x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 34 - TWO DIFFERENT WORLD

  • 99001 words
  • 102000 words
  • Out of 139348 words

Category: Love Stories

Views 234

09 Jun 2025
Start ads
After Image Ads
yajiraka daga tafiyan dakayiba a'a, amma dai abokin ka ya tsaya amadaddin ka yama mahaifiyarka komi dakaine zakamata, Allah ya jikan ta da rahama" gyadamusu kai yayi idanunshi sunyi jajir ya lankwashe kafa yana kallon gate din gidansu yana ganin kaman zaiga Mama tafito ta kwalamai kira Arham, yakai kusan minti talatin awajen zaune, saida jama'an suka watse bayan sun gama kari sanan yamike tsaye ahankali batare daya kalli Waleed ba yay cikin gidansu, wani irin tafiya yake harya karasa falonsu da babu wasu mata dayawa ya tsaya chak yanabin fuskan kowada kallo, Ammi ne datake kallonshi in disgust, sai Mom, sai Sadiya da takife kanta kan kafafunta har lokacin takasa daina kuka sai Maman Sadiya take wani irin kallonshi irin kallon nan na Yayata tai asaran haihuwanka, Mom ce ta danne zuciyanta tace "yahakuri Arham" ahankali yace "dagodiya" Maman Sadiya ne taso ta daure iya daurewa but takasa, dan gani take shine sanadiyan mutuwan yayarta, cikin wani irin yanayi na kunan rai tace "mekazo yimana agida eh Arham? Meya kawoka? Ba kace bazaka kara zuwaba, tana rashin lafiya tana nemanka kaki zuwa yanzu me amfanin zuwanka bayan ta rasu?" wani irin murmushi tayi tace "Arham duniyan nan nada girma kuma wlh duk wanda uwarshi tamutu tana fushi dashi toya tabe, kaje zakagani" wani irin ja idanunshi sukayi jin jiri jiri nakamashi yasa yazauna atsakar dakin kaman wani almajiri dayazo bara, tabe baki Ammi tayi ta mike tsaye ta kalli Mom tace "tashi mutafi we have wedding" sanan ta kalli Maman Sadiya tace "yar uwa bari mutafi gida, kinsan gobe bikin Waleed, kome kikeso kisa Sadiya takirani a wayar dana bata tasanar dani in sha Allah zan aiko muku dashi" tsugunnawa tayi tashafa kan sadiya dake kuka har lokacin tace "ya isa yarinyar kirki, kidena kuka kinji, kozaki bini" dagokai Sadiya tayi da jajayen idanunta ta kakaloma Ammi murmushi, murmushi itama Ammi tayi tace "inkun gama zaman makoki zanzo sai asan yanda za'ayi bazadai ku kara komawa kauyeba, in kinason karatu zan maidake school Sadiya, inkuma aurene saikiyi auren ki kinji" gyadamata kai Sadiya tayi sanan tace "to sai anjiman ku" cikeda so Maman Sadiya tace "angode Hajiya Allah yasaka da alkhairi, Allah kuma ya sanya albarka abiki" suka wuce suka fita har waje, awaje suka sami Waleed attending to some guest, kiranshi Ammi tayi. "Waleed" ahankali yadago kanshi, wani mugun kallo da Ammi tamai dan tasan halinshi sarai zaice mata bazai tafi gidaba yasa yamusu sallama yataho, motansu ya shiga sukuma suka shiga baya yaja motar Ammi tace "you've done your best wanda ko danta baiyiba, yanzu tunda Allah ya kadoshi yadawo gida, kabarshi da aikinshi go and concentrate aurenka gobe, use today to tell your wife zakai aure kanajina ko, ranan bakwai dukma dawo gabaki daya mu sakeyin gaisuwa" gyadama Ammi kai kawai yayi dan bayason surutu, agida ya ijiyesu sanan yawuce gidanshi.


