x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 11 - TWO DIFFERENT WORLD

  • 30001 words
  • 33000 words
  • Out of 139348 words

Category: Love Stories

Views 225

09 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
"wai me hadinki da rooftop ne kinsan karfe nawa kuwa? Kowa na gida ya shirya ke kinanan Amarya har yanzu sanye da kayan bacci, karfe sha daya fa za'a daura yanzu is 20min after 9" ware idanu Widad tayi sai yanzu ma ta lura gari yawaye sosai ita datake nan tun duhun asuba, da sauri ta mike Sabeeha tace "yi sauri zomuje ki shirya" gyadamata kai tayi tace "to, Sabeeha kinyi kyau" shafa kumatun ta Sabeeha tayi tace "kema haka kinyi kyau dudda ai bakiyi kwalliyan ba" dakin Amah suka karasa agurguje akasa tai bayi tai wanka tafito sanye da bathrub, Amah ta watsa mata harara tace "yarinya sai shegen nawa keda yakamata ki riga kowa shiryawa kece ta karshi jibi goma saura" turobaki tayi ashagwabe tace "Amah wai banace kiyakuri ba, aifa bansan lokaci yawuce hakabane fa ko Sabeeha?" da sauri Sabeeha tace "Amah bafa tasani bane kuma tabaki hakuri kinki kodai kishi kike zata kwacemiki Ahmad dinki" fashewa akai da dariya harda masuma Widad din makeup, sanda Amah ta shiga nema hakan yasa aguje Sabeeha tafita daga dakin tana dariya, Widad kuma ta gimtse dariyanta kafin Amah ta rafka mata sandar.





Wuraren 11 aka gama shiryata tsaf cikin lebsa r'batia blue(sunan kayan), yanada mugun kyau kayan dogon rigan ne daya amsheta, kalan blue da fari, kunnenta yaji hadaddun yan kunnaye hannayenta da warwarori na zinare, farin gyalen amare Amah ta dauramata kan saman gashinta da aka gyara tsaf sanan tajuyo tamata kiss cikeda so tace "zauna anan dan Amarya bata fitowa akafa, bari naje chan tsakar gida wajen su babanki, yanzun nan neggafa asisitance zasuzo afitar dake, I love you" murmushi tasakin ma Amah tace "jazakillah Amah" gyadamata kai Amah tayi tana dogara sandarta tafita, babu kowa aciki kowa na waje dan nanne ake bikin, duk yan ciki sun fita sabida Aby na raba kyauta.

Tana zaune shiru adaki tana kallon kanta a madubi ganin kyawun datayi yay yawa sai kewan Aby take sabida tun safe bataga Aby ba gashi aka'ida Amarya bata gani iyayen ta sai an fitar da ita acikin (amaria) a kaita wajen daurin auren dan Amarya bata tafiya da kafanta, tana cikin yan tunane tunane ta akai knocking kofar dakinsu faduwa taji gabanta yayi da sauri tajuyo tareda bada izinin shigowa wani ma'aikacin gidansu ne ya shigo yana sanye cikin wani uniform blue da purple, cikeda girmamawa yace "ga amaria ne abakin kofa anbamu izini mufito dake baya, Aby nason magana dake kafin mukaiki wajen daurin auren, motarshi na wajen" murmushi tayi tace "Aby" gyadamata kai yayi yace "bismillahi" mikewa tayi ahankali cikin blue embroidered dress din lebsa r'batia tasake kallon kanta amadubi sanan ahankali tafara tafiya, bude mata kofa ma'aikacin yayi tafita anan taga maza guda shida, dama a adaltance maza bakwai da ake kirada negaffa assistance ke daukan Amarya bayan ta shiga cikin amaria su daura hannayen abin akan kafadarsu sukaita chan wajen daurin auren, bude mata kofan sukayi ta tsugunna ahankali tashiga ciki ta zauna tare da tattare kasan gown dinta, cike da girmamawa yace "kin zauna da kyau? Are you comfortable?" gyadamai kai tayi tace "Alhamdulillah thank you" maida kofar yayi yarufe sanan yasauke labulen daya rufe kofan tabaya da akama ado ta yanda babu wanda zai iya hango amarya, daukan kafafuwan sukayi suka dagata sama suka daura akan kafadunsu instead of suyi tsakar gida sai sukai kitchen da ita, bude kofan bayan kitchen din sukayi suka fice babu kowa ata wurin, sanan suka cigaba da tafiya sukai gate din dake ta wurin bude gatedin sukayi suka fita, babu kowa ta wajen sabida daman Babanta yasai filin wajen babuma mutane sai wata katuwar bakar mota dake wajen, karasawa sukayi har gaban motan sanan suka sauketa, suka bude tafito ahankali, kallon wajen tayi sanan ta kalli daya daga cikin motar mahaifinta data gani awurin a pake murmushi tayi tace "Aby na ciki?" gyadamata kai sukayi, ahankali tasa hannunta tabude bayan motan daba kowa zata shiga taji saukan wani abu kaman tsumma a bakinta da hancinta within 3 good secs dip kanta yadauke, da sauri suka rirrike ta suka shigada ita cikin motan sanan wanda yazo yakirata yama direban da fuskarshi ke sanye da mask magana "yi sauri kutafi, yanzu mu zamuje daukota adaki as scheduled kumuje yara" da gudu suka dauki amaria suka tafi shikuma direban yaja motan dawani fitinannen gudu yabar anguwan.
Wanan kenan!!!






