x

Login

Remember me
Forget password ?
x

sign up

Chapter 6 - RANAR BIYAN BUƘATA Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba

  • 15001 words
  • 18000 words
  • Out of 59040 words

Category: Love Stories

Views 278

20 Jul 2025
Start ads
After Image Ads
kawai ta yi. Matar uba ta cuci Irshad gashin nan dai Mutum har Mutum. Sadaukin Namiji ɗan kwalisa ga kyau da dukiya ya tara duk wani quality da mace ke buƙata wurin da namiji, sai abu guda da ya rasa shi ne magana, duk da dama can haka yanayin halittar sa take ba Mutum ne shi mai yawan surutu ba, sai kuma ya haɗu da wannan iftila'i daga Allah Sanadin azabtar War matar ubansa a gare sa, ya dena maganar da a ke fahimta sai dai tazo a rarrabe ƙarfi da yaji ta mayar da shi mai in'ina bisa son zuciya irin nata... Mahaifiyarsa Balarabiyar Ethiopia ce nufin Allah shi ne ya haɗa ta da Alhaji Haashir har ya kai su ga aure, sai dai auren bai je ko'ina ba suka rabu, ba komai ne sanadi ba sai tun lokacin da ta sama ciki ta nuna bataso shi kuma Alhaji Haashir ya ce yana son abin sa, an yi tashin hankali da ita sosai a wancan lokacin sai da kyar a ka samu ta haƙura bata fitar da cikin ba ai kuwa tana haihuwa a asibitin ta bar masa jaririnsa wai kafin yaje gida faɗawa dangi sai dawowa ya yi ya tarar da jariri ita kuma Aabirah ta yi tafiyarta, ransa ya ɓaci sosai da hakan shi ne ya zama sanadin rabuwarsu, har yau dake motsi. Haka Badan yanaso ba ya mayar da jaririn hannun Mahaifiyarsa kafin daga bisani ya ƙara Aure zuwa lokacin yaron da ya ci suna Irshad ya kai shekara ɗaya da rabi a duniya, shi ne ya ɗauke sa daga hannun Mahaifiyarsa ya mayar da shi Wurin matarsa Abida. Da zuciya ɗaya ya yi hakan kuma ta tabbatar masa zata kula masa da ɗan sa tamkar nata kuma ya yarda da ita har ya kai ga bata yaronsa. Ai kuwa nan ta tasa yaro ƙaramin sa da shi da azaba nau'i nau'i ba tare da wani dalili ba haka yaron ya taso cikin karɓar azaba daga hannunta kuma Alhaji Haashir bai taɓa lura da hakan ba sakamakon kasancewar sa mutum ne ɗan kasuwa ko lokacin kansa baya samu bare kuma na Iyalansa....
Bai ankara da azabtar da yaron da take ba sai Ranar da dubunta ya cika ta saka ma Irshad yaron da ba zai wuce shekaru goma a duniya ba a wancan lokacin garwashin wuta a baki wai dan kawai ta kira Sunansa yaƙi ya amsa. Sanadin hakan yaron ya zama kamar kurma babu um bare um'um. Ran Alhaji Haashir idan ya yi dubu to ya ɓaci da abin da ta yi ai kuwa a wurin ya rattaɓa ma ta saki har biyu lokaci guda. Irshad ya daɗe yana jinya a Babban Asibiti dake Malaysia da taimakon Allah tare da jajircewar likitoci maganar sa ta ɗan dawo sai dai ba ta fitowa daga bayama ya koma in'ina.... A can ƙasar Malaysia Alhaji Haashir ya bar sa ya ci gaba da karatu bai dawo da shi Nigeria ba har sai bayan da ya ƙara Aure ya Aura Safiyya da suke kira da Aunty Amarya zuwa lokacin kuma matsawar da Danginsa da ita kanta Abida ke masa ya sa ya dawo da ita bawai dan ransa yaso ba... Kuma haka Rayuwar Irshad ta ci gaba da gudana a Malaysia iyakar sa da su sai dai yazo musu hutu, a hakan ne har ‘yar shaƙuwa ta shiga tsakanin sa da matar baban nasa, burin Irshad tun yana yaro bai wuce zama wani a ɓangaren ɗaukar hoto ba, sai dai shi kuma Mahaifinsa kasuwanci yakeson ya karanta, hakan ya haƙura ya yi biyayya ya karanci kasuwanci sai dai gefe guda yana ɗaukar course ta ɓangaren karatu a kan ɗaukar hoton. Bayan wasu shekaru ne kuma bayan ya kammala karatun sa ya dawo Nigeria ba tare da ya fara aiki ba Alhaji Haashir Mahaifinsa ya yi masa wata Babbar bazata ta hanyar basa damar zuwa wani tafiya na ƙaro ilmi ta ɓangaren ɗaukar hoto a sri Lanka na ƙasar Indiya, ya yi farin ciki sosai da hakan kuma ba tare da ɓata lokaci ba ya shirya kuma ya tafi tsawon watanni Biyar, a can ne kuma wani babi na daga ƙaddararsa amma ya fannin Soyayya ya faru Tsakanin sa da Ariana kyakyawar budurwa mai ɗaukar hankalin duk wani lafiyayyen namiji da ya san kansa.....

