Arham baimai reply din message dinshi ba yasa yatada motar direba yabude mai yawuce yafita daga gidan.
Agaban gidansu Arham yay parking motarshi yabude yafito yatura gate ya shiga gidan, babu kowa a tsakar gidan, sallama yayi yabude kofa ya shiga falon Mama ce ta amsa mai ahankali, saikuma tasaki murmushi tace "Waleed kaida bakaji sauki bane ba kafito? Ya karfin jikin? Maman ka takirani ta sanar dani abin farin cikin daya samemu ubangiji Allah ya raya, ya dayyaba, ya sunan yaron ne"? Murmushi yayi yace "sunanshi Arham Mama" wani iri Mama taji jikinta yay sanyi, sanyin ma karara hakan yasa tama kasa magana, lurada yanayin ta yasa Waleed yace "Mama ina Arham yana nan"? Cikin dan fushi tace "ohon mai rabona dasa Arham a idanuna kwana uku kenan yau" mikewa da sauri Waleed yayi yay corridor falon shiga yayi direct yay gaban dakin Arham, knocking kofar yayi yakirashi. "blood" jin shiru yasa yatura kofar ahankali ya shiga cikin dakin, dakin babu haske sai uban duhu, ahankali yamika hannunshi ya kunna switch hakan yasa dakin yya haske, Arham ya hango kwance kan gado bai lulluba ba dagashi sai gajeren wando fuskarshi ta kumbura suntum tsabagen dukan dayaci, jikinshi duk tabon ciwo dawani irin sauri Waleed yay gadon yace "subhallahi blood who did this to you eh? Waya maka haka"? Yay maganan yana dago Arham zaune, tashi zaune Arham yayi yana wani irin kallon Waleed din da sauri Waleed ya sauka yay bayinshi, ruwan zafi ya dauko yajefa towel ciki yazo yazauna akan gadon cikeda tausayi ya matso towel din kaman zaiyi kuka yakai kan fuskarshi yana dannamai yace "blood am so sorry, am ashamed of abinda Ammi na tasa aka maka, look what they did to you, this people are heartless, sorry blood" yay maganan yana gaggasamai, ijiye ruwan akasa Waleed yayi bayan yagama yasauka daga kan gadon yanabin dakin dayay kacha kacha da kallo yace "kasha any medication, kaci abinci?" dudduba dakin yayi ganin baiga maganin anything ba yasa yadau ruwan yakai bayi yafito sanan yadawo kan gadon, hannunshi yadaura kan kafadar Arham yana kallonshi kaman yanda Arham din ke kallonshi, ahankali yace "talk to me blood meke maka ciwo eh? Sanan wani abinci zakaci let me go out and get it for you, kafada min please ina da ina ke maka ciwo mow"? Wani irin kallo Arham kemai kafin ahankali yakai hannunshi ya kabar da hannun Waleed daga kan kafadarshi yace "wato halinka Waleed naban mamaki" ahankali Waleed na kallonshi yace "halina blood kaman ya"? Dan murmushi Arham yayi yakai hannunshi ya share fuskarshi dahar lokacin lema leman ruwan da Waleed yagasamai jiki kekai yace "kaida uwarka kunsan polisawa sunzo sun kamani sunmin bugun mahangurba shine yanzu zakaso kana wani rawan jiki kana bani kulawa kaman bakasan hakan yafaru ba" sassauta murya Waleed yayi ahankali yace "blood listen to me, I have no reasons to lie to you koda chan banmaka karyaba yanzu ne zan maka karya, believe me bansan Ammi tasa amaka abu makamancin hakaba, a lokacin danasani saida nasa aka janye aka sakeka, blood you are my only friend danai basing life dina dashi in this world, bazan taba hurting nakaba no matter what, besides you are morethan a friend to me, you are my blood Arham" tabe baki Arham yayi sanan ya nunashi da yatsa yace "ku masu kudin nan feels zaku iya duk yanda kukaga dama aduk lokacin dakuka so, zaku iya duk yanda kuka so aduk lokacin dakukaga dama, listen to me Waleed wlh zan gwadama aduniyan nan dudda uban kudinga, kadaiga mahaifinka nada kampany akasan waje dake gina boat dawasu kampanoni, mahaifiyarka nada kampany da business da dama ko, amman wlh zan nuna maka duk wayan nan kudin da dukiyan dakuka tara bazai