Ahankali take bude idanunta sabida kanta dataji yamata wani irin mahaukacin nauyi kaman an dauramata buhun simenti, jikinta namata nauyi, irin nauyin nan da jikinka kakeji yamaka bayan alluran kashe zafin ciwo ya saki, wani irin mahaukacin iska dataji yana kadata yasa tabude idanunta da kyau tangaran tana kallon inda take data kasa gane inane, hasken datake gani yasa tajuyar da kanta saitin hasken, kofa tagani abude wani wagagegen kofa saikuma fili haka datake hangowa na kasa bayan clean filin kuma bishiyoyi ne da shukoki take hangowa, cigaba dabin filin tayi da kallo taga jirage ne kaman irin jiragen airforce dinan amman wanan bana airforce bane guda uku, da duka karfinta ta daddage ta lallaba ta tashi zaune tana dafa fuskanta tana kara bude idanunta dakyau kafin da sauri tace "Aby, Aby" tai maganan tana mikewa tsaye tana tangal tangal sai a lokacina takalli inda take cikin jirgi take irin jirgin datake gani a TV da news jirgin airforce dake transporting weapons, ko troops gashi bataga kowa ciki ba, dafa bangon jirgin tayi ganin zata fadi dan batada karfi ko digi kafin tafara tafiya ahankali zatai wajen kofan. "ku kamota!" taji anfada agadarance da sauri ta juyo, Umm tagani tana sanye da dogon riganta hadadden daga gani tasa kayanne dan bikin ta, cikeda isa take tafiya tana fitowa daga cockpit din cikin jirgi wasu karfafan maza guda biyu biyeda ita, tsayawa Widad tayi chak tace "Umm! Assalamu Alaykum Umm, me mukeyi anan ina Aby na dakeson magana dani? Me wayan nan zasumin mesa zasu kawoni nan, su suka kawoni? Waya kawoni nan Umm?" tai maganan tadan daburce sabida mazan dasukayo kanta guda biyu, ko amsata Umm batayiba saidai tasami wata plastic kujera kaman dan ita aka ijiye ta zauna akai tareda crossing leg tana kallonsu, fashewa da kuka Widad tayi ganin gardawa sun rirrike ta sun dagata chak sun kawota gaban Umm sukasamata gwuiwa akasa tai kneeling right before Umm jikinta na shaking, da sauri cikin kuka ta daura hannayenta kan cinyan Umm tace "Umm dan Allah kiyakuri mukoma gida kinji me mukeyi anan dajin? Eh" murmushi Umm tayi tace "yau Widad ne agabana tana kuka tana rokona, naga in kikaga mahaifinki kinamin kallon farko kika gaidani baki sakemin nabiyu saidai in ubanki yasa nazo ma kwashe plate din dakika gama cin abinci dasu ki dagokai ki kallen koba hakaba? Yau ina ubanki yazo nan yabaki kariya mana? Bazai zona"? Cikin kuka Widad tace "wlh bahaka bane amman kiyakuri Umm, kinji bazan karaba kiyakuri dan Allah, karkisa sumin komi" gyadmatakai Umm tayi tana tabe baki tace "zaki gida?" da sauri Widad da jikinta har rawa yake tace "z......zani.....zani gida Umm" murmushi Umm tasakeyi takai hannu ta shafa fuskarta da kukan datayi dukyay ruining makeup din tace "you look beautiful, so beautiful da fuskarki kaman na mahaifiyar ki, daman gift nasa akawo ki nabaki but saina baki tsoro kafin nan, gift din bikin ki" tai maganan tana bin jirgin da kallo tace "jirgin nan jirginane, da kudaden dana tara iya zamana tareda mahaifinki nasayeta a black market, nasa aka gyarata tsaf, babu abinda bai aiki, anytime nakeson na shiga cikin wata kasa da wanan jirgin nike zuwa, babu wanda yasan inada ita sai y'ata Sabeeha, shine naga amatsayin ki na y'ata yakamata nakawoki kiga jirgin da idanunki kinaso? Shine gift din dazan baki kinaso"? Taima Widad tambayan tana karkada kafa tana murmushi tana kallonta, gigirza mata kai Widad tayi alamun a'a saikuma da sauri ta gyada ma yakai alamun eh ganin wani mugun kallo datamata, cije lips Umm tayi tasaki tace "good gurl tashi to kitafi da sauri, is official nabaki jirgin yazama naki tashi kitafi to, motanmu nawaje in mukakai gida kyayi signing papers din so that officially it becomes yours, tashi kitafi, clean your face kar Aby yace nasamai y'a kuka" tashi tayi jikinta har bari yake tajuya tafara tafiya batako waigen baya burinta kawai