_sorry guys, I've been at the station jiyan nan all through, i will be fully stable gobe, and normal posting continues_
[01/11, 14:05] M Shakur: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_💫






✍️ M SHAKUR








5️⃣0️⃣






Tundaga gate yakejin kukan Arham parking yayi yashiga cikin gidan, a falo ya tarar da mai rainon yaron da Arham matan tagaji sai jinjigashi take ga zanin gayo a hannunta alamun daga bayama ta sauke shi, maida kofa yayi yarufe yakarasa wajen yamika hannun ya karbai da sauri yace "why is he crying like this ina maman shi?" anatse mai rainon tace "takoma baccin safiya yallabai tace kar atadata harsai ta tashi zata fito ta amsheshi" ji Waleed yayi ranshi ya baci, baicema mai rainon komiba sanan yawuce yay sama dashi, dakin Ilham din yabude ya shiga dakin duhu, hannu yasa ya kunna wutan dakin dakin yay haske hakan yasa tabude idanunta ta waigo hada ido sukayi da Waleed daya dauki Arham dake kuka, cikin muryan bacci tace "Baby maisa ka dauko shi saina tashi zan bashi nono, please ka mayar mata dashi" wani mugun kallo yamata yace "kirashi and breastfeed this boy" jitayi ranta yabaci dan da daddare Arham baya bari tai bacci shan nono yake, ta tsani ana shamata nono, tashi zaune tayi ahankali sanan tamika hannu batashi yayi tana karbanshi cikeda fushi takaimai shegen duka abaki yaron yawani irin kwala mugun ihu dan daduka karfinta ta mari bakinshi tace "shegen fitinannen yaro babu abinda yasani sai nono" tsawa Waleed yadaka mata yace "are you mad Ilham" itama cikin fushi tace "ga yaron dazaka tambaya nan ko he is mad, yaro yahanani sukuni yahanani sakat, nono nono nono wani irin abune haka, kasheni zaiyi wlh nagaji" tai maganan tana ciro nono takai bakinshi amman ina yamaki karba sabida tsabagen zuciya da yanda yake ihu, cikin fushi ta kalli Waleed daya tsaya yana kallonta tace "kaga halin ja'irin yaron ko, kangararre kaman ubanshi, matsiyacin d......." wanketa da lafiyayyen mari Waleed yayi yace "karki kara zaginmin yaro, karki kuma kara kiranshi da kangararre, come Arham" yadauki yaron yajuya yafita daga dakin yaron sai kwala ihu yake yasauka kasa ya sami mai rainon shi yace "anmai wankan safe"? Girgixa kai tayi yace "hadomin ruwan shi" ruwa tawuce tahado Waleed yaciremai kaya tun yana school aka koyamusu yima jariri wanka dan suna amsan haihuwa, Arham na kuka yama yaron wanka tsaff sanan ya shirya shi cikin kayan da takawo mai sanan yadauki madaran dayasa aka damamai yabashi da kyar yasamu yaron yasha, shegen zuciya yanasha sai bacci, bama mai rainon shi shi yayi ta goyashi sanan ya wuce sama dakinshi yabude ya shiga yay wanka sanan yabi lafiyan gado, wuraren 1 yafarka wanka yasakeyi ya shirya yafito Ilham yagani a falo yar aiki na matsa mata kafa ko kallonta baiyi yawuce yafita mosque, yana dawowa yawuce dakinshi ya zauna kan gado yana kallon setin akwatinan ta daya mata guda 12, sanan ya kwalamata kira. "Khadija, Khadija" daga kasa ta amsa da na'am sanan ta taso tayo sama, dakinshi da tunda tadawo yaune take shiga ciki tabude ta shiga tanabin dakin da kallo da hadaddun akwatunan dake jere akasa, karasawa tayi ta zauna kusada shi tana kallon akwatin tace "gani baby, wayan nan akwatunan masu kyau fa" ahankali yace "nakine" washe baki tayi ta kallai tace "nawa"? Gyadamata kai yayi yace "yes nakine, am getting married tommorow kimin addu'a" wani irin kallo tamai gabanta ya yanke yafadi tace "aure zakayi Waleed, ni xakama kishiya"? Hannunshi yamika yadauki laptop dinshi yabude tareda gyara zama ya jingina da bango yana kunnawa yace "am getting married tommorow Khadija, sunan yar uwanki Saheeba" "tufiakwa! Kishiyata can never be yar uwata, wai Waleed are you for real nizaka karawa kishiya eh Waleed? Duka duka auren namu wata nawa eh, nizaka cuta? Ni zaka ciwa amana? Nizaka ha'inta ta hanyar yomin kishiya kumama sai ana gobe aure sanan zaka sanar dani eh Waleed" sosai ihunta ke cikama kunne hakan yasa yanuna mata kofa yace "get out please aiki nakeso nama Mummy a laptop, excuse me" yanuna mata kofa, fashewa da kuka tayi tace "wlh wlh indai hakane bazan zauna dakaiba saidai ka zaba koni ko ita wlh bazan yardaba" ganin har lokacin kofa yake nuna mata babu alamun wasa yasa tawuce tafita tana masifa.
Dakinta ta shiga tadauki waya takira Mummy, Mummy na dauka tafashe da kuka tace "Mummy kinji ni Waleed zai ciwa amana wai kishiya zaimin, Mummy duka duka shekaran mu nawa da aure dazaimin kishiya eh Mummy, saisa wlh akashe duk namiji badan goy......" tareta Mummy tayi ta hanyar "ina zuwa yarinya, yimin shiru" shiru tayi kirjinta na tafarfasa, Mummy tace "kiketa wani bala'i ni banda kishiya ne" cikin wata yar kankanuwar murya tace "kinada shi" Mummy tace "good, inada shi but har yanzu kina gidana, har yanzu nikeda fadan baban ku, kowace kishiya da halina take zama, sanan ba akanki za'a daurataba, inaso ki natsu ki kwantar da hankalinki kinada karamin yaro a hannu ki kulada yaronki sanan kibawa mijinki kula da komi dayakamata, kishiya is just a normal thing, maza ne they're naturally polygamous in nature, so I advice you to calm down kinajina, banson in karaji kina hayaniya ko wani abu kinjini " gyadama Mummy kai tayi wasu hawaye masu dumi na sauko mata tace "uhm" sanan ta katse wayanta, wani irin fashewa tayi da kuka kaman ranta zai fita why is Allah testing her like this, Arham ya dauramata ciki ta haihu yanzu yaci amanan ta bayan ya cinyemata kudade duka, saikuma ga Waleed yanzu kishiya zai mata ubanwa zai aura ma, yaushe ma Waleed yafara kallon mata dahar zai mata kishiya, kuka tasha tai ma'ishi koda aka kawo mata Arham ko kallonshi batayi ba yaron sai tsala ihu yake saidai Waleed yafito ya amsheshi yasa amai madara a kawomai yabashi, har dare Ilham kuka take hakanan ya shareta danshi baison rashin kunya yakuma lura abinda tafiso kenan.
*********