taimakeka da komiba saika gane kurinka Waleed" shiru Waleed yayi yana kallon idanun Arham, all he could see was hatred, tsantsan tsana kawai yake gani a kwayar idanun Arham, wani iri yaji yanaji kaman zaiyi kuka saikuma yahana kanshi, ahankali yana kallon Arham din yace "Arham all wanan fadan da maganganun is it akan kawai natambayeka ina kake kai kudin ka? But why do I feel kaman there's more to this case, blood na kalli idanunka abu daya kawai nake gani shine tsantsan tsana ta, blood mena maka? Menataba maka? What have I done to you please kafadi mini watakila bansani ba please tell me kaji my friend" da sauri Arham yanuna kanshi yace "friend? Nine friend dinka Waleed? I can never be a friend to rich kids sabida all they know is sumaka ihu, suyi controlling naka, suyi matching naka and step your your neck aduk lokacin dasukaga dama, Waleed zaka iya tuna how many times kakemin ihu kakemin tsawa in your office kanamin fada"? Wani irin hawaye ne Waleed yaji sun gangaromai shaaarr, hannu Arham yanunamai yace "ba kuka nace kamin ba tambayanka nayi, kasan how many times kakemin ihu aka a office"? Girgiza mai kai Waleed yayi ahankali kafin yafuzar da iska yasa hannu ya share idanunshi tass sanan yanisa yace "I never meant all those shout, badan cin mutunci kowani abubane yasa nayi hakaba, Blood kasanni sama da kowa, and you know how passionate I am towards my work at the orphanage, idan yazo takan orphanage dina ne banson wasa kawai strictly work saisa I do all those to you sabida kai aikin da yakamata kayi, but tunda har ahaka kadauki abun ka fassara am sorry for that too I didn't do it because am rich or whatever I do it cus I feel is my own way of motivating my staff to do more, to perform better, idan akazo kan human resources management akwai two ways of motivating a staff, akwai positive motivation and negative motivation, I guess mine was the negative one but kayakuri" ya karashe maganan ahankali muryanshi tayi sanyi sosai, tabe baki Arham yayi yace "orphanage orphanage orphanage, staff, staff, staff, Mr, Dr. Waleed Warbai the chief CEO of Warbai orphanage home and home of the disables how does the name sound"? Yatambayi Waleed dake kallonshi cikin yanayi na isgilanci sanan yaydan murmushi yace "I will make you a promise yau dinan akuma gabanka, Waleed kome kaci sai Arham yaci! Waleed kome kasaka sai Arham yasaka! Waleed kome kahau sai Arham yahau! Waleed kowani matsayi ka taka sai Arham yataka shima! Sai last thing dazan fada maka is over between us" da sauri Waleed ya kallai, gyadamai kai Arham yayi yace "yes is over tsakanina dakai Dr Waleed Warbai, we should go our separate ways, yanzun haka danake maka magana my resignation letter na gidan marayun ka duk lokacin dakaje za'a baka, ka kama gabanka nakama gabana, daidai da silebiyar dinka karka sake bama Mahaifiyata, Arham bai sanka ba bai san dazaman kaba kaima do me a favour ka kwatanta hakan, is over we are not friends we are not friends, please katashi kafitar min daga daki kabar min gida and yau yakasance rana ta karshe dazaka kara zuwa gidanmu" kasa koda motsi Waleed yayi daga inda yake, hannu Arham yadaga yanuna mai kofar dakinshi yace "out, I said out" yadaka mai tsawa irin na cin mutuncin nan yace "indai kai ba maye bane katashi kafitar min daga daki mara zuciya kawai dolo" sosai Waleed ke kallonshi kafin ahankali yasauka daga kan gadon idanunshi sunyi ja mugun ja yabude kofa ahankali Mama yagani gaban kofan, murmushin dole ya kakalo yace "sai anjima Mama" baima jira amsanta ba yawuce yafita da sauri yya wajen gate yafita yabar gidan ya shiga motarshi yaja dawani irin gudu sanan yabar anguwan.