taganta agida wurin Ahmad dinta da Aby da Amah, daga zaunen Umm tamikama namiji dake kanta hannu, fire extinguisher cylinder yadaura mata a hannu ta karba ta ta tashi tana dagashi da kyar dan acike yake tana kallon Widad dake tafiya ta kusan kaiwa kofa, ahankali take tafiya without making a sound taku uku ta cinmata wani irin daga cylinder tayi ta daddage da duka karfinta da Allah yamata tasakinmata shi akai tawajen kaman bayan kai da keya daidai Widad tasa kafa zata fita daga jirgin taji saukan wani irin heavy abu akanta, sandarewa tayi tareda zaro ido kaman irin wacce aka harben nan, hannu Umm tasa takama bayan riganta ta fizgota cikin jirgin, janta kawai take kaman ta mutu saida tazo daidai tsakar jirgin sanan ta jefar da it tafadi warwas akasa idanunta na juyawa gawani mahaukacin jini dake bulbulowa daga kanta kaman an kunna pampo, bakinta na kokarin motsi amman yakasa idanunta sun juya sun birkice kaman ba idanun mutum ba tsabagen kanta da aka buga, komawa Umm tayi ta zauna tai crossing leg tace "next" da sauri gardawan suka shiga yaye wani abu dasuka lullube da bakin trampoline, coffin ⚰ ne, amma ba irin na Christian ba irin na musulmai, marfin saman anyi huji huji guda goma haka ko mesa oho, bude wa sukayi suka kalle Umm, Widad ta nuna musu da yatsa dat is lying on the floor kaman ba rai ajikinta tace "ku dagata kusata aciki" da sauri dayan yace "Hajiya ai zata mutu ta ina zata dinga numfashi?" kafin Umm tabashi amsan dayan yace "dakiki wanan hujin da akayi name to? Banda haka I've nake it clear ai no question, we don't question wacce tabamu aiki, kasan irin kudaden data biya kuwa, our lives have change, this woman is our live saver, ka kara tambaya I won't mind changing you yanzu yanzun nan" da sauri yace "tuba nike mai gidana" karasawa inda take sukayi suka dagata su kansu saida sukaji tsoron jinin dake zuba daga kanta amman basuda ikon tambaya kudi suke nema kuma shi aka biyasu, sakata sukai aciki yaraf kaman sun ijiye kayan wanki sanan suka rufe, suka juyo suka kalli Umm dake binsu da kallo, murmushi tayi tabude yar purse din hannunta maidan girma taciro kudaden garinsu rappa guda biyar tace "ga la'adan ku wanan kyauta ce sauran saikun dawo" karba sukayi jikinsu haryana bari, tace "inaso yarinyar nan itada gidan mahaifinta har abada, ban kisa sabida addinina yahana kuma duka zunubanta kaina zai dawo inhar na kasheta, wanan ma danayi na rabata da mahaifinta nasan Allah zai yafemin sabida laifi daya ne kadai zaka roki Allah da baya yafewa aduniyan nan shine shirk, hada Allah dawani, bantaba shirka ba kuma bazan tabayiba kuma ko wanan ma danayi Allah yaga dalilina, ku kaita danesa, kufitar da ita daga kasan nan gabaki daya, ku kaita chan wata kasan, cikin worse kasashen damukeda shi aduniyan nan gabaki daya, wulakantacciyan kasa zaku kaita wanda yan garin cikima neman hanyar fita daga ciki suke, kasar da weather ta is harsh, kasan da rayuwa acikinta zai zame mata annoba da ukuba, kasan da kisa ake kullum ana shayar da matsafa organs din dan Adam, kasan da al'adunsu ya banbanta da namu far far, kasan da Widad yar mai kudin nan bazata taba iya rayuwa ciki ba, kasan da mahaifinta bazai taba tunani tana wurin ba, sanan karku kaita kasar dake nan kusa dan nasan mahaifinta zai iya saka abinda ya mallaka na karshe danya nemota, ku kaita da nesa karku sake kuyi landing kar akamaku mahaifinta nada connections, daga sama zaku jefo akwatin chan takarata nasan koda tafarka bazata tuna damuba kafin namata wanan dukan a daidai wanan bangaren kan saida nai bincike dan haka zan tafi kuma kutafi ina tafiya, dan trust me nasan anjima akwai total lock down a morroco dan neman Widad" godiya suka mata ta tashi tafice motar dake pake awurin tashiga suka bar dajin. Wanan kenan!!
[05/10, 09:32] Aishat Muhammad: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫





✍️ M SHAKUR





1️⃣4️⃣


*_NIGERIA_* 🇳🇬
Wani irin juyawa jirgin yayi kafin kace me jirgin yabace a hazo, kwashe yaran aka shigayi ana lodasu a mota yayinda wajen yacika security personnel da some marine forces dake wajen, wasu mutane guda uku ne sukayo wajen Waleed na tsaye inda yake suka shiga cikin ruwan kaman sune search force, sun duba ruwan basuga komiba saidai suka dawo tareda coffin din, Arham ne yakaraso inda Waleed yake tsaye bayan ya tabbatar da staff dinsu suntafi da yaran yace "meya faru just now blood? Jirgin sama right above our head? That's strange, bantaba ganin hakaba sanan ya jefar da akwatin gawa a ruwa is that even okay no wa.... " hannun da Waleed yadagamai yasa yay shiru ya kalli inda Waleed ke kallo da sauri, mutane biyun ne suka fito daga ruwan rikeda akwatin dayake abude suka ijiye bakin ruwan sanan suka fito da sauri Waleed yay wurin Arham biye dashi, tsayawa chak sukayi suna kallon akwatin da jini yabata sosai garuwa ciki, dayan dake cire kayan ruwan da yasaka ne kafin ya shiga cikin ruwan yace "I don't understand, jirgi kawai yazo yajefo mana akwatin gawa lafiyan su kalau ko bazugani da kyau sun zaci nan bolane" da sauri dayan yace "ni nama zaci gawa aka yardan mana ashema akwatin ce kawai, to Allah dai ya kyauta amman wanan abu haka, we will report to the police ashigar da karan susan inda zasu jefar da waste dinsu jibi yanda suka daga ma bakinmu hankal....." shiru yayi ganin Waleed ya tsugunna yanabin jikin akwatin da kallo yana shafa akwatin da hannu kaman maiso yagano wani abu, kafin idanunshi su sauka kan dan kunne kwaya daya dayake makale acikin hole din shan iskan nan da akayi kaman ramin yatokare dankunen dayakeda fadi dan dankunne yama ramin kadan abinda yanashi fita kenan da ruwa shima yay sweeping nashi away, ahankali Waleed yasa yatsanshi yaciro dankunen yamike tsaye yana kallo daya daga cikinsu yace "wow dan kunnen mai kyau halan yayimoshi yayi a ruwan, muje Bala mutafi da akwatin" daukan akwatin sukayi harzasu tafi da sauri Waleed yace "are you sure kunduba ruwan nan da kyau babu kowa ciki?" "yallabai babu inda bamu dubaba ai indai wanan rafin dakake ganine babu wani lungu da sako dabamu saniba cikinshi, bayau muka fara ceto rayukan mutane acikinshi ba" gyadamausu kai kawai yayi suka wuce suna zance, Waleed yajuya yana kallon ruwan da sauri Arham yace "don't tell me u want to go in da kanka" juyowa Waleed yayi ya kalleshi yace "of course yes, ga dankunne nagani a box din" da sauri Arham yace "this is river Waleed, ruwa ne, the coffin can pick the ear ring anyway aruwan, kagama wuce mutafi dan wlh kana kara making attempt din shiga ruwan nan zan