Yau babban rana ce ga Waleed da Widad, gabaki daya dagashi har ita babu wanda ya runtsa, shi kawai Allah Allah yake gari yawaye yaga ya auri Saheeba tadawo mallakinshi, shi karan kanshi yarasa wani irin so yake mata, kawai son yarinyar yake bana wasaba, dayake karfe shadaya ne bikin hakan yasa yay wanka yafito shiru yayi yazauna akan gado yana tunani shikenan yanzu baida aboki he is on his own, da ace yanada aboki da yanzu yama fitomai da kayan dazai saka, girgiza kai kawai yayi yatashi dan bayason yafara tuna Arham kuma yazaro kayan dazai saka daga wardrobe, wasu fararen shadda ne masu mahaukacin kyau, hasken su zai iya kashema ido, shiryawa yayi tsaf kamshi natashi daga jikinshi kaman yay barin turare, takalmi ya sanya yadau wayarshi yarike yana kallon agogon hannunshi sanan yabude kofa yafito yana taku daidai, ahankali yabude dakin Ilham ganinta yayi zaune kan gado baijinma tai wanka ba tai busubusu riganta dukya jike da ruwan nono, wani mugun kallo tamai hakan yasa ahankali yace "yallabiya nazo namiki sallama ne, amin addu'a" wani mugun harara ta sakinmai tace "ubangiji Allah karya kaika lafiya, Allah ya tarwatsa auren" shiru yayi yana kallonta ganin yanda takejin wani masifa kaman zata tashi ta dakai, baison yabiye mata hakan yasa yajuya kawai ya sauka kasa, bude mota yayi ya shiga yaja har anguwan su dayaga an cika dudda fa simple wedding ne amman mutane sun cika gidansu, yana zuwa ya shiga rumfar da aka tanada dan daura aure, wasu manya manyan limamai ne guda biyu daya ya wakilce shi dan Uncle baisamu daman zuwaba daya kuma ya wakilci Widad dan anmusu bayani ba'asan kowa nataba tsintarta akayi ya wikilce ta aka daura aurensu da akan sadaki dubu dari uku, sanan suka bashi marriage certificate dazai shiga yaje suyi signing shida ita.