Bin bayan Waleed Mama tayi da kallo taji gabaki dayan maganan su sabida ita kanta tadamu tun ranan batada Arham a idoba sabida fushin datake yi dashi yasa taki zuwa tadubashi, hakan yasa Waleed na shiga dakin tabiyo bayanshi.
Tura kofan dakin tayi ta shiga, hada ido tayi da Arham da yana ganinta ya saukar da kanshi kasa, ahankali dawata irin murya dake rawa sosai Mama tace "Arham Waleed kama wanan cin mutuncin, Arham anya nina haifeka kuwa? Anya nonon nan nawa kasha"? Takama nonon ta tanunamai, saikuma tafashe da kuka sosai dan her heart is so heavy tace "wlh wlh da'ace a asibiti na haifeka Arham da na rantse maka da Allah dayau dinnan sainace bakaine danda nahaifa ba, anchanza mini kai a asibiti, amman agida na haifeka dagani sai unguwar zoma" tafashe da kuka sosai, sanan ta share idanunta tass da bakin zaninta tace "wlh albasa batai halin ruwa ba, babu ta inda ka gado malam mahaifinka, baban ka malami ne, wayan nan manya manyan malaman da ayau a Abuja dasu akeji duk ubanka ya koyarda su Arham, Arham ubanka malami ne, kakanka malami ne, amman kaiko Arham shaidanin yaro ne" tafadi haka tsabagen yanda zuciyarta ke tafarfasa, cikin ihu da fada da kunan rai tace "Arham wai shinko katuna waye Waleed koko kamanta ne?" tamai tambayan tana kallonshi sanan tace "Arham kanajin tsoron Allah kuwa? Arham kana kokarin ka tabbatar da cewan mutane kadau mutum daga rana ka maidashi inuwa shi saiya maida kai rana, Arham kai butulu ne eh? Yanzu inda ace zaka tashi kaje sip dinan naka zan rantse da Allah nakuma kara idan akwai kayanka daka saya da kudinka basu wuce kala biyu, Arham gabaki dayan sitiranka Waleed kisiya maka, Arham yaron nan nasonka har kuka naji yana maka kanamai ihu kana cewa ba kuka kace yamaka ba, matarshi ta haihu yarada ma danshi sunanka Arham duk baka ganin abubuwan nan? Da ace Waleed bai tsamoka daga talauci dahar yau ayaba kake saidawa, Arham Arham Arham" Mama tama rasa maizata cemai saikuma tafashe da kuka tace "kaga yanda idanun yaron nan suka taru da jini dukan dakamai? Amman bai rikeka ba ya tattako yazo wajenka, bari kaji bazan taba bari ka wulakanta mai sonka ba wlh, bazan taba bari ka wulakanta wanda ya chanza mana nidakai rayuwa ba, Arham bazan taba bari ka wulakanta Waleed ba domin ka wulakanta yaron nan kadauka nika wulakanta aduniyan nan, dan haka dau wayar ka ka kirashi agabana kasa handsfree dan naji, kabashi hakuri sanan kafadimai duk abubuwan daka fadamishi wasa kake kanajina "! Mama ta dakamai tsawa, dago idanunshi Arham yayi ya kalli Mama yace "Mama kiyakuri amman wlh ni bazan kirashi ba, kuma kidena cewa ya taimake mu babu abinda Waleed yamana Allah ne yataimake mu kuma shine yamana komi wlh, daman shi Allah haka yake abinshi inya tashi taimaka maka saiya nemo wani ya taimaka maka ya hanyar shi, tunda ai shi Allah bazai sakko kasa yamika maka kudi da hannunshi ba yace gashi Arham saidai yay amfani dawani, dan haka wlh Mama ni Allah ne yamin komi babu wani mahaluki daya isa yataimaken, Shidin banzan shi, kudin shi na banza meyake dashi, shi