*WANNAN KE NAN...*


____
_Jan Hankali_

*_Dan Allah Iyayen mu mata a dinga haƙuri da Rayuwa musamman a kan riƙon ‘ya‘yan Miji, wani abun sai an daure amma duk da hakan a dinga haƙuri ana kawar da kai bawai dan mijin ki ya baki yaronsa da K'addda ta fitar da Mahaifiyarsa daga Gidan ba, ke kuma shikenan kin sama hanyar Azabtar da wannan yaron ba kuma tare da ya yi Miki komai ba. Ko kuma wai dan ke kina da wani kwakwkwaran hujja ko dalili ba. A daure a riƙe yaran da basa tare da Mahaifiyarsu tsakani da Allah domin ba'a san yadda Rayuwa zata kasance ba a gaba._*

*Mu tara a next page domin jin yadda zata kaya.*


*_Don't Forget to Like, Comment, and share Fisabilillah, domin waɗan nan sune supporting nawa da zakuyi ku ƙaramin gwarin gwiwa Nkd's ce taku a har kullum ✍️✊🪄_*
_______
________
_______
___
*Masu Buƙatar a haɗa musu Book Cover ko banner, poster, birthday flyer, flyer, logo e.t.c dai duka Muna yi cikin farashi mai rahusa ku tuntuɓe wannan lambar (0708 521 2808.)*

𝑃𝑒𝑟𝑓𝑒𝑐𝑡𝑙𝑦 𝑝𝑒𝑛'𝑠..... ✍💫


*💫..RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

*©Nainarh KD Nkd's... ✍️*


*Arewabooks: @Khadeejarth Sabi'u Yahyah.*


_Dedicated To Oum Yasmeen.❤️_

https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20


*Ep_15-16*


*-100, Obafemi Awolowo Way, Jabi, Abuja, Nigeria.*


*ANNABELLA POV.*


Ta yi tsaye bakin ƙofar hannunta riƙe da handle na ƙofar, tunani take a kan ta shiga ne ko kuwa dai ta koma?.

A lissafin ta yau sati guda ke nan da Jaish mijinta yake kulle a ɗaki tun Ranar da ya sama labarin mutuwar Uncle ɗin sa commissioner ya rufe kansa a ɗaki babu irin bugu da naci da batayi masa ba a kan ya buɗe amma yaƙi. Alhininta bai wuce kar ya cutar da kansa ba kuma tana da tabbacin tsawon sati gudan bai saka komai ba a bakin sa.

Wannan shi ne abin da yafi ɗa ga ma ta hankali, duk da cewa tsawon watanni uku ke nan da Auren su amma babu wani shaƙuwa tsakaninsu, kuma ba komai ne dalilin hakan ba sai irin Auren da suka yi, Aure ne na sirri da Mahaifinta da kuma Uncle nasa da a ka kashe suka shirya, biyayya kawai ta yi wa mahaifin ta wato Mr Aabdar Dawlah sai dai tana mamakin dalilin sa na haɗa Aure tsakanin ta da wanda ba addininsu ɗaya ba, ita Christian yayin da shi kuma yake musulmi. Ta kuma sauke ajiyar zuciya a karo na Barka tai tana da tarin tambayoyi da takeso ta yi masa.
Shi ba, da yake matsayin miji a gare ta sai dai bata kai ga yi masa ba domin bata sama fuska ba, gashi kisan da a ka yi ma Uncle nasa ya biyo baya, da shi ne ya dagula komai.
Wannan karon nannauyar ajiyar zuciya ta kuma sauke wa ba tare da ko ɗar ba ta kai hannu da niyyar buga ƙofar sai taga ta buɗe ke nan a buɗe take, to yaushe ya buɗe bata sa ni ba?.