danna ma Ammi kira" wani mugun kallo Waleed yamai yace "toka kira munafuki" yana maganan yafada ruwan da sauri Arham yace "Waleed" gabanshi nafaduwa yana kallon ruwan da Waleed ya nitse ciki, arude Arham yace "Waleed wai me haka sai wani abu yasameka acikin ruwan nan eh? Come out please" kusan 10min Waleed yadauka cikin ruwan sanan yafito ahankali, Arham yace "kagani kaima bakaga komin ba, kafi wayance iya aikinsu ne kawai kaje ka jika kayanka a banza" ballamai harara Waleed yayi yay gaba abinshi Waleed ya bishi da sauri yanadan dariya yace "wlh kacika rigiman banza, kawai daga ganin dan kunne shikenan" Waleed baice mai komiba har sukaje children section din, zai shiga ciki saikuma ya kalli Arham yace "lemme go and get Khadija and change" gyadamai kai Arham yayi Waleed yawuce.
Knocking yayi tareda bude dakin yashiga, daidai lokacin Ilham tafito daga bayi tana sanye da hadadden jeans din daya kawomata as gift jiya da crop top din da hakanan yadauko let's just say he's use to seeing ladies yan gayu dress in them so practically he wants to see his wife dress like that, tana ganinshi ta taho da gudu zata fada jikinshi ta rungumeshi yakoma baya yace "am wet baki gani" binshi tayi da kallo cikeda mamaki zatamai tambaya yawuce bayi, fitowa yayi daure da towel yazo ya chanza kaya, tajowa wajenshi tayi da sauri saikuma tarike waist tamai wani irin juyi tace "bakace nayi kyauba, nayi kyau?" dan murmushi yayi kawai yakarasa bakin gado ya zauna bayan ya chanza kayan yace "is nice" wani irin blushing tayi ta taho da gudu ta zauna kan laps dinshi sanan ta manna mai kiss a lips dinshi tace "thank you" gyadamata kai yayi kawai sukia shiru, ganin yamata shiru yasa tace "Dr jirgin na landing awajen nanne dazu naji karan jirgi kaman akaina" ahankali yace "it just came and yakuma juya" gyadamai kai tayi tana kallon yanda yake maganan yace "get dress let's go out" cikeda wani irin murna ta dagashi wardrobe taje da sauri taciro gyale mai kyau dazai shiga da jeans din sanan takoma gaban mirror ta yaryada uban kwalliya tasa jan baki sanan ta yafa gyalen awuya tajuyo ta kallai yana danna waya tace "na shirya" dagokai yayi ya kalleta dauke kai yayi yace "change into something native" wani iri taji taso sufita ahaka ko Arham yaga shape dinta da kyau saikuma ta share tai gaban wardrobe din dakin wata pink atampa taciro da aka mata riga da skirt ta shirya tsaf ciki kayan sun mugun kamata suranta yafito sosai, tayafa gyalen daya shiga da kayan tasaka flat shoe sanan tazo gabanshi tace "Baby let's go" dagokai yayi ya kalleta sai kawai yamike tsaye yamaida wayan aljihu yay gaba, bude mata kofa yayi tafito sanan shima
End Ads