idan ma yaga asalin masu kudi guduwa zaiyi yaboye wlh irinsu Otedola, Zuckerberg da sauransu, shidin me shidin banzan shi, dan ubanshi nada kampani a kasan waje yake mana kapapa yana daga mana kafada wlh bazan kirashi ba" yay maganan ranshi duk abace, rungume hannu Mama tai aciki tana kallon Arham kaman tasami TV, ahankali Mama tace "Arham Annabi yace a kullum mudinga kallon nakasa damu bana sama damu ba hakan zaisa mungode ma Allah da kyau, Arham batun yau nake karantan wani abu tattare dakaiba amman yau Allah ya bayyanamjn abin gabaki dayanta Hassada kakema Waleed" da sauri Arham yana daga murya yace "shi awa zan tsaya inamai hassada Mama? Ubanme yakeda shi? Allah ya kyauta kafin na ganshi naga masu kudi dubu ni mama kima dena min maganan wani Waleed banson jinta, dashi da wanan matsiyaciyar uwarnan nas...." bai karasa maganan ba Mama taxuba ma bakinshi mari, sanan tacire slippas din kafarta tahau dukanshi ta ko'ina tace "Arham kaci uwaka, bani na haifeka ba, wanan bakin halin naka da bakar zuciya uwarka da ubanka basu dashi, wayanda suka taimake ka kake zagi eh, kai wani irin butulu ne, Arham ni kake so kabama kunya aduniyan nan" dudda dukanshi take bakinshi kin mutuwa yayi yace "ki kasheni Mama, dama batun yau nasan kinfison Waleed kan danda kika haifa ba, Waleed nada kudi, yasai miki gida da mota, gaki da generator ga solar, ga kayan abinci ga kudin kashe wa ba dole ba, Mama ki kasheni sabida Waleed, badai danni banda kudiba banda gidan marayu ba saisa bakisona nima ba zakiga abinda zai faru Mama kicigaba da dukana har saina daina numfashi, badai kowa dukana yake akan Waleed dan gata ba, ajebota kucigaba nikuma namuku alkawarin sainaima Waleed abinda dukanku bazaku iya taimakon shiba wlh, wlh kuwan, kiyita dukan" yakara mika mata kanshi dantaji dadin duka, dukanshi Mama tayi har saida Sadiya taji ta shigo da gudu taja Mama baya dake haki kaman zata mutu tace "sadiya kibarni na kashe yaron nan nahuta dan ba da'na bane, Sadiya kibarni, Arham nason yacimin mutunci, Sadiya Arham nason ya kunyatani aduniya, dawani idanu yakeson na kalli mutanen nan dasuka mana komi a rayuwa eh" tafashe da kuka, rungumeta sadiya tayi itama tahau kuka tace "Mama yakuri kidena kuka dan Allah" cikin wani irin fushi Arham ya tashi ya finciki key motarshi yafita daga dakin ya barsu awajen idanunshi sunyi jajir.
Waleed rasa inda zashima yaji dadi aranshi yayi kirjinshi sai wani irin mugun tafarfasa yake, baisan ya akayi ba yadaiga yazo gidan marayun shi, parking motarshi yayi yafito sai gaisheshi ake yama kasa amsasu da sauri da sauri yake tafiya har zuwa cikin asibitin shi, direct ward din da Widad ke kwance yake, bude kofar ahankali Ya shiga maida kofar yayi yarufe yana kallonta ganin bacci take, direct yawuce gadon da sauri zama yayi kan plastic chair gaban gadon kawai yakifa kanshi kan gadon kukan dake cinshi tun adakin Arham ya shiga sakinshi awajen ahankali yana shesheka, maganganun Arham gets to him sosai, sun shigeshi was he that bad kaman yanda Arham ya suffanta shi? Was he?.