Sannu a hankali take taka wa ta shiga katafaren palon tana ƙarewa ko'ina kallo domin wannan shi ne karon ta na farko da ta hauro sama part ɗin sa. Har ta shigo. Ƙari sawa ƙofar Bedroom ɗin ta yi tare da kai hannu ta murɗa shima a buɗe yake, sa kai ta yi ciki ta shiga.

Sai dai me turus taja ta tsaya lokacin da idanunta suka yi ma ta Kyakyawan gani.


Fitowarsa daga Bathroom ke nan ƙugunsa ɗaure da towel yayin da yake goge sumar kansa da take da tsayi da wani ƙaramin towel dake hannunsa, dogo ne fari tas ƙaƙƙarfa wanda duk inda wani gwarzon saudarkin Namiji yake to Jaish ya kai ko ma a ce ta kera sa.


“Oh Gosh. Am so sorry Sir...”


Ta faɗa da sauri tana juyawa domin barin Bedroom ɗin. Ƙirjinta na wani irin bugu na tashin hankali domin zata iya cewa kaf Rayuwarta wannan shi ne karo na farko da ta ga wani ɗa Namiji a haka, Bama wannan ba babu abin da ya fi bata tsoro sai irin ƙirarsa da ta gani muraran.




Tsaye ya yi yana bin ta da kallon nazari, kamar dai ko yaushe kyakyawar fuskarsa a tamke tamau sai da yaga ta kusa ƙofa sannan ya saita Muryarsa
tare da kiran Sunanta da wata kalar da murya da ita Annabella ta kasa tantance ta.

“Annabella...!”


Dakatawa ta yi ta ɗan saita nutsuwarta tare da Juyowa tana fuskantar sa ba kuma tare da ta amsa ba sai zuba masa lumtsatsun idanunta da ta yi. Ya kawar da kai tare da ƙari sawa gaban wani makeken lafiyayyen Dressing Mirror ya ja stool tare da zama. Tsawon sakanni ba tare da ya ce ma ta komai ba. Ita ma tana tsayen ba ta ce komain ba.


“Haka ne ko sunan naki?.”


Ta ɗan kallesa jin tambayar da ya yi ma ta da tafi kama da ta rainin wayo. Sai dai ta danne tare da faɗin.

“E.”
A taƙaice.


“Mene ne ya kawo ki nan?.”


Sai da a ka kuma ɗaukar tsawon sakanni ashirin kafin ya jefo ma ta wannan tambayar.

“Am'um just dama kawai na zo ne domin dubaka and Ina so na faɗa maka ina son zuwa Gidan mu in anjima.”


Yanzun ma still sai da a ka kuma kwashe kusan minti ɗaya da ‘yan sakanni da alama tattaro kalaman da zai faɗa yake sannan ya ce.

“Kada ki sake. I mean karki sake shigowa nan ko kuma tunkarar wurin da nake and already na faɗa Miki koma ina ne kike da buƙata zaki iya zuwa ba sai kin tambaye ni ba coz i don't care...”


Wannan karon Annabella ta kawo ita wuya, zuciyarta tafarfasa take. Kamar ko yaushe tunani take a kan mene ne dalilin mahaifin ta na ha ɗa ta Aure da wannan mutumin, ba ta ce masa komai ba domin batajin zata iya wata magana a halin da take ciki yanzu. Da gaggawa ta kai hannu kan handle na ƙofar domin fita, sai dai cak ta dakata da buɗewar da take ƙoƙarin yi sakamakon maganar da taji ya kuma.


Duk da bai so ƙara magana ba, amma hakan ya daure ya ce. “Kar ki ƙara saka kalan waɗan nan kayan dake jikin ki, na tsani jar kala da jan kaya, har wannan kwalliyar mai kama da ta aljanu bana buƙatar ki sake yi muddun kinsan zamu haɗu idan kuma ba haka ba....!”


