshi Waleed baiyiba, ciro wayarta tayi takira Inspector agaban su tace asaki Arham din sanan ta katse wayan, sanan ta kalli Mom tace "stay with him nizan tafi gida" tana maganan tadau jakanta cikeda fushi tafita daga dakin zuciyarta kaman zai tsage yafashe, Mom zata bita Mama tace "bari nina bita ki zauna dashi" juyawa Mama tayi tafita daga dakin, Mom kuma ta zauna kan kujera takifa kanta kan gado tai shiru tana tunani.



Koda Mama tafito har motar Ammi direba yajata sunyi gaba, awani irin hankali Mama takarasa motarsu, baya tabude ta shiga direba ma baya cikin motar da alamu masallaci yaje, fashewa da kuka tayi sosai, intace dukan da Arham yama Waleed bai mata ciwo ga wlh tai karya, ta bala'in jin ciwon dukan nan kaman me, Waleed d'a ne wlh, dan halas d'a na kwarai, tasan harga Allah tanaso aramamai amman da Waleed yafarka yayma Ammin shi maganganun nan saida ranta ya sosu, bala'in sosuwa ma, Waleed d'ane da kowace uwa zatai alfahari dashi aduniyan nan, taji kunyan abinda danta yamai wlh taji kunya, tasan Ammi tagaya mata maganganu amman ko kadan bataji zafinsu ba dan tasan ciwon dakake ji in wani yakama maka d'a yadaka ba gaira ba dalili, Arham bakin halinshi da bakin zuciyanshi tamai yawa, kuka tayi mai suna kuka amotar nan hakanan ma taji bazata iya komawa cikin asibitin tahada ido da Waleed ba, tana zaune direban ta ya shigo yace "Hajiya yakuri ina masallaci ne mutafi?" gyadamai kai tayi tace "eh mutafi", tada motar direban yayi suka fita daga gidan marayun.



Direban Ammi nakaiwa gidan bamata jira yabude mataba tabude tafito, ahankali take tafiya dan bamata gani sosai, kanta wani irin bugawa yake kaman ana dukanshi da gatari, falo tabude ta shiga, yar aikinta da gudu tafito tana mata sannu da zuwa ko iya amsata bata iya tayiba tawuce stairs tai sama ahankali tabude dakinta ta shiga, yarda jakanta tayi anan tsakiyar dakin tawuce kan gadonta da kyar ta zauna tamika hannunta ta shiga tattaba saman kan side drawer dinta wani goran magani ta dauka da sauri, sanan ta bude taciro wasu kwayoyin magani na masu hawan jini guda biyu ta jefa abaki ta hadiye sanan tadauko bottle water ta kurbi ruwa kadan tasha,
End Ads