Kaman amafarki taji kaman ana kuka ahankali wanda sautinshi ke kaiwa har kokon kirjinta, bude idanunta tayi kaman wacce ta firgita ta kalli ko'ina kafin ta kalli gefenta, kan mutum tagani kife kan gadon, gashin kan nawani irin shining sunyi sili sili tsabagen gyara dasuka ji, dudda bataga fuskarshi ba amman tagane mutumin nanne bargon jikinta tayaye da sauri taja jikinta ahankali ta tashi tazauna tana kallonshi tai raurau da ido, ahankali tadaga hannunta ahankali tadaura akanshi, jin soft hannu dake dauke da dan danshi danshin zufa akan sumanshi yasa yadago kanshi ya kalleta da jajayen idanunshi da hawaye yacikasu sosai, wani irin kallonshi take hankalinta yatashi sosai ganin yana kuka ahankali yakai hannunta kan fuskarshi sharemai hawayen tayi da sauri tana girgizamai kai, jiyayi zuciyarsshi tawani irin tsinke baisan lokacin daya tashi daga kan kujeran yazauna abakin gadon ya rungume cikinta tsam ba, fuskarshi nakan cikinta yasaki kuka ahankali cikin harshen turenci yace "Saheeba baki sanni ba, dudda duka yanzu 10month kikayi da sanina, dan zaman dakikayi tareda ni please ki gayamin am I a bad person? I know I makes different decisions, but kowani decision zan dauka abune dazai kawo cigaba dakuma raya wanan gidan marayun, you know ana yawan cewa breakup masoya ne kawai irin couples haka ke breakup ba'asan cewa akwai friendship breakup ba and the shit hurts badly" yasaki kuka sosai akan cikinta dayasa tahau girgiza mai kai tana bubbuga kanshi alamun yay shiru tana kokarin magana takasa but kana ganinta kasan ta mugun damu, ahankali yace "I am so saddd, I don't know who to talk to, banma san mesa nazo wajenki ba bayan bazama kingane menake cewaba, but crying ajikinshi anyway makes me feel better, am sorry natashe ki kinji" yay maganan yana dagowa daga jikinta tareda tashi daga kan gadon yana juyawa da sauri batare dayabari sun hada idoba, hannunshi yaji anrike gam hakan yasa ya tsaya chak, dirkowa tayi dagakan gadon tana rikeda hannunshi ta zagayo tagaban shi ahankali ta tsaya tana kallonshi, gani yayi itama idanunta sunyi ja, ahankali tabude bakinta tana kallonshi takai almost 20sec tana kokarin iya maganan dazatayi sanan cikin yar siriruwan muryanta tace "you aren't a bad person" tai maganan tana kara kai hannunta yakama dayan hannunshi tarike gam, sanan ta kallai tace "you are a goodman" tai murmushi dayasa hawayen idanunta suka zubo, saikuma ta washemai baki tace "and I love you" tasakin mai wani heart melting murmushi dayasa all her dimples suka lotsa, wani irin ajiyan zuciya yasauke yasan bamatasan metake cewaba, sanan this is not the first time ake cemai I love you besides Ilham tasha fadimai kalman nan countless time but yau da Saheeba tafadi saida heart dinshi yakusan skipping out, like he felt the words har cikin diddigan kashin jikinshi sosai yay nisa yana tunani yaji an fizge hannunshi, firgigit ya farka yaga ita ke janshi, zaunar dashi tayi akan gado ga mamakin shi daiyaga tasa hannayenta akan kafadarshi ta turashi ya kwanta tana murmushi, samun kanshi yayi da kwanciya yana wani iri kallon yanda takemai murmushi kaman yau yafara ganinta, stethoscope din dayake dauka kullum dake kan bed drawer dinta inya shigo dubata ta dauka ta makala a kunnenta tsaf tana murmushi sanan tazo bakin gadon tana ware Big lulu eyes dinta ta daura hannu kan lips dinta tana kallonshi alamun yamata shiru sanan takai bakin stethoscope din ta daura kan saman kirjinshi ta saman riga lumshe ido yayi da sauri yana sauke wata nauyayyan ijiyan zuciya jin hannunta kan jikinshi, ita kawai she is doing it jokingly ne but jin beat din kirjinshi acikin kunnuwan ta yasa tawani irin kwalalo ido a tsorace ta fizgo daga kunnenta ya yar, dan dariya yayi yatashi yazauna ahankali itama dariya tayi saikuma ta makemai kafada ta taho dagudu tawani fada jikinshi ta daure hannayenta tabayanshi tana murmushi, wani irin natsuwa ne yaji ya shige shi, lumshe ido yayi tareda manna hancin shi cikin gashinta, murya chan kasan makoshi yace "I love you Saheeba".
[21/10, 21:43] Aishat Muhammad: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_💫