Ya ɗan cije bakinsa ba tare da ya ƙari sa ba, yana ɗan Girgiza kai tare da lumshe ido kaɗan. Ya jingine bayan sa jikin stool ɗin da yake zaune.



Annabella da maganganun sa suka shigeta kwarai tare da bata mamaki kuma kanta ya ɗaure matuƙa, ta kai duba i zuwa kayan dake jikinta it her favorite color, ja ba shi ne best color nata. Sanye take cikin wata ɗamammiyar English Gown Red color, ƙafafun ta da wasu High hills takalma masu tsini, fuskarta kuwa tasha ɗanɗa sheshan make-up da wani red jan baki da ta sha, dama gata fara ta yi kyau sosai ta fito kamar wacca zata fita Gasar SARAUNIYAR KYAU ta Duniya. 👑😍

Dama hakan take Annabella mace ce mai son gayu da tsafta sosai ga iya kwalliya.

Buɗe ƙofar ta yi tare da fita ba tare da iya ce masa komai ba tsaban takaici.


Dafe kansa da ya fara sara masa ya yi yayin da mummunar tunaninsa yake basa dama na aikata abin da ƙwaƙwalwarsa take hasaso masa yayin da zuciyarsa take kuma tursasa masa hakan. Da ƙarfin gaske yakai hannun sa duka biyun tare da dafe kan nasa yana sakin wata ƙara yayin da yake ƙoƙarin ganin muryar da take masa amsa kuwa a koda yaushe cikin kunnen sa bata sama Nasara a kan sa ba, sai dai hakan ya cutura babu abin da ke amsa kowa a kunnen sa fa ce wannan zazzaƙar muryar nata da ba zai taɓa mantawa da ita ba duk da idanunsa a rumtse suke amma hasaso masa wannan kyakyawar fuskar nata yake tana tsaye gaban sa ta ɗan durƙusa kaɗan, kamar ko yaushe sanye cikin jar Doguwar riga fuskarta wadace da make-up hannunta riƙe da kaifaffiyar wuƙar da take yawo da ita saman wuyansa, jajayen laɓɓanta suna furta... “Burina ka kirani da Mommy hakan kaɗai ya wadatar kuma zan kyale kayi Rayuwar ka kamar sauran ‘ya‘ya... If not kuma...” Ta yi Shiru ba tare da ta ƙari sa ba tana cizon laɓɓanta tare da ɗan luma wuƙar a wuyansa har sai da jini ya ɗan ɓullo daidai lokacin shi kuma ya saki ƙarar azaba tare da faɗi ƙasa sunamme.....


A gigice ya watsar da kayan dake saman Dressing Mirror ɗin yana kuma sakin wata gigitacciyar ƙara tare da zubewa a ƙasa yana fitar da wani gigitaccen numfashi.... *_Ya tsani jar kala, ya tsana ganin mace da make-up, ya tsani ganin kyakyawar mace Finally ya tsani kyawawan mata fiye da komai a Rayuwarsa_*🥺😳




___
*_DSS Headquarter Maitama Evenue Abuja._*


*UMNIA POV.*

A fusace D.G Bilal Yusuf Bilal ya watsar da files ɗin dake hannunsa a saman desk dake gabansa tare da Miƙewa tsaye ya daki desk ɗin da ƙarfi, yana watsa gigitattun idanunsa a kan ta yake faɗi cikin wata kalar kakkaurar murya a tsawace.


“Mene ne wannan Officer bafa wasa kikazo yi nan ba, ace wannan ƙaramin binciken ya gagare ki gamawa kinsan irin matuƙar takuramin da a ke ne ta sama wai ma mene ne kika bincike tsawon kwanaki goman nan?.”


Ya ƙari sa a zafafe yana kallon ta.


Ƙara cije laɓɓanta ta yi tana ƙoƙarin controlling kanta tare da saita nutsuwarta ta buɗe Murya da kyar kai da ji kasan ta kawo iya wuya ta ce.


“Mun yi bincike a kan gashin da a ka samu kuma mun tabbatar da gashin na mace ce kuma mun gano ko wacece sannan mun isa gareta, sunanta Clara aikin ta ne kai saƙo daga restaurant da take aiki zuwa Wurin da a ke buƙata a wancan Ranar ma ta kai ma commissioner pizza ne da kuma shawarma kamar yadda ya buƙata, a yadda muka bincika shi ne a wancan Ranar ƙoƙarin raping nata ya yi ita kuma ta yi yadda ta yi iya ƙarfin ta ta buga masa kwalba a kai sannan ta gudu iya abin da muka Gano ke nan bayan mun bincike ta.”