Godiya yamusu sosai sanan aka shiga Walima ana fitomusu da kayataccen abinci aka shiga yi, cikin gidansu yayi yana mamakin mutanen dasuka cika gidan aranshi yana Ammi, Ammi she will never change, tagama cewa babu wanda zata gayyata but see people, shashin shi yayi sai guda akeyi da aka ganshi, shiga bangaren nashi yayi yazauna afalo sanan yadauki wayarshi yakira number Asma'u, ringing uku ta dauka tace "hello Ya Waleed Ango" murmushi yayi yace "Hello Ma'u kanwar Ango" kyalkyacewa da dariya tayi dan maganan yabata dariya, dan gajeren tsaki yayi yace "Common, bakira nayi dan kiyitamin dariya ba, ki kawomin matata bangarena" da sauri tace "Ya Waleed wlh Ammi tahana tace sai anjima idan ankaita gidan ka" akumbure yace "ke ina wasa dakene, cewa Mom certificate zatai signing nabaki 5min idan baki kawota ba kin shiga uku" ya katse wayan dib.


Widad dake zaune akan kujera makeup artist namata applying wani new makeup na white gown din data saka tace "what is it Moxi"? Hararanta Asma'u tayi cikin harshen turenci tace "dalla mayyar miji, tuntuni kike tambaya na shi, gashinan shima yace nakaiki kiyi signing marriage certificate" wani irin cool smile tasaki she really miss him, tadade bata ganshi ba, fita Asma'u tayi daga dakin tai dakin Ammi dake magana da Mom, tace "Ammi Ya Waleed yace naraka Saheeba bangaren shi tayi signing marriage certificate" tsaki Ammi tayi tace "yaci gidansu bazata ba, ko yaushe ne ai ina zata iya signing certificate din zai wani ishi mutane to bazata zoba" da sauri Mom tace "wai Adda mai matsalan ki da yarona ne eh?" ta kalli Asma'u tace "wuce ki rakata kinji" cikeda jin dadi Asma'u tafita daga dakin tana rawa, Ammi tai murmushi tana kallon Mom tace "yayi kyau ni akewa yan ubanci ko" dariya Mom tayi sosai tace "anyi kema ai kinamin fin haka kikaga su Abdul, ni natafi" tawuce tafita daga dakin murmushi Ammi tayi tabi bayan kanwar nata da kallo ita kadan tasan she is so lucky da Allah yabata Mom amatsayin kanwa, Mom is everthing with triple plus.



Gyarata akayi tsaf aka lullubeta da net tana wani irin mahaukacin kamshi, ita kanta Asma'u tsayawa tayi tana kallon Widad din dan wlh tunda take bata taba ganin mace mai kyawunta ba, ana yawan cewa farare fari ne kawai ya cecesu amman munana ne, but in the case of Saheeba kyakkyawan yarinya ce ta karshe, ita ko kadan batama yarinyar ma kallon bahaushiya ko fulani haka, tanama Saheeba kallon baturiya ne wacce ma badaga Nigeria takeba, dan duksu Ammi sunfi mata kallon yar fulani dan akwai asalin yan fulani dako zo basuji da hausa but ita batamata kallon yan fulani. Ganin ta tsaya tana kallonta yasa Widad kaman zatai kuka tace "let's go" baki takama tace "waike banace miki kidinga jin kunya ba" murmushi tayi daya lobar da dimples dinta batace komiba, Asma'u tabude kofa suka fito yan falo suka fara buda, Mom na tsakar gida but jin ana guda yasa saida tajuyo dantaga meakeyi, subhanallah tsarki ya tabbata ga Allahu subhanahu wata'ala daya hallice wanan hallita, Widad nada kyau batada kiba hakan yasa akai gown din yabi daidai jikinta saiya wani irin fito da dirinta da shape dinta, anmata applying simply makeup dan yarinya ce dat is already beautiful she don't need heavy makeup, sanan akabi pink dan karamin lips dinta, dawani sexy pinkish lipstick dayasa tai kaman wata hurun ini, tasaka hill ba chancjan ba dan tanada tsayi sai abin yabada wani classic look, ajiyan Zuciya Mom ta sauke tana kallonsu yanda Widad ke tafiya daidai dakuma yanda tai kyau yasa ahankali tace "Waleed Allah yasa baka auri abinda yafi karfin muba, anytime I look at this girl I feel kaman yar wanice dan is written all over her, Allah yabaku zaman lafiya Allah yakade fitina" fitowa waje sukayi Mom ta zaro kudi tana murmushi ta watsa musu akahau ihu sanan sukai flat din Ya Waleed da ita.
[01/11, 14:05] M Shakur: 💫 _TWO DIFFERENT WORLD_ 💫