Ta ɗan yi Shiru tana sauke ajiyar zuciya tare da ci gaba da cewa.


“Sorry Sir ina mai tabbatar maka da cewa koma wanene makashin yana dab da shiga hannun mu am very sure?.”


Ya ƙura ma ta idanu kamar mai son tabbatar da kalaman ta, ita ma ta zuba masa nata kaifaffun idanun Zuciyarta a jagule da ɓacin rai lissafa yadda zata wanke fuskarsa da tafi na shouting da ya yi ma ta take. Ta ɗan Girgiza kai tare da cije laɓɓanta tana damƙe Hannunta na dama ta kawar da kai.....


________
_Zakuga Page ɗin is very short. E ku kukaja coz of bakwa comment bakwa like ko reacted balle uwa uba share a gaskiya banajin daɗin hakan sam, ku daure kuna Comment in sha Allah Ni kuma nayi alƙawarin zaku dinga samun Long page wata Rana ma two page's a rana._

*_If not kuma a gaskiya indai banga canji daga gare ku ba next page will be delayed ❌🪄_*

______
*_Don't Forget to Like, Comment, and share Fisabilillah, domin waɗan nan sune supporting nawa da zakuyi ku ƙaramin gwarin gwiwa Nkd's ce taku a har kullum ✍️✊🪄_*
_______
________
_______
___
*Masu Buƙatar a haɗa musu Book Cover ko banner, poster, birthday flyer, flyer, logo e.t.c dai duka Muna yi cikin farashi mai rahusa ku tuntuɓe wannan lambar (0708 521 2808.)*




*💫..RANAR BIYAN BUƘATA...💫*
_(Rai Ba'a Bakin Komai Yake Ba!)_

*©Nainarh KD Nkd's... ✍️*


*Arewabooks: @Khadeejarth Sabi'u Yahyah.*


_Dedicated To Oum Yasmeen.❤️_

𝑃𝑒𝑟𝑓𝑒𝑐𝑡𝑙𝑦 𝑝𝑒𝑛'𝑠..... ✍💫

*Ep_17-20*


https://whatsapp.com/channel/0029VaEZtE15a2429vfcpf20




*-25, Aminu Kano Crescent, Wuse, Abuja, Nigeria.*


Ɗaki ne madaidaici wanda ya fi kama da ɗakin taro ko bincike na kwararrun jami'ai duba da yadda gefe guda na bangon ya kasance ɗauke da Black detective board an yi Linking pictures na mutane da red thread, wuri guda jikin board ɗin ɗauke da wasu rubuce rubuce wasu kuma alamar tambaya ne haɗe da sunaye a jikin wasu pictures ɗin, pictures na mabanbantan mutane da wurare ne a jikin detective board ɗin.



Su biyar ne a ɗakin huɗu suna zazzaune saman wasu kujeru yayin da ɗaya take tsaye tana magana.


Lulu ta saita Muryarta dake ɗauke da ɗan ɓacin rai sannan ta ce.


“A halin yanzu muna da buƙatar sake wani plan about our mission saboda gaba ɗaya plan ɗin mu ya rushe sakamakon mutuwar commissioner da bamu san wanene ya aikata ba da kuma dalilan sa sai dai yanzu ba wannan ne a gaban mu ba, i think we should go to our next target and handle it.”


Ta faɗa tana jinjina kai tare da zura Hannu a aljihun baƙin Wandon jeans dake jikinta tare da mayar da dubanta zuwa gare su.


“Yanzu ta ina ya kamata mu fara ke nan sannan ina ga bai kamata muce zamu bar case ɗin mutuwar commissioner ya tafi a haka ba ya kamata mu binciki lamarin ko nace makashin....”


“Yeah, go on, i am listening to you.”


Cewar Lulu tana kallon Maiji ta yi maganar.


“E shikenan ai ina nufin Mu fahimta cewa ko wanene ya kashe commissioner ya yi ne domin abubuwa biyu zuwa uku, na farko ko
End Ads