✍️ M SHAKUR





5️⃣1️⃣






Waleed dake zaune kan kujera jin yanda ake guda ana ihu sabida ganin Amarya da akayi yasa yakasa daurewa yatashi ta window shi yaleko ahankali yana kallonsu, wani irin ijiyan zuciya yasauke daya hango Widad, kasa daukanshi kafafun shi sukayi hakan yasa yakoma da sauri yazauna jikinshi ko ina bari yake har wani dan sanyi sanyi yaji, daman haka akeji idan ka auri wanda kakeso, he is feeling anxious and eager gawani irin snayi danaji yanaji kaman ana cikin pik of hammatan, jin har yanzu basu isoba wanda yaci ace sun iso bangaren shi yasa yakara tashi da sauri yay window yaye labulen yayi kadan ya kalli tsakar gidan saikuma bai gansu ba daidai anbude kofar falonshi, da sauri yasaki labulen yajuyo suka hada ido da Asma'u datake kallon inda yake tace "laaaaa Ya Waleed lekomu kakeyi" wani irin mugun kallo yamata hakan yasa ta taushe bakinta dan mugun dariya ke cinta, dauke kai Waleed yayi shi adole ba kallonsu yakeba yadan sosa kanshi sanan yakoma kan dogon kujeran dayake kai ya zauna yadagokai ya kalli Asma'u dahar lokacin dariya take gimtsewa yace "excuse us madam tunda kin kawota" kafada ta makemai tajadiye dariyan tace "ai Ammi tace na tsaya na jira tai signing nakomar da ita" at this point kasa daurewa yayi yacire takalmin kafarshi guda yamike yayi kanta dawani irin gudu ta kwasa tana "wayyo Ammi Ya Waleed zai dokan" ita kanta Widad saida tai dariya dudda batajin mesuke cewa dan hausa sukeyi sanan ya tsaya chak daidai wajen kofan inda Widad take atsaye, ahankali yajawo kofan ya kulle tareda saka jamlock sanan yatsaya shi yana kallon kofa ita kuma tana facing cikin dakin tana murmushi, murya chan kasa batare daya kalleta ba yace "what can I say? What can I do? I never knew that one behaves like this anytime he is getting married to love of his life, Saheeba kinsan yanda nakeji kuwa? I feel kaman nafita this compound inta ihu ina jumping telling everyone that this girl is now mine, she is my wife, and...." yay dan shiru kafin yajuyo ahankali ya tsaya adaidai bayanta yabude hannunshi murya chan kasa yakira sunanta kaman mai whispering yace "Saheeba turn around" ahankali tajuyo tai facing nashi tasakin mai wani irin alluring smile, hannunshi yamika ahankali yakai kan net din da aka lullube mata fuska dashi sosai hannayenshi suka shiga rawa innailaihi the whole thing is so new to him baitaba sanin haka akeji ba in ka auri wacce kakeso jikinshi wani irin rawa da bari yake, ganin yanda hannayenshi ke rawa sosai yasa awani irin hankali ta daura soft hannayenta dasuka sha hadadden first class lalle akan nashi takama hannun tarike gam tana kallon fuskarshi tacikin net din suka rike net din tare, cikin wata irin murya tace "this signifies that together we can overcome anything that come our way not alone Ya Waleed" yanda tai maganan tafurta kalaman har cikin ranshi saisa yaji this is the first time take kiranshi kuma yasan sabida taji
End Ads